Citation: Ahmad, A.A. (2024). Waƙa-Kwaikwaye: Zaƙulo Wasu Sigoginsa Daga Bakin Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 56-61. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.007.
Waƙa-Kwaikwaye:
Zaƙulo
Wasu Sigoginsa Daga Bakin Sa’idu Faru
Daga
Aliyah Adamu Ahmad
Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya,
Jami’ar Jihar Sakkwato,
Sakkwato.
Lambar Waya: 08095059926,
08133314217
Imel: aliyahadamu@yahoo.com,
drpullo@gmail.com
Tsakure
Nazarin
tsari a cikin waƙoƙin makaɗa da mawaƙa ba
sabon abu ba ne, ana samun irin wannan take (nazarin zubi da tsari) a cikin
kundaye da litattafai da dama. Amma tsarin waƙa-kwaikwaye
a matsayin waƙa ba
duk ɗalibai
suka waye da shi ba. Ba kuma kowane mawaƙi ya waye da yin amfani da shi a
matsayin salon tsattsafin waƙoƙinsa ba,
wato tsarin da yakan bijiro da shi cikin tsari
na gaba ɗaya na
waƙoƙinsa da
aka saba, ko da kuwa yana naɗe a bakinsa da cikin waƙoƙinsa,
sai a taras bai san yana amfani da shi tsarin ba. Domin tallata wannan tsari, a
sake fahimtarsa, a ci gaba da amfani da shi, aka nemi zuwa da wannan maƙala
wadda za ta yi tsokaci kan wannan tsarin har aka yi ƙoƙarin
mene ne sabo wanda ba a faɗa ba a ambata
sosai ba a maƙalar
farko a kan shi waƙa-kwaikwaye
amma sai aka ga shi cikin waƙoƙin
Sa’idu Faru. Bayan an saurari waƙoƙinsa
biyu, da na wanda yana ɗan
sarki da wanda yana sarki ya yi musu waƙa, da aka kalato a hannun waɗanda suka tanade su, an nemi ƙarin
bayani a hannun masu sha’awar waƙoƙinsa,
da wasu malamai masu nazarin waƙoƙin waɗanda kuma suka ji daga wasu
iyalansa domin ƙarin
fahimta. Abin da wannan maƙala ta
fahimta shi ne, Sa’idu Faru lalle gwani ne na bijirowa da wannan tsari na waƙa-kwaikwaye,
ta kuma fito da wasu sigogi aƙalla biyu da wannan tsari yake
da su. Bayanan da ke biye sun tabbatar da hakan.
Gabatarwa
A
shekara ta 2021 da
aka gabatar da sakamakon wani bincike da mai wannan maƙala ta
kira ‘Waƙa-kwaikwaye:
Daɗaɗɗen Adabin Hausawa na Auren Waƙa da
Wasan kwaikwayo’[1],
an bayyana ma’anar waƙa-kwaikwaye
kamar haka:
Abin da ake nufi da
waƙa-kwaikwaye a wannan maƙala shi ne, waƙar da aka tsara ta
yadda za a ji ko kalli aiwatarwarta tamkar ana sauraren ko kallon waɗanda ke magana tamkar
cikin wasan kwaikwayo ne ake gabatar da su. Maganar cikin waƙa-kwaikwaye kan
kasance ta wasu ce ba ta mawaƙin ba. Haka kuma waƙa ce wadda ita ce
gimshiƙin wasan kwaikwayon da ta ƙunsa kuma harshenta
da salonta duk na waƙa ne da ke taimakawa
ga bayyana duk wani saƙo da mawaƙin yake son ya isar
ga jama’a. Wannan tsari da aka kira waƙa-kwaikwaye akan same
shi cikin waƙar baka da kuma rubutacciyar
waƙa. (Aliyah, 2021, sh.19)
Haka nan kuma an
bayyana muhimman sigogin da wannan waƙa ta ƙunsa, wato salon hira
da na zayyana da na labari, to amma akwai wasu waɗanda su ma sukan taka rawa kamar
rerawa musamman idan waƙar ta fito a sutudiyo aka rera ta ko aka yi ta domin a
saka ta ciki.[2]
Tun bayan rubuta
wannan maƙala aka ci gaba da nutsar da bincike a kan waƙa-kwaikwaye, musamman
fitowar batun gudanar da wannan taro na ƙasa da ƙasa a kan rayuwa da
waƙoƙin Sa’idu Faru Malamin
Waƙa
Mai Kwana Ɗumi na Mamman na Balaraba. Babbar ribar da wannan
muhimmin taro ya haifar tun
ba a kawo ga wannan rana ta gudanar da shi ba ita ce samar da zauren tattaunawa
yau kusan watanni huɗu. Cikin wannan
tattaunawa lalle an yi ta musayar ra’ayi dangane da Sa’idu Faru da waƙoƙinsa, an kuma anfana sosai.
