Ticker

6/recent/ticker-posts

Zumunta a Wakokin Baka Na Hausa: Nazari Daga Wakokin Makada Sa’idu Faru

Citation: Maikwari, H.U. & Dalhal, I. (2024). Zumunta a Waƙoƙin Baka Na Hausa: Nazari Daga Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 117-126. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.016.

ZUMUNTA A WAƘOƘIN BAKA NA HAUSA: NAZARI DAGA WAƘOƘIN MAKAƊA SA’IDU FARU

Daga 

Haruna Umar Maikwari
Department of Hausa Language,
Federal College of Education (Technical), Gusau
Ƙibɗau: maikwariharuna@gmail.com
Lambar Waya:07031280554

Da

Ibrahim Dalha
Government Day Secondary School Birnin Kudu,
Ministry of Education Science & Technology, Dutse,
Jigawa State
Ƙibɗau: Ibrahimdalha1@gmail.com
Lambar Waya: 08060574254 

Tsakure

Ga ɗabi’ar ɗan’adam, tunaninsa da hikimarsa sukan saje da juna da na wani mutum da yake kusa ko kuma nesa da shi. Don haka al’adar ɗan’adam ta tabbatar da haɗuwar ra’ayi ta fuskokin addini ko sana’a ko kuma wani lamari na rayuwa kan haifar da ɗorewar dangantaka ta musamman a tsakanin al’umma. Wannan bincike yana da manufar gudanar da nazari domin ƙyallaro wani abu dangane da samuwar zumunta a wasu daga cikin ɗiyan waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru da kuma na wasu Mawaƙan ƙasar Hausa na fada. Binciken ya yi amfani da hanyoyin da suka haɗa da: Sauraren waƙoƙin baka daga bakin maƙagansu ta hanyar amfani da memori da tuntuɓar wasu masana da suke da masaniya game da waƙoƙin nasu. Haka kuma, nazarin bai kawar da kai ga leƙa wasu wallaffun ayyuka da aka gudanar ba. Ayyukan da aka mayar da hankali a kansu sun haɗa da, wallafaffun matanonin waƙoƙin baka da kuma nazarce-nazarcen da wasu manazarta da ɗalibai suka gudanar. An yi amfani da Bahaushen tunanin da ke cewa: “Da abokin daka akan sha gari” a matsayin hanyar da aka ɗora binciken a kanta. Binciken ya fito da sakamako tare da bayar da wasu shawarwari da za su ƙara wa Borno dawaki. Wasu daga cikin sakamakon da nazarin ya gano su ne: Mawaƙan baka na fada suna amfana da fasahohin junansu inda sukan yi amfani da kalmomi masu alaƙa wajen waƙe iyayen gidansu. Har wa yau, nazarin ya gano cewa, akwai bambanci a tsakanin satar fasaha da waƙeƙeniya da kuma zumuntar fasaha. Binciken ya bayar da shawarar cewa, waɗanda suke da ilimin kwamfuta a cikinmu da su ɓullo da wasu manhajoji da za a riƙa jin muryoyin mawaƙanmu na baka irin su Sa’idu Faru, Salihu Jankiɗi, Ibrahim Narambaɗa da kuma Musa Danƙwairo da Aliyu Ɗandawo Shuni da sauransu da dama.

1.0 Shimfiɗa

Haɗuwar tunanin wani rukuni na al’umma yakan yi amo a fasahohinsu na baka da kuma na sarrafa albarkatunsu na yau da kullum. Irin wannan haɗuwar tunani takan samu a dalilan zama wuri guda da tarayya da juna wajen gudanar da wasu sana’o’i da kuma gamuwar ra’ayi. Idan aka yi duba da kyau, akwai hasashen cewa, samun yawaitar ƙungiyoyi da jam’iyyun siyasa a wannan ƙarni na 21 yana da alaƙa da dalilin zumuntar tunanin wasu al’ummu da suke da manufa iri guda. Ga al’adar ɗan’adam, tunaninsa yakan saje da na abokin zamansa ko kuma wanda suke hulɗar sana’a iri ɗaya. Idan aka samu irin wannan sajewar tunani, ƙauna da zumunci sukan ƙullu ta yadda akan zama tamkar abu ɗaya har abin ya zama zumunta. Hakan kuma shi ne yakan sanya a riƙa amfani da kalmomi iri guda na sadarwa. Wani lokaci ma wani yakan yi amfani da kalmomin da wani ya saba magana da su domin ya bayyana wani abu na tunaninsa. Idan kuma aka samu akasi tunaninsu da ra’ayoyinsu suka saɓa, shi ne hakan yakan haifar da wasu bambance-bambance ta fuskar ra’ayoyi inda har ake samun waƙeƙeniya a tsakanin mawaƙa. Kamar yadda masu sana’o’i na ƙira da noma da wanzanci da dangoginsu suke da zumunta a tsakaninsu[1], haka su ma mawaƙan ƙasar Hausa sukan yi ƙoƙarin ganin zumuncinsu ya ƙullu da abokan sanaarsu ta fuskokin fasahohinsu na waƙa da dangoginsu. Wannan yanayi na sajewar tunani a tsakanin al’umma shi ne wannan bincike yake kallonsa a matsayin zumuunci a waƙoƙin baka. Wannan bincike yana da manufar nazarin zumuntar da ake samu a tsakanin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru da sauran takwarorinsa mawaƙan baka na fada[2]. An yi wannan tunani ne domin a nuna irin yadda yanayin zamantakewar Hausawa yake ɗamfare da juna ta fuskokin al’adunsu na mu’amalarsu da kuma abubuwan da suka shafi waƙoƙinsu.

