Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarken Tubalan Gina Jigon Gargadi a Wakar Korona Biros Ta Abdullahi Abubakar Lamido

Citation: Karofi, I.A., Ado. A. and Lawal, M. (2024). Tarken Tubalan Gina Jigon Gargaɗi a Waƙar ‘Korona Biros’ ta Abdullahi Abubakar Lamiɗo. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 280-288. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.034.

TARKEN TUBALAN GINA JIGON GARGAƊI A WAƘAR ‘KORONA BIROS’ TA ABDULLAHI ABUBAKAR LAMIƊO

Isah Abubakar Karofi
Sashen Nazarin Harshen Hausa,
Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita, Dutsinma, Katsina

Abdulrahman Ado
Sashen Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina

Muntari Lawa
Department of English
Isa Kaita College of Education, Dutsinma, Katsina

Tsakure

Rubutacciyar waƙa saƙo ne wanda aka gina shi a kan tsari mai ƙa’ida ta baiti, ɗango, kari, amsa-amo da rerawa da daidaita kalmomi da zaɓen su da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba. Don haka, marubuta waƙoƙin Hausa na tsara waƙoƙinsu domin su isar da saƙonninsu a kan fannoni daban-daban ta hanyar amfani da wasu tubala waɗanda za su taimaka masu wajen cim ma saƙon da suke son isarwa ga jama’a. Wannan takarda ta fito da yadda Abdullahi Abubakar Lamiɗo ya yi amfani da wasu tubala wajen tsara saƙon da waƙarsa take son isarwa ga masu karatu. An yi amfani da salon nazari wajen fitar da wasu tubala guda shida waɗanda suka gina babban jigon waƙar na gargaɗi.An gudanar da wannan bincike bisa manufar bayyana wa masu nazari wasu tubalan da mawaƙan Hausa sukan yi amfani da su domin gina waƙoƙinsu domin cim ma manufofinsu na yin waƙoƙin. An bi hanyoyi biyu kawai a wajen gudanar da wannan binciken, wato hanyar karantawa daga wasu rubutattun bayanai da suka danganci rubutaccen adabi da kuma hira da aka yi da wasu masana a kan rubutaccen adabi. An ɗora wannan bincike a kan ‘Ra’in Gudummuwar Adabi’. Sakamakon binciken ya nuna cewa, ana iya yin amfani da tubalan nazarin waƙoƙin Hausa, waɗanda wasu masana nazarin waƙoƙin Hausa suka samar, domin yin nazarin kowace irin waƙa ta Hausa, don bayyana manufar waƙoƙin Hausa, waɗanda marubuta waƙoƙin Hausa suke rubutawa.

Fitilun Kalmomi: Tarke, Tubalai, Jigo, Gargaɗi, Waƙar Korona Biros, Abdullahi Abubakar Lamiɗo

Gabatarwa

A wannan bincike, an yi nazarin yadda wani marubucin waƙoƙin Hausa, watoAbdullahi Abubakar Lamiɗo ya rubuta waƙarsa a kan annobar “Korona Biros.” A cikin waƙar, an yi nazarin yadda ya yi amfani da wasu tubalan nazarin waƙoƙi, waɗanda shi marubucin ya yi amfani da su ya gina waƙarsa a bisa jigon gargaɗi.

2.0 Sharar Fage

Jigon gargaɗi wani babban jigo ne da marubuta waƙoƙin Hausa suke gina waƙoƙinsu da shi, domin fitar da manufofin da suka sanya aka rubuta waƙar. Cutar Korona biros kuwa, wata muguwar annoba ce da ta faro daga gabashin duniya a hankali-a-hankali ta watsu tamkar wutar daji zuwa sassan duniya gabas da yamma, kudu da arewa(Bala da Imam, 2020:100).

Cutar ba ta bar manyan garuruwa ba  ballantana ƙananan garuruwa waɗanda ƙarancin kula da lafiya ya yi masu zaman dirshan. Wannan takarda ta yi duba ne a kan jigon gargaɗi a waƙar Korona biros wadda Abdullahi Abubakar Lamiɗo ya rubuta a yayin da cutar Korona ta zaman wa duniya babban ƙalubale ta fuskar magancewa. Malam Abdullahi ya yi amfani da ƙananan jigogi cike da kalmomi na hikima masu ɗauke da zantuka ko saƙonni wajen ƙulla gargaɗi a kan illar cutar Korona Biros kamar yadda ya kira ta a waƙarsa. Tubulan ko ƙananan jigogi sun ba marubucin damar ƙara wa waƙar tsawo da armashi ga masu karantawa.

3.0 Manufar Bincike

An gudanar da wannan bincike bisa manufar bayyana wasu tubalan nazari da wasu masana suka samar domin yin nazarin rubutattun waƙoƙi a Hausa.

Haka kuma, ana son a bayyana ire-iren wasu daga cikin tubula koƙananan jigogin nazarin waƙoƙin da Abdullahi ya yi amfani da su wajen gina kalmomin gargaɗi a cikin waƙarsa ta Korona Biros.

Bayan nan, ana son a kuma bayyana yadda Malam Abdullahi ya yi amfani da waɗannan tubala wajen gina waƙarsa ta gargaɗi a kan annobar Korona Biros.

4.0 Hanyoyin Gudanar da Bincike

An bi hanyoyi guda biyu wajen gudanar da wannan bincike. Da farko, an bi hanyar karantawa daga wasu rubutattun bayanai, waɗanda suka haɗa da bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu da wasu takardu da aka gabatar a wasu tarurrukan ƙara wa juna sani.

Hanya ta biyu kuwa, ita ce ta yin hira da wasu mutane da aka gana da su. A nan, an yi hira da ɗaya daga cikin editocin littafin wato Khalid Imam, wanda aka samu wasu bayanai da aka sanya a cikin wannan bincike. Haka kuma, an yi hira da wasu masana rubutaccen adabin Hausa. A wajensu aka samu wasu bayanai na tubalan nazarin waƙoƙin baka da kuma wasu ƙananan jigogin da suke ɗauke da ire-iren waɗannan tubala.

5.0 Hanyar Ɗora Aiki

An ɗora wannan takarda bisa ‘Mazhabar Rubutacciyar Waƙar Baka’.  Wannan ra’i ne wanda ya fi mayar da hankali ne ga tattaro ra’ayoyin manazarta kan hanyar nazarin rubutacciyar waƙar Hausa. Masanin da ya assasa wanna ra’i shi ne Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo a shekara ta 1975 har ya rubuta littafi mai suna Gadon Feɗe Waƙa. A kuma 1981 ya fito da Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa da kuma Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon tsari) a shekarar ta 2007. Masanin ya assasa wannan ra’in domin samar da hanyar nazarin rubutacciyar waƙa na bai-ɗaya karɓaɓɓe ga kowane mai nazari. Daga cikin magoya bayan wannan ra’i akwai; Abdullahi Bayero Yahya da Isa Mukhtar da Aminu Lawal Auta da Halima Abdulƙadir Ɗangambo da Ɗahiru Abdulƙadir da Mustapha Shu’aibu da sauransu (Gusau, 2015:21-22).

Da yake takardar tana magana ne a kan tubalan da suka gina jigon gargaɗi na waƙar ‘Korona Biros’ ta yi daidai da yadda Mazhabar Rubutacciyar Waƙar Baka ta bayyana yadda ƙananan jigogi irin su faɗakarwa da gargaɗi da jan hankali da wa’azi da nasiha da sauransu a matsayin tubalan da suke haɗuwa su tayar da babban a rubutacciyar waƙar baka. Waɗannnan tubala da Mazhabar ta zo da su an yi amfani da su wajen cim ma burin takardar.

6.0 Bayanin Diddigin Waƙa

Bayanin diddigin waƙa ya danganci sanin salsalar waƙa da bayanin yadda aka sami waƙar domin tarke ko nazarinta. Haka kuma, a tabbatar da shekarar da aka yi wannan waƙa (Yahya, 2014, sh.129).

Wannan waƙa an wallafa ta a shekarar 2020 a cikin littafin Corona Blues (A Bilingual Anthology of Poetry), wanda Ismail Bala da Khalid Imam suka yi wa edita. Lambar fejin waƙar 122 zuwa 125. Waƙar ‘yar ƙwar huɗu ce mai baiti talatin da huɗu (34).

Abubakar Abdullahi Lamiɗo an haife shi a garin Gombe kamar yaddaya nuna a cikin waƙar a baiti na 34.

6.1 Bayanin Tubalan Gina Jigo

Tubalan ginin turke ko jigo wasu maganganu ne da aka bi aka ƙuƙƙulla waƙa da su don ta ƙara tsawo, amma ba su ne babbar manufar waƙar ba (Gusau, 2003 sh. 30).

