Citation: Malumfashi, A.S., Galadima, S.S. & Jangebe, S.A. (2024). Nazarin Turken Yabo Da Zuga A Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 135-141. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.018.
NAZARIN TURKEN YABO DA ZUGA A WASU WAƘOƘIN MAKAƊA SA’IDU FARU
Na
Abubakar Salisu Malumfashi
Da
Sani Sama’ila Galadima
Da
Shu’aibu Abdullahi Jangebe
Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Tarayya Gusau, Jihar Zamfara
Tsakure
Babban maƙasudin wannan
takarda shi ne Nazarin turken yabo da zuga a wasu waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. Amfanin da turken yabo da zuga a cikin waƙoƙin baka na Hausa
wani saƙo ne na nuna yabo
da kuma zuga ga wanda ya yi wata kyauta da kuma nuna bajinta ko ƙwazo. Makaɗa Sa’idu Faru yana daga cikin irin mawaƙan da suka yin amfani da irin waɗannan turaku don
haka ne wannan muƙala ta yi nazarin
yadda makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da waɗannan turaku a cikin waƙoƙinsa. A wajen
gudanar da wannan bincike an bi hanyoyin samun bayanai da suka haɗa da tattara waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru musamman waɗanda suka shafi wannan nazari sannan kuma an nazarci bugaggun littattafai
da kundayen bincike da takardu na ilimi. Bayan haka an tattauna da masana da
manazartaadabin da harshe domin samun ingantattun bayanai. A ƙoƙarin cimma manufa,
an yi amfani da mazhabar waƙar Baka Bahaushiya
wacce ta bayyana hanyoyin da ake nazarin yadda ake nazarin waƙar Baka
Bahaushiya. Wanda ya jagoranci wannan mazhabar shi ne Sa’idu Muhammad
Gusau. Bayan kammala wannan muƙala an lura da
cewa makaɗa Sa’idu Faru yana amfani da turken yabo da zuga a cikin
waƙoƙinsa.
Fitilun Kalmomi: Yabo, Zuga, Gwarzantawa, Caccaɓawa, Kururutawa
1.0 Gabatarwa
Yabo da Zuga a waƙoƙin baka na Hausa wasu muhimman tubalai ne waɗanda yawancin makaɗan baka, musamman a waƙoƙinsu na fada sukan yi amfani da su
wajen gina waƙoƙinsu. Hakan ta ba Sa’idu Faru damar samar da turakun yabo da zuga suka yi
fice a cikin waƙoƙinsa. Wato ke nan a waƙoƙin Sa’idu Faru akwai zumunci mai ƙarfi da a tsakanin tuken yabo da zuga da waƙoƙinsa. Haka kuma, kasancewar yabo da
zuga hanya ce ta wani lafazi da ake yi ga wani mutum, ko wani abu domin a
bayyana halayensa da siffofinsa abin sa ne. Akan dubi abubuwa da dama domin
gina turken yabo da zuga, abu ne mawuyaci ga mawaƙin baka ya yi waƙa ba tare da yin
amfani da turken yabo da zuga ba, musamman waƙar Sarauta. Waƙoƙin baka na Hausa kan zamo wata taska ta adana hikimomi da harshen Hausa ke
da su.
Makaɗan baka na yi wa waƙoƙinsu kwalliya ta yadda mai sauraro zai samu karsashi a duk lokacin da yake
sauraron waƙoƙinsu. Waƙoƙin Sa’idu Faru suna ɗauke da hikimomi da balagar harshe ta yadda mai sauraro zai samu karsashi a
duk lokacin da yake sauraron waƙoƙinsa. wannan takarda ta fito da yadda
Sa’idu Faru kan shirya dabaru wajen shirya waƙoƙinsa masu ɗauke da turken yabo da zuga.
Turke yana nufin saƙo ko manufa ko bayani
ko ruhin da waƙa ta ƙunsa wadda kuma shi ne abin da waƙar ke son isarwa ga mai sauraro ko karatu ko nazarinta. Yahya (1997:75).
Wannan ya nuna cewa, saƙon da mawaƙi ke ta ƙoƙarin ya ga ya isar ga mai sauraro ko karatun waƙa shi ne turke. To hanyar turke ne aka fahimtar manufar wawaƙi.Gusau (2003:38) ya bayyana turke shi ne abin da waƙa take magana a kansa wanda ya ratso ta tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta. Wato dai turke shi ne ainahin manufar waƙa.
