Citation: Lamido, I. & Maikadara, B.I. (2024). Salon Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari a Waƙar Amadu Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 207-213. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.026.
Salon Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari a Waƙar Amadu Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda
Na
Ibrahim Lamido PhD
Sashen Koyar da Harshe da Kimiyyar
Harshe
Jami’ar Tarayya ta Kashere, Jihar Gombe
Da
Bara’atu Inuwa Maikadara PhD
Sashen Koyar da Kimiyyar Harshe da
Harsunan Afirka
Makarantar Horas da Aikin Ɗan Sanda da ke Wudil, Jihar Kano
Tsakure
Wannan bincike ya yi nazarin salon
sarrafa harshe a ɗaya daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru.
Nazarin wanda ya karkata a nazarin salon sarrafa harshe a fannin kimiyyar
harshe, ya duba salon zaɓen kalmomi na Sa’idu Faru a waƙarsa ta Amadu Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda. An yi amfani da hanyar nazarin salo da sarrafa
harshe na Leech da Short (1981) aka aiwatar da nazarin. Waƙar wadda ita ce babbar ginshiƙi a bayanai da binciken yake buƙata an same ta ne a kafar sadarwa da kuma rubutacciyar ta
a diwani da manazarta suka tattara na wasu waƙoƙin baka. Binciken
ya nuna irin kalmomin rukunan nahawu da aka yi amfani da su musamman Suna, da Wakilin
suna, da Aikatau, da Bayanau. An kuma yi nazarin nau’o’in Adon Magana a waƙar da makaɗin ya yi amfani da su, musamman
Siffantawa da Jinsintarwa. Haka nan an ga irin ganguna da makaɗin ya faye amfani
da su da yadda duka waɗannan sassa manya da ƙanana na nahawu da adon magana suka taimaka wajen isar da
manya da ƙananan saƙonnin cikin waƙar.
Keɓaɓɓun Kalmomin
Nazari: Salo, Sarrafa Harshe,
Nazari, Suna, Aikatau
Gabatarwa
Salon sarrafa harshe a waƙoƙin baka wata hanya ce da makaɗa suke bi su kyautace
tunaninsu a waƙa. Makaɗi yakan sarrafa
tunaninsa cikin azanci domin ya cim ma burinsa na isar da saƙon waƙa. Salon waƙa ya ƙunshi abubuwa da
dama da suka haɗa da adon harshe da aiwatar da harshe (Gusau 2003:61-62). Wannan takarda ta
kalli wani sashe na aiwatar da harshe a waƙa,wato zaɓen kalmomi. Wannan fanni ya shafi irin kalmomin da makaɗi ya zaɓo ya zuba a cikin ɗiyan waƙarsa. A yayin da bincike ya gudana da dama a kan abin da
ya shafi salon sarrafa harshe a waƙa ciki har da ɓangaren da wannan
bincike ya shafa, amma an lura akwai rashin yalwar bincike a abin da ya shafi
nazarin kalmomin waƙa musamman a mahangar Ilimin Kimiyyar Harshe.
Wannan shi ya zaburar da masu bincike wajen duba yanayin zaɓen kalmomi a waƙoƙin Makada Sa’idu Faru ta mahangar Leech da Short (1981) wanda ya shafi
kimiyyar harshe da adabi. Nazarin ya duba irin kalmomin da makaɗin ya yi amfani da
su musamman a waƙarsa ta Sarkin Kiyawa Amadu.
Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru
Shekara ta 1932 ita ce shekarar
haihuwar Makaɗa Sa’idu Faru. An haife shi a Faru da ke yankin Maradun da ke cikin ƙaramar hukumar Talata Mafara. Mahaifinsa shi ne Makaɗa Abubakar Ɗan Abdu ɗan Alu mai Kurya. Makaɗa Sa’idu Faru ya
yi gadon kiɗa daga wajen mahaifinsa wanda shi ma ya gada daga mahaifinsa Alu makaɗin kurya ta kiɗin yaƙi, kuryar da ake yi wa kirari da “Kuryar gangar mutuwa”. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi ƙuruciyarsa a garin Banga da ke Ƙaurar Namoda garin mahaifiyarsa amma daga bisani ya dawo Faru. Ya yi
karatun allo inda ya yi zurfi a karatun Alƙur’ani, amma bai yi karatun boko ba.
Makaɗa Sa’idu Faru ya
koyi waƙa a wurin mahaifinsa Makaɗa Abubakar. Mutum
ne mai baiwar ƙwaƙwalwa da ke cike da fasaha da hikima. Da taimakon mahaifinsa wanda gare shi
shi kaɗai ya naƙalci waƙa da hikimomi ya koyi salailai iri-iri da yake amfani da su a waƙoƙinsa. Bayan ya samu cin gashin kansa, waƙar da ya fara ita ce waƙar da ya yi wa sarkin Yamman Faru Ibrahim. Ya yi wa sarakuna da dama waƙoƙi da ‘ya’yan sarakuna ciki har da sarkin musulmi Muhammadu Maccido ɗan Abubakar. Ya
fara masa waƙa tun yana riƙe da muƙamin Sarkin Kudu. Sauran fitattun
mutane da ya yi wa waƙa sun haɗa da:
a.
Sarkin Musulmi Abubakar na III
b.
Sarkin Yawuri Alhaji Muhammadu Tukur
c.
Sarkin Sudan Na Wurno Alhaji Shehu
d. Turakin Kano
Ahmadu
e.
Sarkin Kiyawa Abubakar Ƙaura-Namoda da saura da yawa.
Bincike ya nuna Makaɗa Sa’idu Faru bai
taɓa yi wa wanda ba sarki ko ɗan sarki waƙa ba. Shi da kansa aka ce ya tabbatar da haka.
Makaɗa Sa’idu Faru
yakan shirya waƙoƙinsa a gida kafin
ya je ya sadar da ita a waje. Yakan riƙa bitar ɗiyan waƙar daya shirya kafin lokacin da zai je ya sadar da ita.
Ko kai tsaye zai shirya ta , zai nemi sunayen iyayen sarkin da na kakanninsa da
na sauran danginsa. Waƙar da ya shirya a gida ta fi tsaruwa
fiye da wadda ya yi kai tsaye.
Makaɗa Sa’idu Faru ya
yi waƙoƙi da yawa, amma waɗanda ake jin sun
fito da shi a a duniya su ne waƙoƙin da ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo. Yaransa masu
masa karɓi su ne Mu’azu Daudun kiɗa wanda yake ƙane ne gare shi, kuma Ɗangaladimansa. Da
akwai Ɗandaudu, da kuma Ali. Makaɗa Sa’idu Faru ya
sami alkairai masu yawa a dalilin kiɗa da waƙa. Makaɗa yana da matan aure guda 3 da ‘ya’ya 26 da jikoki 20 (Gusau 2005:117-125).
Matakan Nazarin Salon Sarrafa Harshe Mahangar Leech Da
Shorts (1981)
Mukhtar (2010:24) ya zayyana matakan
da Leech da Short suka tsara a mahangarsu ta nazarin salon sarrafa harshe a
matani na adabi. Ga su kamar haka:
a.
Matakin Kalma
i.
Kalmomi ne sauƙaƙa ko masu tsauri
ii.
Kalmomin Suna, ɓoyayyu ne ko
bayyanannu
iii.Yaya yanayin amfani da kalmomin sifa
iv.Kalmomin aikatau da yadda suke taimakawa
wajen daukar saƙon matani.
v.
Yanayin amfani da kalmomin bayanau
b. Matakin Nahawu
i.
Ire –iren jumlolin matani na bayani ko
umarni ko tambaya
ii.
Nauyin jumlolin matani
iii.Ire-iren ganga a matani da tsarinsu
iv.Yankin suna
v.
Yankin aiki
vi.Sauran nau’o’in yanki-yanki na jimla
vii. Zubin jumlolin
matani
c.
Zantukan Hikima
i.
Na nahawu da na kalma kamar kalmomin
kari ko na ƙulla dangantaka ko na daidaito ko
bambanci.
ii.
Na ƙwayoyin sauti/haruffa kamar ƙarangiya ko amsa
amon kari
iii.Maganganun azanci da adon harshe kamar siffantawa
da kamantawa da jinsintarwa
d. Dangantaka Tsakanin Jumlolin Matani
i.
