Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Aure Da Take Soyayya Da Tsohon Saurayinta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Dama Ina da tambayane shin mene ne hukuncin wadda take da aure Kuma take cewa tana son wani daban awaje misali ace shi ɗin tsohon saurayintane Kuma Allah baiyi auren nasu yayuwuba har takaima ayanzu tana da mijin amma Kuma har yanzu bata daina Kiran wance tsohon saurayinnata da masoyiba, mene hukuncinta shin auran  zai'tabuwa adalilin Hakan? Allah ya Karawa malam sani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Hukuncinta shine mai cin amanace. Domin kuwa anan taci amanar mijinnata saboda kula tsohon saurayinta da takeyi a can waje batareda sanin mijinba. Wannan duk yana ɗaya daga cikin planning da shaiɗan yake don ya raba aure tsakanin mata da miji. Kuma hakan ya nuna ita ɗin ba mumina bace ba, don haka bazata yi nasara a rayuwarta ba indai har bata tuba ta daina ba, meyasa akace ba mumina bace ba ? Mu duba me Allah ya ce a cikin Suratul Mu'uminun ayata 8:

وَالَّذِينَ هُمْ لِأَمَانَاتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُونَ

(Kuma waɗanda suke, sũ ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarwa ne).

Rashin tsare alƙawari da kuma rashin riƙon amanar auratayya shine zaisa a kirata da mai cin amana kuma hakan yana nufin bazatayi nasara ba idan bata tuba ba, domin kuwa Allah SWT ya zayyano wasu daga cikin masu nasara a rayuwar duniya da ta lahira a cikin ayar farkon Suratul Muminun:

قَدْ أَفْلَحَ الْمُؤْمِنُونَ

(Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ)

Wanda su waɗannan muminan sune masu gadon Aljannatil Firdous kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin ayata 10 zuwa ta 11 a Suratul Muminun:

أُولَٰئِكَ هُمُ الْوَارِثُونَ ۝ الَّذِينَ يَرِثُونَ الْفِرْدَوْسَ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ

(Waɗannan, sũ ne magãda. Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne)

Sannan kuma akwai hadisai sahihai da suka tabbata daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam akan illar cin amana, ɗaya daga hadisan shine hadisin da Bukhari ya kawoshi a cikin littafinsa Al-Adabul Mufrad littafi na 8, volume na 73, mai lambata 117 wanda aka rawaito daga Abu Hurairah RA wanda ya ce Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce alamomin munafuki guda 3 ne, na 1 idan yayi zance sai yayi ƙarya, na 2 idan aka amince masa sai yayi ha'inci na 3 idan yayi alƙawari sai ya saɓa.

Anyiwa Shaikh Umar Sani Fagge tambaya akan cin amana, ya ce: A ranar lahira za'a kawo amana a ɗora akan siradi, duk wanda yaci wannan amanar to sai ta dinga zabtare naman jikinsa gwargwadon yawan amanar nan da yaci anan duniyar.

To kinga anan mijin ya amince mata da manufar idan ya aureta bazata kula wasu a waje ba ballantana kuma tsohon saurayinta, anan ta zamo munafuka saboda cin amanar da tayi. Don haka Idan har tana son nasara a rayuwar nan da ta can sai ta tuba ta koma ga Allah domin samun rabo fiddunya wal akhira

Muna roƙon Allah yasa ta gane tayi taubatun nasuha.

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato, Usmannoor_Assalafy_

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ƘARIN BAYANI

HUKUNCIN MATAR AUREN DA TAKE SOYAYYA KO KULLA DANGANTAKKA DA WANI NAMIJIN DABAN

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, ina cikin damuwa kwarai. Na yi aure yau shekara guda, amma har yanzu zuciyata tana tare da tsohon saurayina. Ba na jin son mijina sosai, kuma idan na shiga damuwa, sai na kira tsohon saurayin nan na ji muryarsa nake jin sanyi a raina. Na san abin da nake yi ba daidai ba ne, na yi kokarin goge lambarsa amma na kasa mantawa da shi. Malam, wace shawara za ka ba ni domin na ceci aurena kuma na ji tsoron Allah?

𝐀𝐌𝐒𝐀

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Dafarko, ya kamata ki sani cewa wannan halin da kike ciki yana daya daga cikin manyan makidun Shaidan (Al-Waswasah) domin ruguza miki dakin aurenki da kuma jefa ki cikin fushin Allah. Shaidan yana kawata wa mutum abin da yake Haram, ya kuma sanya masa kyamar abin da yake Halal.