Gusau (2008:376) ya bayyana yabo shi ne
ambaton kalmomin sambarka da nufin nuna amincewa da hali ko wani abin da mutum ya
yi nagari. Shi kuwaYahya (1997:86) cewa ya yi idan an ambaci yabo ba lalle ana nufin
faɗar kalmomin ƙwarai ga wanda ake yi wa waƙa ba. A ra’ayinsa yabo cikin wasu waƙoƙin musamman waƙoƙin maza yakan ɗauki ma’ana da
dama kamar yabo ta fuskar ta’addanci ko yabo ta fuskar aikata abin kunya ko yabo
ta fuskar bajinta ko yabo ta fuskar fifiko ko yabo ta fuskar ƙarfi ko asiri ko dubara.
Gusau, (2008:377), ya bayyana ma’anar zuga da cewa: “Zuga tana ɗauke da wasu kalmomi ne da ake amfani da su a koɗa wani mutum a cicciɓa shi, a nuna fifikonsa kan wasu. Zuga
takan tsuma mutum ta sa masa kuzari da kwarin guiwa. A wajen zuga mutum ana yin
amfani da kalmomin wasawa ko kumburawa ko fifitawa ko naƙastawa da tauye daraja da sauransu”.
Gusau (2002:302-303), ya nuna, turken zuga zalla shi ne a sami waƙa ɗaya wadda babbar manufar wato saƙonta babba ya ƙunshi wasu
maganganu waɗanda aka gina su da zimmar tsima wani mutum ko a sa masa kuzarin aikata
wani abu nan take. Kalmomin zuga sukan sa mutum ya yi kamar ana tsikarasa har
ya zaburo ya yi wani abu ba tare da da damuwa kuwa ko zai kai shi ga halaka ba.
Mutum ba ya yi wa kansa zuga da kansa, sai dai wani mutum daban ya harguɗa shi. A wannan yanayi ne zuga ta bambanta da kirari, mutum na iya yi wa
kansa kirari, sannan yana iya yi wa waninsa kirari (Gusau, 2001:36-37).
2.0 Taƙaitaccen Tarihin Makaxa
Sa’idu Faru
Makaɗa Sa’idu Faru mutumen garin Faru ne ta cikin ƙaramar Hukumar Maradun da ke Jihar Zamfara. An haife shi ne a wajajjen
shekara ta 1932. Sunan mahaifin Sa’idu Faru shi ne Abubakar Ɗan Abdu. Kakaninsa su ne makaɗa Abdu, da Abu mai Kurya, dukkan waɗannan makaɗa an yi su ne a garin Faru, sai dai mahaifiyar Sa’idu Faru mutumniyar Banga
ce ta cikin ƙasar Ƙaura- Namoda ce, kuma a can aka haife ta. (Gusau, 2005).
Ana kuma yi masa laƙabi da “Ɗanumma” wanda matar ƙanen ubansa ta sanya masa, saboda ba ya faɗin sunanta, sai dai yana kiranta Umma. Shi ya sa ita kuma ta dinga kiransa Ɗanumma, amma wannan laƙabi bai shahara a tsakanin mutane ba, balle ya danne sunansa na yanka watau
Sa’idu. Shi kansa Sa’idu Faru yakan yi wa kansa da kansa kirari yana cewa:
Jabora: Ɗan umma Rungumi
: Ɗan Tumba Rungumi
Yawancin ƙurciyar Sa’idu Faru ya yi ta a garin Banga ta Ƙaura- Namoda inda aka haifi Uwarsa, amma kafin ya girma ƙwarai sai ya koma wurin tsohonsa makaɗa Abubakar a Faru. Sa’idu Faru kamar
sauran makaɗan fada ya yi gadon kiɗa ne ta wajen mahaifinsa. Kakansa na
sama makaɗa Alu makaɗin Kurya ne ta kiɗin yaƙi wadda aka yi wa kirari da “Kurya Gangar Mutuwa”. Makaɗa Alu ya yi waƙoƙi da yawa a zamanin yaƙi, sai dai ba za a iya kawo shi a yanzu ba saboda tsawon lokaci. (Gusau,
2005:17).