Jigo kamar yadda Auta (2017, sh. 139) ya bayyana shi, da muhimmin saƙo ko manufar da mawallafi yake son isarwa ga jama’a. Wato abin da waƙa ta ƙunsa dangane da manufa. Ya ƙara da cewa a cikin waƙoƙi akan sami wani baiti da mawallafi yakan faɗi ƙwayar jigonsa. Wato saƙon waƙar, sannan ya yi amfani da jawabin jigo da za su taimaka masa ya tayar da wannan ƙwayar jigon. Domin gane jigon waƙa, ana iya bin ta a taƙaice baiti bayan baiti ana taƙaita abin da mawallafi ya faɗa ba tare da yi wa waƙar sharhi ba.

Kowace waƙa tana ginuwa ne a kan jigo ko saƙo, abin da ya karkasu zuwa babban jigo da ƙaramin jigo ko turke da tubalai waɗanda da su ne ake gina kowane jigon waƙa (Yahya, 2015 sh.10).

6.3 Wasu Tubalan Gina Jigon Gargaɗi a Waƙar

C.N.H.N.  (2006:159) ya bayyana ma’anar gargaɗi da

“Jan hankali ko yin kashedi ko horo”.

Dangane da abin da masana suka bayyana a kan ma’anar gargaɗi kuwa, masana irin su (Gusau, 2008 sh. 385 da Auta, 2017 sh. 26 da Ɗangambo, 2012) duka sun yi tarayya wajen bayyana gargaɗi da hanya ce wadda ta ƙunshi tunasarwa kan yi ko bari da yi wa mutane nasiha, hannunka-mai-sanda tare da jan hankali da kuma tsoratarwa a kan faɗawa cikin ruɗani ko halaka a sakamakon aikata wani abu.

Amma a tawa fahimtar, gargaɗi ya danganci yi wa mutum jawabi a kan munin aikata ko yin wani abu ta hanyar fito da sakamako kai tsaye na hatsari da zai iya faruwa nan gaba idan ba a kiyaye ba wanda ƙarshensa ba zai yi daɗi ba.

Marubucin waƙar wato Abdullahi ya yi amfani da tubula masu armashi waɗanda suka taimaka masa wajen ƙara fito da babban saƙonsa na gargaɗi a cikin waƙarsa ta Korona Biros. Marubucin ya zaɓo tubula masu ratsa jiki da jan hankali daban-daban da suka haɗa da sanarwa daga shugaban al’ummar Musulmai (Sarkin Musulmai) da izinin ci gaba da addu’a a gida da jan hankali daga likitoci da umurnin sanya takunkumi da gargaɗin zuwa asibiti a duk lokacin da aka sami canjin jiki da saƙon nasiha da kafa hujja daga malaman addini a kan annobar da gargaɗin yawaita yin sadaka da neman gafarar Ubangiji da kuma horo a kan ƙaurace wa masu ƙaryata zuwan korona biros da sauransu.

Ga wasu daga cikin tubula da Abdullahi ya gina waƙarsa kuma aka bayyana su a wannan nazari su ne kamar haka:

6.3.1 Sanarwa/Kira Daga Shugaban Al’ummar Musulmi

Ƙamusun Ingilishi da Hausa (2021:118) ya bayar da ma’anar kira da

“A buɗa baki a kira wani ko wata dabba da ƙarfi”.

Haka kuma, a dunƙule kira daga shugabannin al’umma ya danganci gudanar da jawabi kai-tsaye ko ta wata kafar sadarwa domin al’umma su ji, su kuma aiki da abin da shugaba ya sanar. Aikin shugaba ne ya sanar da duk wani abu wanda zai amfanar ko cutar da al’ummar da yake yi wa jagoranci. Jagorancin al’umma yakan fara daga zamantakewar iyali zuwa ta unguwa, sai ta gari wadda mai gari ko dagaci yake shugabanta. Gamayyar garuruwa suke haifar shugabancin gunduma, shugaban gunduma shi ne ake kira da hakimi, taruwar gundumomin hakimai suke samar da sarkin yanka wato sarki mai daraja ta ɗaya ko ta biyu. Dukkan umurni na yi ko hani yana fitowa daga bakin sarkin ƙasa, sannan ya biyo ta hannun hakimai zuwa dagatai zuwa masu unguwanni waɗanda su ne suke da alhakin isar da saƙon sarki ga sauran mutane. Bayan zuwan addinin Musulunci a ƙasar Hausa, sai tsarin ya mayar da Sarkin Musulmi a matsayin shugaban ƙasa na Musulmai shi ne yake da alhakin yin sanarwa ta gargaɗi kamar yadda waƙar da ake yin nazari ta fara buɗewa da jawabin Sarkin Musulmi (Karofi, 2013 sh. 14-15).