Yanayin ƙulla dangantaka tsakanin jumlolin matani
ii.
Hanyar ruwaito matani kai tsaye ne daga
mawallafi ko an ari bakinsa ne?
Wannan takarda ta taƙaita a nazarin amfani da kalmomin rukunan nahawu a waƙar da ake nazari. Haka nan kuma an duba zantukan hikima
da suka haɗa da kalmomin adon magana da sarrafa harshe.
Bayani a Taƙaice a Kan Waƙar Alhaji Amadu Sarkin Kiyawa na Ƙauran Namoda
Wannan waƙa kamar sauran waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru waƙa ce da aka rera ta cikin ƙungiya da makaɗa Sa’idu Faru a matsayin jagora tare da
masu masa amshi da ƙari. Gindin waƙar shi ne: “Gwauron Giwa Jirayi Gaba na Amadu”. Sannan waƙar da ta zo hannun masu bincike tana da ɗiya 19 ne. an kuma
cirato ta ne daga Gusau (2014). Masu bincike ba su iya tantance rerawar farko
ce ko ta biyu ba ce. Ɗiyan waƙar suna da zubi mai gauraye, a inda wasu ɗiyoyin matsakaita
ne wasu kuma dogaye ne. dangane da tsari, galibin ɗiyoyin gauraye ne
na bayarwa daga jagora da ƙari da ga ‘yan amshi. Sai dai an sami wasu ɗiyoyin kaɗan waɗanda jagora ya ci
karensa babu babbaka. Ma’ana babu ƙari da ‘yan amshi suka yi masa a cikinsu. Turken waƙar yabo ce ga Alhaji Amadu Ssarkin Kiyawa na Ƙauran Namoda. Amma an jejjefa wasu ƙananan turaku na zuga da koɗa kai.
Zaɓen Kalmomi a Waƙar Alhaji Amadu Sarkin Kiyawa na Ƙauran Namoda
A ƙarƙashin wannan an yi nazarin wasu
azuzuwan nahawu da kalmomin aro da na kari waɗanda makaɗa Sa’idu Faru ya
yi amfani da su a waƙarsa da fa’idar da kalmomin suke bayarwa a isar da turakun cikin waƙar tasa.
Sunaye
Suna ya kasu nau’i-nau’i kamar yadda
magabata suka karkasa. Daga cikin nau’o’in akwai waɗanda makaɗa Sa’idu Faru ya
yi amfani da su.
Sunan Yanka
Waɗannan su ne sunaye
waɗanda aka keɓe su ga wani mutum ko dabba ko abu guda. Ire-iren waɗannan sun fito a
waƙar Amadu Sarkin Kiyawa. Misali:
‘Mu’azu’ a ɗa na 2
‘Amadu’ a ɗa na 6
‘Sa’idu’ a ɗa na 4
‘Ɗanmaliki’ a ɗa na
‘Jankiɗi’ a ɗa na 10
Narambaɗa a ɗa na 10 da
sauransu
Ga misalin inda wasu daga cikin waɗannan sunaye suka
fito a waƙar:
Ka tabbata Malam Sa’idu ya iya Ishiriniyya
(Ɗa na 4 saɗara ta 3)
yaro in taƙamar salon magana ag gare ka,
ce amadu ƙanƙarin ƙamado
(Ɗa na 6 saɗara ta farko da ta
2)
Dodo mai tabshi Jankiɗi,
Narambaɗa ya san muna da waƙa koƊandawo
Bayan su wanda yat taɓan,
Bana sai ya jiya
(Ɗa na 10 saɗara ta 4-7).
Duba yadda makaɗin ya yi amfani da sunayen yanka wajen
isar da turakunsa na yabo da koɗa kai. Alal misali a saɗaru na cikin ɗa na 10 an yi amfani
da sunayen Jankiɗi da Narambaɗa da Ɗandawo ya ba da dama wajen fito da
kwatancen da makaɗa ke yi na makaɗan da yake ragawa. Waɗannan kalmomi sun
taimaka kaifafa kwatancen. Ma’anar ba za ta fito ba in da Suna – Gamagari aka
yi amfani da shi.