Wasu waƙoƙin mawaƙin da ba a sani ba an same su a wannan
zaure. Akwai ma wani wanda aka yi ta konkomawa gare shi don a samu waƙoƙin da ba a da su, ko
biɗar ƙarin bayani game da
su. Wannan bawan Allah shi ne Alhaji Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin
Magaji, wanda ko cikin lokacin da ya tafi jinya bai daina bayar da gudummuwar
ba. Sauran ribar kuwa ga ta nan kullum muna samu daga maƙalun da ake
gabatarwa. Ita ko mai wannan maƙala ga ‘yar tata
gudummuwa nan kusa a gaban mahalarta.
Waƙa-kwaikwaye daga Malamin Waƙa
Lokaci da fili ba za
su bari a baje kolin ribar da mai wannan maƙala ta samu ba sakamakon
yin kurma cikin waƙoƙin Sa’idu Faru, sai dai ta ɗan ƙyallaro ɗaya ko biyu. Akwai
sauransu tuli ta baro gida kamar yadda “malamin waƙa mai kwana ɗumi” ya bar waƙoƙi tara gida lokacin
da ya je da guda inda Sarkin Yawuri! Ga ƙyallarowar nan a
gabanku.
Lalle Waƙa-kwaikwaye Daɗaɗɗen Tsarin Waƙa Ne
Ƙara samun ƙwarin gwiwa kan iƙirarin cewa waƙa-kwaikwaye daɗaɗɗen tsarin waƙa ne na Hausawa, ya
samu ne saboda samun sa cikin waƙoƙin Sa’idu Faru. An
san cewa Faru bai yi makarantun boko ba balle a ce daga waƙoƙin Turai ya koyi yin
irin wannan waƙa. Da ma maƙalar farko ta
tabbatar da haka ta kawo misalai
daga waƙoƙin baka da rubutattu na da da na yau. Sa’idu
Faru ƙarin tabbaci ne. Waƙoƙin biyu da aka yi
nazari a nan sun ƙunshi wannan tsari na waƙa-kwaikwaye
aƙalla
har sau biyar. Waƙar da mawaƙin ya yi wa Sarkin
Kudu da take da rerawa biyu ko uku, ‘Gardaye Zo Kai Man Iso’ ko kuma ‘Kana
Shire Baban ‘Yan Ruwa’, ta ƙunshi tsarin har sau huɗu, uku a jere, ɗaya a daban. A cikin
wannana waƙa akwai tsarin waƙa-kwaikwaye da ya ƙunshi mawaƙin da kuma wasu mutane, sannan akwai wanda ya ƙunshi mawaƙin da tsuntsaye. Ga
misalai biyu daga waƙar:
Da mutane:
Ina ƙamnak ka Muhammadu
Na tabbataƙ ƙamna ta kakai
Ko kai niyyab ba mu dawakuna
Samnan bahwade sara yakai
Ya ce ko ka ba mu dawakuna
Ran da Sallah ka tashi Ƙaura mukai
Ya ce ko ka ba mu dawakuna
Ran da Sallah ka tashi Ƙaura mukai
Mamman Haraka sai yaj jiya
Yac ce kai ko ƙarya kakai
Ƙaura da Gusau da Kwatarkwashi
Ɗangulbi da Bunguɗu ham Maru
Duɗ ɗai na ga Mamman Sarkin Kudu
Ɗan Dikko yana can yaj jiya
Wannan magana ta tabbata
Da’ inda rana ka fita gabas
Har inda rana taka faɗuwa
Duɗ ɗai na ga jikan Ɗanhodiyo
Babu inda mulkinai yat tsaya
(Sa’idu Faru: Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa).