Abdullahi ya yi amfani da jawabin kira daga Sarkin Musulmi a baitinsa na farko kamar yadda za a gani.

Ga shi dai Sarkin Musulmi,

Yai kiran dukkan Musulmi,

Da su ɗau magana ta ilmi,

            Ba zancen masu gardama ba. (Baiti na 1).

A baitin da yake a sama, ya nuna yadda Sarkin Musulmi ya yi kira da babbar murya ga dukkan Musulmai da su gaskata maganarsa dangane da wanzuwar cutar Korona Biros a Nijeriya. Ya kuma gargaɗi mutane (Musulmai) baki ɗaya da su ɗauki maganar likitoci da masu ruwa-da-tsaki a kan harkar su kuma gujewa maganganu masu ƙaryata wanzuwar cutar a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.   

6.3.2 Nasiha Daga Malaman Addini

Kalmar nasiha tana nufin kyakkyawar shawara (CNHN, 2006:357). Dangane da asalin kalmar kuwa, Hausawa sun ɗauko kalmar ce daga harshen Larabci. Haka kuma, Larabawa dai ne suke da kalmar shawara wadda ake fassara nasiha da ita. Amma dukkan waɗannan kalmomi sun shiga cikin rumbun kalmomin Hausawa sun zauna daram, sun saje. Duk da haka, za a iya Hausantar da ma’anar kalmar nasiha ko ta shawara da “gyara-kayanka” wato wasu maganganu waɗanda ake gayawa mutum domin a yi masa gyara a kan wata fahimtarsa kan wani abu ko matsala. Yin nasiha na canza mutum daga rashin sani zuwa sani ko kuma yarda da wani abu wanda a baya bai yarda da shi ba ( Malumfashi, 2018 sh. 460-461).

Marubucin waƙar, ya kawo baituka waɗanda ya fito da nasihohi daga malaman addinin Musulunci sanannu suka yi dangane da cutar Korona Biros wanda suka kafa hujjoji daga Hadisai da Kur’ani kamar yadda baituka suka zo da su.

Mallamai sun yo bayani,

Bisa Hadisi da Kur’ani,

Da jawaban masu fannin,

Likitoci ba da yaudara ba. (Baiti na 2).

Sunka ce cutar Korona,

Maganinta a je a zauna,

Dukkanin taro a daina,

Ba kawai salla ta Jumma’a ba. (Baiti na 3).

Mallamanmu suna nasiha,

Da jawabi ga fasaha,

Kan dabarun kare sihha,

Ga sunayensu ban rage ba. (Baiti na 9).

Sheikh Sharif Muftin ƙasarmu,

Dr. Khalid shugabanmu,

Sheikh Abubakar Igwaninmu,

Birnin Kudu bai rawar ƙafa ba. (Baiti na 10).

Sannu Dakta Bashir Aliyu,

Mai Hadis, Tafsir, Zakiyyu,

Rabbana Sarki Ganiyyu,

Ya tsare mana lafiyarka Baba.  (Baiti na 11).

Sai mu je gun Sakwwatawa,

Dakta Mansur masu bai wa,

Masu gadon Annabawa,

Bai bar mu cikin dibi-dibi ba. (Baiti na 12).

Shehu Ibrahim Makwarri,

Yai jawabai tun a fari,

Masu gamsarwa da tsari,

Bai yi sassauci ga mai musu ba. (Baiti na 13).

Dakta Sani gwanin hadisi,

Wanda ko da bai da sisi,

Ba shi yin ƙarya ga nassi,

Kuma ba zai kare biddi’a ba. (Baiti na 14).

Ga Gwani Salissu Shehu,

Shugaban wa’azi da sulhu,

Masanin boko da fiƙhu,

Har maƙaid Shehu bai bari ba. (Baiti na 15).

Shehu Ahmad Murtalawa,

Dakta Ahmad Dogarawa,

Sai Gwani Mansuru Yelwa,

Sheikh Disinan ma bazan bari ba. (Baiti na 16).

Wanga su am Malamanmu,

Masu ƙarfafa zuciyarmu,

Masu tsabar tausayinmu,

Kuma ba naira suke hari ba. (Baiti na 17).