1.1 Fashin Baƙin Ƙusoshin Taken Bincike

 A wannan muhalli, an mayar da hankali wajen fayyace ma’anonin muhimman kalmomin da aka gina taken wannan bincike da su. Wato fitillun kalmomin da suka haska wannan take, waɗanda suka haɗa da: su ne: Zumunci da kuma waƙar baka.

1.1.1 Zumuci

CHNN, (2006:136) ya bayyana ma’anar zumunci da cewa: “Kyakkyawar dangantaka ta jini ko ta aure ko kuma ta abota tsakanin mutum da mutum, d-d da zumunta.” Wannan ma’ana ta haska wa wannan bincike cewa, zumunci kalma ce da take da ma’anar zaman tare wanda yake haifar da kwaikwayar juna wajen gudanar da wata magana ko aiki ko kuma duk wata fasaha.

1.1.2 Waƙar Baka

Wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da amshi, (Gusau, 2003:xiii). Bisa wannan ma’ana da aka bayar, wannan takarda tana da ra’ayin cewa, waƙar baka ita ce, shiryayyen zance ne da ake ƙulla shi cikin hikima wanda kuma ake rerawa ta hanyar bin raujin wani kiɗa.

1.2 Farfajiyar Bincike

Kaucewa abin da Hausawa suke cewa: “Wuce makaɗi da rawa.” Shi ne ya sanya aka ga dacewar yi wa wannan maƙala kadada. Sakamakon haka, takardar ta taƙaita ga laluben wuraren da aka samu zumuntar fasaha a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru da na sauran takwarorinsa mawaƙan fada. Mawaƙan da takardar ta mayar da hankali a kan fito da zumuntarsu ta fuskar waƙa a tsakanisu da Saidu Faru sun haɗa da: Makaɗa Salihu Jankiɗi da Ibrahin Narambaɗa da Musa Ɗanƙwairo Maradun da kuma Ahmadu Mailauni Bakura. Bugu da ƙari, kasancewar masana suna ganin mafiya yawancin waƙoƙin fada ana gina su ne a kan wasu tubalai guda goma (10) [3]. Takardar ta mayar da hankali a kan uku daga cikin tubalan da ake gina waƙoƙin fada da su inda aka bayyana wuraren da aka samu zumuntar a tsakanin Makaɗa Sa’idu Faru da ta sauran mawaƙan da aka lissafo a baya. Ke nan, maƙalar ta taƙaita ga laluben zumuntar da ake samu a waƙoƙin baka a tsakanin Sa’idu Faru da takwarorinsa mawaƙan fada a tubalan waƙoƙin fada da suka haɗa da: Yabo da zuga da kuma roƙo. Domin haka ba a tsammanin a ga kutsen waƙar wani mawaƙi da ba na fada ba.

1.3 Hanyoyin Bincike

Kamar yadda Hausawa suka haƙiƙance da cewa: “Sanin wurin bugu shi ne ƙira.” Haka masana suka tabbatar da cewa, nagartaccen bincike yana ƙunshe da ingantattun hanyoyin tattara bayanai. Sakamakon haka, wannan maƙala ta yi amfani da waɗannan hanyoyi a matsayin dabarun da suka samar da bayanan da ake nema. Hanyoyin da aka yi amfani da su kuwa su ne:

i.        Da farko, an fara da samun waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru tare da sauraren su ta wayar hannu saboda neman bayanan da ake lalube. Hakan ya sa aka fara nazartar wasu ɗiyan waƙoƙinsa da suke a rubuce, musamman na cikin Diwanin Waƙoƙin Baka wanda Gusau (2009) ya wallafa.

ii.      Sauraren wasu hirarraki da aka gudanar da Maigirma Alhaji Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN Kaduna) a kan rayuwa da tarihin Makaɗa Sa’idu Faru a shekarar 2018-2019.

iii.   Leƙa ɗakunan karatu, musamman na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato da na Jami’ar Bayero, Kano inda aka yi katarin samun wasu ayyuka masu alaƙa da binciken da aka gudanar.

iv.   Shiga cikin rukunin shafin sada zumunta na whatsApp (WhatsApp group) wanda a ka ƙirƙire shi musamman domin yayata shirye-shiryen wannan taro. Wannan shafi ya ƙara wa wannan takarda ƙwarin gwiwa saboda muhimman bayanan da aka amfana da su daga wurin ma’ilmanta na kusa da na nesa.

v.      Baya ga haka, maƙalar ba ta kawar da kai da tuntuɓar masana al’adun Hausawa ba. Wannan dalili ya sa aka tuntuɓi Farfesa Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan da Farfesa Yakubu Aliyu Gobir da kuma Dr. Nazir Ibrahim Abbas duka a Jami’ar Usmanu Danfodiyo. Haƙiƙa tuntuɓar waɗannan masana ya ƙara wa wannan takarda armashi tare da yi mata jagora a kan inda ta dosa.

1.4 Hanyar Ɗora Aiki

Masana da manazarta sun tabbatar da ɗora ayyukan bincike a kan tunanin magabata yakan taimaka wajen yin jagora ta yadda ba za su kauce daga kan turba ta ilimi ba. Sakamakon haka, wannan maƙala an ɗora ta a kan tunanin Hausawa da yake cewa: “Da abokin daka akan sha gari.” An yi wannan tunani ne saboda ganin yadda mawaƙan baka suke amfani da fasahohin junansu wajen ƙulla ɗiyan waƙoƙinsu. Ke nan, a wannan takarda, abokin daka shi ne, mawaƙi. Gari kuma shi ne, waƙoƙin da ake samu a bakunan mawaƙan baka waɗanda sukan haska wa junansu hanyoyin ƙirƙirar wasu sababbin ɗiyan waƙoƙin da za su rera wa masu gidansu da kuma masu ƙaunar sana'arsu ta kiɗa da waƙa. Wannan ya nuna amfanuwar da mawaƙa suke yi da junansu ya yi daidai da abin da Hausawa suke cewa: “Yaro da gari abokin tafiyar manya ne.”