Ban da Sunan Yanka na mutane da akwai na dabbobi da wasu abubuwa, kamar:
Garuruwa
‘Faru’ a ɗa na 17
‘Sakwato’ a ɗa na 12
‘Rara’ a ɗa na 17
Dabbobi
‘Giwa’ a ɗa na 3
Abubuwa
‘Katifa’ a ɗa na 17
‘Labule’ a ɗa na 17
‘Kuɗɗi’ a ɗa na 6
‘Jalalaini’ a ɗa na 4
‘Ishiriniyya’ a ɗa na 4
Waɗannan kalmomi na
sunayen yanka sun taimaka wajen ƙara fito da ma’anar ƙananan saƙonni da suke cikin ɗiyoyin da suka fito. Alal misali:
sunayen yankuna irin su ƙasar Rara da Faru
a ɗa na 17 sun taimaka wajen fayyace wa mai sauraro wuraren da makaɗin ya ziyarta da
fahimta abubuwan da makaɗin ya bayyana aukuwarsu a wuraren.
Hakazalika, sunayen bargo da katifa da
labule waɗanda ya yi amfani da su duka a ɗan waƙa na 10 sun fayyace irin kayan shimfiɗu ado na ɗaki da yake son
gwadawa a ɗan waƙar.
Suna Gama-gari
Suna gama-gari akasi ne na sunan yanka
wanda yake ɗaukar duk wani suna wanda ba a keɓe shi ga mutum ko abu guda ba. Makaɗa Sa’idu Faru ya
yi amfani da wannan nau’i na suna wajen saƙa zaren tunanin waƙarsa. Alal misalin irin waɗannan sunaye da akwai:
‘Malam’ a ɗa na 4
‘Makaɗa’ a ɗa na 7
‘Birni’ a ɗa na 8
‘Yarinya’ a da na 17
Ta (ita)
Kalmar ‘yarinya’ da ya yi amfani da ita a ɗan waƙa na 17 inda yake cewa:
“Dan nan sai na game da da yarinya,
tag gane ni, ni ko sai na nig ga ta”
(Ɗan waƙa na 17 saɗara 10 da 11).
A waɗannan saɗaru inda aka yi
amfani da kalmar yarinya a saɗara ta farko, kalmar ta taimaka wajen
sakaya ma’ana. Alal misali inda makaɗin ya so sai ya ambaci suna. Makaɗa sukan yi amfani
da irin waɗannan kalmomi in suna son sakaya sunan wanda suke magana a kansa.
Hakazalika a saɗara ta biyu wakilin suna ‘ta’ aikau da ‘ta’ karɓau hikima ce ta
tattalin kalma a inda makaɗin ya yi amfani da su a madadin sake
maimaita sunan yarinya musamman a gurbin aikau.
Aikatau
Makaɗa Sa’idu Faru ya
yi amfani da kalmomin aikatau nau’i-nau’i a waƙarsa
Kalmar aikatau kalma ce da take nuna
aiki a cikin jimla. Kalmomin aikatau suna taka muhimmiyar rawa a zance musamman
wajen gwada ayyukan da aka yi ko ake da niyyar yi ko aka riga aka yi su. Makaɗa Sa’idu Faru ya
yi amfani da kalmomin aikatau nau’i-nau’i. Kamar: masu gaɓa ɗaɗɗaya:
‘Ba’ a ɗa na 4
‘Yi’ a da na 4 da na 10
‘Ga’ a ɗa na 17
Akwai masu gaɓa bibbiyu kamar:
‘ɗauko’ da ‘jawo’ da ‘ɗore’ a ɗa na 4
‘ƙage’ da ‘tula’ da ‘aza’ a ɗa na 17
Akwai masu gaɓa uku-uku kamar:
‘tabbata’ a ɗa na 4
‘taƙama’ da ‘maƙalle’ da ‘ƙarahi’ a ɗa na 5
‘Dakata’ a ɗa na 8
waɗannan kalmomin sun
taimaka wajen kaifafa ma’anar cikin ƙananan turakun waƙar. Alal misali, duba yadda makaɗin ya zaɓi amfani da kalmar
aikatau ‘ratsa’ da ‘kama’ da ‘ƙulle’a ɗa na 17 waɗanda suka daɗa fito da hoto
labarin da makaɗin yake bayarwa a inda yake cewa:
“Dan nan muka ratsa ƙasar Rara (saɗara ta 6)
Dan nan nik kama gardama taƙ ƙulle “(saɗara ta 16)
Makaɗin inda ya so,
yana iya amfani da kalmar ‘bi’ ko ‘shiga’ a madadin ‘ratsa’. Hakazalika da zai
iya amfani da kalmar ’riƙa’ a madadin ‘kama’ da kuma ‘fara’ ko ‘wakana’ a madadin ‘ƙulle’.