Ga bayanin matsayar shari'a da kuma shawarwari na zahiri:

1. Wannan Soyayya Cin Amana Ce

A Musulunci, matar aure tana karkashin amana da kariya ta mijinta. Duk wata soyayya, sha'awa, ko kulawa ta bangaren zuciya da gangar jiki, hakin mijinki ne kadai. Kulla alaka da wani namijin daban, koda ta waya ce ko ta tattaunawa, ana kiranta da "Zinar Zuciya" ko "Zinar Harshe".

Manzon Allah (SAW) ya ce: الْعَيْنَانِ زِنَاهُمَا النَّظَرُ، وَالأُذُنَانِ زِنَاهُمَا الاسْتِمَاعُ، وَاللِّسَانُ زِنَاهُ الْكَلاَمُ... وَالْقَلْبُ يَهْوَى وَيَتَمَنَّى، وَيُصَدِّقُ ذَلِكَ الْفَرْجُ أَوْ يُكَذِّبُهُ

"Idanuwa zinarsu ita ce kallo, kunnuwa zinarsu ita ce sauraro, harshe zinarsa ita ce magana... zuciya kuma tana yin kwaɗayi da buri, sannan al'aura ta gaskata hakan ko ta ƙarya shi." (Sahih Muslim: 2657).

2. Haɗarin "Takhbib" (Ruguza Auren Wani)

Shi kuma wannan saurayin da yake amsar kiran ki yana tattaunawa da ke, ya sani cewa yana aikata babban zunubi da ake kira Takhbib. Manzon Allah (SAW) ya ce:

 لَيْسَ مِنَّا مَنْ خَبَّبَ امْرَأَةً عَلَى زَوْجِهَا

"Ba ya tare da mu (ba ya kan tafarkinmu) wanda ya ɓata wa mutum matarsa (har ta ji ba ta son mijin ko ta karkata zuwa ga wani)." (Abu Dawud: 2175).

3. Matakan Magance Wannan Matsala

Domin ki tseratar da kanki daga fushin Allah da kuma kunyatar duniya, dole ne ki dauki wadannan matakan da zafi-zafi:

Yanke Sadarwa Gaba Daya: Kada ki ce zaki goge lambar kawai; ki sauya taki lambar ma idan hakan zai sa ya daina samun ki. Duk wata kofa da zaki ji muryarsa, to kofa ce ta zuwa wutar jahannama.

Fuskantar Mijinki: Ki sani cewa wannan mijin naki shi ne rufin asirinki. Shaidan yana nuna miki ba kya son sa ne kawai domin yana so ki wulakanta ni'imar da Allah Ya baki. Ki yi kokarin nemo kyawawan halayensa ki rika dubawa.

Yawaita Zikiri da Neman Tsari: Duk lokacin da tunaninsa ya zo miki, ki ce: "A'uzubillahi minash Shaidanir Rajeem", sannan ki tashi ki yi alwala ko ki shagaltu da wani aikin gida.

Tsoron Mutuwar Ba-Zata: Ki yi tunanin idan Allah Ya dauki ranki kina cikin waya da shi ko kina tunaninsa, yaya zaki hadu da Ubangijinki?

4. Addu'ar Neman Tsoron Allah

Ki dage da wannan addu'ar da Manzon Allah (SAW) yake yawan yi:

 يَا مُقَلِّبَ الْقُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ

"Ya Mai juya zukata, Ka tabbatar da zuciyata a kan addininKa." (At-Tirmidhi).

Kuma ki roki Allah Ya sanya miki son mijinki a zuciya:

 اللَّهُمَّ حَبِّبْ إِلَيَّ زَوْجِي وَحَبِّبْنِي إِلَيْهِ

"Ya Allah, Ka sanya mini son mijina, Ka kuma sanya masa so na."

𝐊𝐚𝐦𝐦𝐚𝐥𝐚𝐰𝐚

Yar'uwa, wannan saurayin naki na da, ba masoyinki ba ne. Da ace masoyinki ne, da ba zai raba ki da Allah ba, kuma ba zai rika tattaunawa da matar wani ba. Masoyinki na gaskiya shi ne mijinki wanda yake ciyar da ke, yake tufatar da ke, kuma yake zaune da ke a matsayin matar aure. Ki tuba tun kafin asirinki ya tonu, domin idan hakan ta faru, kowa zai guje miki, har shi kansa saurayin.

WALLAHU A'ALAM

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments