Citation: Bunza, D.B. & Mafara, S.Y. (2024). Yanayin Tubalin Roƙo A Wasu Waƙoƙin Sarauta Na Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 142-149. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.019.
YANAYIN TUBALIN ROƘO A WASU WAƘOƘIN SARAUTA NA MAKAƊA SA’IDU FARU
Na
Dano Balarabe Bunza,
(Ph. D)
Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
Email: danobunza@gmail.com
Lambar Waya:
07035141980
Da
Dr. Sani Yahaya
Mafara
Abdu Gusau
Polytechnic, Talata Mafara, Zamfara State
Email: saniroro114@gmail.com
Phone numbers: 08065240341, 07012184370
Tsakure
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da
yanayin tubalin roƙo a zubin ɗiyan wasu waƙoƙin marigayi Sa’idu
Faru na sarauta. An yi amfani da wasu dabaru a lokacin gudanar da wannan
bincike da suka haɗa da neman waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru da
nazarin su domin ganin haƙar ta cim ma ruwa. Ba
tare da samun waƙoƙin ba, babu dabarar
da za ta amfani wannan bincike. Biye ga dabarar neman waƙoƙin Sa’idu Faru na
fada da nazarin su domin fito da tubalin roƙo daga gare su, sai
neman ayyukan da aka yi a kan makaɗin ko da ya yiwu a yi tsintuwar guru
cikin suɗi, duk da yake ba a
sami ganin aikin da aka yi mai kama ɗaya da wannan ba. Wata dabara da aka
yi amfani da ita da ta taimaka don gudanar da wannan bincike ita ce dabarar yin
hira da wasu masana wannan fannin adabin baka da ya shafi waƙoƙin bakan Hausa. Haka
kuma an leƙa rubuce-rubucen wasu masana da za su taimaka
wa wannan bincike. An yi amfani da hanyar nazarin waƙoƙin baka ta Farfesa
Sa’idu Muhammad Gusau domin ta zama hanyar da aka yi koyi da ita a wajen
gudanar da wannanaikin bincike. Haƙa ta cim ma ruwa a
inda aka sami tubalin roƙon wasu abubuwa
daban-daban a cikin waƙoƙin Sa’idu Faru na
sarauta kamar yadda binciken ya nuna.
1.0 Gabatarwa
Roƙo yana ɗaya daga cikin ƙananan tubalin ginin turke a waƙoƙin baka na sarauta da masana suka tabbatar da samuwarsa
jefi-jefi a cikin waƙoƙin makaɗan fada. Kowane makaɗi na karɓa sunan maroƙi, domin tun a zamanin dauri idan aka ce maroƙi ko makaɗi, abu ɗaya ake nufi. Makaɗi ba ya roƙo sai a cikin waƙa, kamar yadda ba ya
godiya ga kyautar da aka yi masa sai a cikin waƙa, domin yin roƙon da godiya ga
kyautar da aka yi masa a cikin waƙa ya fi sauri da sauƙin isar da saƙo yadda ake buƙata. Jin roƙon da godiya ga wanda ya bayar da kyauta a cikin waƙa ya fi ɗaga darajar maroƙin a idon wanda ya
bayar da kyauta fiye da wadda zai yi masa tsakaninsu da juna. Wannan kuma ya
faru ne, saboda ba domin Allah aka yi kautar ba, sai don gudun faɗuwar girma da habaici
ko zambo daga idon maroƙin da kuma buƙatar duniya ta ji
wane mai kyauta ne a ɓangaren mai ba da kyautar. Makaɗa na amfani da damar
da suka samu a lokacin da suke yin waƙa su cusa buƙatunsu zuwa ga wanda suke yi wa waƙa ko masoyansa. Sukan yi amfani da dabaru daban-daban a
cikin waƙoƙin da suke yi na sarauta domin kai ƙoƙon baransu ga wanda suka ƙuduri yin hakan. Dabarun da suke amfani da su sun haɗa da roƙo kai tsaye da nuni zuwa ga abin da suke buƙata da zugar roƙo da kuma godiya
gabanin kyauta (Bunza, 2009: 123-127). Al’adar makaɗan fada ce su yi roƙo tare da cusa roƙon a cikin wasu waƙoƙinsu da suke yi wa ubannen gidajensu da masoyan masu
gidajensu.