Ga shi dai sun ba da hujja,

Lokacin da ake da haja,

In da duk aka ba da hujja,

Ai sai bi ba da gardama ba. (Baiti na 18).

Waɗannan baituka da suke a sama, marubucin waƙar ya ambaci sunayen malaman addini sanannu da dama na ƙasar Hausa waɗanda suka yi wa’azi da yin nasiha daga Hadisai da Kur’ani domin mutane su gaskata abin da likitoci suka faɗa dangane da cutar Korona Biros kuma hakan ya yi daidai da cewar Annabin rahama (S.A.W.) da kuma cewar Kur’ani, idan annoba ta shigo cikin gari ku ƙauracewa taro da cakuɗuwar jama’a a wuraren taruwa kamar masallaci da kasuwa da sauransu. Malaman addinin sun ƙara gaskata maganar likitoci na zama gida da ƙauracewa cincirindon mutane a kodayaushe domin hakan zai hana yaɗuwar wannan annoba a cikin al’umma. Hatta salloli biyar da ta ranar Jumu’a duka sun yi nasiha a kan barin su cikin jam’i hakan ya yi daidai da koyar addinin Musulunci na hana yaɗuwar annoba cikin al’umma.

6.3.3 Jan Hankali ta Fuskar yin Tsafta da Kiwon Lafiya

Tsafta na ɗaya daga cikin abubuwan da suka sa mutum (ɗan’Adam) mai hankali ya bambanta da maras hankali, shi ya sa mawaƙi Abdullahi ya yi amfani da salon jan hankali na yin tsafta da kyautata kiwon lafiya domin ƙauracewa wannan annoba kamar yadda za a gani a cikin ‘yan baitoci.

Bayan haka ɗau mataki,

Ka sako “mask” nan a baki,

Hannuwa ka lizimci wanki,

Ba sai a wurin naɗar tuwo ba. (Baiti na 7).

In kana jin zazzaɓi fa,

Ko yawan tari da zuffa,

Ba batun wani kaffa-kaffa,

Maza je can hospital a duba. (Baiti na 8).

Waɗannan baituka da suke a sama, marubucin waƙar ya yi amfani da su domin jan hankali ta fuskar sanya takunkumi (mask) da yawan wanke hannaye a kai akai ba don komai ba, sai don yawaita tsafta da kiwon lafiya. Baya ga haka, marubucin ya kawo yanayi na rashin lafiya wanda ya kamata a ɗaukar wa mataki na zuwa asibiti da gaggawa kamar zazzaɓi da yawan tari da zufa duka dai alamu ne da ke nuna yiwuwar Korona.

6.3.4 Bayar da Izinin ci gaba  da yin Addu’o’i  a Gida

Bayar da izini ya shafi amincewa a gudanar da wani abu a bisa ƙayyadadden tsari wanda zai kai ga samun nasarar wani abu da aka sanya a gaba. Malaman addinin Musulunci sukan bayar da izinin yin addu’o’i a duk lokacin da wata masifa ko annoba ta shigo cikin al’umma suna yin haka don nuna koyi ga Annabin rahama (S.A.W.). 

Marubucin waƙar Korona Biros, ya kawo wani baiti wanda yake bayar da izini ga dukkan Musulmai da su duƙufa wajen yin addu’o’i har da halwa don roƙon Allah ya sauwaƙa wannan annoba cikin ƙasarmu Nijeriya kamar haka:

Shehunai sun ba da fatwa,

Kan buƙatar fara halwa,

A gida, kowa da kowa,

Ya yi salla don ya roƙi Rabba. (Baiti na 4).

Maganin cutar Korona,

Babba dai shi ne a zauna,

A gida yawo a daina,

Ba tare da yale addu’a ba. (Baiti na 5).

Addu’a kam ba kamarta,

Ba makami samfurinta,

Tashi duk dare don ka yi ta,

Ba a samu kamarta gun tsari ba. (Baiti na 6).

Marubucin ya fito da bayanan izini da malaman addinin Musulunci suka ba al’umma na duƙufa a kan yin addu’o’i kowa da kowa a gidaje don roƙon Ubangiji Allah ya hana yaɗuwar wannan annoba ta Korona Biros a nan Nijeriya da sauran ƙasashen Musulmai. Abdullahi ya jaddada muhimmancin yin addu’a da daddare domin dacewa da neman tsarin Allah ga cutar zamani ta Korona Biros.  