Makaɗa Sa’idu Faru an sa shi makarantar Allo inda ya yi zurfi ga karatun Alƙur’ani mai tsalki. Amma bai sami ilimin
Muhammadiya da yawa ba. Haka kuma ba a sa shi makarantar boko ba, domin haka
bai san komai ba game da sha’anin boko. Alalhaƙiƙa tun makaɗa Abubakar, waƙoƙinsa suka daɗa kyautatuwa ta hanyar Fasaha da hikima tare da ƙwaƙwalwar da Allah ya ba shi. Tun Sa’idu
Faru yana da shekaru goma aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gari- gari. Bayan da ya cimma shekaru goma sha shida ya soma karɓi, amma a wannan lokaci ne kuma aka haɗa su tare da ƙanensa Mu’azu wanda shi ne Ɗangaladimansa a
halin yanzu.
Bayan ga tsohonsa makaɗa Abubakar, Sa’idu Faru bai koyi kiɗa ga kowane makaɗi ba, dukkan salailai iri- iri da yake sakawa a waƙoƙinsa tushensu mahaifinsa da baiwar da
Allah ya ba shi ta gane fasalin waƙa. Da tsahon Sa’idu Faru ya rasu,
sai ya ɗauki gabata waƙa, ya sa himma da ƙwazo yana ta yi har zuwa yau.
Da Sa’idu Faru ya samu cin gashin kansa, ya fara da wata waƙa mai daɗin gaske, ƙunshe da hikimomi. Ga kaɗan daga cikinta:
Gindin waƙa: Ba da maza Ɗan Joɗi na iro,
: Iro magajin Shehu da Bello.
: Hasken hitila ba ɗai da wata ba,
: Tauraro haskenka subahin,
: Dawaya kora ɗimau na waƙili,
: Uban Sarkin zagi Bello na yari,
: Ruwa da kada ɗibgau na magaji,
: Sai tsohon wawa ka shigarsa.
Wannan waƙar da ya fara yi ita ce wadda ya yiwa
tsohon Sarkin Yamman Faru Ibrahim. Daga nan Sa’idu Faru ya ci gaba da yi wa Sarakuna da ‘ya’yan Sarakuna waƙoƙi, har zuwa lokacin da ya sadu da
Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Ɗan Sarkin Musulmi Abubakar. Ya soma yi wa Sarkin Kudu Macciɗo waƙoƙi tun lokacin da yake Talata- Mafara yana riƙe da muƙamin Sarkin Gabas watay Uban ƙasar Talata- Mafara. Daga cikin waƙoƙin da ya yi masa akwai wannan:
Gindin waƙa: Kana shire baban yanruwa,
: Na Bello jikan Ɗanfodiyo,
Jagora: Gardaye zo ka yi man iso,
: Faɗa mashi murna nizzaka,
: Ɗan Sardauna jiman Hassan.
‘Yan amshi: Babban ɗa ga Baura Sarkin kudu,
Na Alƙali baban zagi,
Mai ja ma ya bari Ɗan Amadu.
Jagora:: Na Sarkin Gobir Amadu,
‘Yan amshi: Ci fansa ga wan Sarkin ƙaya.
Jagora: : Alhamdu Lillahi duk kan nuhi,
‘Yan Amshi : Rabbul- alamin ni nau nuhi.
Jagora:: Ka san kiɗi ba karatu ba ne,
‘Yan amshi: Ballanta mai Istigifari in mun gama.
Jagora: Alhaji baba MuhammaduMacciɗo,
‘Yan amshi : Baba barka da hayawa Maliya.
Jagora: Yan Jidda sun tariya da kyau,
‘Yan amshi: Domin sun ga Muhammadu Macciɗo,
: Bajimi jikan Ɗanfodiyo,
: Mai gaba da kai bai sha daɗi ba.
(Sa’iduFaru: Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo)
Makaɗa Sa’idu Faru Allah ya albarkace shi da matan aure guda uku (3) tare da
‘ya’ya ishirin da shida (26) maza da mata, a cikin sha ɗaya (11) sun rasu, sauran goma sha biyar (15), yana kuma da Jikoki kimanin
ishirin (20). (Gusau,2005:125).
Makaɗa Sa’idu Faru yana shirya waƙarsa a gida kafin ya fita zuwa ga wanda zai yi wa ita. Sannan zai dinga
bitar ta kimanin kwana biyu domin ta zauna a ƙirjinsa da ya isa wurin wanda zai yi wa waƙar, ya san wadda zai yi masa kai tsaye. Wata ko takan zo ba shirya ta ba,
amma sai in an riga a san sunayen iyayen Sarkin da na kakaninsa da na sauran
danginsa. Waƙar da aka shirya a gida ta fi wadda aka
yi kai tsaye a wurin wasa tsaruwa da daidaituwa. Ga ɗan waƙa wanda Sa’idu Faru ya nuna a cikinsa yana tsayawa gida ya shirya waƙoƙinsa. Shi ne:
Jagora: Ga waƙa nan wadda nay yi yima,
‘Yan amshi: Ɗa tara ta mun bar takwas gida,
: Sai in kai murnaz zaƙƙwawarmu,
: In aika ka yanzu su taho,
: Mu ka kiɗi mu ak kiɗi saboda mu,
: Allah yay yi wa gudummuwa,
: Da waƙa haw wata na iya wata.
(Sa’idu Faru: koma shirin daga na Bubakar Waƙar Yawuri Muhammadu Tukur).
Makaɗa Sa’idu Faru bai yi wa wanda ba Sarki ba waƙa ba, kuma ya tabbatar da cewa ba zai taɓa yiwa wanda ba Sraki waƙa ba. Daga cikin Sarakuna da Hakimai da ‘ya’yan Saraki da ya yi wa waƙoƙi akwai:
Ø SarkinYamman Faru Ibrahim
Ø Sarkin Yaƙin Banga Sale da Abubakar
Ø Sarkin Kiyawa Abubakar Ƙaura- Namoda
Ø Sarkin Gabas Na Mafara Muhammadu
Ø Sarkin Musulmi Abubakar III
Ø Sarkin Yawuri Alhaji Muhammadu Tukur
Ø Sarkin Sudan Na Wurno Alhaji Shehu
Ø Sarkin Kano Ado Bayaro
Ø Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
Ø Turakin Kano Amadu
Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin Sarakai da Hakimai da ‘ya’yansu da ya yi wa waƙa. (Gusau, 2005:121).
Sa’idu Faru yana amfani da kayan kiɗa na kotso. Kuma yana da yara masu yi masa
karɓi a waƙa, daga cikinsu ƙanensa Mu’azu Daudun kiɗa watau Ɗangaladimansa. Sai Daudu da kuma Ali.
Waɗannan su ne masu taimaka masa a wajen waƙa.
Makaɗa Sa’idu Faru ya rasu a sanadiyar wata rashin lafiya da ya yi fama da ita,
a wajajen shekarar 1994. Allah ya jiƙansa da Rahama amin.
3.0 Turken Yabo
A turken yao akwai abubuwa da adama da kan sa makaxa suke amfani da su yabi
wanda suke yi wa waƙa. Misali, yabo na
asali ko na kyauta ko jarunta ko na iya gudunar da mulki da makamantansu. Ga
misalin yabo a cikin wasu waƙoƙin na Sa’idu Faru.
Gindin waƙa:Kana shirye baban ‘yanruwa,
: Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
Jagora: Gardaye zo kayi man iso,
: Faɗa mashi murna niz zako.
‘Yan Amshi : Babban ɗa ga Baura Sarkin Kudu,
: Na alƙali baban zagi,
: Mai ja ma ya bari ɗan Adamu.
Jagora : Na Sarkin Gobir Amadu.
‘Yan Amshi : Ci fansa gagon Sarkin Ƙaya.
(Sa’idu Faru: Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).
Ida aka duba waɗannan ɗiya waƙa za a ga cewa ɗauke suke da bayanin turken yabo, musamman ma yabo kan
asali a nan mawaƙin yana yaba Sarkin da cewa shi jika ne
ga Shehu Usmanu Ɗanfodiyo kuma ɗa yake ga Baura. Anan ana yaba basarake a kan asalin inda ya fito, wato shi
zuri’ar Shehu Ɗanfodiyo ne.
Makaɗa Sa’idu Faru ya ci gaba da amfani da turken yabo a cikin waƙarsa ta Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo, inda mawaƙin ke cewa:
Jagora: Baba na shamaki mai hana noma.
‘Yan amshi: Baba ganɗon gabas raba kaya.
Jagora: In ga na shamaki mai hana noma.
‘Yan amshi: Baba ganɗon gabas raba kaya.
Duk a cikin waƙar ya ci gaba da
wannan turken na yabo.