2.0 Waiwayen Tarihin Sa’idu Faru a Taƙaitace

Babu shakka, akwai ayyukan magabata da suka fayyace tarihin rayuwar Makaɗa Sa’idu Faru kafin wannan bincike. Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da: Gusau (1996:117) da Furniss (1996:176) da kuma Ɗanmadamin Birnin Magaji (2019). Don haka, ambaton wani abu daga cikin tarihin Makaɗa Saidu Faru a wannan takarda tamkar cikon sunna ne makaho da waiwaye. Duk da haka, Saidu Faru dai an haife shi a garin Faru da ke yankin ƙasar Maradun ta Ƙaramar Hukumar Mulki ta Talatar Mafara da ke tsohuwar Jihar Sakkwato a shekarar 1932 kamar yadda Gusau (1996:117) ya tabbatar[4]. Sunan mahaifinsa Makaɗa Abubakar ɗan Abdu. Kakansa wanda ya haifi babansa sunansa Alu Maikurya. Ke nan, makaɗa Sa’idu Faru ɗan gado ne a fagen kiɗa da waƙa. Makaɗa Sa’idu ya gudanar da yawancin ƙuruciyarsa a garin mahaifiyarsa da ke garin Banga ta Ƙauran Namoda. Kodayake bayan da ya tasa ya baro gaban kakannin nasa inda ya koma gaban mahaifinsa. Saidu Faru ya yi karatun allo a ƙuruciyarsa, amma bai yi karatun boko da na littattafai ba. Bayan ya dawo gaban mahaifansa ne sai sabgar kiɗa da waƙa suka shige masa gaba. Makaɗa Sa’idu ya koyi waƙa a wurin mahaifinsa Makaɗa Abubakar. Ya fara bin sa waƙa tun bai fi shekara goma ba. Sa’idu ya zama mawaƙi mai cin gashin kansa bayan rasuwar mahaifinsa. Ga aladar Saidu Faru ba ya yi wa kowa waƙa sai wanda ya jiɓinci sarauta. Haka kuma, yana amfani da kotso a matsayin kayan kiɗansa. Yakan shirya waƙarsa a gida kafin ya bayyana ta a gaban wanda zai rere wa. Saidu Faru ya rera waƙoƙi da dama, amma waɗanda ya yi wa mai gidansa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo su ne suka fi yawa da shahara, saboda biyayyarsa da ƙaunar da yake yi masa. Kodayake Allah bai nufe shi da riskar lokacin da Mai’alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ya zama Sarkin Musulmi ba. Makaɗa Sa’idu Faru ya rasu a shekarar 1987 ya bar mata da ‘ya’ya da jikoki da dama, (Danmadamin Birnin Magaji, 2019). Yanzu haka (2024) ɗansa Ibrahim Sa’idu Faru ne ya gaje shi wajen gudanar da sabgoginsa na kiɗa da waƙa.

3.0 Dalilan Samuwar Zumuntar Waƙoƙin Baka na Hausa

Al’adar mawaƙan baka ta ƙulla zumuntar waƙa a tsakaninsu ba za ta rasa alaƙa da wasu dalilai ba. Wannan ne ya sa wannan maƙala take da ra’ayin cewa, waɗannan su ne dalilan da suka sanya ake samun zumunta a waƙoƙin baka na fada:

i.        Mafiya yawancin mawaƙan baka na fada sun fito ne daga yanki guda, wato ƙasar Zamfara. Don haka karin harshensu da al’adunsu da fasahohinsu suna da alaƙa da juna.

ii.      Salon waƙoƙinsu da kayan kiɗansu duka suna da alaƙa da juna. Misali, makaɗan fada ga al’ada sun fi amfani da kotso da taushi a matsayin kayan kiɗansu.

iii.   Tsarin mulkin sarakunan da suke wa waƙa kusan abu ɗaya ne, saboda dukkaninsu zuriyar gidan Shehu Usmanu Danfodiyo ne da ta almajiransa. Don haka akan ji nason addini da na jarumtar yaƙi da na nasaba da kuma na tarihi a cikin ɗiyan waƙoƙinsu.

iv.   Kalmomin da ake yabon sarakuna ko ake amfani da su a fada keɓantattu ne na musamman. Kafin-Hausa, (2002:249) ya rawaito Sa’idu Faru da kansa ya bayyana musu cewa, dalilin da ya sa ba ya yi wa wanda ba shi da muƙamin sarauta waƙa, saboda ba shi da kalmomin da zai tsara musu waƙa. Wannan dalili ya sa duk wani mawaƙi da yake kiɗan fada da kalmominsu na mulki yakan yi amfani. Don haka ba kowane mawaƙi ne yake iya waƙoƙin fada ba, saboda tanadin kalmominsu da tattalin yadda ake amfani da su sai wanda ya san yadda suke da kuma yadda ake amfani da su.

v.      Zumuntar da ke tsakanin gidajen sarakunan ta auratayya da ta addinin da kuma ta jini ta yi amo sosai wurin mawaƙan kowane sarki. Wannan ya ba da hasken samun zumuntar waƙa a wurin mawaƙansu.