1.1 Taƙaitaccen Tarihin
Alhaji Sa’idu Faru
An haifi Sa’idu a garin Faru a shekarar 1932 (cikin Makaɗa da Mawaƙan Hausa na Gusau, shafi na 117). A wata majiya kuma,
cewa aka yi an haife shi a shekarar 1916 a wata hira da aka yi da ɗansa kuma halifansa a
shekarar 1981, a garin Faru cikin ƙaramar hukumar mulkin Talata Mafara, yanzu kuma, ƙaramar hukumar mulkin Maradun tajihar Zamfara. Sunan
mahaifinsa Abubakar, sunan kakansa Abdu, sannan kama-kunnen makaɗa Alu mai kurya ne. Mahaifiyarsa mutunmiyar garin Bang
ace ta ƙaramar hukumar ƙaura Namodar jihar Zamfara.
A taƙaice, Sa’idu ɗan jihar Zamfarane gaba da baya bayan rabuwa da tsohuwar
jihar Sakkwato.
Sa’idu na da laƙabi bayan sunansa na
yanka, da ake ce masa Ɗan’umma. Ya sami laƙabin a sanadiyyar kiran da yake yi wa matar ƙanen mahaifinsa da suna Umma. Ita kuma, ba ta kiran
sunansa, sai ta ci gaba da kiran sa Ɗan’umma. Sannu a
hankali laƙabin ya bi Sa’idu, sai dai laƙabin bai yi fice a cikin gari sosai ba.
Dangane da ƙuruciyarsa, ya fara zama a garin Banga inda mahaifiyarsa
ta fito, amma baan ya fara girma sai ya komo wurin mahaifinsa ya ci gaba da bin
sa a waurin kiɗa. Bayan ya kai shekara goma sha biyar sai ya fara shiga
cikin amshi ana yi tare da shi. A lokacin ƙuruciyarsa bai yi
karatun book ba, sai dai ya taɓa na Muhammadiya gwargwado inda ya sauke ƙur’ani mai girma. Haka kuma, bai sami karatun littattafan
addini ba, irin Ƙawa’di da Ahalari da sauransu. Ra’ayin waƙa ya ɗauke masa hankali, kuma shi a tauye shi daga yin karatun
boko da na Arabiyya mai yawa.
Bayan laƙabinsa, yana da kirarin da yake yi wa kansa da ‘Ɗan’umma Rungumi, Ɗantumba Rungumi. A ɓangaren iyali kuma,
Sa’idu ya auri mata uku, sannan ya haifi ‘ya’ya ishirin da shida da su, kuma
yana da jikoki ishirin. Cikin ikon Allah ‘ya’yansa goma sha ɗaya sun riga mu gidan
gaskiya kafin rasuwarsa. Sa’idu ya ƙara yi wa kansa
kirari a cikin wani ɗan waƙa inda ya ce:
“Sa’idu malamin waƙa, mai kwana ɗumi,
Na Mamman da Balaraba”.
Bayan haka akwai wurin da makaɗin ya lissafo duk
wanda ke cikin ƙungiyarsa ta waƙa inda ya ce:
Mu’azu: ɗantumba marafan kiɗi,
ɗandaudu
ad daudun kiɗi,
Muhammadu Makaman kiɗi,
Ga Shehu Ciroman kiɗi,
Ga shi nan kuma ga Sarkin Fada mun yi layi,
Yaran Sa’idu Faru na mu,
Waƙa ɗai mukai kama’ an aza
gargare,
A kai a kama zak kyau,
In don kwaramniya ba fasali ba ne.
A nan Mu’azu ya kawo sunayensu a matsayin yaran Sa’idu
Faru su biyar kamar yadda aka ga ya kawo sunayensu da matsayin kowannensu a
cikin ɗan waƙar da aka kawo a sama. Har yanzu makaɗin ya kawo sunayensu
su shida kamar haka:
Jagora: …………………………………,
Barwa mu shidda muna game,
Sarkin makaɗanmu shina gaba,
Duk kowane tashi ƙawa daban,
Yac ce man nai ƙaton ciki,
Kowag ga shi zaune ga innuwa,
Yai taiɓa yai ƙaton ciki,
Yara: Ko da makaɗin Sarkin Masar,
Yag ga Sa’idu sai rainai yai haki.
Bayan haka kuma, Sa’idu Faru ya tsaya wurin Sarkin Kudu
tun ranar da suka haɗu a matsayin shi ne ubangidansa ba wani ba. Ya nuna haka
a cikin wani ɗan waƙarsa kamar haka:
Sa’idu malamin waƙa mai kwana ɗumi,
Na Mamman da Balaraba,
Ban wuce gonata da irina ba,
Inda Sarkin Kudu nits tsaya ɗ2.
A cikin ɗan waƙar akwai nuna ƙana’a da makaɗa Sa’idu ke da a
rayuwarsa kan nuna ba ya da ubangida bayan Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo tun ranar da Allah
ya haɗa su. A nan aka tsaya dangane da kawo taƙaitaccen tarihin Makaɗa Sa’idu Faru a cikin
wannan maƙalar da aka shirya kan “Turken Roƙo a Cikin Waƙoƙin Sarauta na Sa’idu Faru”.