A wannan ɗan waƙa ana iya a fahimci
cewa mawaƙin yana faɗa wa ubangidansa Sarkin Kudu cewa akwai wani wawan
bafade daga cikin yaransa wanda ke zaton yana iya ya yi makircin da zai hana
ubangidan yin alheri ga jama’a. A nan waƙa-kwaikwaye ne mawaƙin yake ƙoƙarin ya tsara wanda
ya shafi shi mawaƙin da ubangidansa. To amma tsarin na waƙa-kwaikwaye bai fito
sosai ba saboda babu magana daga ubangidan. Sai fa idan mun ƙaddara maganar da zai
iya yi, wato a taƙaice mu ɗauka cewa shafe maganar ne mawaƙin ya yi. Yin wannan ƙaddartawa ba laifi ba
ne a nazarin waƙa. A kan haka muna iya mu ce maganar da Sa’idu Faru ya
shafe ita ce ta ubangidan, wato, ‘wane ne wannan bafade, Sa’idu Faru?’. To amma
sai ma mawaƙin ya hutar da manazarcin waƙarsa ko mai sauraren
ta ta hanyar fitowa ƙarara da tsarin na waƙa-kwaikwaye. Mawaƙin ya kawo muna
martanin da wasu fadawan (?) Sarkin Kudu biyu suka yi wa wannan saunan bafade.
Sun mayar da martanin kamar a zahiri ko halarce, ga su nan
ga bafaden a gabansu.
A jimlace a wannan ɗan waƙa za a fahimci cewa
mawaƙin ya yi amfani da salon tsattsafi ya saka tsarin waƙa-kwaikwaye ciki,
tana ƙyalli kamar kwalli a kan daɓe.
Da kuma tsuntsaye
Can na taɓa yat tafiya kaɗan
Sai ni’ ishe burtu na kiyo
Shina ta waƙas Sarkin Kudu
Rainai ya daɗe Sarkin Kudu
Alisabbinane ɗan Amadu
Allah shi ƙara mai nasara
Nic ce burtu waƙa akai
Yac ce lalle waƙa nikai
Waƙam Mahamman Sarkin Kudu
In na yi ta za ni wurin kiyo
In niz zo abinci sai na ije
(Sa’idu Faru: Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa).
Wannan shi ne tsarin waƙa-kwaikwaye na uku cikin ita waƙar saboda kamin sa akwai wani inda mawaƙin ya ci karo da suda uwar tsuntsaye. Ita ma tana rera waƙar nan da mawaƙin ya yi wa Sarkin Kudu.Shi burtu cewa ya yi waƙar ta zamar masa tamkar wani du’a’in da yake yi idan zai je
kiyo. Wannan magana ta burtu ta bambanta da ta suda wadda ta ce
saboda jin daɗin da take ji sai da ta sa a ranta cewa da sarauta
take yi da ta ce ma Sa’idu Faru ya yi mata waƙa kamar wannan ta Sarkin Kudu.
A lura da cewa cikin waɗannan misalai biyu duka ana samun salon hira da na labari: hira tsakanin tsuntsayen da mawaƙin; labari wanda mawaƙin yake ba ubangidansa. Duk kuwa waɗannan salailai suna cikin muhimman sigogin tsarin waƙa-kwaikwaye.
Ita kuwa waƙar da mawaƙin ya yi wa Sarkin
Zamfaran Zurmi, da take da amshin, /Wada Yaz zo Da Lafiya Na Kanau Ya Dawo da
Girma//Bajinin Sardauna Amadu Mai Takakka Ga Arna/, tana da shi wannan tsarin
sau guda, duk da yake a ciki an tsinci wata sigar da bayani zai zo a kanta a gaba
kaɗan.
Alibawa kuna ganin
hwansakku wurin Sule babu dama
Giwa ta sha ruwa tai
miƙa
ta taushe gurbi
Alibawa kuna ganin
hwansakku wurin Sule babu dama
Giwa ta sha ruwa tai
miƙa
ta taushe gurbi
Kuma ‘yan ɗiyanta sun shiga
Sun sha su fara ƙarhi
Kuma ‘yan ɗiyanta sun shiga
Sun sha su fara ƙarhi
‘Yan namu suna jin ƙisa ba damar su kurɓo
‘Yan namu suna jin ƙisa ba damar su kurɓo
Sai bil’amu uban
dibara
Shi ɗai yaz zo ga giwa
Sai bil’amu uban
dibara
Shi ɗai yaz zo ga giwa
Albarkacinki niz zaka
In samu ruwan danis
sha
Albarkacinki niz zaka
In samu ruwan danis
sha
Giwa ta ba shi fili
Ya samu ruwan dayas
sha
Ya sha ya kuma ba ɗiyanai
Ya wa dangi kirari
Yac ce ya ƙwato da ƙarhi
Zomo ya ce
tsaya shege
Lallashin ta kay yi
In ƙarhi gaskiya na
Koma ebo gabana
(Sa’idu Faru: ‘Wada
yaz zo da lafiya, Na Kanau Kuma Ya dawo da Girma’ Sarkin Zamfaran
Zurmi Sule).