4.0 Zumuntar Waƙoƙin Sa’idu Faru da Wasu Takwarorinsa Mawaƙan Fada

 Wannan takarda tana da ra’ayin cewa, zumuntar mawaƙan baka tana da bambanci da satar waƙa. Dalili kuwa, a zumuntar waƙoƙi an fi mayar da hankali a kan ƙulla alaƙa da manufar mawaƙa ta fuskokin kalmomin ɗiyan waƙa. Saɓanin satar fasaha da akan saci raujin murya da na kiɗa da kuma kayan cikin waƙa gaba ɗaya. Hakan ne ya sa Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun yake bayyana wa al’umma cewa, akwai wani makaɗi da yake sace masa waƙa idan ya talitta ta. Inda yake cewa:

Jagora : Makaɗin ga mai ruwan gahiya.

Yara: Gayyatai ba ta da sa’a,

Jagora : In nai waƙa ya sace,

 Yara : Ya zam babban ɓarawo

Gindi : Mai ban tsoro Sadauki,

 : Hassan ɗan Shehu Malam.

(Musa Ɗanƙwairo Maradun: Waƙar Hassan Usman Ciroman Katsina).

Kasancewar waƙoƙin baka na fada suna da faɗi musamman idan ana buƙatar a fayyace abubuwan da suka ƙunsa a farfajiyar nazarin al’adun Hausawa. Don haka aka ga dacewar mayar da hankali a kan wasu tubalai da mawaƙan suke amfani da su. Wannan dalili ya sa aka taƙaita nazarin a kan tubalan yabo da zuga da kuma na roƙo.

4.1 Yabo

Yahya, (1997:117) yana da ra’ayin cewa, jigon yabo yana da fuskoki guda shida (6) da mawaƙi kan bi ya gina saƙonsa. Waɗannan jigogi kuwa su ne: Addini da jarumta da mulki da asali da kyauta da kuma hali na gari. Wannan magana da ta yi daidai da tunanin Gusau (2008:376) a inda yake fayyace yabo da cewa: “Ambaton kalmomin sambarka da nuna amincewa da hali ko wani abin da mutum ya yi na gari.” Kodayake Gusau, (2008:376) yana da ra’ayin cewa, akan gina turken yabo ta hanyar amfani da tubalai waɗanda suka haɗa da addini da asali da nasaba da kyauta da karimci ko baiwa da iya mulki da jarumtar yaƙi da hali da ɗabi’a da kirari da roƙo da habaici da kuma zambo ga wani. Waɗannan bayanai na masana sun tabbatar da cewa, waƙoƙin baka na fada kusan ana iya cewa, tubalin yabo ya kere kowane a cikinsu. Don haka wannan takarda ta fi mayar da hankali a kansa.

4.1.1 Yabo ta Fuskar Addini

Addini a wannan takarda yana nufin tafarkin Musulunci. Mawaƙan baka na fada suna dubin tushen fadojin da suke wa waƙoƙi da cewa sun kafu ne a dalilin jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo da almajiransa. Wannan dalili ya sa kowane lokaci sukan yi ƙoƙarin su ga cewa, sun gina waƙoƙinsu da tubalin yabo ta fuskar addini. Sukan yi haka ne da manufar nusar da al’umma inda aka fito, da kuma wurin da aka dosa. Baya ga haka, yin hakan yakan ƙara zama wani hannunka-mai-sanda dangane da tushen waɗanda suka gada, saboda kada su bari wuta ta mutu a hannunsu.

Ga al’adar mawaƙan baka na fada, bayan sun yabi sarkinsu da daraja da kuma buwaya, sukan yi ƙoƙarin fito da halayensa domin su tabbatar wa da al’umma cewa, ba banza ba ƙuda a kan warki. Wato, buwayar da ɗaukakar da yake da ita suna da alaƙa da ɗabi’u da halayensa na bin addini. Kasancewar Sarakunan ƙasar Hausa suna ƙarƙashin daular Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, makaɗan sukan yi ƙoƙarin fito da halayensu ta fuskar bin addinin Musulunci sau-da-ƙafa. Don haka a kowane lokaci sukan bayyana ƙoƙarinsu na kauce wa ayyukan da addinin Musulunci bai aminta da su ba. Misali, Sa’idu Faru yana yabon Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo da ƙin aminta da mu’amala da barasa (giya) da taba sigari da sauran ayyukan ɓarna. Ga abin da yake cewa:

 Jagora: Da biskit da minti da taba sigari,

Yara: Biskit da minti da taba sigari,

: Da lemu da soda da kwalbat sitawut,

: Bai ya da aza su ko sau guda ba,

: Ya ɗau wasiccin da Usmanu yac ce,

: Abincinsu ba namu ne ba,

: Yawanci abinci daɗi gare shi,

: Kowanenmu ne yai ta ci ba ruwanai,

: Wancan na ci sai ta ci bai ci can ba.

Gindi: Bajimin gidan Bello Mamman na Yari,

: Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.

(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi amfani da wannan hikima inda ya ƙulla wasu ɗiyan waƙa da suke da zumunta da zaren tunanin fasahar Sa’idu Faru dangane da ɗabi’un Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo na riƙo da addinin Musulunci inda yake cewa:

Jagora : Macciɗo shiryayyen ɗan sarki,

Yara : Ba ya kaba’ira Mamman,

 : Sannan ba ya shan giya,

: Ƙarya ka ganai yana caca,

: Ƙarya ka ga nai yana karta,

: Daga alheri sai fa addini.

(Musa Danƙwairo Maradun: Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).

 

A wata waƙa ta daban kuma yana cewa:

Jagora : Mamman ba ya yin batun banza,

Yara: Maganar da duk ya faɗa ma ta zauna.

Jagora/Yara: Mamman ba ya caca ba ya riya,

: Kuma ba ya ‘yan shaye-shayen zamunna.

Gindi : Jikan Hassan Sarkin Kudu,

: Gagarau mai jiran daga Mamman.