2.0
Tubalin
Roƙo a Wasu Zubin Ɗiyan Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
A cikin wannan muƙala za a farauto tubalin roƙo a cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru da kuma tantance fuskokin da ya yi amfani da su a lokacin
da yake roƙon a cikin waƙoƙinsa na sarauta. Hakan zai bayyana tare da tabbatar da yaƙini a lokacin da aka tsunduma a cikin bayani ta
hanyar kawo misalan ɗiyan waƙoƙin da suka dace da batutuwan da aka kawo. Ga bayani tare da misalan ɗiyan waƙa da suka danganci fito da tubalin
roƙo ta fuskokin da za a kawo kamar haka:
2.1 Roƙo a Bayyane
Wannan roƙo shi ne yanayin da makaɗi ko mawaaƙi ko maroƙi ke fitowa fili ba tare da sakaya buƙatarsa ba, ya faɗe ta a bayyane zuwa ga wanda yake roƙo. A cikin waƙoƙin sarauta, maroƙi ko makaɗi kan fito fili ya faɗa wa sarkinsa ko
maigidansa buƙatarsa dangane da abin da yake son a yi masa ko a ba shi.
A nan mai roƙo zai faɗi sunan abin da yake so a ba shi kamar abin hawa ko kuɗi ko kujerar haji da
sauransu. A nan babu wani laɓe-laɓe, makaɗi kan fito wuƙa zage ya faɗa wa wanda ake roƙo abin da ake roƙon sa. Ga misali kaɗan kafin a kai wurin
fashin baƙin roƙo a cikin waƙoƙin fada:
Jagora:
Na yi biɗam mota ga Wakili,
‘Y/Amshi: Albarkam Muhamman Sarkin Kudu.
2.2 Roƙo a Fakaice
Wannan nau’in roƙo kuwa, ya saɓa da wanda aka yi bayania sama. A nan, makaɗi kan sakaya lokacin
da yake gabatar da buƙatarsa ga maigidansa. A nan ne wanda bai kula sosai ba
kan rasa fahimtar abin da maroƙi ke nufi, wani lokaci ma sai an bayyana masa abin da
makaɗi ke nufi. Ga misalin nau’in wannan roƙo a cikin wata waƙa kamar haka:
: Na yi mafalki nai salla Makka nai ɗawafi,
: Kuma na rungumo siyabi da bagaruwa da
tasbahohi,
: An ce mini Alhaji baital fasalin kiɗi,
: Manzon Sarki wanga mahwalki in Allah ya
nuhwa,
: A shirya shi ya zan haka,
…………………………..
Idan aka kula sosai a nan, makaɗin na roƙon kujerar haji ne a fakaice ba kai tsaye. Ana iya cewa
roƙo a fakaice, roƙo ne da ake amfani da
dabarar ɓoye manufa sai an natsu sosai ake fahimtar abin da makaɗi ke nufi. Duk wanda
yake bamin harshe ba ya iya tantance abin da makaɗi ke nufi a wurin da
ya aika saƙonsa a fakaice/ɓoye. Idan aka lura da ɗan waƙar da ke sama mai ɗauke da roƙo a fakaice, wani zai zaci makaɗain na bayyana wa
jama’a wani mafarki da ya yi ne a daren da ya gabaci ranar da ya yi wannan waƙa. Wurin da roƙon yake shi ne:
: Manzon Sarki wanga mahwalki in Allah ya
nuhwa,
: A shirya shi ya zan haka,
…………………………..
Abin da makaɗin ke nufi da wannan zance shi ne, idan Allah ya sa akwai
rabo yana roƙon a biya masa kuɗin kujera domin ya je ya sauke farali. Ba kowa ke ia
fahimtar maganar makaɗa da haka ba, shi ya sanya aka kira wannan roƙo da suna roƙo a fakaice ko ɓoye, mai nufin makaɗin bai fito fili ya faɗi buƙatarsa kai tsaye zuwa ga sarki ba. Mai yiwuwa ne sarki ma
ya rasa ahama da abin da makaɗin ke nufi, sai an ƙara fayyace masa.