Jagora: Ko ni makaɗanka uban zagi.
‘Yan amshi : Na gaji a ba mu dawakuna,
: Na gaji a ba mu jukunkuna,
: Na gaji a ba mu garuruwa,
: Muhammadu in Allah yai nuhi,
: Ba mu gani da mutanenai duka.
Anan mawaƙin watau Sa’idu Faru yana yabon Basaraken ne ta nuna cewa shi Basaraken yana da halin
kyauta saboda halin kyautar da ke gare shi, shi ya sa mawaƙin ya yaba shi. Inda har munga cewa mawaƙin ya nuna cewa saboda yawan kyautar da yake ba su har ya hana su yin noma.
Domin abincinsu da suturarsu duk tana bisa wuyan shi Sarki.
Wani yabo a kan asali ko zuri’a. Mawaƙin na cewa:
Mu’azu: : Dibi ƙafarka zuwa bisa hannuwa,
: Zaman Shaihu ne ba wata za’ida,
: Sarkin Musulmin wata ran kake,
: Da imani da mu’ujjiza.
‘Yan amshi : Na nan ga Malan Macciɗo.
Mu’azu: Tun ga Aliyu mai sango naj jiya,
: Halin ga da Bubakar yar riƙa.
‘Yan amshi : Macciɗo kai ka shirin gado haka.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo)
Idan aka kalli waɗannan ɗiya za a ga cewa yabo ne makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Basarakre. Anan yana yaba shi a kan asali da tushe
ya nuna cewa Muhammadu Macciɗo ya yi kama da Sarkin Musulmi kai shi
ma zai zama Sarkin Musulmi na wata rana, watau shi zai gadi gidan.
Ga misalin wani yabo ta fuskar kyauta.
Gindin waƙa: : Bajinin gidan Bello Mamman na yari,
: Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.
Mu’azu: Faɗo gaskiya Bello kai Shehu yac ce,
: Bari masu so duk su maishe ka yaro,
: Da kyauta da ilmi da neman dalili,
: Da gode wa Allah da Istingifari,
: Da su Bello ɗan Shehu yat tsarma kowa,
: Ka kai kamab Bello ka gadi moyi.
‘Yan amshi : Saura ka kai inda mai hausa yak kai.
Jagora : Baba ya ba mu bandur guda duk na lailai.
‘Yan amshi : Ya ba mu farm goma yac ce mu ɗunke,
: Ga takalumma na fam shidda- shidda,
: Hula kalabus guda goma yab ban,
: Kyauta irin taka jikan Mu’azu,
: Don ba a cewa mutum ba kawatai,
: Sai Larabawan Masar masu girma.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo).
Anan yana yaba shi da kyauta, wanda har ya nuna cewa na wanda ya kai shi
kyauta in ba Larabawan Masar ba.
Wani misalan turken yabo a cikin waƙar Turakin Kano Alhaji Amadu. Mawaƙin na cewa:
Gindin waƙa: Tsakin tama na Abashe,
: Ana shakka haye ma Amadu,
: Mai daraja na Wambai,
: Ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano.
Jagora : Wasu sun yi gidan rediyo na banza.
‘Yan amshi : Ko sisin kwabo ba su ba kowa,
: Satan maroƙa dai sukai,
: Zama wayo ba ya fid da taba,
: In dai ni sha ta babu daɗi watsawwa nikai,
: In tai in biɗo wata inda mai daɗi take.
Mu’azu: : Ɗan Sarkin da ka kyautaj jikka,
‘Yan amshi: : Ɗan Hashim Kano ɗai a haka.
Mu’azu : Ɗan Sarkin da ka kyauta riga.
‘Yan amshi : Ɗan Hashim Kano ɗai a haka.
Mu’azu : Ɗan Sarkin da ka kyautah hawa.
‘Yan amshi : Ɗan Hashim Kano ɗai a haka.
Mu’azu : Ɗan sarkin da ka kyautam mota.
‘yan amshi : Ɗan Hashim Kano ɗai a haka.
: Duk wanda yaz zam irin haka,
: Ko badaɗe shina Sarkin Kano.
(Sa’idu Faru: Waƙar Turakin Kano Alhaji Amadu).
Anan munga cewa mawaƙin yana yaba Basaraken da cewa shi mai kyauta ne ya basu kyautar kuɗi da riguna da mota da kuma har kyautar bayi yi shi kai. Ya kuma nuna cewa
wannan kyautar duk Kano ba mai yinta sai Hashim.