(Musa Ɗanƙwairo Maradun : Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).

4.1.2 Yabo ta Fuskar Zuga

 Wannan nau’i na yabo yana ɗauke da wasu kalmomi da sukan nuna wanda ake yi wa waƙa sama yake da duk takwarorinsa. Sakamakon haka Yahya, (1997:131) ya nuna irin wannan yabo yana sosa zuciyar basarake har ta kai shi ga jin ya fi kowa kuma mai aikata abin da ya ga dama ne ba tare da samun wani mai iya tare shi ba. Misalin irin wannan nau’i na yabo a zumuntar mawaƙa shi ne:

Jagora : Dandikko yana can yaj jiya,

: Wannan magana ta tabbata,

: Duk inda rana ta fita Gabas,

: Har inda rana taka faɗuwa,

: Dut ɗai na jikan Danhodiyo,

: Babu wurin da mulkinai yats tsaya.

 Gindi: Kana shire baban ‘yan ruwa,

 :Na Bello jikan Ɗanhodiyo.

(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).

A wannan ɗan waƙa, makaɗa Sa’idu Faru ya nuna duk duniyar Musulmi tana ƙarƙashin mulkin Sarkin Muslmi Muhammadu Macciɗo. Don haka kowane Sarki yana ƙarƙashin ikonsa ne, wato tamkar hakimi ne a wurinsa. Makamancin wannan yabo na zuga dai Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun da Amadu Mailauni Bakura sun yi shi a wasu daga cikin ɗiyan waƙoƙinsu. Danƙwairo ya yi wa Sarkin Musulmi Macciɗo irin sa, yayin da shi kuma Amadu Mailauni Bakura ya yi wa Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi. Ga bin da suke cewa:

Jagora : Ɗan Sardauna jikan Hasan,

 Yara : Ci banza ubangijin Yari.

Jagora : Da inda rana ke fitowa,

: Har inda rana taka faɗuwa,

: Gabar da Yamma dama da hauni,

: Mamman mulkinku ya kai can,

Jagora/Yara : Indai akwai masu yin salla.

Gindi : Ɗanmaigayya na Jekada,

: Mamman ya wuce reni.

(Musa Ɗanƙwairo Maradun: Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).

Shi kuma Makaɗa Amadu Mailauni Bakura yana cewa:

 Jagora: Dam mahitar rana,

: Har a kai mafaɗa,

: Baba dun ga naku na,

: In dai maisalla ne,

: Baba kai Allah yab ba.

 Yara : Babu yanzu duw wani mai mulkinmu ban da kai.

Gindi : Ibrahim Jikan Mujadadi,

: Kai kag gaji Hassan da arziki.

(Amadu Mailauni Bakura: Waƙar Ibrahim Jikan Mujaddadi)

A waɗannan ɗiyan waƙoƙi da aka kawo, duka mawaƙan guda biyu, sun yi zumunta da Sa’idu Faru ta fuskar yabo mai ɗauke da zuga, inda suke nuna tun daga mahudar rana har zuwa faɗuwar ta suna ƙarƙashin mulkin Sarkin Musulmi. Wannan yana da manufar suna son su nuna gaba ɗaya duniyar Musulmi yake mulka ba iya daular Shehu Usmanu Danfodiyo ba. Hakan ya sa suka yi amfani da kalmar mahudar rana, wato gabashin duniya, zuwa mafaɗar ta, wato yammacin duniya ke nan.

A ɓangare ɗaya kuma, makaɗa Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Musulmi Macciɗo ta hanyar zuga kamar yadda Salihu Jankiɗi ya yi wa Sarkin Musulmi Abubakar na III. Haƙiƙa an samu zumunta idan aka dubi yadda makaɗan suka tsara ɗiyan waƙoƙin yabon nasu inda suke nuna irin buwayar da Allah ya yi wa iyayen gidan nasu ta hanyar lissafo wasu abubuwa da suka keɓanta da su. Ga yadda suke cewa:

Jagora: Wanna ɗan sarki yak kammala bai kai ga Macciɗo,

 Yara: Girma Allah yai ma da yawa baba duniya.

Jagora: Kashi bakwai kak kwasa ‘yan sarki na kallo.

 Yara: Gidan gwani kai kak kai ga irin wagga maslaha.

Jagora: Ga ka ɗan mai daraja,

 : Ga ka jikan Usmanu Kurɗabi na Hodiyo,

 : Ga ka Sarkin nasara,

: Ga ka Alhaji Macciɗo,

: Ga jikka ta yi dubu,

: Ga ka mallami kake,

: Ga ka mummuni kake,

: Ga ka ba ka za’ida,

: Abin da du Allah kai wa mutum,

: Baba yai maka.

(Sai’du Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).

Shi kuwa makaɗa Salihu Jankiɗi a waƙarsa ta Sarkin Musulmi Abubakar na III yana cewa:

 Jagora: Wa ka dambe da mai ƙarhi tara?

Yara: Kai na Allah kai na Ma’aiki,

: Ga jihadi ga alheri,

: Ga hanƙuri ga ƙarhin arzuki,

: Ga muhibba inda Abubakar,

: Rabbu Allah yai ma ɗaukaka.

Gindi : Abubkar ɗn Shehu Baƙadire,

: Na Bello sai Madi ko ba a so.

(Salihu Jankiɗi: Waƙar Sarkin Musulmi Abubakar na III).

Bugu da ƙari, mawaƙan baka na fada sukan yi amfani da wasu abubuwa a matsayin kinaya domin fito da darajar iyayen gidansu. Misali, Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da gizago[5] wajen zuga Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris. Ga abin da yake cewa:

Jagora: Shehu gizago ba ka da sabo,

 Yara: Mai sassaƙa tsare hannunka,

: Don ka da a sassaƙe ma hannu.