2.0 Tubalin Roƙon Wasu Abubuwa a
Wasu Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru
Kowane makaɗi yakan yi amfani da tubalin roƙo a waƙoƙinsa, sai dai ba kowane maroƙi am makaɗi ba. A kan haka ne makaɗa Alhaji Sa’idu Faru
ya kira kansa maroƙi a cikinwani ɗan waƙa wurin da ya ce:
: Manyana ma’aikatan
gwamnati,
: Manyan ma’aikatan En
e,
: Almajirinku na an
nan,
: Nan bisa gare ku
Allah,
: Yash shirya muna
abinci,
: Na roƙe ku in da hali,
:…………………………..
A cikin ɗan waƙar da aka kawo a sama makaɗa Sa’idu Faru ya kira
kansa da bakinsa almajiri, mai nufin maroƙi. Sa’idu ya ƙara fitowa da abin da yake nufi da almajiri a inda ya faɗi cewa aikin makaɗi roƙo. Kalmar almajirinku da ya yi amfani da ita a sheɗara ta uku a cikin ɗan waƙar, ya bayyana abin da yake nufi da ita a sheɗara ta shida, duk dai
a cikin ɗan waƙar. Kalmar almajirinku da maroƙinku duk abu ɗaya suke nufi a cikin ɗan waƙar da Sa’idu ya kawo a sama. Haka kuma, alheri/kyauta ita
ke sa maroƙi ya yi waƙa. Abin da ke tabbatar da haka shi ne, wanda duk ke yi wa
maroƙi rowa ba zai sami yabo da godiya daga gare shi ba, sai
dai habaici da zambo tare da nuna ba ya ko buƙatar kyauta daga gare shi bale ya roƙe shi. Makaɗa Sa’idu Faru ya faɗi haka a cikin wani ɗan waƙarsa wurin da ya ce:
Jagora: Muhammadu dalilinka niz zo Talata,
‘Y/Amshi: Muhammadu dalilinka niz zamni
Hausa,
: Kwas san mu gidan ga nan anka san mu,
: Kuma ba mu wuce nan
ba nan munka dage,
: Ban zo gidan ɗanbita niy yi roƙo ba,
: Ko ya raba lafia ba
ruwana.
3.1 Roƙon Sutura
An yi bayani a sama cewa, makaɗa kan yi amfani da
wasu dabaru guda huɗu lokacin da suke neman sarki ko wani masoyinsa ya ba su
wani abu a lokacin da suke rabkar tafashensu. Haka kuma dabarun sun haɗa da roƙo kai tsaye da nune zuwa ga abin da ake so da zugar roƙo da kuma yin godiya gabanin kyauta. Makaɗa Sa’du Faru na ɗaya daga cikin makaɗan da suka yi amfani
da waɗannan dabaru a cikin waƙoƙin da suka rera na fada, domin yin roƙo ga ubangidansa ko masoyin ubangidansa. Ya yi amfani da
dabara ta kai tsaye a fagen roƙon suturs ga wanda ya roƙa. Ya yi irin wannan roƙo ga Sarkin Yaƙin Banga Alhaji Sule ƙaura Namoda lokacin da yake yi masa kiɗa. Ga abin da ya ce:
Jagora: ………………………
: Balantana Sale yau
kana sarki,
: Kwasau uban Zagi na Alu ko da,
: Zamanin kana ɗan sarki Cigari na
Amadu,
‘Y/Amshi: Na Garba ka bab barin muna ragga,
: Wai
has su ja ƙasa.
Jagora: Na Garba,
‘Y/Amshi: Ka bab barin muna ragga,
: Mu
dud da Rungumi.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Yaƙin Banga Alh. Sule ƙaura Namoda).
A cikin ɗiyan waƙar da ke sama ‘yan amshi suka yi maganar roƙon sutura, amma jagora ya ingiza su domin su faɗi maganar. Jagoran kiɗin ya jawo a faɗi wannan maganar roƙon sutura ga Sarkin Yaƙin Banga Alhaji Sule ƙaura Namoda. Jagoran waƙar ya nuna tun Sule na ɗan sarki yana yi musu
alheri bale yanzu da yake shi ne sarkin. Maganar mai harshen damo ce. Mai
yiwuwa makaɗa na nufin Sarkin Yaƙin Banga na ƙaura Namoda ba ya barin su da tsofaffin tufafi, mai nufin
yana ba su kyautar tufafi. A
ma’ana ta biyu kuma, mai yiwuwa roƙo ne suke yi da ya ba su suturar sanyawa ga jiki domin
nasu sun tsufa har sun fara yagewa. Ana sane da irin shigar da makɗi ke yi musamman a
lokacin gudanar da waƙa, ka ce sarki ne idan ba ka san shi ba. A kowace fuska
dai aka yi amfani da maganganun biyu, roƙon suturar sawa ne
suke yi. Haka kuma, a lokacin da makaɗa na kiɗa, maganar da ya faɗi da bakinsa da wadda ɗangaladimansa ya faɗa da wadda ‘yan amshi
suka faɗa, duk sun riga sun kitse tsakaninsu tun kafin a shigo
filin kiɗa. Duk wurin da aka sami kuskuren magana ɗaya daga cikinsu zai
shigo da gyara nan take domin nuna ba haka aka shiryo daga gida ba, kuma duk
lokacin da aka sami irin wannan dambarwa, akan yi amfani da kiɗa domin nuna an sami kuskure,
kamar yadda ya taɓa faruwa tsakanin Ibrahim Narambaɗa da yaransa inda ya
ce:
Jagora: Da a ce maka ɗan mai gona,
‘Yan Amshi: Da a ce maka ɗan mai taru,
: Gara a ce ma mai taru.
Ba tare da wata jayayya ba, sai Narambaɗa ya sake, kuma ya ce
musu ku riƙa haka nan. Hakan ya faru sanadiyyar
ba haka aka shiryo daga gida ba. Shi kuma da ya ahama, sai ya sake tasa magana
saboda ya tuna yadda aka shiryo maganar tun gida cewa ba ɗan mai gona aka
daddale a faɗa ba, ɗan mai taru aka tsaro maganar.
Ala ayyi halin dai, muhallish shahid dais hi ne a kawo
wurin da makaɗa ya roƙi suturar sawa ga wani sarkin da ya yi wa kiɗa, kuma an kawo. Ba
wannan kaɗai ba, ko faɗar tufafinmu sun tsufa da makaɗi ke yi zuwa ga wanda
yake yi wa kiɗa/waƙa, masana sun bayyana cewa roƙon sutura ne.
3.2 Roƙon Abin Hawa
Abin hawa a nan yana ɗaukar abubuwa da
dama. A wani wuri makaɗi na roƙon doki a matsayin abin hawa. Wani lokaci kuma, yakan faɗa da bakinsa cewa
mota yake roƙon a ba shi. A zamanin da, dawaki ake amfani da su domin
yin tafiye-tafiye daga wani wuri zuwa wani, musamman lokacin da babu mota ko
lokacin da take da ƙaranci. Akan yi amfani da dawaki domin zuwa yaƙi da sauran lalurori irin aika saƙonnin kar-ta-kwana da sauransu. Bayan an sami wadatar
mota da ganin bambancin da ke tsakanin mota da doki ta fuskar saurin biyan buƙata, sai aka rage anfani da dawaki face kaɗan, aka raja’a ga
ababen hawan Bature irin mota da babur da sauransu. Da wuyan gaske a ji makaɗi ya roƙi jirgin ƙasa bale na sama a cikin waƙarsa saboda ba abubuwan hawa ne kamar mota ba. Haka kuma,
ko waɗanda makaɗi ke yi wa waƙa ba su da jiragen
kansu bale mai roƙon su ya roƙa a ba shi. Lokacin da aka samu yalwar mota ma, makaɗa kan roƙe ta ga waɗanda suke yi wa kiɗa. Ga misalai da dama na ɗiyan waƙoƙin da aka tsinci makaɗa Sa’idu Faru ya roƙi abin hawa da suka haɗa da dawaki da motoci
baki ɗaya:
Jagora: Na
yi biɗam mota ga Marahwa,
‘Y/Amshi: Albarkam Muhamman Sarkin Kudu.
Jagora: Na
yi biɗam mota ga Marahwa,
‘Y/Amshi: Albarkam Muhamman ɗan Amadu.
Jagora:
Na yi biɗam mota ga Wakili,
‘Y/Amshi: Albarkam Muhamman Sarkin Kudu.
Jagora: Baba ya ba mu riga ta fan asshirin,
‘Y/Amshi: Baba ya ba mu riga ta fan arba’in
daidai,
: Baba
saura mota na Attahiru,
: In ji
injin shina canza waƙoƙi
Makaɗa Sa’idu Faru ya roƙi mota ga Marafa a
cikin ɗan waƙa na farko, kuma ya roƙi mota ga Wakili a cikin ɗa na biyu da aka
kawo. A cikin ɗan waƙa na uku da ke biye
ma, ya ƙara roƙon mota ga baba bayan ya faɗa cewa ya ba su
riguna na fam ishirin da kuma na fam arba’in. Makaɗin ya yi amfani da kalmar
biɗa wadda ke nufin roƙo a cikin ɗiyan waƙar. Makaɗin ya ci gaba da roƙon abin hawa ga wasu
kamar haka:
Jagora: Ko ni makaɗinka Uban Zagi,
‘Yan Amshi: Na gaji a ba mu dawakuna,
: Na gaji a ba mu jukunkuna,
Jagora: Albarkar Nana uwad Daji,
Ba mu
doki Muhamman Sarkin Kudu.