4.0 Turken Zuga
Makaɗa Sa’idu Faru shahararre ne wajen yi wa Sarakuna waƙoƙi don nuna fasaharsa da hikimarsa da
Allah ya bashi, ya yi amfani da turken zuga a cikin wasu waƙoƙinsa da ya gabatar. Misali a cikin waƙarsa da ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo.
Gindin waƙa: Kana shirye baban ‘yanruwa,
: Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
Jagora : Baban mai abu Faru na mai akwai.
‘Yan amshi : Dan giwa kome tad daɗe,
: Na tabbata yin giwa take,
: In ji Sarkin Burmin Birnin Kaya.
Jagora : Babban daji kake ɗan Abu,
: Ko icce ko namun dawa,
: Ko manya ko ‘yan ƙanƙana.
‘Yan amshi : Kowa ƙamam Mamman shikai,
: Mamman jikan Attafiru,
: Baba na sidi Mamman gwarzon cika.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).
Anan mawaƙin yana zuga Basaraken da cewa shi ɗan Sarki komi tad daɗe sai ya yi sarki kuma shi babban daji
ne hatta da itace ƙamnarsa suke.
Wani misalan zuga a cikin waƙar Sarkin Fulanin Bunguɗu Alhaji Shehu. Sa’idu Faru na cewa:
Gindin waƙa: Koma shirin yaƙi,
: Jan damishin gidan kure Shehu.
Jagora : Na Garba.
‘Yan amshi: Bai da abokin baranke babban maifada.
Jagora : Zaure mijin gida.
‘Yan amshi: Ɗan Amadu koway yi gum da kai,
: Bai cin riba.
Mu’azu: Shehu ya yi iyaka ƙaura,
: Shehu ya yi iyaka ƙaura,
: Ya yi iyaka ƙasar Maradun,
: Nan Kudu bai da.
‘Yan amshi: Iyaka, Baciri da nan har tabkin Chadi.
Jagora: Nan Kudu.
‘Yan amshi : Bai da iyaka Baciri da nan har tabkin Chadi.
Jagora : Nan Kudu.
‘Yam amshi: Bai da iyaka, Baciri da nan har tabkin Chadi.
(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Fulanin
Bunguɗu Shehu).
A nan mun ga cewa mawaƙin yana zuga Basaraken da cewa a fagen yaƙi gwarzo ne kuma kowa ya yi kabra da shi to ba ya cin riba. Mawaƙin yana koɗa Sarkin da cewa yana ban tsoro da firgitarwa a fagen daga.
A ci gaba da amfani da turken zuga a cikin wasu waƙoƙin Sa’idu Faru. Mawaƙin ya yi amfani da
zuga a cikin wata waƙa wadda ya yi wa
Turakin Kano Amadu. Mawaƙin na cewa:
Gindin waƙa: Tsakin tama na Abashe,
: Ana shakka haye ma Amadu,
: Mai daraja na Wambai,
: Ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano.
Jagora : Toron giwa ba togewa.
‘Yan amshi : Ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano
Jagora: Tsaye da kyawo zamne da kyawo.
‘Yan amshi: Amadu kanfaragin Sarkin Fada,
: Kasarmin Galadiman Kano,
: Kurum kake mai ban tsoro,
: Ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano.
Jagora: : Baba kware kake.
‘Yan amshi : Ba faɗawa ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano.
(Sa’idu Faru: Waƙar Turakin Kano
Amadu)
Dangane da waɗannan ɗiya waƙoƙi idan an kalle su, Sa’idu Faru yana zuga Basaraken da cewa shi tsakin tama
ne bai tamnuwa, kuma shi toron giwa ne ba a taron gabansa. Kuma kware ne kowa
ya faɗa zai kare ƙafa. Wannan duk zuga ce yake yi wa shi
Turakin Kano. Haka kuma ya nuna mana cewa shi ba a haye masa domin ana
shkkarsa. Mawaƙin yana koɗa gwaninsa da cewa shi tsakin tama ny ya buwayi tamna, kowa tamni yanzu haƙoransa na zubewa.
