Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Ke Satar Kuɗaɗen Mijinta

HUKUNCIN MATAR DA KE SATAR KUƊAƊEN MIJINTA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Dan Allah malam inada tambaya ne shin ya halatta macce ta ɗauki kuɗin mijinta batare da saninsa ba? domin biyan wasu 'yan bukatu nata kanana da be biya mata su na cikin gida haka da nata dana yaranta kuma malam yanada kuɗi amma inka tambaya sai yace bedashi, kuma malam bayarwa ne beyi sannan ko kyautar kuɗi aka bata ko yaranta sai ya karɓe kuma malan ko kitso zasu inta tambaya sai yace beda.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Haramun ne mace ta ɗauki wani abu daga dukiyar mijinta ba tare da izininsa ba. Sai dai idan abinci ne ba ya ciyar da ita yadda zata Qoshi da ita da 'diyanta. Ko sutura idan ba ya basu, ma'ana ya barsu cikin tsiraici.

Akwai hadisin da Imamul Bukhariy ya ruwaito ta hanyar Hindu bintu Utbah, matar Abu Sufyan tazo ta tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa mijinta yana da dukiya amma ba ya bata abinda zata ci.. Shin ya halatta ta ɗauki wani abu ba tare da saninsa ba, domin ta ciyar da kanta da 'ya'yanta??.

Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace mata "KI ƊAUKI GWARGWADON ABINDA ZAI ISHEKI DAKE DA 'YA'YANKI (BA TARE DA ƁARNA KO TA'ADI BA).

Amma Kamar kuɗin kitso, Kuɗin kayan kwalliya, kuɗin biki, wannan ba wajibi bane, sai dai yana cikin kyautatawar da Allah yayi umurni a yiwa mata. Yace :"KU ZAUNA DASU TARE DA KYAUTATAWA".

Ibnu Jareer da Ibnu Abi Hatam da Abu Dawud sun ruwaito hadisi daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: "MAFIFICIYAR MACE ITA CE WACCE IDAN KA KALLETA ZATA SANYAKA FARIN-CIKI, IDAN KA UMURCETA ZATAYI MAKA BIYAYYA, IDAN KUMA BAKA NAN ZATA KIYAYE MAKA AMANAR KANTA DA DUKIYARKA".

To kinga anan idan kika zamto kina yi masa satar kuɗaɗensa, ba kya cikin matayen kirki awajen Allah, sai dai kina cikin sahun maciya amana da kuma masu yin zamba cikin aminci. Kuma idan baki nemi yafewarsa ba, lallai sai Allah ya karɓa masa hakkinsa aranar Alqiyamah aranar hisabi.

Kiji tsoron Allah ki tuba ki dena sata, domin hakika Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya tsine wa ɓarayi (kuma kina cikinsu har sai kin tuba tukunna). Kuma yace ɓarawo ba mumini bane har sai ya tuba".

Allah ya shiryeki tare damu, ya shiryi dukkan mataye masu irin wannan halin. Ameen.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments