Citation: Mafara, S.Y. & Bunza, D.B. (2024). Dabbobi Da Ƙwari Da Tsuntsaye a Wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 150-162. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.020.
DABBOBI DA ƘWARI DA TSUNTSAYE A
WASU WAƘOƘIN SA’IDU FARU
NA
Dr. Sani Yahaya Mafara
Abdu Gusau Polytechnic
Talata Mafara, Zamfara State
Email: saniroro114@gmail.com
Phone numbers: 08065240341, 07012184370
Da
Dano
Balarabe Bunza, (Ph. D)
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato
Email: danobunza@gmail.com
Lambar Waya:
07035141980
Tsakure
Waƙa babban tafarki ce
na bayyana falsafar mawaƙa wajen ilmantarwa a
fannin adabi da sauran fannonin ilimi. Ana kuma iya kallom saƙonnin da ke ƙunshe a cikin waƙoƙi ta fuskoki da dama.
Wannan bincike ya yi bayani ne a kan dabbobi da ƙwari da kuma
tsuntsayen da makaɗa Sa’idu Faru ya
ambata a cikin waƙoƙinsa, inda ya yi
amfani ne da su domin ya fito da wasu halaye na waɗanda yake yi wa waƙa, ta hanyar nuna
zaruntaka ko ƙwazo ko kasawa ko yaba masu ta ɓangarori daban-daban
na rayuwa, ko amanarsu ko adalcinsu da sauransu. Manufar wannan bincike ita ce
fito da dabbobi da tsuntsaye da kuma ƙwarin da makaɗa Sa’idu faru ya
ambata a cikin waƙoƙinsa. Sai kuma fito
da muhimancin dabbobi da ƙwari da tsuntsaye ga
Bahaushe wajen gina adabinsa, don faɗaɗa ilimi da kuma raya
adabin Hausa. Binciken ya gano cewa lura ita ce mizanin gano duk wata ɗabi’a ko wani hali na
duk wata halitta. Da shi ne mawaƙan suka yi amfani
suka gano halaye da ɗabi’un dabbbobi da ƙwari da tsuntsaye har
suka fara bayyana su a cikin waƙoƙin.
Gabatarwa
Wannan maƙala za ta yi nazarin dabbobi da ƙwari da tsuntsayen da makaɗa Sa’idu Faru ya ambata a cikin waƙoƙinsa na yau da kullum. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su ne domin ya fito da
halaye mabambanta na Sarakuna da ‘ya’yansu da fadawa da masu jiran gado da
makusanta ga sarakuna da sauransu. Daga cikin halayen akwai jaruntaka ko kwaɗayi ko tsoro ko kyauta ko rowa ko rinjaye da sauransu,
domin yi masu zambo ko habaici da sauransu. A cikin takardar an kawo taƙitaccen tarihin makaɗa Sa’idu faru. An
kuma yi bayanin muhimmancin wannan maƙalar da kuma dabarun
da aka bi wajen samo bayanan da aka yi amfani da su wajen gabatar da wannan maƙalar. Bayan wannan
kuma sai aka fito da dabbobi da ƙwari da tsuntsayen da
Makaɗa Sa’idu Faru yi
amfani da su wajen dabbantar da waɗanda yake yi wa waƙa, in da aka bayar da
misalai da waƙoƙinsa daban-daban. Daga nan kuma sai aka yi bayanin
sakamakon bincike da kuma kammalawa. Daga ƙarshe aka bayyana
tushen bayanin da aka gabatar sannan sai ratayen hotunan wasu dabbobi da ƙwari da tsuntsayen da
makaɗa ya ambata a cikin
waƙoƙinsa.
Takaitaccen
Tarihin Rayuwar Marigayi makaɗa Sa’idu Faru
An haifi makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru ta cikin ƙasar Maradun, ƙaramar hukumar Talata Mafara a wajajen
shekara ta 1932.
Gusau, (2010 117). Sunan mahaifinsa Makaɗa Abubakar ɗan
Audu, mutumin Faru ne. Sunan kakansa Alu mai kurya. Dukkan waɗannan makaɗan an
yi su ne a garin Faru. Mahaifiyarsa mutumiyar Banga ta cikin ƙasar Ƙauran Namoda ce, kuma a can ne aka haife ta. Yawancin ƙuruciyar Sa’idu Faru ya yi ta a garin
Banga ta Ƙauran
Namoda inda aka haifi uwarsa, amma kafin ya girma ƙwarai sai ya koma wajen tsohonsa makaɗa Abubakar a Faru. Sa’idu Faru kamar sauran makaɗan fada, ya yi gadon kiɗa a wajen mahaifinsa da kakansa. Sa’idu na da laƙabi bayan sunansa na
yanka, da ake ce masa Ɗan’umma. Ya sami laƙabin a sanadiyyar
kiran da yake yi wa matar ƙanen mahaifinsa da suna Umma. Ita
kuma, ba ta kiran sunansa, sai ta ci gaba da kiran sa Ɗan’umma. Sannu a
hankali laƙabin ya bi Sa’idu, sai dai laƙabin bai yi fice a
cikin gari sosai ba.
