BUDURWATA TANA YAWAN YI MIN ƘARYA, INA NEMAN SHAWARA:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslam alaikum. Malam Allah ya saka bisa irin taimakon da kukeyi mana akoda yaushe. Allah ya jikan mahaifa. Ameen. Malam neman shawara nake nema gareka. Malam wacce nake sonta da Aure na ke yawan samunta da yimin karya. Kuma malam inayin iyaka bakin kokarina wajen janyo hankalinta akan illan karya da makamancin hakan. Domin irin posting ɗin da kakeyi akan hakan ina yawan nuna mata illar hakan, amma har yanzu Allah baisa ta daina ba. Malam ni kuma ina kaunarta, domin ina shirin tura iyaye na gidansu nema.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikas salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hakika Ƙarya tana daga cikin Manyan zunubai (Alkaba'ir) kuma ita ce tushen mafiya
yawan miyagun laifuka. Domin hakika malaman tarbiyyah suna ganin cewar mutukar
mutum ya siffantu da Ƙarya, to zai iya aikata kowanne irin laifi ma.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce :
"KU GUJI YIN ƘARYA DOMIN ITA TANA KAIWA ZUWA GA FAJIRCI (BUSHEWAR ZUCIYA) SHI KUMA
FAJIRCI YANA KAIWA ZUWA GA WUTA. KUMA MUTUM BAZAI GUSHE YANA YIN ƘARYA KUMA YANA SON YIN ƘARYA BA, FACHE SAI AN
RUBUTASHI AGUN ALLAH CEWA LALLAI SHI MAKARYACI NE".
shawara da zan baka ita ce : ka cigaba da yi mata
wa'azi ako yaushe tare da bata shawara akan Ƙawayen da take yawo dasu. Watakila ko tana ganin
irin wannan halayen daga garesu ne. Kayi kokari ka rabata da wannan mugun halin
amatsayinta na wacce nan gaba kake sa ran za ta zamanto uwar 'ya'yanka, kuma
malamar farko garesu wacce ita za ta basu tarbiyyah.
Wajen zabar matar aure, Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya bamu shawara muhimmiya ya ce : "LALLAI KU AURI
MA'ABOCIYAR ADDINI". Malamai suka ce Ma'anar Ma'abociyar addini ana nufin
mace mai tarbiyyar, mai kyawun halaye kamar hakuri, kunya, gaskiya, rikon
amana, girmama manya, etc.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.