Jagora: Bisa albarkar Sarkin Kudu,
‘Y/Amshi: Su wane ana miƙa muna,
Jagora: Bisa albarkar ɗan Amadu,
‘Y/Amshi: Su wane ana miƙa muna,
: Amma wane huskash shanu yakai,
:
Macciɗo roƙon doki niz zaka,
: Kai bari na ci iyakar gargare,
: Mai
roƙon doki don sukuwa,
: In an
ba shi mota karɓa yakai,
: Mai
roƙon riga ‘yar Bidda,
: In an
ba shi kore karɓa yakai.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo)
Wurin da ya ce “Ba mu doki Muhamman Sarkin Kudu” roƙo ne yake yi. Daga nan sai makaɗin ya ci gaba da
neman a ba shi abin hawa ta amfani da kalmar roƙo ƙarara, inda ya ce “Macciɗo roƙon doki niz zaka’. Ya nuna ya roƙi dokin domin yin sukuwa, tare da haka idan aka ba shi
mota a madadin dokin da ya roƙa, ya ce amsa zai yi. Haka kuma ya ce mai roƙon riga ‘yar Bida idan aka ba shi wadda ba ita ba, zai
karɓa. Wannan na nuna makaɗi kan roƙi abin da yake son a ba shi, amma kuma duk abin da aka ba
shi ba mayarwa yake yi ba. A cikin ɗan waƙa mai zuwa kuma, mota makaɗin ya roƙa kamar haka:
Jagora: Sai ka yi man mota,
‘/Amshi: Duk lardin ƙasag ga mu an ba mu mota.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Fulanin Bunguɗu Alhaji Shehu).
Makaɗa sa’idu Faru ya kai ƙoƙon baransa wajen Sarkin Fulanin Bunguɗu inda ya ce sarkin
ya yi mai mota, wato ya ba shi kyautar mota, su kuma ‘yan amshi suka faɗa cewa duk lardin ƙasar ga an ba su mota. Wannan na nuna cewa Sarkin Fulani
kaɗai ya rage ya ba su mota domin an ba su motoci ko’ina a
lardin ƙasar Hausa. Dangane da roƙon abin hawa ke nan da aka tsinta a cikin waƙoƙin Sa’idu Faru na sarauta.
3.3 Roƙon Kuɗi
Akan yi wa kuɗi kirari da masu gida rana. Mawuyacin abu ne a sami kuɗi ana zaune cikin
inuwa. Haka kuma, a duniyar wannan zamani da kuɗi ake gudanar da mafi
yawan lalurorin rayuwar yau da kullum. Sanin haka ya sanya makaɗa Sa’idu Faru amfani
da wannan dama ya roƙi Turakin Kano kuɗi kyauta domin ya je aikin haji. Ga ɗan waƙar da roƙon kuɗi ya fito a cikinsa kamar haka:
Mu’azu: Amadu mai cika ni aza ni ka ba ni kuɗi in tai haji,
‘Y/Amshi: In hawo bisa marsandi ina rabkak kiɗi,
:……………………………………..
(Sa’idu Faru: Waƙar Turakin Kano Alhaji Amadu).
Makaɗa Sa’idu Faru yaroƙi kuɗi ga Turakin Kano
domin ya je aikin haji a cikin ɗan waƙar da ke sama, kuma ya nuna idan aka ba shi kuɗin da ya roƙa, zai hawo mota marsandi, yana tafia ana rabkar kiɗi. Abin sani a nan
shi ne, ko makaɗa Sa’idu Faru ya sami kuɗin ko bai samu ba,
wurin da roƙo ya fito a cikin waƙoƙinsa na sarauta ake nema, kuma an samu. Haka kuma, a
wannan wuri kaɗai aka sami ganin inda makaɗin ya roƙi a ba shi kuɗi kai tsaye. Ba an ce
nan kaɗai ba ne, a’a.