6.3.5 Horo a kan Ƙaurace wa Masu Ƙaryata Zuwan Korona Biros

Ga shi dai sun ba da hujja,

Lokacin da ake da haja,

Inda duk aka ba da hujja,

Ai sai bi ba da gardama ba. (Baiti na 18).

Kar ku yarda da masu musu,

Ban da sauraron batunsu,

In ka ɗau zancen irinsu,

Baka ɗau hanyar riga-kafi ba. (Baiti na 19).

Ban da ma tsabar jahala,

Wa ya kai su Imamu salla?

Wa ya kai su biya ga Allah?

Ba a kai sukiran Ubangji ba. (Baiti na 20).

6.3.6 Kwaɗaitarwa ga Shugabanni da Attajirai kan Ciyarwa a Lokaci Korona

Tubalin gargaɗi na kwaɗaitarwa ga shugabanni da attajirai kan ciyarwa ga mutanen da suke kulle a gida, babu fitowa don sallah da ciniki ko kasuwanci. Marubucin waƙar ya yi amfani da wannan tubali inda ya gina wasu baituka masu jan hankali da kwaɗaitarwa ga waɗanda suke masu hannu-da-shuni da shugabanni da su sadaukar da dukiyoyinsu wajen ciyar da mutane a yayin zaman Korona kamar yadda za a gani a ƙasa.

Amma na fa akwai bayani,

Dole ne fa zan yi nuni,

Gun masu hannu-da-shuni,

Hanzari ne ba batun gudu ba. (Baiti na 21).

Masu kuɗɗi na kira ku,

Tallakawa na jiranku,

Don ku kawo taimakonku,

Kuma ba canjin kuɗin suga ba. (Baiti na 22).

Albishir ya masu naira,

Wagga dama ce ku lura,

Ku yawaita halina hairan,

Ba dunƙule naku hannuwan ba. (Baiti na 23).

Shugabanni zan kira ku,

Ku ji tsoron Khalikinku,

Ku bi kadun ‘yan ƙasarku,

Ba kui wasa da lafiya ba. (Baiti na 24).

Kar saboda corona ɓirus,

Ai ta amfani da biros,

A yawaita su sata-ɓirus,

Ba ku ba mabiyanku tallafa ba. (Baiti na 25).

Toh, ku fara rabon abinci,

Don a ɗan rage wanga ƙunci,

Tun da dai kuka sa ƙunci,

To karya zamo ba kui shiri ba. (Baiti na 26).

Masu rauni duk ku duba,

Da waɗanda ba sui shiri ba,

Ba su tanadi ‘yan kuɗi ba,

Masara ma sam ba sui awu ba. (Baiti na 27).

Kar ku bar su cikin zalama,

Kar ku sa su shiga nadama,

Kun hana su zuwa su nema,

Sannan ba ku basu ko kwabo ba. (Baiti na 28).

29. Sun guje cutar Korona,

Sun shige ɗaki su zauna,

Ga cikinsu yana ta ƙuna,

Bai sami abin da zai taɓa ba. (Baiti na 29).

Tun daga baiti na 21 har zuwa na 29, marubucin waƙar ya yi amfani da salon jan hankali ne na kwaɗaitarwa ga masu mulki da attajirai da su ciyar da mutane waɗanda annobar Korona ta killace su a cikin gidajensu ga shi babu kuɗi, ba abinci a wajensu ballantana su zauna cikin jin daɗi da aminci. Don haka, marubucin ya yi ta nanata muhimmancin yin taimako ga mutane don kaucewa wata sabuwar cutar da za ta iya bijirowa ta sata-ɓirus, sakamakon matsin da zaman zai haifar ga talakawa.

7.0 Kammalawa

Wannan takarda ta nazarci tubalai ne waɗanda suka tattaru suka tayar da jigon gargaɗi a waƙar Korona Biros ta Abdullahi Abubakar Lamiɗo ya rubuta. An bayyana ma’anar tubali da ta jigo da ta kalmar gargaɗi. An kuma yi bayanin yanayin tubalan ginin jigon gargaɗi a waƙar Koron Biros. Sannan kuma, an tantance tubala daban-daban waɗanda su ne Abdullahi (marubucin waƙar) ya sadar da jigonsa na gargaɗi a waƙarsa. An kuma kawo bayanan tubalan da misalan baitukan waƙa daga tubalan suka haɗa da tubali na kira daga shugaban al’umma da na nasiha daga malaman addini da na jan hankali ta yin tsafta da kyautata kiwon lafiya da bayar da izinin ci gaba da yin addu’o’i a gida da horo a kan ƙauracewa masu ƙaryata zuwan Korona da kuma kwaɗaitarwa ga shugabanni da attajirai kan ciyar da al’umma abinci a yayin kullen Korona. A sakamakon bincike an gano cewa waƙar ta cancanci a yi nazarinta domin ta ƙunshi wasu tubala waɗanda suka gina babban jigo na gargaɗi.Kuma waƙar ta mallaki muhimman ɓangarori da tarke yake buƙata a yayin nazarinsa. Ana bayar da shawara ga manazarta da masu bincike da su ɗauki wani ɓangaren nazari a wannan waƙa domin a gudanar da wani bincike a kansa.