Adon Harshe
Adon harshe wata dabara ce ta yi wa harshen
waƙa kwalliya. A yayin kwalliyar akan zaɓo wasu kalmomi ne
a zayyana waƙa da su, a ƙawata ta sosai ta yadda zai jawo hankalin masu sauraro (Gusau 2003:54).
Akwai hanyoyin yi wa harshen waƙa kwalliya da dama. Daga ciki an kawo waɗanda Makaɗa Sa’idu Faru ya
yi amfani da su a waƙarsa:
Jinsintarwa
Wannan wata dabara ce ta ɗaukar jinsin wani
abu a bai wani abun daban. Ya karkasu kashi-kashi: akwai mutuntarwa da
dabbantarwa da abuntarwa da kuma abuntarwar abuntarwa. A waƙar da ake nazari an sami abuntarwar abuntarwa. Ga misali:
“Dan nan nik kama gardama taƙ ƙulle” (Ɗa na 17)
A misali na sama an sami abuntarwar
abuntarwa inda aka ɗauki gardama wanda abu ne da ake
aikatawa tsakanin mutane waɗanda ra’ayinsu a kan wani al’amari bai
zo ɗaya ba. Sai aka maishe shi wani abu wanda ya shafi kaya ko maɗauri da ido yake
iya gani, ta hanyar ba shi ɗabi’a ko siffa na ƙullewa. Wato dai an san maɗauri igiya ko tsumma shi ake ƙullawa. Wannan ta fuskar aiki ke nan. Haka nan ta fuskar
abin da ake ƙullewar. A nan ma an abuntar da
gardama. An ɗauki siffar wani abu da ido ke iya gani da za a saka cikin tsumma a ƙulle aka bai wa gardama wadda ido ba ya iya gani.
Misali na biyu duka a ciki ɗa na 17 dai shi
ne:
“wanda yai tuwon gishiri,
Shin da me yaka mai kayan miya?”
Makaɗin ya ambaci waɗannan saɗaru a waƙar da cewa ba’a yake yi, to amma a wannan nazari an kalle su ta fuskar jinsintarwa. A nan
an sami abuntarwar abuntarwa, a inda aka ɗauki gishiri wanda wani abu ne da ake
saka wa a miya, sai aka ba shi yanayi ko siffa na hatsi da ake tuƙa shi a yi tuwo da shi.
Ƙarangiya
Wani adon harshe da aka samu a cikin waƙar shi ne ƙarangiya. Gusau
(2003:61) ya bayyana ƙarangiya da cewa wata dabara ce ta
luguden harufa ko kalmomi ko wasa da harshe cikin baƙaƙe da kalmomi. Akan riƙa maimaita wata gaɓar kalma ko ƙwayar sauti ya dinga tafiya bai ɗaya a cikin kalmomi da saɗarun waƙa. Ƙarangiya nau’i ne na adon harshe da ya shahara a waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. Ga
‘yan mislaia a waƙar da ake nazari:
“Yaro in taƙamar salon magana ag gare ka,
Ce Amadu ƙanƙarin ƙamaɗo
Na maƙalle ƙanƙara ba ta cika,
Baran ƙamaɗo ƙirgin cikin ruwa”
“karatun salon magana mukai,
Korau na kwa rarame,
Ka tashi ka kamo kware
Ka roƙo mana koramin kware,
Kowaz zo kware ka san in ba,
Koramin kware kora ta a kai,
Kowaz zo kassuwar kware,
Yaka riƙƙe samun kuɗɗin kware”
(Ɗa na 6)
Hakazalika a ɗa na 11 yana cewa:
“Shusshuka toron tami gaton sansane,
Sa samari su samo ma tsalla,
Tsala na can ga tsalle ta tsane”.