Cikin wannan ɗan waƙa a fili tsarin waƙa-kwaikwaye yake inda
za a ga dila (bil’amu) da zomo da mawaƙin ya kawo su suna magana
da juna. Haka kuma ga giwa ita ma mawaƙin ya saka ta cikin
waƙa-kwaikwayen,
to amma sai gaba za mu kawo bayanin shigarta ciki.
Wannan waƙa-kwaikwaye ƙunshe yake da salon
labari da na hira da kuma na zayyana. Mawaƙin ne yake ba masu
sauraren waƙarsa bayani game da ‘ya’yan sarki, abokan jayayyar
gwarzon mawaƙin, wato Sarkin Zamfaran Zurmi Suleiman. Wannan bayani da
mawaƙin ke bayarwa turken habaici ne cikin
salon labari.
Har yanzu dai wannan ɗan waƙa ya tilasta masu
saurare da ganin giwa ta fake rafi bayan ta shiga ciki ta sha ruwa ta fito ta
yi miƙa, ‘ya’yanta su ma sun zo sun shiga rafin sun sha ruwa su
ma sun fara walwala. Ita kuwa giwa tana nan tsaye bakin rafin. Masu sauraren waƙar har yanzu da idon
zukatunsu suna ganin sauran dabbobin daji da ba su kai girma da ƙarfin giwa ba, tsoro
ya hana su shiga wannan rafi duk kuwa da ƙisar da ta haddabe
su.To amma Sa’idu Faru
ya tuna muna cewa dila (bil’amu) da yake mai dibara ne da wayo cikin dabbobi
sai ya tafi inda giwa ya yi ta yi mata fadanci har ta amince mai da ya shiga
rafi da shi da ‘ya’yansa su ɗebe ƙisar da
ta dame su. Da ya sha ruwa shi da ‘ya’yansa sai ya tafi wurin sauran dabbobi ya
yi musu alfahari tare da cewa shi da ƙarfi kuma bisa ga dole
giwa ta bar shi ya sha ruwa, da shi da ‘ya’yansa! To amma daga cikin ƙananan
dabbobin akwai kuma wani mai hankali, wato zomo. Zomo bai yarda da fankamar da
dila ya yi masu
ba, cewa wai da ƙarfi ya
je ya sha ruwa wai giwa tana wurin tana kallo ta bar shi ya sha ruwa wai don ba
ta iyawa da ƙarfin
dila! Shi ne zomo ya ce
ma dila idan har da
gaske ne ƙarfi ya
nuna wa giwa to ya koma a gabansa ya sake ɗebo ruwan
don kowa ya sheda!!
Duk fa
wannan tsarin waƙa-kwaikwaye
cikin salon zayyana da salon hira ne mawaƙin ya kawo shi tare kuma da
salon labari. Masu sauraren waƙar
za su kasance waɗanda
tsarin waƙa-kwaikwaye
ya yi tasiri a kan zukatansu.
Haka
nan kuma duk waɗannan
misalai sun fito ne daga bakin mawaƙin da ya rayu cikin daɗaɗɗiyar
al’ada, wanda kuma ba makarantar Boko ya yi ba balle a ce daga adabin baƙi ne ya
naƙalto
tsarin waƙa-kwaikwaye.
Tsarin adabin Hausawa ne daɗaɗɗe.
Tsari ne wanda ana iya cewa yana cikin jinin ɗan
Adam, Bahaushe kuwa ko tantama babu yana cikin ‘ya’yan Adamu.
Sigar Shafe ko Haɗiye Magana ko Giɓin
Jimla
Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo ya yi bayanin
‘giɓin
jimla’, abin da a nan nake son in kira ‘shafe magana’ ko ‘Haɗiye magana’, cikin
aikinsa kamar haka:
(abin da ake nufi da
giɓin
jimla shi ne) Sau da yawa za a ga akwai wurare a cikin waƙa inda za mu iya cewa
an bar giɓi
wanda ake fatan mai karatu ko mai sauraro ya cike da fahintarsa. (Ɗangambo, 2007, sh.
56).