Manazarta

Auta, A.L. (2017). Faɗakarwa A Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Bayero Uniɓersity, Printing Press.

Bala, I. da Imam, K. (2020). Corona Blues (A Bilingual Anthology of Poetry). Whetstone Publishers

C.N.H.N (2006). Ƙamusun Hausa. Ahmadu Bello Uniɓersity, Printing Press.

Ɗangambo, H.A. (2012). Kwatanta Tubalan Gina Jigo Tsakanin Rubutattun Waƙoƙi da Ƙagaggun Labarai na Hausa. [Kundin digiri na uku da ba a buga ba]. Sashen Koyar da    Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙoƙin Baka. Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2008). Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Fisbas Media Serɓices.

Gusau, S.M. (2015). Mazhabar Ra’i da Tarke A Adabi Da Al’adun Hausa. Century Research and Publishing Limited.

Karofi, I.A. (2013). Sarautar Iyali Da Ta Sana’o’in Gargajya Tsakanin Al’ummar Hausawa. Cikin Mujallar Multi-Disciplinary. (IKCOE-MDJ). Isa Kaita College of Education, Dutsinma. Ɓolume (5). Number 4. pp14-21.

Kurfi, M.M. (2021). Ƙamusun Ingilishi da Hausa. Himma Publishers.

Malumfashi, Z.A. (2018). Tarken Wasu Ɗiya Na Faɗakarwa Ta Nasiha A Wasu Waƙoƙin Dr. Mamman Shata. Cikin Studies in the Songs of Dr. Mamman Shata Katsina. Department of Nigerian Language, Umaru Musa Yar’adua Uniɓersity. pp 459-468.

Yahya, A.B. (2014). Gudale Waƙar soyayya: Misalin Gazl (Ghazal) Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Garkuwan Adabin Hausa A Festschrift In Tribute To Abdulƙadir Ɗangambo. Department of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity. pp125-138.

Yahya, A.B. (2015). Rerawa Ruhin Waƙa Da Matsayinta A Waƙoƙin Hausa Na Baka Da Rubutattu. A cikin mujallar Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies.Department of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity. Special Edition, pp 10-15.