(Ɗa na 11).
Waɗannan duka misalai
ne luguden gaɓoɓin kalma da makaɗin ya riƙa jejjefawa yana ƙawata waƙar tasa da su. Leech da Short (1981) sun bayyana irin wannan nau’i na adon
magana na nuna zurfin laƙantar harshen mai
matani da gogewarsa a iya kwalliyar zance.
Kinaya
CNHN (2006:245) ya bayyana kinaya da
cewa ita ce: “saye ko ɓoye ma’ana ko siffar abu saboda wani
dalili. A waƙa kinaya dabara ce ta sakaya zance
wadda take juyar da abu daga ma’anarsa ta asali zuwa ga wata ma’anar ta sakayawa. Ga yadda makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da kinaya
wajen sakaya zancen waƙarsa:
“Dan nan nig game da yarinya,
Tag gane ni, ni ko sai nig ga ta,
Sai tac ce mai kiɗin ga,
Mai sisi me nai maka,
Kac ce ke gafarakki ‘ya yarinya kike,
Tac ce nai ma yawa,
Nac ce ƙarya ki kai......”
“Tac ce mani ran da ka yi shuka ta fito,
Da me kake noman bisa?,
Noman bisa kiy yi tambaya?,
Za ni hwaɗa miki...”
(Ɗa na 17).
Saɗaru na 6 zuwa na
10 za a ga an yi sayen maganganu masu nauyin gaske waɗanda makaɗin ya yi alkunya
da su wajen isar da wannan ƙaramin saƙo a labarin gamuwarsa da yarinya da yake bayarwa.
Sarrafa Harshe
Wannan ya shafi gwanintar harshe a waƙa, ta yadda za a yi amfani da wasu dabaru a sarrafa shi
ko a aiwatar da shi cikin hikima domin burge masu sauraro. A ƙarkashin wannan za a duba abubuwa guda biyu cikin dabaru
da dama da suka shafi sarrafa harshe:
Kalmomin Aro
Kalmomin aro ko baƙin kalmomi su ne kalmomin da makaɗi ya ara daga wasu harsuna ko wani
harshe guda ya tsattsarma a cikin wadiyan waƙarsa domin ya burge masu sauraro. Al’ada ce ta makaɗan dauri na Hausa
sukan yi aron kalmomi daga harshen Larabci da wasu kalmomin na harsunan
al’ummomi makusanta musamman a harshen Larabci. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba
da ilmin addini da wasu da dama daga cikin makaɗan suke samu tun
ma kafin su fara waƙa, wasu ma tun a ƙuruciya. Makaɗa Sa’idu Faru kamar yadda aka ambata a baya ya yi karatun allo ya san
addini, wannan shi ya sa ba za a yi mamaki ba in an sami aron kalmomi a waƙoƙinsa musamman daga harshen Larabci. Ga
misalan aron kalmomi a wasu ɗiyoyin waƙar da ake nazari:
“Mu ja Attahiyatu az-zakiyatu mu
sallame,
Mu ɗauko Tabbat yada abu lahabi wa tabba
ma
Mu jawo was shamsu wa luhaha”
(Ɗan waƙa na 4)
Ɗan waƙa na sama, misali
ne na yadda makaɗa Sa’idu Faru ya yi aron kalma daga harshen Larabci. Layukan da aka kawo waɗanda duka sun
shafi nassoshi ne daga Alƙur’ani da hadisi na nuna irin tasirin addinin musulunci a
rayuwar makaɗin da neman tsari daga Allah mahalicci da ayoyinsa masu girma.
Duk da wannan misali da aka kawo a
sama, ana iya ka da baki a ce aron kalmomi bai yi tasiri a waƙar ba sosai.