Mai maƙalar nan ta bi sahun
malaminta, da cewa a cikin waƙa-kwaikwaye akan ci karo da inda mawaƙi ya bar giɓin magana,
la’alla kalma ɗaya ce ko kalmomi da dama
ko ma jimla ko jimloli sukutum, kuma mai karatu ko saurare ne mawaƙi ke nufin ya cike giɓin.
A cikin waƙar Sarkin Zamfaran Zurmi Sule, Sa’idu Faru ya yi irin
wannan nufi yana cewa:
Sai bil’amu uban
dibara
Shi ɗai yaz zo ga giwa
Albarkacinki niz zaka
In samu ruwan da nis
sha
Albarkacinki niz zaka
In samu ruwan da nis
sha
Giwa ta ba shi fili
Ya samu ruwan da yas
sha
Ya sha ya kuma ba ɗiyanai
(Sa’idu Faru: ‘Wada yaz zo da lafiya, Na Kanau Kuma Ya dawo da Girma’ waƙar Sarkin Zamfaran Zurmi Sule)
A nan akwai shafe magana
har sau biyu. Wuri na farko shi ne tsakanin layi na biyu da na uku. Mai saurare
yana iya cike giɓin
da, /Ya ce/ wanda zai haɗe da layin na uku sai
ya zamo /Ya ce
albarkacinki niz zaka/.
Shi kuwa wuri na biyu
mai irin wannan haɗiye magana ya biyo
bayan da dila ya ce, / In samu ruwan danis sha/. Maganar da mawaƙin ya haɗiye ita ce zuciyar
mai saurare ke iya cikewa kamar haka:
Sai giwa tac ce kak ka damu
Dila na ba ka dama
Shiga ka sha ruwa
To amma shi mawaƙin bai faɗi wannan magana ba
saboda ba ta zama ita ce
muradinsa ba. Muradin yana can gaba inda ƙaryar da dila ya yi
shi kuwa zomo ya ƙure shi da neman ya je ya ɗebo ruwan daga tafkin a gabansa. Haɗiye maganar da mawaƙin ya yi bai hana shi
gina waƙa-kwaiye ba ko ya yi amfani da salon hira ko labari balle
zayyana ba..
2.0.3Mawaƙi Cikin Waƙa-kwaikwaye
Mawaƙi ma kan shiga cikin
waƙa-kwakwayen
da ya yi. Abin da ake nufi a nan shi ne mawaƙin ya kasance shi ne
ke bayar da labarin abin da ke faruwa tsakanin fitattun waɗanda ke cikin waƙa-kwaikwayen da ya saƙa. Ya yi amfani da
salon labari amma shi ne da kansa mai fitowa cikin salon. To sai dai a lura da
cewa mafi yawan waƙar da ke ƙunshe da salon labari a
zahiri mawaƙin ne yake cikin salon.
Cikin wannan ɗan waƙa da ke a nan ƙasa za a ji mawaƙin ne yake amfani da
salon labari cikin waƙa-kwaikwaye.
Waƙag ga da nay maka
Mammadu
Tun dak
Kabi
Na ji
daɗin ta Mamman Sarkin
Kudu
Tun dak
Kabi hak Kano ham Masar
Hab
birnin Legas hab Bici
Kowa ya ji waƙas Sarkin Kudu
Ni ko daɗinta
da nij jiya
Can dauri zaman daji mukai
Da kay yi waƙas Sarkin Kudu
Mamman yaɗ
ɗaukan yar riƙa
Mun san manyan mutane ƙwarai
Mun san ƙananan mutane kuma
Mun kammala dum mun ƙasura
Barwa mu shidda muna gume
Sarkin makaɗammu shina gaba
Duk kowane tashi ƙawa daban
Yai taiɓa yai ƙaton ciki
Kowag ga shi zamne ga innuwa
Ko da makiɗin sarkin Masar
Yag ga Sa’idu sai rainai yai haki
(Sa’idu Faru: Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa).
Waƙa-kwaikwaye ne saboda
mawaƙin ya “rabu biyu”[3] ne, da shi da yaransa. Shi
ne a layi na ɗaya da na biyu, su
kuma yaran suka yi sauran layukan. Amma fa waƙar Sa’idu Faru ake
cewa, ko kuma a ce, “Sa’idu Faru ya ce”. Ɗan mu’abba, ma’abba,
ko maba ne kurum ke cin gashin kansa cikin waƙa saboda shi wani ɓangare ne na adabi daban yake yi, ba na waƙa ba.