Ratayen Waƙar

Waƙar Korona Bairos

Abdullahi Abubakar Lamido

1 Ga shi dai Sarkin Musulmi,
Yai kiran dukkan Musulmi,
Da su ɗau magana ta ilmi,
Ba zancen masu gardama ba. 

2. Mallamai sun yo bayani,
Bisa Hadisi da Kura’ani,
Da jawaban masu fannin,
Likitoci ba da yaudara ba.

3. Sun ka ce cutar Korona,
Maganinta a je a zauna,
Dukkanin taro a daina,
Ba kawai salla ta Jumma’a ba.

4. Shehunai sun ba da fatwa,
Kan buƙatar fara halwa,
A gida, kowa da kowa,
Ya yi salla don ya roƙi Rabba.

5. Maganin cutar Korona,
Babba dai shi ne a zauna,
A gida yawo a daina,
Ba tare da yale addu’a ba.

6. Addu’a kam ba kamarta,
Ba makami samfurinta,
Ta shi duk dare don ka yi ta,
Ba a samu kamarta gun tsari ba.

7. Bayan haka ɗau mataki,
Ka sako “mask” nan a baki,
Hannuwa ka lizimci wanki,
Ba sai a wurin naɗar tuwo ba.

8. In kana jin zazzabi fa,
Ko yawan tari da zuffa,
Ba batun wani kaffa-kaffa,
Maza je can hospital a duba.

9. Mallamanmu suna nasiha,
Da jawabi ga fasaha,
Kan dabarun kare sihha,
Ga sunayensu ban rage ba.

10. Sheikh Sharif Muftin ƙasarmu,
Dr. Khalid shugabanmu,
Sheikh Abubakar Igwaninmu,
Birnin Kudu bai rawar ƙafa ba.

11. Sannu Dakta Bashir Aliyu,
Mai Hadis, Tafsir, Zakiyyu,
Rabbana Sarki Ganiyyu,
Ya tsare mana lafiyarka Baba.

12. Sai mu je gun Sakkwatawa,
Dakta Mansur masu bai wa,
Masu gadon Annabawa,
Bai bar mu cikin dibi-dibi ba.

13. Shehu Ibrahim Makwarri,
Yai jawabai tun a fari,
Masu gamsarwa da tsari,
Bai yi sassauci ga mai musu ba.

14. Dakta Sani gwanin hadisi,
Wanda ko da bai da sisi,
Ba shi yin ƙarya ga nassi,
Kuma ba zai kare biddi’a ba.

15. Ga Gwani Salissu Shehu,
Shugaban wa’azi da sulhu,
Masanin boko da fiƙhu,
Har maƙaid Shehu bai bari ba.

16. Shehu Ahmad Murtalawa,
Dakta Ahmad Dogarawa,
Sai Gwani Mansuru Yelwa,
Sheikh Disinan ma bazan bari ba.

17. Wanga su am Malamanmu,
Masu ƙarfafa zuciyarmu,
Masu tsabar tausayinmu,
Kuma ba naira suke hari ba.

18. Ga shi dai sun ba da hujja,
Lokacin da ake da haja,
In da duk aka ba da hujja,
Ai sai bi ba da gardama ba.

19. Kar ku yarda da masu musu,
Ban da sauraron batunsu,
In ka ɗau zancen irinsu,
Baka ɗau hanyar riga-kafi ba.

 

20. Ban da ma tsabar jahala,

Wa ya kai su Imamu salla?

Wa ya kai su biya ga Allah?

Ba a kai sukiran Ubangji ba.

 

21. Amma na fa akwai bayani,

Dole ne fa zan yi nuni,

Gun masu hannu da shuni,

Hanzari ne ba batun gudu ba.

 

22. Masu kuddi na kira ku,

Tallakawa na jiranku,

Don ku kawo taimakonku,

Kuma ba can jin ku]in su ga ba.

 

 

 

23. Albishir ya masu naira,

Wagga dama ce ku lura,

Ku yawaita halina hairan,

Ba dunkule naku hannuwan ba.

 

24. Shugabanni zan kira ku,

Ku ji tsoron Kalikinku,

Ku bi kadun ‘yan }asarku,

Ba kui wasa da lafiya ba.

 

25. Kar saboda corona ɓirus,

Ai ta amfani da biros,

A yawaita su sata-ɓirus,

Ba ku ba mabiyanku tallafa ba.

 

26. Toh, ku fara rabon abinci,

Don a dan rage wanga ƙunci,

Tun da dai kuka sahu ƙunci,

To karya zamo ba kui shiri ba.

 

27. Masu rauni duk ku duba,

Da waɗanda ba sui shiri ba,

Basu tanadi ‘yan kuɗi ba,

Masara ma sam ba sui awu ba.

 

28. Kar ku bar su cikin zalama,

Kar ku sa su shiga nadama,

Kun hana su zuwa su nema,

Sannan ba ku ba su ko kwabo ba.

 

29. Sun guje cutar Korona,

Sun shige daki su zauna,

Ga cikinsu yana ta ƙuna,

Bai sami abin da zai taɓa ba.

 

30. Addu’ar mazlumikun san,

Babu shamaki gunta tun can,

In dai suka yi ta kun san,

Allah ba zai ƙi addu’ar ba.

 

31. Rabbana Sarkin saurauta,

Wanda Kai ne mai nagarta,

Damuwa fa ta tsananta,

Yayewa na gare  Ka Rabba.

 

32. Mun yi roƙo gun Ka Allah,

Mun yi tuba gun Ka Jalla,

Don yawan Azumi da salla,

Ka raba mu da jarrabar ga babba.

 

33. Toh a nan ne zan yi birki,

A cikin ɗan wanga aiki,

Addu’ata wanga aiki,

Rabbana Sarki Gwani ya karɓa.

 

34. Gombe ne babban gari na,

Lamdo Abdullahi suna,

Kuma Amir ne laƙƙabi na,

A gidanmu suna kira ni Baba.

(Bala da Imam, 2020 sh. 122-125)

 

Waka

Post a Comment

0 Comments