Dabarun Bincike
An yi amfani da
dabaru daban-daban a lokacin gudanar da wannan bincike da suka haɗa da neman waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru da
nazarin su domin ganin haƙar da ake so a yi ta cim ma ruwa. An samu waƙoƙin ne ta hanyar
amfani da na’urorin ci gaban zamani, kamar su, faifan CD da kaset na rikoda da
saurarensu a kafofin sada zumunta na zauren Sa’idu Faru da zauren makaɗa da mawaƙan Hausa da zauren
Sa’idu Faru conference. Bayan tattara waƙoƙin da nazarinsu,
domin fito da sunayen dabbobi da ƙwari da kuma
tsuntsaye waɗanda makaɗa Sa’idu faru ya yi
amfani da su wajen yi wa mutane zambo da habaici a cikin waƙoƙinsa, sai kuma
nazarin ayyukan da aka gabatar masu kama da wannan kuma ba a samu wani aiki
wanda ya yi daidai da wannan ba. Bayan wannan an yi hira da masana adabin Hausa
da kuma makusanta ga mawaƙin domin fayyace abubuwan da suka shige wa mai nazari
duhu. Dukkan bincike ba zai rasa muhimmanci ba, don haka kowane binciken ilimi
mai muhimmanci ne ga al’umma duk yadda yake kaɗan. Wannan bincike na da muhimmanci ta
fuskoki da dama. Zai fito da rawar da makaɗa Sa’idu faru ya taka ta amfani da dabbobi da
ƙwari
da tsuntsaye wajen raya adabin Hausa, musamman ta ɓangaren waƙoƙi. Yana da muhimmanci
ga ɗalibai masu nazari
don su samu abin tuntuɓa da yin nazari,
musamman in an taskace shi. Yana da muhimmanci a fagagen adabi da kuma al’adar
zamantakewar Hausawa. Yana da muhimmanci ga masu nazarin rayuwar dabbobi da ƙwari da tsutsaye ta
zahiri. Yana da muhimmanci ga masu nazarin zamantakewar dabbobi da ƙwari da tsutsaye da
sauran halittu. Haka kuma zai zama ƙari a cikin rumbun
adabin baka na Hausa da gudummawa ga ilimi.
Yana da muhimmanci
domin zai samar da wani bayani wanda zai kasance kamar wata taska wadda ake
adana bayanan da suka shafi dabbobi da ƙwari, da tsuntsayen
da ke cikin waƙoƙin Sa’idu faru. A taƙaice, muhimmancin
wannan bincike shi ne ƙara wa juna ilimi dangane da waƙoƙin da Sa’idu faru ya
yi amfani dadabbobi da ƙwari da tsuntsaye wajen fito da halayen mutanen da yake
yi wa waƙa ta hanyar zambo ko habaici.
Ma’anar
Dabba
Ma’anar Dabba: Kalmar ‘dabbobi’
jam’i ne na kalmar ‘dabba’. Wannan kalma baƙuwa ce. An aro ta ne
daga harshen Larabci. Dabba na nufin duk abin da ke tafiya a saman ƙasa ko abin da ke da
yawan gashi. Misali, “Dabba wajhuhu, ma’ana: Fuskarsa ta yi gashi ko tsufa”, Ko
kuma a ce, “Dabba jis’muhu, ma’ana: “jikinsa ya tsufa ko ya yi gashi”. (ƙamusun Larabci mai
suna, Almu’ajamul waseed, 1972:291, harafin daal)
A cikin
Alƙur’ani
mai girma, suratul Hud Aya ta 6, Allah (SWT) yana cewa:
Larabci: Wa ma min daabbatin fil ardi illa alal Lahi
rizƙuha...”
Fassara: Kuma
babu wata dabba a cikin ƙasa face ga Allah arzikinta yake…” (Alƙur’ani mai fassara na
Abubakar Gummi).
Masana
da dama sun yi ƙoƙarin fitowa da ra’ayoyinsu game da fahimtarsu ta wannan
kalma ta “Dabba”. Domin cimma nasarar wannan, an kalli abin ta fuska biyu,
ma’ana ta ɓoye da ma’ana ta
zahiri.
i. Ma’ana ta
zahiri.
ii. Ma’ana ta
boye.
Ma’ana ta zahiri: ita ce ma’anar da aka
fi saurin fahimta kai tsaye a cikin al’umma. Masana da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anar
kamar haka:
Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006) ya fassara
kalmar dabbobi kamar haka: “Dabbobi dukkan halitta mai ƙafa huɗu”. Abraham (1947) ya
ce: “Dabbobi, wasu halittu ne masu ƙafafu huɗu na gida da na daji.”
Bargery
(1934) ya bayyana cewa:
1. Dabba
na nufin dukkan abu mai rai ne in ka ɗebe tsire-tsire, wato ba nufi muke dabbobin
gida da daji kaɗai ba, amma har
tsuntsaye da su macizai da kwaɗi da kifaye.
2. Dabbobi
wasu halittu ne masu ƙafafu huɗu jikinsu lulluɓe da gashi.
Ma’anar Ɓoye: Bahaushe na amfani da fahimtarsa ta la’akari da
siffofi da halaye da ɗabi’a da kuma yanayin
abu kamin ya ba shi suna ko matsayi. Wasu lokuta sai a rasa gane mai sunan ko
manufarsa. Misali:
i.
Bahaushe kan kira duk wata halitta
wadda bata cika hankali ba wajen gudanar da harkokin rayuwarta da suna “dabba”.
ii.
Bahaushe yakan kira mutum da suna
“dabba”, idan ya kasance mai ƙarancin
fahimta ko rashin iya bayani saboda daƙiƙancinsa.
iii.
Bahaushe kan kira kowace halitta da
“dabba” idan ta kasance mai tafiya a kan ƙafafunta huɗu ko ta zama mai jan ciki,
musamman dabbobin da suke mu’amala da su a gida, na daji kuma su kira su da
dabbobin daji ko namun daji.
East
da Imam (1949:139) sun bayyana ma’anar dabba kamar haka: In mun ce ‘dabba’ muna
nufin duk abu mai rai ne in ka ɗebe tsire-tsire. Watau, ba nufin mu
kai dabbobin gida da na daji kaɗai ba, waɗanda mu ka fi saninsu da suna dabba har da tsuntsaye da
macizai da kwaɗi da kifaye har da kwari da tsutsotsi.
Ma’anar
Ƙwaro
Akwai
saɓani dangane da
ma’anar kalmar ƙwaro da abin da ta ƙunsa a Hausa. Akwai
ma’anarta ta gargajiya wato ta asali da kuma wadda aka tsira saboda sauyin
zamani. A yau Kalmar na iya zama:
i. Bahaushe
kan kira duk wani mugun mutum da suna ƙwaro, kamar maye da ɓarawo da kwarto
da sauran masu kama da su, ko kuma mai naci kamar wurin karatu da sauransu.
ii. Bahaushe
na kiran duk wata ƙaramar halitta mai cutarwa ƙwaro, kamar su maciji
da kunama da Rina da zuma da sauransu.
iii. Bahaushe
(musamman Basakkwace) kan kira duk wani mutum da ba Bahaushe ba da ƙwaro kamar Yarbawa da
Inyamurai.
Kalmar ƙwaro ta ɗauki ma’anoni
dabam-daban dangane da nahiyar da mutum ya fito da kuma irin halittar da ya ɗauka ita ce ƙwaro, amma duk da
haka masana sun kawo ma’anoni dabam-daban dangane da halittar da suka ɗauka ƙwaro, wasu daga cikin
ma’anoin sun haɗa da:
Bargery
(1934), a cikin littafinsa mai suna A
Hausa-English Dictionary and English-Hausa vocabulary ya kawo ma’anonin ƙwaro kamar haka:
i Duk wani ƙaramin ƙwaro ko
ƙananan halittu da ba su da ƙashin
baya.
ii Ɓarawo
ko wani mugu kamar maye ko dabbobi kamar Kada ko Kura. Misali ruwan nan suna da
ƙwari ko dajin nan yana da ƙwari.
iii Ƙananan duwatsu da
mata ke kitso da shi, ana samunsu ƙasan ruwa.
Shi
kuma Ƙamusun Hausa (2006: 292-293) ya bayyana ma’anar ƙwaro da:
i Wata ƙanƙannuwar
halitta dangin su kiyashi ko cinnaka.
ii Duk
halittar da ke cutar da ɗan Adam wadda don haka ake tsoron ta, kamar Kura ko Kada
ko Maciji.
iii Boka.
iv Maye.
v Abin
da aka tufka da kaba mai launi daban-daban don ado a hannu ko ɗuwawu a yara.
vi Wani ɗan ƙaramin ƙarfe da
ake maƙale lifidi da shi (Ƙamusun Hausa
2006:292-293)
Abin
lura a nan shi ne, dangane da ma’anonin ƙwaro da aka bayyana a
sama, an kira kura da kada da maciji da sunan ƙwari ne saboda
haliyyar da suke da ita irin ta ƙwari, wato mugunta da
ƙeta,
amma kuma ba ƙwarin ba ne.
Mahe
(2008) ya ce: Bahaushe ya fi danganta ƙwari da ƙananan halittu
raunana waɗanda ba su fi a taka
su da ƙafa ba, ko a murje su da hannu, irin su kiyashi da
tururuwa da fara da ƙuda da buzuzu da sauransu. A cikinsu akwai manya da ƙanana da masu tashi a
sama da masu dudduƙe a ƙasa.
Hassan
(1995:2) ya bayyana kalmar ƙwari da cewa: Halittu ne waɗanda Allah maɗaukakin Sarki ya yi
waɗanda al’adunsu da ɗabi’unsu da
haliyyarsu ta sha bamban da sauran halittu kamar tsuntsaye da tsutsotsi da
sauransu. Ya ci gaba da cewa a wurin Mafarauta duk dabbar da ke cikin daji sun ɗauke ta ƙwaro, don haka ne ma
idan zasu shiga daji suke neman tsari daga ƙwarin da ke ciki, ko
kuma su ce dajin nan akwai ƙwari da yawa.
Ana iya
kiran ƙwari da wasu ƙananan halittu waɗanda ke rayuwa bisa ƙasa, suna rayuwa ta
hanyar haihuwa, idan rayuwarsu ta ƙare su mutu. Ƙwari na da yawa sosai
don sun fi kowane rukunin halitta da ke bisa ƙasa yawa, kuma sun fi
kowane jinsi watsuwa da sauri, sannan zasu iya rayuwa a ko’ina matuƙar yanayin wurin ya
gamsar da su. An gano masu yawa cikinsu sannan kuma akwai miliyoyi da ba a gano
ba, kamar yadda East da Imam suka ce a lttafinsu mai suna “Ikon Allah”.
“Can
asali ƙwari daga ruwa suke, daga ciki suka fito suka zo suka
mallaki tudu ka ga wannan bai ishe su ba, ga su nan har suka koyi dabarar tashi
sama.sun daɗe ƙwarai a duniya. Ga su
da dabara da iya tsari da tsananin yawa. (East da Imam, 1949:245)
A taƙaice bisa ga bayanan
da suka gabata ana iya cewa kalmar ƙwaro ta ƙumshi ƙananan halttu waɗanda ba su da ƙashin baya, akwai
masu tashi sama ta amfani da fukafukai, akwai kuma masu tafiya a ƙasa, ana samunsu a
gidaje da daji da kuma cikin ruwa, kamar ƙwarƙwata da ƙuma da ƙazumzumi da kiyashi
da sauro da kunama da tururuwa da sauransu”.
Saboda
haka duk wani abu mai rai da ke yawo a doron ƙasa, ya haɗa da dabbobi masu ƙafa huɗu da mutane da
tsuntsaye da sauran su duk suna amsa wannan suna na dabba. Hausawa kuma sai
suka ware mutane daban, su kuma masu ƙafa huɗu su kira su da
dabbobi. Asalin sunan da Hausa ke kiran dabbobi kafin aro kalmar ‘dabba’ shi ne
“bisa” (tilo), “bisashe” (jam’i) ga dabbobin gida; na daji kuma “namun daji”,
na ruwa kuwa “naman ruwa”.
Waƙar Baka: Ita kuma waƙa masana da manazarta
sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar waƙa ta yadda suka
fahimce ta. Wasu sun bayar da ma’anar ta gaba ɗaya, wasu kuma sun rarraba ma’anar ta
fannin rubutacciya da kuma ta waƙar baka, kamar haka:
Gusau
(2003) a wurin shi, Waƙa wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake
zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin shiryawa da
daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da amshi da kiɗa.
Ma’anar
Tsuntsu
A bisa nazari, shi tsuntsu halitta ce wadda take da ƙafafu biyu, amma tana tashi
sama, don haka za a same ta tana da fikafikai. Kazalika, halitta ce ‘yar ƙwai. Abin nufi, takan haifu ta
hanyar yin ƙwai, ta kuma ƙyanƙyashe. Bugu da ƙari, akwai wasu tsuntsaye da suke zaune a cikin dazukan ƙasar Hausa, amma akwai wasu waɗanda suke na gida ne, waɗanda ke zaune tare da mutane, a cikin gida. Baya ga
haka, wasu tsuntsayen suna yin rayuwa a kan tudu, amma wasu suna yi ne a cikin
ruwa (Sa’id da wasu (editoci), 2006:460).
Dabbobi Da Ƙwari Da Tsuntsaye A
Cikin Waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru.
Makaɗa Sa’idu Faru ya
ambaci dabbobi da ƙwari da tsuntsaye da dama a cikin waƙoƙinsa, domin ya fito
da kuma ya bayyana halayen uwayen gidansa da kuma halayen masu jiran gadon
sarauta da kuma halayen ‘ya’yan sarakuna da fadawan da kuma makusanta ga
sarakuna, ta hanyar yi masu zambo ko habaici da sauransu. Misali:
A cikin wata waƙar Dagacin Banga a
masarautar Ƙaura Namoda, sarkin yaƙi Sule, mai gindi
kamar haka: “Gwabron Giwa uban
Galdima Ɗantumba ginjimi, Gamshiƙan Amadu na mai gandi
kai a uban Zagi”, yana cewa:
Jagora:
Jan Zakara yayi ƙiƙiriƙi,
Ya tare
garkar gidan ubanai,
‘Y/Amshi: Ya bar kwaɗɗo shina cikin rame,
Ya lanƙwashe tsara.
Jagora: Ɗiyan Alibawa kui ta
biya, Don Allah ya yo uban Zagi.
‘Y/Amshi: Domin Kura ta wuce ana ɓacin laka kamar ita.
Jagora: Ko jiya na
iske Gamdayaki da Tuji, Sun iske Jinjimi.
To sun ko mirɗa gardama, Sun iske
su Bubuƙuwa ruwa,
Dan nan kulmen da ac cikin gurbi, Ya
amsa gaisuwa.
Jagora: Dan nan sai Jinjimi da yas sulata yas
suntulesu dut.
‘Y/Amshi: Shi ko Tuji da ad da girman baki yak
kwashe Jinjimi,
Dan nan Bubuƙuwa da tar rura ta
gangamesu dut.
Jagora/’Y: Ran nan
nis san duniyag ga komi nane wani gwanin wani.
Jagora: Zama Giwa ta fito kiwo tai nisa ta zo
ta sha ruwa,
‘Y/Amshi: Ku ji ɗan zomo na faɗin faɗa ma su Tsari Tsara ku tay gida.
A cikin ɗiyan waƙar da ke sama makaɗin ya yi amfani da waɗannan tsuntsaye ne waɗanda suka bambanta
wajen girma, misali bubuƙuwa da tuji da jinjimida gamdayaƙi duk tsuntsaye ne
kuma ba girmansu ɗaya ba, wannan ya fi
wannan, wannan ya fi wannan. Bayan waɗannan tsuntsaye ya ambaci giwa da zomo da
tsari da tsara, suma ba girmansu ɗaya ba, saboda giwa ta fi su girma. To
mawakin ya yi amfani da waɗannandabbobin domin ya nuna cewa har gobe akwai bambanci
tsakanin halittu, idan ka fi wani, to kai kuma wani ya fi ka. Daga ƙarshe dai yayi amfani
da salon fifiko domin ya nuna bambanci tsakanin wanda ya ke yi wa waƙa da sauran sarakuna
ko masu jiran gadon sarauta.
A cikin waƙar sarkin kudu macciɗo, mai gindi kamar
haka: “Mai babban rabo gimshikin Sarkin sharifai” yana cewa:
Jagora:
Toron giwa yana abinda ya kai
ya shigo dawa,
‘Y/Amshi:
‘Yan namu suna ta gaisai sun
ba da gaskiya,
Bil’amu na cikin sabara ya ɓoye kainai,
Zomo ya taho ya tsaya ya gaida Toro,
Shi ya yarda Allah
kawa kowa nagarta.
Su kuma ɗiyan waƙar da ke sama, makaɗa Sa’idu Faru ya kawo
toron giwa wanda yake ya fi kowace halitta da ke cikin daji girma, saboda haka
dole sauran namun dajin su yi masa biyayya. Bil’amu (Dila) saboda wayo ya ƙi fitowa, amma sauran
namun daji irin su zomo da sauransu duk yi biyayya. A nan makaɗa yana son ya nuna
irin martaba da girman da ke ga sarkin Musulmi Macciɗo, idan ya fito kowa
zai zo ya yi gaisuwa duk sun yarda da Allah ke ba da mulki sai wani guda da ke
da jayayya ya ƙi zuwa ya yi mubaya’a. A taƙaice waɗannan dabbobin (‘yan
namu) masu jiran gado ne, shi kuma toron giwa sarki ke nan ka ga ba su haɗuwa. Ma’ana Macciɗo kamar yadda toron
giwa ya ke a daji to shi ma haka yake a cikin mutane.
Sannan a cikin wata
waƙar
ta sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo mai gindi kamar haka: “Farin cikin Musulmin
duniya, mai martaba na Abubakar, ci fansa alhaji Macciɗo”, yana cewa:
Jagora:
Wanda bai san daɗin doki ba sai yace jaki hikima garai,
‘Y/Amshi: Kowa na kurɓa ruwan zuma ba shi koma tadda batun maɗi”
Haka kuma a cikin ɗiyan ƙawar da suka gabata,
makaɗa ya ambaci doki da
jaki da zuma da maɗi, sai kuma mota da
fanda. A nan ya na son fito da fifikon sarkin Musulmi a kan sauran sarakuna. Ya
bayyana cewa wanda bai taɓa zama da sarkin
musulmi ba zai ga kamar akwai sarkin da ya fi shi. Shi ne yake cewa wanda bai
taɓa amfani da doki ba,
zai ga hikimar jaki, daga ƙarshe sai ya bayar da amsa na cewa,
kowa na ɗanɗana zuma zai manta da
maɗi saboda zaƙin ya bambanta. A taƙaice yana son ya nuna
cewa duk wanda ya yi hulɗa da sarkin Musulmi
Macciɗo to zai tabbatar da
cewa ya fi kowane sarki.
Haka ma a cikin waƙar sarkin gabas na
Talata Mafara, Shehu Muhammadu Ɗangwaggo, mai gindi kamar haka: “Koma
shirin daga na Muhammadu Shehu ɗan Shehu ganɗon ƙasar Hausa”, yana
cewa:
Jagora: Daudu kullun
mahwalki nikai sabo,
‘Y/Amshi: Shehu ya ba
mu doki da kayanai,
Danda fari biyat wanda an
nan gabas inda liman ka bi zai masallaci.
A cikin waɗannan ɗiyan waƙa da ke sama, makaɗa Sa’idu faru ya
ambaci doki in da ya fito salon roko inda ya ke cewa ya yi mafarkin an ba shi
doki da kayanai, kuma har da siffar dokin da wurin da ake ɗaure dokin ya
bayyana. Ya bayyana dokin da yake shi ne danda mai fari biyar. Ma’ana doki ne
mai tambarin fari a ƙafafunsa guda huɗu da kuma goshinsa. A taƙaice dai doki ya ke
roƙon
sarki ya bashi.
Bayan wannan akwai waƙar sarkin Zamfaran
Zurmi Sulemanu muhammadu, mai gindi kamar haka: “Babban bajinin gidan Sambo
shirinka daban da raggo”. Yana cewa:
Jagora:
Hadari mai taushe rana,
‘Y/Amshi:
Zaki nisa da ƙarhi,
Wada ‘Yan namu ka gigita ba damar su hwarma.
Jagora:
Alibawa suna ganin hwansassu wurin sule babu dama,
Giwa ta sha ruwa tai miƙa ta taushe gurbi,
‘Y/Amshi:
Kuma ‘yan ɗiyanta sun shiga sun
sha sun hwara ƙarhi,
Jagora:
Su ‘yan namu suna jin ƙisa ba damar su kurɓo,
Sai bil’amu uban dubara, sai yaz zo
ga giwa,
Albarkacinki
niz zaka in samu ruwan da nis sha.
Giwa ta bashi hili, yas samu da yas sha,
sha ya
kuma ba ɗiyanai,
Sai yaw
wa dangi kirari, yac ce ya ƙwato da ƙarhi,
Zomo yac ce tsaya shege lallashinta kay yi,
‘Y/Amshi: In ƙarhi gaskiya na koma ɗebo gabana.”
A nan kuma ya yi
amfani da dabbobi manya da ƙanana kamar zaki da giwa su ne manyan
dabobi a cikin daji, duk saura dabbobin ya kira su da ‘yan namu kamar su dila
da zomo da sauransu. A taƙaice yana so ya nuna irin ƙarfin da martaba da
ke ga wanda yake yi wa waƙa. Kamar yadda giwa da zaki suke a cikin daji, to shi ma
haka yake a cikin mutane.
A waɗannan ɗiyan waƙa ma ya ambaci giwa
da zaki domin su ne dabbobi da suke fi sauran namun daji ƙarfi da girma domin
ya fito da irin ƙarfin da ke ga wanda ya ke yi wa waƙa. Ma’ana yana son ya
bayyana cewa kamar yadda giwa da zaki suke a cikin daji, to shi ma wannan
basaraken yana da girma da ƙarfin iko a cikin jama’arsa.
Haka kuma a cikin waƙar sarkin Zazzau
Alhaji Shehu Idris, mai gindi kamar haka: “Gagara gasa bajinin sarki, Shehu
hallaliyar gidan Mamman Allah ya biya maka buƙata kai a babba ga
gidan sambo”. Yana cewa:
Jagora: Toron Giwa ƙi fasawa,
‘Y/Amshi: Toron Giwa ba togewa,
Gogarman magaji Jan Zaki,
Jagora: Namijin Zaki ka fi kyau da ƙarfi,
‘Y/Amshi: Ba a haye
maka cikin birni,
Ba a haye maka cikin
daji.
Jagora: Kolo ya so a bashi sarki,
‘Y/Amshi: An yi biɗa yana cikin daji,
A nan ma ya ambaci dabbobi da tsuntsaye kamar
toron giwa da jan zaki da namijin zaki da kuma kolo. Waɗannan dabbobin
dukkansu masu ƙarfi ne a daji, to kamar yadda suke da ƙarfi a can, shi ma
sarki haka yake da ƙarfi da martaba a cikin jama’arsa. Ya kuma ambaci kolo
(angulu) domin yi wa wani ɗan sarki habaici wanda ba a cika samunsa a cikin gari ba
kusan kullum yana daji.
A cikin waƙar Ɗanmadamin Sakkwato
Usman Ɗangwaggo Bunguɗu, mai gindi kamar haka: “Bajini birni bajini
dawa, na dai gaisheka da ƙoƙari Ɗanmaidaga na Abubakar Usuman kai niz
zaka in gani”. Yana cewa:
Jagora: Manyan kaya
manyan ganwo,
‘Y/Amshi: Jaki kankanbab banza garai
Wasu kaya sai bisa Raƙumi,
Jagora: Su Angulu dai an tsuhwa mahauta,
‘Y/Amshi: Nan aka kwana kowace kasuwa”.