Gindi: Gagara gasa bajimin Marafa,

: Shehu halaliyar gidan Sambo,

: Allah ya biya maka buƙata,

: Kai ab babba ga gidan Sambo.

(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Zazzau Shehu Idris).

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi amfani “gizago” a matsayin abin da ya yi kinaya da shi wajen yabon Sarkin Zazzau Shehu Idris kamar yadda Sa’idu Faru ya yi, inda yake cewa:

Jagora : Gizago ba ka da sabo wandara,

: Mai sassaƙa tsare hannunka,

Yara : In ka ƙiya ya jima,

: Mis sha min kai.

 Gindi : Ba maza kashi tilas su bi ka,

: Malam ɗan Idirisu.

(Musa Ɗanƙwairo Maradun: Waƙar Sarkin Zazzau).

Ga al’adar mawaƙan baka na fada, sukan zuga sarakunansu ta hanyar kamanta su da zuma ko maɗi da sauransu. Kodayake a kowane lokaci sukan mayar da sarakunan nasu zuma wasunsu kuma maɗi ko kuma maɗaci. Misali,

Jagora: Kuma in batun zaƙi a kai,

Yara: Kowa naz zuba ruwan zuma,

: Ba shi ko ta batun maɗi

Gindi: Farin cikin Musulmin duniya,

 : Mai martaba na Abubakar,

: Ci banza Alhaji Macciɗo.

(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).

Haka shi ma Makaɗa Ibrahim Narambaɗa ya yi amfani da wannan zuga, inda ya kamanta Sarkinsa (Sarkin Gobir Amadu) da zuma da damen gero da rago. Abokan hamayyarsa kuma ya kamanta su da maɗi da kwandon wake da kuma ɗan akuya[6]. Ga abin da yake cewa:

Jagora: Maɗi bai kai ga zuma ba,

Yara: Kowal lasa shi ka hwaɗi.

Jagora: Kwandon wake bai kai ga damen gero ba,

: Ɗan akuya ko ya yi ƙahonai,

: Ya san bai yi kamar rago ba.

Gindi: Gogarman Tudu jikan Sambo,

: Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa.

(Narambaɗa: Waƙar Gogarman Tudu).

4.1.3 Magori Wasa Kanka da Kanka (Bugun Gaba)

Mawaƙan baka wani lokaci idan waƙa ta yi musu daɗi sukan yi wata ‘yar gayauna su yabi kansu saboda hikimar da suke da ita. Sukan yi haka ne domin su gwada wa maigidansu (Sarkinsu) cewa ta ɓangarensu na waƙa su ma ba kanwar lasa ba ne. Don haka, sukan bayyana baiwar da Allah ya yi musu ta fasaha a cikin ɗiyan waƙoƙinsu a lokacin da suke yabon iyayen gidansu. Makaɗa Sa’idu Faru ya bi sahun mawaƙan baka na fada wajen bayyana fasaharsa tare da yabon kansa kamar yadda mawaƙan da suka gabace shi suka yi. Ga abin da yake cewa:

Jagora: Sa’idu Malamin waƙa,

Yara: Mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba.

Jagora: Ban wuce gonata da irina ba,

Yara: Inda sarkin Kudu nitc tsaya.

Gindi: Farin cikin Musulmin duniya,

 : Mai martaba na Abubakar,

: Ci banza Alhaji Macciɗo.

Al’adar kowane mawaƙin sarakuna ne ya ambaci kansa da malamin waƙa, saboda a tunaninsu nan ne magaryar tuƙewar darajar da ake so a kai a wannan fage. Don haka Sa’idu Faru ya yi amfani da hikimarsa wajen samo ɗiyan waƙar da za su amsa wannan guri nasa kamar yadda makaɗan da suka gabace shi suka yi. A dai wannan hauji, ga abin da makaɗa Ibrahim Narambaɗa yake cewa:

Jagora: Ke tahi Jekadiya hwaɗa mishi baƙonsa ya zaka,

Yara: Ba samna ba ne Narambaɗa na Malamin kiɗi,

: In ya ce maraba mui ta kiɗi har mu kwan bakwai.

Gindi : Ɗan Isiyaku Makaye,

: Jafaru mai halin mazan jiya zamna da lafiya.

(Ibrahim Narambaɗa: Waƙar Sarkin Zazzau Jafaru).

Haka abin yake ta fuskar zumunta a wurin mawaƙan baka. Shi ma makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun a wannan batu na matsayin malamin waƙa yana cewa:

Jagora : Na shigo Daura Ɗanƙwairo,

: Ana ta murna ana ta taɗi.

Yara: Sun ga Ɗanƙwairo uban ɗumi.

Jagora: Na shigo Daura mai guru ,

: Ana ta murna ana ta taɗi,

Yara: Sun ga Ɗanƙwairo uban ɗumi.

Jagora/Yara: Malamin Waƙa Ɗanƙwairo,

 : Sabon hwaihwai na sunka wallafa.

 Gindi: Shirinka ba ɗai da nasu ba,

: Na Audu giwa abin biya.