Kammalawa
Wannan
maƙala ta
yi magana
ne a kan waƙa-kwaikwaye,
wani daɗaɗɗen tsarin waƙar
Hausa. Inda kuma ta fuskanta shi ne bayani kan wasu sigogi uku na wannan tsarin
waɗanda
bayani a kansu bai fito sosai ba cikin maƙala ta farko wadda mai wannan ta
rubuta. Duk kuma wannan mayar da hankali na maƙalar ta
yau a kan waƙoƙin
Sa’idu Faru ya kasance. Kira ko nuni da maƙalar take
yi shi ne, da farko manazarta su ba waƙa-kwaikwaye
nazarin da ya dace don a fayyace sigoginsa sosai da sosai; nuni na biyu shi ne
masu bincike su zurfafa bincike kan matsayin waƙa-kwaikwaye cikin waƙoƙin
Sa’idu Faru su gano shin wannan tsari salon waƙoƙinsa ne, mafi yawan waƙoƙinsa
suna ɗauke da
shi ne ko kuwa a’a?Haka kuma mai wannan maƙala tana kira ga ɗaliban nazarin waƙa da su
dinga konkomawa ga tarihin Hausawa kafin su kai ga yanke hukumci na abin da
suke bincike a kai daɗaɗɗe ne ko ararre ko kuma sabo ne
ful.
Manazarta
Aliyah, A. A. (2017), Rupert Moultrie East 1898-1975: Tarihinsa da
Sharhi a kan Gudummawarsa ga Adabin
Hausa, Kaduna: Whales Adverts
Limited.
Aliyah, A. A. da Yahya, A. B. (2020), Kukan Kurciya cikin WaƘoƘin
Korona Biyu, Zaria: ABUPRESS.
Aliyah, A. A. (2021), “Waƙa-kwaikwaye: Daɗaɗɗen Adabin Hausawa na Auren WaƘa da Wasan kwaikwayo”, cikin kundin
Karramawa ga Farfesa Sa’idu Muhammada Gusau na Bayero University, Kano wanda ke kan hanyar
fitowa.
Bunza, A. M. (2009), NARAMBAƊA.
Lagos: Ibrash Islamic
Publications Centre Ltd.
Dangambo, A. (2007), Ɗaurayar Gadon Feɗe
Waƙa (sabon tsari), Zaria: Amana publishers ltd.
Gusau, S. M. (2013), Wasanni Don Yara. Kano: Century
Research and Publishing Company.
Gusau, S. M, (2003), Jagoran Nazarin WaƘar Baka, Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M, (2009, 2018, 2019), DIWANI WAƘOƘIN BAKA 1,3,4. Kano: Century Research and Publishing
limited.
Gusau, S. M, (2015), WaƘar
Baka Bahaushiya No 14,
Kano: Bayero UniƁersity
Yahya, A.B (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna: Fisbas
Media SerƁices.
Yahya, A.B (2002), ‘Siffantawa
Bazar Mawaƙa: Wani Shaƙo Cikin Nazarin Waƙa’, cikin Studies in Hausa
Language, Literature and Culture 5: 220-240, (ed.) Bichi
A.Y., Kafin Hausa, A.U. and Yalwa, L.D., Kano: Jami’ar Bayero.
Yahya, A. B. (2013), ‘Tsattsafi: Wani Ɗigo cikin Gulbin
Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa’ cikin ƊUNƊAYE:
Journal of Hausa Studies Vol.1:5, Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.
Yahya, A. B.(2016), Salo Asirin Waƙa (sabon bugu), Sokoto: Guaranty Printers.
[1] Daga bisani kwamitin tsara
kundin karrama malaminta Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya amince daya buga maƙalar cikin kundi wanda a
yanzu haka yana a kan hanyar fitowa in sha Allahu.
[2] Littafin Aliyah Adamu Ahmad
da Abdullahi Bayero Yahya (2020), Kukan
Kurciya cikin Waƙoƙin Korona Biyu ya tattauna
wannan Magana a shafi na 50-59.
[3] A ra’ayin Farfesa Abdullahi Bayero Yahya yayin wata hira da na yi da shi, wanda ni ma na yarda da shi, waƙar baka ta mawaƙi guda ce, ‘yan amshi waƙarsa ce suke rerawa ba tasu ba, sai idan sun fita daga ƙungiyar mawaƙin sannan suke yin tasu waƙar.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.