Ko a nan ma ya ambaci
dabbobi da kuma tsuntsaye. Ya ambaci jaki da raƙumi, domin ya
bambanta fifikon da ke tsakinsu a wajen ɗaukar kaya, ya nuna raƙumi ya fi jaki ɗaukar kaya. A nan
yana yi wa wani ɗan sarki habaici ne,
ya nuna cewa kamar yadda jaki baya iya ɗaukar kayan da raƙumi yake ɗauka, to haka ma
wannan ɗan sarkin baya iya ja
da sarki a wasu ɓangarori na rayuwa.
Ya kuma ambaci angulu domin yi wa wani ɗan sarki mai jiran tsammani habaici, kamar
yadda angulu ke jiran a yanka dabba ya sha jini a mahauta.
Haka kuma a cikin waƙar Sarkin Kiyawan
Kaura Namoda Amadu, mai gindi kamar haka: “Ginjimin gidan Sambo uban yari ma ci
fansa, mai wuyar karo jikan Mamudu marinjayi”. Yana cewa:
Jagora: Jemage ga
halinai bamu san wanda shi ke so ba,
Gashi mai haƙora na,
Ga shi mai kunnuwa
na,
Ga shi baya sauka ƙasa balle a ga
damatai,
‘Y/Amshi: Duk minahikin Allah nan mun ka naɗa babba.
A ɗiyan waƙar da ke sama makaɗa Sa’idu Faru ya
ambaci wani tsuntsu shi ne jemage, domin yi wa wani mai jiran gado habaici,
yana so ya bayyana halinsa na munafurci kamar yadda jemage yake da sifofi guda
biyu, ga shi siffa ta tsuntsaye, kuma ga shi da wata sifa ta mutane wato haƙora irin na mutane da
kuma yanayin yadda ya ke haihuwa kamar yadda mutane suke haihuwa ne. A taƙaice dai yana son ya
nuna wannan ɗan sarkin fuska biyu
gare shi, wato akwai alamun munafurci gare shi.
Sai kuma cikin waƙar Sarkin Kudu Macciɗo, mai gindi kamar
haka: “Gogarman gidan Moyi ci fansa niƙatau”. Yana cewa:
Jagora: Toron Giwa shina abinda yakai ya
fito dawa.
Jagora: In Jaki ya gaza da kaya a azama Raƙumi,
‘Y/Amshi: Ni nasan
kwatancin irin kayanka Jaki,
Jagora: Na ishe Dale tai ƙawa ga jama’arta ba ƙawa,
‘Y/Amshi: Ya rubce kuɗi ya nasa dogon
akwati,
Rana ta jewayo na naɗe ya tai Ilori,”
Su kuma waɗannan ɗiyan waƙar makaɗa Sa’idu Faru ya
ambaci wasu dabbobi da tsuntsaye irin su toron giwa da jaki da raƙumi. Ya yi amfani da
su ne domin ya nuna ƙwazo da kuma halin kyauta wanda sarki ya ke da shi, shi
ne ya ke cewa in jaki ya gaza da kaya a azama raƙumi, ma’ana in ba su
iya yi masa kyauta to su bari sarki ya yi masa. Shi ne yake cewa, na ishe dale
tai ƙawa, ga jama’arta ba ƙawa, wato ya zo wajen
sarki ya yi masa kyauta amma ‘ya’yan sarki ba su yi masa ba, wani daga cikinsu
ma har tafiya ya yi wani gari don kada ya ba shi komi.
Sai kuma cikin waƙar Alƙalin Gusau Shehu, mai
gindi kamar haka: “Ya yi niyar zaman shari’a koyaushe zaki ana tsoron halinka,
gogarman gidan Muhamman Alƙali Shehu”. Yana cewa:
Jagora: Ɗiyan kusa suna hwaɗin,
‘Y/Amshi: Da Burgu ka yin shari’a da anga sata.
A nan kuma ya kawo
kusu (ɓera) da kuma burgu
(gafiya) domin yin habaici ga wani alƙali, inda yake son ya
fito da halin alƙalin na cin hanci. Shi ne ya dabbantar da shi ya ɗauki halin
burgu(gafiya) ya bai wa alƙalin. Ya ce ɗiyan kusa (mutane ko
jama’a) suna faɗin da burgu wato (alƙalin da ya ke yi wa
habaici) ka yin shari’a da an ga sata. A taƙaice yana son ya fito
da gaskiya da kuma amanar da ke ga wannan alƙalin na Gusau. Ya
nuna mutane ma suna yaba masa har suna cewa, in da wani alƙali ne ke yin shari’a
wanda ba shi ba, to da jama’a sun sha wahalarsa.
A cikin waƙar Sarkin Buguɗu Usuman Ɗangwaggo, mai gindi
kamar haka: “Gwabron Giwa
kana da martaba, Usumanu na Bunguɗu uban Marafan Keku na Atto mai wuyar karo”.
Yana cewa:
Jagora: In kaga Kadanni da Dorina,
Ruwa mai ƙarfi sunka ishe,
Jagora: Zarnaƙo ƙaryar faɗa yakai,
‘Y/Amshi: Kowa ka biɗah hwaɗa ya ja zuma,
Sai ya biɗi mai raba su ya rasa.”
Kada kuma da dorina
su ma yana nufin wasu ɗiyan sarki ne da suka
nemi sarautar, shi kuma sarki shi ne gulbin da ya zo ya wuce da su duka, ma’ana
ya yi nasara a kansu. Sai kuma ya yi amfani da wasu ƙwari domin ya nuna
jaruntakar sarki na cewa ba a jan sa wasa da shi, don kowa faɗa masa zai gane
kurensa. Shi ne ya kamanta zarnaƙo da zuma, idan ana
maganar faɗa to zuma ta fi zarnaƙo nesa ba kusa ba.
Sannan a cikin wata
waƙar
ta sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo mai gindi kamar haka: “Ka yi sarki daidai
wada mai yanzu yar riƙa, Alhaji Macciɗo jikan Mamman mai dubun tsari”, yana cewa:
Jagora:
Bajini ɗan gagara gasa Amalin sarakuna,
‘Y/Amshi: Toron giwa ɗan Audu ƙanen Ali ɗan iya.