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Sarkin Daura)

4.1.4 Roƙo

Kasancewar roƙo ɗaya daga cikin tubalan da ake gina waƙoƙin baka na fada da su, don haka ba a cika ƙare waƙa ba tare da an ji motsinsa ba. Da yake buƙatar dara kasawa, mawaƙan baka suna talitta waƙoƙinsu ne da manufar roƙon biyan wasu buƙatunsu a wurin iyayen gidansu. Don haka, CNHN (2006:374) ya fassara roƙo da: “Sana’ar maroƙa ta yi wa mutane kirari ko yabo a yi musu kyauta, ko kuma nenan kyauta daga wani.” Mawaƙan baka sukan ƙulla zumunta ta sigar zaɓen kalmomin da sukan roƙi wani abu daga iyayen gidansu. Kasancewar ba kowane lokaci mawaƙin baka yake roƙon abu kai tsaye ba, sukan gina tubalin roƙo ta hanyar bayar da labari da dangoginsa. Misali, Sa’idu Faru ya yi amfani da wata hikima da Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi amfani da ita a lokacin da yake roƙon mota a waƙarsa ta Janar Hassan Usman Katsina. Ga abin da Sa’idu Faru yake cewa:

Jagora : Manyan ma’aikatan gwamnati,

: Manyan ma’aikatan NA

: Almajirinku na an nan,

: Nan bisa gare ku Allah yas shirya muna abinci,

: Na roƙe ku in da hali don shirya muna,

: Kujera ta mu je hajji.

Yara : Na yi mafarki nai salla makka nai ɗawafi,

: kuma na rungumo mahwarki firami da bagaruwa,

: An ce mini Alhaji Baitul hajji naz zaka.

Jagoa: Wanga mafarki ya Allah yan nufa

: A shirya shi ya zan haka.

 Gindi : Farincikin Muslmin duniya,

 : Mai martaba na Abubakar,

: Ci fansa Alhaji Macciɗo.

 (Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).

A cikin waɗannan ɗiyan waƙa, Sa’idu Faru ya yi amfani da wata al’ada ta ɗan’adam ta mafarki wadda takan bayyana masa wani abu da yake da burin samu ko kasancewa a cikin rayuwarsa. Shi ma Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya yi amfani da mafarki inda ya roƙi mota a wurin Janar Hassan Usman Ciroman Katsina. Ga abin da yake cewa:

Jagora : Ɗanƙwairo na yi mafarki,

 Yara : Ina jin ƙarar inji ko mota za a ba ni.

Jagora : Ƙwairon an ba ka mota,

: An koma an ba ka mota,

: Sai Alhaji Bukar Mandara

: Ya ce ya ba ka mota

Gindi : Baban dodo sadauki,

: Hassan ɗan Shehu Malam.

 (Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Hassan Usman Ciroman Katsina).

5.0 Sakamakon Bincike

Wannan bincike ya gano wasu sakamako a ƙarshensa. Wasu daga cikin sakamakon da wannan bincike ya iya ganowa sun haɗa da:

i.     Mawaƙan baka na fada suna amfana da waƙoƙin junansu inda sukan sarrafa kalmomi masu alaƙa da juna wajen waƙe iyayen gidansu.

ii.   Nazarin ya gano cewa, akwai bambanci a tsakanin satar waƙa da waƙeƙeniya da kuma zumuntar waƙa. Satar waƙa ta rataya a kan kwashe abin da wani mawaƙi daban ya rera ba tare da nuna naƙaltar waƙar aka yi daga gare shi ba. Ita kuma waƙeƙeniya takan mayar da hankali ne ga mayar da martani a tsakanin mawaƙa. Saɓanin zumuntar waƙa, wadda ita kuma ta dogara ne ga amfani da wasu tsirarun kalmomi ko kuma salailai da wani mawaƙi ya yi amfani da su a waƙar da ya rera.

iii.Haka kuma, binciken ya gano cewa, ƙunshiyar tunanin alumma zai iya zama guda ɗaya, musamman idan aka lura da yanayin waƙoƙin makaɗanmu na fada. Wannan dalili ya sa wannan takarda take hasashen al’umma za su iya haɗa kansu su zamanto masu murya guda inda za su iya bayyana abin da suke buƙata a wurin shugabanninsu.

iv.Bugu da ƙari, binciken ya gano tabbacin maganar Hausawa da ke cewa: Wurin da saniyar gaba ta sha ruwa, ta baya ma nan za ta sha.” Sakamakon da yawa daga cikin mawaƙanmu na baka sukan dafi kafaɗun magabatansu wajen samun hasken tsara tasu waƙar. Wannan ya nuna cewa, dole sai mun yi biyayya ga magabatanmu kafin mu iya fito da wani abu na fasaharmu.

v.   Waƙoƙin mawaƙanmu na fada tamkar wata fitila ce da ke haska mana tsarin iko da halayen magabatanmu na jiya waɗanda muke fata su zama ababen koyinmu a yau. Don haka nazarin ya gano cewa, kowane mawaƙin fada yana ƙoƙarin fito da kyawawan halayen maigidansa na karamci da haƙuri da riƙo da addini da dangoginsu. Ƙoƙarin kwatanta abubuwan da suka ƙunsa zai iya zama hanyoyin warware matsalolinmu a yau.

5.1 Shawarwari

Gaskiyar Hausawa da sukan ce: “Mai shawara aikinsa ba ya ɓaci, sai dai ba shi da rufin asiri.” Wannan maƙala tana da tunanin bayar da sharwarin da suka haɗa da:

i.        Akwai buƙatar ƙara faɗaɗa bincike a kan fito da batutuwan da suka shafi al’adun Hausawa da suke ƙunshe a waƙoƙinmu na baka.

ii.      Wannan takarda tana ƙara bayar da shawara ga magabatanmu a tashi tsaye wajen ƙara sanya fasahohin mawaƙanmu na baka a cikin manhajojin makarantunmu tun daga firamare har ya zuwa Jami’o’inmu[7].

iii.   Muna kira ga waɗanda suke da ilimin kwamfuta a cikinmu da su ɓullo da wasu manhajoji da za a riƙa jin muryoyin mawaƙanmu na baka irin su Sa’idu Faru, Salihu Jankiɗi, Ibrahim Narambaɗa da kuma Musa Danƙwairo da Aliyu Ɗandawo Shuni da sauransu da dama.

iv.   Ci gaba da haɗa irin wannan taro ta hanyar zaƙulo mawaƙanmu na baka tare da baje kolin fasahohinsu kamar yadda aka yi a yau, shi ma abin a yaba ne, kuma ana bayar da shawarar a ci gaba da haka.

