𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam mene ne hukuncin Mijin da yake zaluntar Matarsa ?? Ko kuma Mutumin da yake cutar da 'Ya'yansa yake danne musu hakkokinsu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To da farko dai ita shari'ar addinin Musulunci
bata bar komai ba. Kamar yadda aka wajabta ma Mata yin biyayya ga mazajensu,
hakanan su ma Mazan an wajabta musu Yin adalci da kuma kyautatawa dukkan
iyalansu. 'Ya'yanmu da Matanmu duk amana ne ahannunmu. Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam yana cewa: "DUKKANKU MASU KIWO NE. KUMA ZA'A TAMBAYI
KOWANNENKU DANGANE DA KIWON DA AKA BASHI".
Saboda haka duk mutumin da yake zaluntar iyalansa
ta hanyar tauye musu wani hakkinsu wanda ya wajaba akansa, Kamar ciyarwa,
shayarwa, tufatarwa, ilimantarwa, da kuma biya musu bukatunsu na juna, da
sauran hakkoki, ko kuma yake fifita wasu akan wasu, ko wata akan wata, hakika
yana cikin babban laifi.
Ya kamata ya tuba izuwa ga Allah. In dai mutum
yana fatan samun tsira awajen Ubangijinsa, to ya kamata ya gyara. Domin shi
zalunci haramun ne. Allah ya haramta.
A Ɓangaren iyaye kuma, ya kamata su taimaka wa 'Ya'yansu ta hanyar tallafarsu
da kyawawan dabi'u wadanda zasu sanya 'ya'yan su rika ganin girmansu. Bai
kamata Uba ya rika zubar da girmansa agun 'ya'yansa ba. Amma idan ya zamanto
Uban bashi da komai kuma su 'ya'yan suna da dukiya, kuma sunki su taimaka masa,
to ya halatta ya debi gwargwadon abinda zai ci daga cikin dukiyarsu ba tare da ɓarna ba. Saboda hadisin nan wanda Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam yake cewa: "DAKAI DA DUKIYARKA DUK NA MAHAIFINKA NE".
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.