Su kuma ɗiyan waƙar da ke sama an
ambaci dabbobi guda uku, bajini da amali da kuma toron giwa. Waɗannan dabbobin
kowanensu babba ne a zuriyyarsu. Bajini a cikin shanu shi ne mafi girma da kuma
ƙarfi.
Amali a cikin raƙumma shi ne mafi girma da kuma ƙarfi. Toron giwa kuma
shi ne mafi karfi da girma a cikin giwaye. To mawaƙin ya yi amfani da su
ne domin ya nuna irin karfi da girma da ke ga sarkin Musulmi a cikin al’umma,
kamar yadda waɗannan dabbobin suke a
cikin danginsu.
A cikin waƙar ta sarkin Tudun
Falale Alhaji Muhammadu Bala, mai gindi kamar haka: “Ya riƙa da gaskiya
Muhammadun Muhammadu, dangalin/karsanin gidan mai saje shirinka ya yi kyau”,
yana cewa:
Jagora:
Yahihiya da kunkuru shawara guda sukai,
Da Bushiya da Beguwa shawara guda sukai,
Da Kurciya da Hasbiya shwara guda sukai,
Bubuƙuwa da Jinjimi shawara guda sukai,
‘Y/Amshi:
Duk babu wanda yaz zo haji
Babu mai nuhwaz
zuwa.”
A nan kuma ya ambaci
wasu ƙwari da tsuntsaye wato, yahihiya da kunkuru da bushiya da
beguwa da kurciya da hasbiya da bubuƙuwa da kuma jinjimi.
Dukkaninsu ɗiyan sarki ne ya
dabbabantar. Yahihiya da kunkuru gidansu guda sifarsu guda, yahihiya ta fi
kunkuru girma. Bushiya da beguwa gidansu guda sifar guda, beguwa ta fi bushiya
girma. Kurciya da hasbiya gidansu guda sifarsu guda, hasbiya ta fi kurciya
girma. Bubuƙuwa da jinjimi gidansu guda duk tsuntsaye ne, jinjimi ya
fi bubukuwa girma. A taƙaice dai ɗiyan sarki ne ya ke yiwa habaici na rashin samun sarauta.
A cikin wata waƙar ta sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo mai gindi kamar
haka: “Bajinin gidan Bello Mamman na yari, Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya”, yana
cewa:
Jagora: Ina
Bangabanga mai ‘yar Mahuta,
Alade wurin shan giya kah hi suna
A waɗannan ɗiyan waƙar da ke sama ya
ambaci wata dabba wato “Alade”, ya yi amfani da alade domin yi wa wani ɗan Sarki zambo don ya
fito da wani hali nasa wato shan giya domin kowa ya san shi da wannan halin. A
nan ya faɗi wata sifa ta shi
ita ce yanayin naɗin rawaninsa da kuma
halin shi na shaye-shaye
A cikin wata waƙar ta sarkin Sudan
Shehu Malami, mai gindi kamar haka: “Muzakkarin Sarki ɗan Shehu abun biya
Shehu na Ali”, yana cewa:
Jagora:
Gurnanin daji sai giwa,
‘Y/Amshi: Dan Akuya kai tafiyar
Jagora:
Karen buki na nan ya shiga ofis,
‘Y/Amshi:
Amma bai kai ga Biri
Jagora:
Don komi harbinki kunama,
Toron Giwa in yat take ta,
‘Y/Amshi: Babu damar
ta yi motsi.
Haka kuma ya Ambato
sunayen dabbobi a ɗiyan waƙar da ke sama, kamar
giwa da Ɗan Akuya da Karen buki da Biri da kunama domin ya yiwa
wasu zambo ta amfani da sunayensu.
A cikin wata waƙar ta Sakataren D.O Ƙaura, mai gindi kamar
haka: “Ba a yi ma wargi Zaki, saboda ƙarhin rinjaye”, yana
cewa:
Jagora:
Kyawon dan sarki alheri,
Dan
Sarki in bai alheri,
‘Y/Amshi:
Ya zama kotokon Banza,
Jagora:
In ya yi man huskas Shanu,
Ni ko
in yi mai dibin banza.
A nan ma ya ambaci
wata dabba wato saniya don yin zambo ga wanda ba ya yi masa kyauta. Ya ce idan
ka yi masa huskar shanu (game fuska ko ɓata rai) shi kuma sai ya ɗauke ka ba kowa ba.
Sakamakon Bincike
Daga ƙarshen bincken, an
gano cewa ba komi ya janyo saka dabbobi da ƙwari da kuma
tsuntsaye a waƙa ba face sakamakon lura da halaye da ɗabi’un dabbobin.
Wannan lura ita ta sanya Hausawa suka fahimci ɗabi’u da halayensu suka riƙa ambatonsu a cikin
waƙoƙi. To wannan lurar
ita ce tamkar mizani na awon gane halayyarsu da ɗabi’unsu. Ta la’akari da lura ya sanya
mutane suka fahimci irin tsuntsayen da ake samu a lokuta daban-daban, lokacin
rani ne ko lokacin damana ko hunturu da sauransu. Lura ce ke sa a gane wannan
dabba mai faɗa ce, wannan kuma mai
haƙuri
ce, wannan mai tsafta ce wannan kuma mara tsafta, wannan tana da ƙarfi wannan kuma
cima-kwance. A taƙaice, wannan bincike ya gano cewa da lura ne a ke gano
duk wata halayya ko ɗabi’a ta kowace irin
halitta. Wannan shi ne dalilin da ya sa mawaƙan suka fahimci
halayya da ɗabi’un dabbobi da ƙwari da kuma
tsuntsaye har suka saka su cikin waƙoƙinsu. An kuma gano
cewa dabbobi da ƙwari da tsuntsaye suna taka rawa sosai wajen bunƙasa adabin baka.