5.2 Naɗewa

 Wannan takarda ta mayar da hankali ne ga fito da zumuntar waƙa da ke tsakanin Makaɗa Sa’idu Faru da takwarorinsa mawaƙan fada. Maƙalar ta lura da cewa, adawa a tsakanin mawaƙa ita ce takan haifar da waƙeƙeniya. Kamar yadda rashin fasaha ga mawaƙi kuma kan haifar da satar waƙa. A ɓangare ɗaya kuma, kyakkyawar zamantakewa da mu’amalantar juna cikin girmamawa da aminci ita ce takan haifar da zumunta a tsakanin mawaƙa. Hakan kuma shi ne yake jawowa sukan yi amfani da wasu kalmomi da suka fito a waƙoƙin junansu domin ƙulla tasu waƙar. Don haka, wannan bincike yake ganin kasancewar mawaƙan nahiya ɗaya da dacewar ra’ayi da kuma ta sana’a su ne suka haɗu suka samar da zumuntar mawaƙa. Don haka ba abin mamaki ba ne idan an samu zumuntar waƙa a tsakanin Sa’idu Faru da mawaƙan fada takwarorinsa, musamman ta fuskar tubalan da ake gina waƙoƙin fada da su waɗanda suka haɗa da: Yabo da zuga da kuma roƙo.

Manazarta

Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Limited.

Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Al-Ibrash Publication Plc.

C.N.H.N. (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph.

Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa. Edinburgh: Edinburgh University Presss Limited.

Gusau, S. M. (2005). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano: Benchmark Publishers.

Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kaduna: FISBAS Media Services.

Gusau, S. M. (2002). Sarkin Taushi Salihu Jankiɗi. Kaduna: Baraka Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da
 Sigoginsu.
Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka Zaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Ibrahim, M. S. (2003). Kowa ya sha kiɗa (Abokin Hira na 2). Lagos: Longman Nigeria Plc.

Kafin-Hausa, A. U. (2002). Koma-baya a Waƙoƙin Hausa: Waƙoƙin Sarauta. Cikin Bichi, A. Y. Da wasu. Studies in Hausa Language, Literature and Culture the Fith Hausa International Conference Pp.241-255. Centre for the Study of Nigerian Languges, Bayero Uniersity, Kano. Kano: Benchmark Publishers.

Muhammad, D. (1980). Zumunta Tsakanin Marubuta Waƙoƙin Hausa da Makaɗa. Cikin Yahaya, I. Y. da wasu (editoci) Harsunan Nijeriya na X Pp. 85-102. Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano.

Muhammad, M.S. (1997). Zumuncin Bahaushe. Kudin Digiri na Ɗaya (B.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo.

Tsoho, M. Y. (2004). Waƙeƙeniya Ko Yaƙeƙeniya: Nazari Kan Yaƙi da Waƙa a Waƙoƙin Baka. Harshe Journal of African languages, Vol. 2 Pp.86-99. Department of Nigerian and African Languages, Ahmadu Bello University, Zaria. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Yahya, A. B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Service.

 

Yahya, A. B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas Service.

 

Waƙoƙi da Abubuwan da Aka Saurara

1.      Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

2.      Waƙoƙin Makaɗa Salihu Jankiɗi.

3.      Waƙoƙin Makaɗa (Dr.) Ibrahin Narambaɗa.

4.      Waƙoƙin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo.

5.      Waƙoƙin Amadu Mailauni Bakura

6.      Waƙoƙin Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo.

7.      Waƙoƙin Abdu Nabiddigau Maigambara.

8.      Sauraren Hirar da Rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN, Kaduna) ta yi da Alhaji Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji a kan Tarihin Rayuwar Makaɗa Sa’idu Faru a shekarar 2019.



[1] Makaɗa Abdu Naburdugau mai gambara yana cewa:

Jagora: Sarkin noman gari shi da maƙerin gari,

Wanzamin gari, wa za ya raba su?

[2] Domin ƙarin bayani, a dubi Muhammd, D. (1980), Zumunta Tsakanin Marubuta Waƙoƙin Hausa da Makaɗa. Cikin Harsunanan Nijeriya na X , Jami’ar Bayero, Kano. Maƙalar ta fito da zumuntar da ke tsakanin marubuta waƙoƙi da makaɗa, inda aka kawo misalai daga waƙoƙi 30 waɗanda wasu mawallafa 12 suka ari kari daga makaɗan baka. Maƙalar ta nuna cewa, ba da karin Larabci kaɗai Mawallafa suke tsara waƙoƙinsu ba, suna arowa daga makaɗan baka.

[3] Hira da Alhaji Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji a Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN Kaduna) a shekarar 2019.

[4] Yanzu (2024) garin Faru yana ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Mulki ta Maradun da ke jihar Zamfara.

[5] Abin sassaƙar turmi, (CHNH, 2006:168).

[6] Don neman ƙarin bayani a dubi, Bunza, A. M. (2009:171), Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre.

[7] Wannan takarda ta sani akwai manyan malamai da suke ta wannan ƙoƙari, amma dai muna roƙonsu da suka ƙara ƙaimi wajen wannan aiki nasu, saboda kada wuta ta mutu a hannunmu.

Sa'idu Faru

Post a Comment

0 Comments