Sa’idu Faru ya yi waƙoƙi ne na Sarakuna waɗanda suke sha’awar a dinga kwarzonta su ana fifita su a kan talakawansu, da
ma wasu ‘ya’yan Sarakuna. Haƙiƙa, Sa’idu Faru gwani ne wajen shirya waƙoƙin zuga, kuma ya kan ɗora su a wuraren da suka dace. Daga ciki misalan waƙoƙin zuga akwai waɗannan:
Gindin waƙar: Gwabron giwa na shamaki baba uban Gandu,
: Abu gogarman magaji mai kamsakali daga,
: Ni kiɗan yaƙi nay yi ma Abu na Isau,
: Ba ni son kana zaunawa banza,
: Ka ɗauki takobi da bindigogi da bakunkuna,
: Ka sa sirdi,
: Ma bu sansani sai bakin Tsahre,
: Kano da Katsina, Kwantagora hak Kazaure,
: Riƙon Namoda na, shi na ac can,
: Garba ka amshe riƙon duk da Umaru,
: Umaru yab bam ma.
(Sa’idu Faru: Sarkin Kiyawa Abubakar Ƙaura- Namoda).
Gindin waƙa : Gwabron giwa uban Galadima,
: Ɗan Sambo gimshimi,
: Gamshiƙan Amadu na mai Gandi,
: Kai a uban zagi,
Jagora: Gogarman,
: Namoda bai magana wani ya walwalat,
Jagora : Banda da gudu han da razana,
‘Yan amshi: Ka san Sarki ba shi waiwaye,
: Ko da jan D.O yag gani,
Jagora : Ka san Sarki,
: Ba shi waiwaye, ko da jan Gwamna yag gani.
(Sa’idu Faru: Sale Sarkin Yaƙin Banga)
5.0 Sakamakon Bincike
A wannan bincike ko nazari da aka gudanar, an gano cewa makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da turakun yabo da kuma zuga a cikin wasu waƙoƙin nasa, wanda mafi yawan su yafi
amfani da su wajen tsara waƙarsa, domin isar da saƙo ga masu sauraro. Haka kuma, an gano cewa, tun lokacin da Sa’idu Faru ya
haɗu da Sarkin kudu Macciɗo kafin ya zamo Sarkin Musulmi bai tafi
zama ƙarƙashin wani Basarake ba face shi. Sa’idu Faru makaɗan sarakuna ne, kuma yana amfani da kotso a matsayin kayan kiɗansa domin shi ya tarar ana kaɗawa a gidansu. Binciken ya gano wani laƙabi da aka yi wa Sa’idu Faru wato “Ɗanumma”, ko “Ɗan Inna” kuma wannan laƙabi matar mahaifinsa ta sanya masa, duk da yake ba a faye kiransa da shi
ba, amma yana bambanta shi a cikin waƙa idan yana yi wa kansa kirari yana cewa: “Ɗan Tumba Rungumi” ko “Ɗanumma Rungumi”. Kuma bincike ya
gano cewa makaɗa Sa’idu Faru mutum ne mai balagar waƙa kuma ga hikimar da Allah ya hore masa ta shirya waƙa kuma ya tsarata ta yi daɗi ba wata gargada ko kwa-gaba-kwan-baya.
Binciken ya gano cewa Sa’idu Faru gadon kiɗa ya yi ba haye ba.
6.0 Kammalawa
A takardar kamar yadda aka gani mun yi bayani ne a kan wasu muhimman
turakai a wasu waƙoƙin Sa’idu Faru. Turakun da wannan takarda ta
dubo su ne turken yabo da zuga. An yi bayanin kowanensu daidai gwargwadon hali
tare da kawo fitattun ɗiya daga wasu waƙoƙin don kafa hujja. Ko shakka babu Sa’idu Faru ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa adabin al’ummar Hausawa da ingantasu. Ana fata za
ta zama mai amfani ga ɗaliban ilimi a dukkan matakai, da ƙalubale gare su wajen yin zuzzurfan nazari a wannan ɓangare.
Manazarta
Gusau, S. M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano. Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2005) Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano. Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Kano. Benchmark
Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da
Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers
Limited.
Gusau, S. M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2014) Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Biyu. Kano. Century Research and Publishing
Limited.
Gusau, S. M. (ND)Sarkin Taushi Salisu Jankiɗi. Kaduna Baraka Press and Publishers Limited
Ibrahim, M. S. (1983), Kowa Ya Sha Ƙida. Lagos. Longman Nigerian Plc.
Yahya, A. B. (1997) Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna Fisbas Media Service.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.