Shawarwari
Wannan fanni na
ilimin dabbobi da ƙwari da tsuntsaye, yana da yawa ko faɗin gaske. Don haka
yana da matuƙar muhimmanci a samu wasu masu sha’awar bincike daga ɗaliban ilimi su ƙara zurfafawa. Akwai
abubuwa da dama da za a iya gudanar da bincike dangane da abin da ya shafi
harkar dabbobi da ƙwari da tsuntsayen da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a
cikin waƙoƙinsa, kamar abin da ya shafi zambo da habaici da
sauransu.
Kammalawa
An fara binciken da
gabatarwa inda aka yi bayanin abubuwan da takardar za ta ƙunsa da bayanin
dabarun binciken da aka yi amfani da su domin ganin binciken ya kammala cikin
nasara. Haka ma an bayyana muhimmancin binciken a daidai wannan lokaci. Bayan
wannan kuma, sai Taƙaitaccen tarihin makaɗa Sa’idu Faru. Daga nan sai taken maƙalar da aka yi
bincike a kansa, wato dabbobi da ƙwari da tsuntsaye a
cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru, waɗanda ya yi amfani da su wajen yi wa mutanen
da yake son ya bayyana wa al’umma halayensu masu kama da na dabbobin. An yi
bayanin sakamakon wannan bincike. An kuma bayar da shawarwari ga masana da masu
sha’awar nazarin waƙoƙin Sa’idu Faru ta ɓangaren dabbobi da ƙwari da tsuntsaye.
Daga nan sai aka kammala binciken da wannan bayani, sai aka zayyana tushen
bayani da kuma hotunan wasu daga cikin dabbobin da ƙwari da tsuntsayen da
aka yi amfani da su a cikin wannan aikin.
Manazarta
Abdullahi, I. S. S. (2008) Bamaguje Da
Ɗan Akuya: Soyayya Ko Ƙiyayya? Maƙalar da aka gabatar a Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ado, A. (2011) Wasa Da Kura a Ƙasar Katsina. Maƙalar da aka gabatar a Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya. Katsina: Jami’ar
Umaru Musa Yar’adua:
Aminu, N.I. (2015) Kaza ga Bahaushe Jiya da
Yau. Algaita Journal oa Current Reseach in Hausa Studies (Special Edition).
Kano: Ahmadu Bello University Press. vol. 1, no. 1(631-638)
Asma’u, S. (2015) Ƙwarin Ƙasar Hausa: Nau’o’insu da Tasirinsu ga Adabin Baka da
Wasu Al’adun Hausawa. Kundin digiri na biyu. Kano: Jami’ ar Bayero.
Bargery, G. P. (1993) A Hausa-English
Dictionary and English-Hausa vocaɓulary (2nd Edition). Zaria: Ahmadu
Bello University Press Ltd.
Bunza, A. M. (1999) Raɗaɗi da Zogin Cuta a Ma’aunin Bahaushe:
Tsokaci daga Waƙar Kunama ta
Garba Mai Tandu. A cikin Hausa Studies. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza, A. M. (2011) Kura a Ma’aunin
Adabin Hausa. Maƙalar da aka
gabatar a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina.
CSNL, (2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University
Press Ltd.
Ɗanyaya, B. M. (2007) Bahaushen Zakara
Ya fi Mutum Iya Zama Da Iyali. A cikin Mujallar Makarantar Hausa, Sakkwato.
Ɗanyaya, B. M. (2007) Karin Magana 54 a
Kan Kura. A cikin Mujallar Makarantar Hausa, Sakkwato.
Dogarai, I. A. (1992) Namun Daji a Ƙasar Hausa: Ire-Irensu Da Magungunan
Da Aka Samu Daga Gare su. Kundin digiri na farko, Kano: Jami’ar Bayero.
East, R. M. da Imam, A. (1949) Ikon
Allah, Littafi Na 3 & 4. Zaria: NNPC.
Funtuwa, B.A. (1975) Gandun Dabbobi:
Na Goarge Orwell, Ibadan university press limited, in Association
with Oxford University Press.
Gusau, S. M. (1996) Makaɗa Da Mawaƙan Hausa. Kano: Usman Al’ amin Publishing
Company.
Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa Yanaye-Yanayensu Da
Sigoginsu. Kano:
Benchmark Publishers Limited.
Mahe, I. A. (2008) Amfanin Dabbobi A
Fagen Gina Adabin Hausa. Kundin digiri na biyu. Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Mu’azu, A. H. (2012) Tasirin Dabbobi a
Adabin Baka na Hausa. Kundin digiri na biyu. Sakkwato: Jami’ ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Mu’azu, A. H. (2009) Gurbin Dabbobi Da
Ƙwari A Cikin Waƙoƙin
Baka Na Hausa. Takardar da aka gabatar domin ci gaba da binciken kundin
digirina biyu. Sakkwato: Jami’arUsmanu Ɗanfodiyo.
Mu’azu, S. M. (2015) Dabbobi a Tunanin
Bahaushe. Kundin digiri na uku. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Nasiru, A. (2010) Maza Majaya Amale:
Sana’ar Fatuci Da Raƙummai A Jihar
Kebbi (Nazarin Kirarin Raƙumi
Na Illon Geza). Takarda da aka gabatara taron ƙara wa juna sani, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sakina, A.A. (2018) Kwarin Ƙasar Hausa A Farfajiyar Tunanin
Bahaushe. Kundin digiri na uku. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Shinkafi, R. H. (2012) Garba Mai Tandu
Shinkafi Da Waƙoƙinsa. Kundin digiri na biyu. Sakkwato:
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Usman, B. B. (2000) The Traditional
Medical Care of Donkey: Tsokaci Daga Waƙar
Garba Mai Tandu. Taron ƙara
wa juna sani. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ratayen hotunan wasu dabbobi da ƙwari da
tsuntsayen da aka ambata a cikin iyan waƙoƙin da
aka yi amfani da su