3.4 Roƙon Kujerar Hajji
Aikin haji na ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar da aka
sami bayaninsu acikin shari’ar Musulunci. An sharɗanta wa kowane
musulmi zuwa aikin hajji sau ɗaya a rayuwarsa idan
ya sami hali. Idan kuma Allah bai ba shi hali ba, an ɗauke masa. Haka aikin
hajji yake kamar fitar da
zakka. Mai dukiya ke fitar da zakka domin sai an mallaki abin bayarwa ake
bayarwa. Daga cikin abubuwan da makaɗa Sa’idu Faru ya roƙa a cikinwaƙoƙinsa da ya yi na sarauta akwai roƙon kujerar haji. A nan, ba kansa kaɗai ya roƙa ma kujerar hajin ba, har da yaransa. A cikin roƙon, Sa’idu ya ba da sharaɗin cewa, idan da
hali. Ke nan, idan ba hali, bai aza musu ba. A cikin roƙon har nuna ya yi cewa ya yi mafarki yai salla a garin
Makka har da ɗawafi tare da rungumo tufafi da bagaruwar Makka da
tazbahohin yin salati har ana kiran sa alhaji. A kan haka ne ya yi wa manzon
Sarki saƙo zuwa ga sarki cewa yana buƙatar wannan mafarki da ya yi, mayar masa da shi a farke
ta hanyar biya musu kuɗin kujerar haji domin mafarkin ya kasance gaskiya. Ga
abin da ya ce a cikin ɗan waƙa na ƙasa:
Jagora: Manyan ma’aikatan gwamnati,
: Manyan ma’aikatan N.A.,
: Almajirinku na an nan,
: Nan bisa gare ku,
: Allah Yash shirya muna abinci,
: Na
roƙe ku in da hali,
: Don
shirya muna kujera,
: Ta mu je haji,
: Na yi
mafalki nai salla Makka,
: Nai ɗawafi,
: Kuma
na rungumo siyabi da bagaruwa da tasbahohi,
: An ce
mini Alhaji baital fasalin kiɗi,
:
Manzon Sarki wanga mahwalki in Allah ya nuhwa,
: A
shirya shi ya zan haka,
: Wanga
mahwalki in Allah ya nuhwa,
: A shirya
shi ya zan haka ɗ2,
: Allah
ya nuhe ni Sa’idu mu tai Makka,
: Ni da
baba Alhaji Macciɗo ɗ2.
Babu shakka Sa’idu ya buƙaci a biya masa kujerar hajji tare da yaransa duka. Ya ƙara nuna buƙatar yana son ya je aikin haji tare da ubangidansa Sarkin
Musulmi Muhammadu Macciɗo, har da maimaita faɗin maganar saboda
muhimmancinta gare shi, da kuma tsananin kwaɗayin a biya masa kuɗin kujerar Makka.
3.5 Roƙon Muƙamin Sarauta/Mulki
Mafi yawan mutane na da sha’awa ga sha’anin mulki ko da
ba ‘yan sarauta ba ne. Makaɗa Sa’idu Faru babban misali ne kuma sheda ga wannan zance
da aka faɗa. Ba ɗan sarauta ba ne, amma ya nuna sha’awarsa ga sha’anin
mulki a inda aka sami ya roƙi ubangidansa Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo a ba shi matsayin
sarauta idan Allah ya ba shi matsayin Sarkin Musulmi, ko da na wani gari ne ko ƙauye. Ga abin da ya ce lokacin da yake roƙon muƙamin sarauta a wurin ubangidansa:
Jagora: Ko ni makaɗinka uban Zagi,
‘Yan Amshi: Na gaji a ba mu dawakuna,
: Na gaji a ba mu jukunkuna,
: Na gaji a ba mu garuruwa,
: Muhammadu in Allah yai nuhi,
: Ba
mu gari da mutanenai duka.
A cikin ɗan waƙar da Sa’idu Faru ya kawo ya nuna cewa ya yi gadon roƙo domin ya gadi a ba su dawaki da kuɗi da kuma mulkin wasu
garuruwa. Saboda wannan ne ya roƙi Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo cewa idan Allah ya
cika masa gurin zama Sarkin Musulmi, to shi ma ya roƙa a sami garin da aka ba shi waƙilcin mulkinsa, domin a dama da shi.
A nan aka kawo ƙarshen wannan bincike
mai taken ‘Turken Roƙo a Cikin Waƙoƙin Sarauta na Sa’idu Faru’, kuma an gar oƙon da abubuwan da makaɗin ya roƙa a bayyane ba tare da ɓoyon komai ba.