Kalmomin Karin Harshe
Bai zo da mamaki ba idan aka ka da baki
aka ce an sami tasirin karin harshen sakkwatanci a waƙar da ake nazari, kasancewar makaɗin ya fito daga yankin Hausawa masu
amfani da wannan kari. Don haka ana iya cewa dole ne a samu tasirin karin harshen
a waƙoƙinsa. Leech da
Short (1981) sun bayyana irin wannan tasiri da cewa wani abu ne da yake nuna
alaƙar mai matanin adabi da da al’umma masu karin harshen. Misalai da dama a waƙar na nuna yalwar amfani da karin Hausr Sakkwato a waƙar. Ga ‘yan misalai:
i.
‘Umfani’ maimakon ‘amfani’ a ɗa na 13 inda yake
cewa:
“ ganinka umfanina
yakai”
(Ɗa na 15)
ii.
An kuma sami ƙarfafawa inda ake ninka baƙi a ƙarfafa furuci. Misali:
“yanzu tare da ni kay yi ta”
( Ɗa na 15)
A nan an ninka ƙwayar sautin /y/.
“Ni ko sai niw wuce”
(Ɗa na 17).
A nan kuma ƙwayar sautin /w/ ce aka ninka.
“yaron in taƙamar salon magana ag gare ka”
(Ɗa na 6)
A nan kuma an
ninka ƙwayar sauti /g/.
iii.
Hakazalika an tauye lafazin wasu
kalmomi da suka haɗa da: wakilin suna namiji tilo mutum na
uku ‘shi’ ya yi tauye shi a cikin waƙar kamar yadda aka
san karin sakkwatanci da hakan: ga misali:
“In kaza yab bugai da urya zaƙi ya kai”. (Ɗa na 9)
‘Bugai’ maimakon buge shi – a nan an tauye
wakilin suna shi aka bar wasalinsa na ƙarshe ‘i’ da aka goya a
jikin aikatau ‘buga’.
A gefe ɗaya aikatau ‘yi’
ya koma ‘i’ kamar yadda yake a karin sakkwatanci. Ga misali:
“ganinka umfanina yakai”
Yakai maimakon yake yi
(Ɗa na 13)
“Nic ce ƙarya ki kai”
(Ɗa na 17)
‘Ki kai’ maimakon kike yi
Misalai na sama duka suna nuna yadda
aka sami aukin tauye lafuzan wasu kalmomi a dalilin tasirin karin Sakkwatanci a
waƙar.
Kammalawa
Wannan takarda ta yi magana a kan
dabarun salon sarrafa harshen waƙa na Makaɗa Sa’idu Faru.
Takardar ta yi magana a kan salo da sarrafa harshe na Waƙar Sarkin Kiyawa Ahmadu wadda Makaɗa Sa’idu Faru ya
rera. A waƙar an ga yadda kalmomin rukunan nahawu
da makaɗin ya yi amfani da su musamman sunaye na yanka da gama-gari. An kuma ga
ire-iren aikatau waɗanda aka gwada yadda suka taimaka wajen
tafiya da saƙonnin cikin waƙar, bugu da ƙari an yi nazarin wasu dabarun adon
harshe musamman jinsintarwa wadda makaɗin ya yi zancen waƙarsa kwalliya. an kuma ga yadda makaɗin ya yi amfani da salon magana/ƙarangiya wadda ya riƙa luguden ƙwayoyin sauti da gaɓoɓin kalma don nuna
gwanintar harshe. An kuma kawo wasu dabarun aiwatar da harshe da makadin ya yi
amfani da su da suka haɗa da: zaɓen kalmomi da
kalmomin kari, aron kalmomi musamman daga harshen Larabci.
Manazarta
Abba, M. & Zulyadaini, B. (2000). Waƙar Baka. Zaria: Gaskiya Corporation Limited.
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press
Ltd.
Gusau, S.M (2014). Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i Na Biyu. Kano: Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin
Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishere Limited.
Gusau, S.M. (2005). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Leech, G. & Short. M. (1981). Stylen
in Fiction: A Linguistics Introduction to English Fictional Prose. (Second Edition).
Longman Publishing Group. Amazon.com.
Mukhtar, I. (2010). Introduction to
Styistics Study. Kano: Benchmark Nigeria Ltd.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.