4.0 Sakamakon Bincike
Binciken da aka yi a kan roƙo a cikin waƙoƙin Sa’idu Faru na Sarauta ya gano abubuwa da dama. Da
farko dai binciken ya gano Sa’idu ɗan gado ne a cikin sha’anin waƙa ba ɗan haye ba. A ɗan tarihin da aka kawo na makaɗa Sa’idu, an nuna
mahaifinsa da kakansa duk makaɗa ne. Ke nan, ba abin mamaki ba ne domin an sami ɗan gado ya yi abin da
ya gada, Haka kuma, an gano cewa, tun lokacin da Sa’idu ya haɗu da Sarkin Kudu
Macciɗo kafin ya zama Sarkin Musulmi, bai taɓa zama ƙarƙashin wani basarake ba face shi. Haka kuma, Sa’idu makaɗin sarakuna/fada ne
kuma makaɗin kotso domin shi ya tarar ana kaɗawa a gidansu. Haka
kuma, Sa’idu na da laƙabin da matar ƙanen mahaifinsa ta
sanya masa, duk da yake laƙabin bai bi gari ba (ba a san shi sosai ba). Binciken ya
gano Sa’idu na da kirarin da yake yi wa kansa, har jama’a suka san shi da shi,
suka ci gaba da yi. Haka kuma, binciken ya gano cewa tun ranar da ya haɗu da Sarkin Kudu
Muhammadu Macciɗo, bai koma yi wa kowane sarki waƙa ba da sunan shi ne ubangidansa, kamar yadda aka gani a
cikin taƙaitaccen tarihinsa. Ba wannan kaɗai ba, binciken ya
gano cewa makaɗa Sa’idu Faru fasihi ne fa fagen waƙar baka, kuma ya share shekaru da dama yana waƙoƙin fada. Bayan waɗannan abubuwa da binciken ya hango, akwai matsala kan
shekarar haihuwar makaɗa Sa’idu Faru domin a wani wuri 1932 aka rubuta. A wani
wuri na daban kuma, 1916 aka ce an haife shi. Dangane da wannan sai a sama muna
(mu ɗalibai) mafita dangane da shekarar da makaɗa Sa’idu Faru ya zo
duniya. Haka kuma binciken ya gano cewa babu mishkila a kan shekarar da makaɗin ya bar duniya,
wato 1987.
Binciken ya gano akwai wurare da dama a cikin wasu waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru da ya kai ƙoƙon baransa ga ubangidansa (Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo) da wasu sarakunan
da ya yi wa waƙa. An sami ɗiyan waƙa da dama da ke ɗauke da roƙo a cikin waƙoƙin da Sa’idu Faru ya yi wa wasu masu riƙe da muƙamin sarauta ko ‘ya’yan sarauta da sauran irinsu. Ya roƙi abubuwa daban-daban ga waɗanda ya yi wa waƙa da suka haɗa da sutura da kuɗi da kujerar haji da abubuwan hawa da suka haɗa da doki da mota da
sauransu. Maroƙi kan sami biyan buƙatar wasu abubuwa da
ya roƙa daga waɗanda ya roƙa, wasu kuma ya jira, ko ya samu ko kuma a haƙura har wani lokaci idan da rabon samu. Waɗannan abubuwa ne
binciken ya hango a cikin wasu waƙoƙin Sa’idu Faru, kuma ya ƙuduri aniyar tsamo wasu daga cikinsu domin a yi wa mai
karatu susa gurbin ƙaiƙayi ta fuskar kawo wurin da makaɗa ya yi roƙon da abin da ya roƙa da kuma wanda aka
roƙa.
3.0 Kammalawa
An fara binciken da gabatarwa inda aka yi bayanin
abubuwan da takardar za ta ƙunsa da bayanin dabarun binciken da aka yi amfani da su
domin ganin binciken ya kamala cikin nasara. Haka ma an bayyana muhimmancin
binciken a daidai wannan lokaci. Biye da su kuma, an kawo ire-iren roƙo da suka haɗa da roƙo kai tsaye da roƙo a fakaice. Taƙaitaccen tarihin makaɗa Sa’idu Faru ya biyo
bayan ire-iren roƙo. Daga nan sai taken maƙalar da aka yi bincike a kansa, wato ‘Turken Roƙo a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru na Sarauta’. A ƙarƙashinsa an sami roƙon abubuwa
daban-daban da Sa’idu ya gabatar zuwa ga waɗanda ya roƙa da suka haɗa da roƙon sutura da abin hawa da kuɗI da kujerar haji da
kuma muƙamin sarauta/mulki. A ƙarshe aka kawo sakamakon bincike dangane da abin da
binciken ya hango.
Manazarta
Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation.
Bargery, G. P. (1933). Hausa-English
Dictionary and English- Hausa Vocabulary. London: Oxford University
Press.
Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic
Publications Centre.
CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa Kano. Kano: Cibiyar Nazarin
Harsunan Nijeriya.
Ɗangambo, A. (1989). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph...
Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Zaria: Amana Publishers Ltd.
Gusau, S. M. (1996). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kaduna: Fisbas Media Service.
Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka A ƙasar Hausa. Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin
Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers
Limited.
Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited Nigeria.
Skinner, N. (1980). An Anthology of Hausa Literature. Zaria: N.N.P.C.
Yahya, A.B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Service.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.