Citation: Isah, Z. (2024). Hoton Mata a Bakin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 214-219. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.027.
HOTON MATA A BAKIN MAKAƊA SA’IDU FARU
Daga
Zainab Isah
Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa
Yar’adua, Katsina
xyyynab@gmail.com
08035872583,
08029322226
Tsakure
Makaɗa Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin
shahararrun makaɗan fada na ƙasar Hausa. Yawancin
waƙoƙin makaɗan fada na ƙasar Hausa sun fi
karkata kan turken zambo, yabo, zuga, koɗa kai, ban-dariya da
addini, musamman ga maza. Sannan kuma, makaɗan ba su cika yi wa
mata waƙa ba, ballantana su faɗi wata daraja da
baiwa da Allah Ya yi wa mata. Ta haka ne wannan takarda ta duba yadda Sa’idu
Faru ya nuna muhimmancin mata da irin gudunmawar suke bayarwa a cikin waƙar “Mai
Babban Ɗakin Ƙasar Kano.”
Wannan waƙa ta taimaka wajen nuna cewa su ma makaɗan fada ba a bar su a
baya ba wajen nuna matsayin mata a cikin al’umma. Manufar takardar, ta yi
nazarin wannan waƙa ta fito da irin muhimmancin da makaɗin ya ba mata.
Hanyoyin tara bayanai sun haɗa da: wallafe-wallafe da faifai na CD
da aka yi a kan waƙoƙinsa. Wannan bincike
zai taimaka wajen fahimtar irin gudunmawar da mata suke bayar wa a cikin
al’umma, musamman don jin haka daga bakin makaɗi irin Sa’idu Faru.
Haka kuma, binciken zai kuma buɗe ƙofar nazarin fannonin
adabi daban-daban.
1.0 Gabatarwa
Makaɗan baka na ƙasar Hausa suna ɗaya daga cikin rukunin jama’a da suke taimakawa wajen bunƙasa harshe da fahimtar
da al’umma muhimman al’amuran rayuwa. Kuma suna ƙoƙarin gargaɗi da wayar da kan
jama’a sha’anonin rayuwa daban-daban. Makaɗan sukan shirya zantuka na hikima da suke
zaburar da jama’a dangane da dabarun tafiyar da rayuwa. Gusau (2003) ya nuna al’adu
da ɗabi’un Hausawa zalla
su ne suka yi tasiri wajen samuwar waƙoƙin baka na Hausa.
Harshe da adabin Hausawa sun daɗa faɗaɗa fagage a waƙoƙin baka. Saboda haka,
a iya cewa makaɗan baka suna cikin
sahun gaba wajen raya al’adu da harshe da adabin Bahaushe. Idan kuwa haka ne,
sun zama wata madogara ta gyara ɗabi’u da al’adun jama’a. Duk da wannan
gudunmawa da makaɗan fada suke bayarwa,
musamman na dauri, sun fi ƙoƙarin tallata maza da
gwarzanta su da koɗa su da yabon su. Ba
a cika jin
ɗuruyar mata sosai a
bakunansu ba, sun fi tsarma su cikin yabon wani, ba su cika
ɗaukar su kacokam su
waƙe
ba. Sai a aka samu wannan shararren makaɗa ya yi wannan jan aiki. Ya waƙe mace, ya bayyana
ayyukan da take iya yi, da gudunmawarta ga al’umma. Don haka, manufar wannan
takarda ta yi nazarin waƙar ‘Mai Babban Ɗakin Kano’ da bayyana
irin yabo da makaɗa Sa’idu Faru ya yi
mata. Cikin yabon ya nuna muhimmancin mata da irin gudunmawar da za su iya ba da wa
cikin al’umma, har ma ya nuna irin ayyukan da suke yi daidai da maza. A wani
wajen ma ya nuna fifikon mata kan maza.
2.0 Makaɗa Sa’idu Faru
An haifi makaɗa Sa’idu Faru a garin
Faru ta cikin ƙasar Maradun, ƙaramar hukumar
Talatar Mafara a wajejen shekara ta 1932. Sunan mahaifinsa makaɗa Abubakar ɗan Audu, shi kuwa
makaɗa Abdu, Alu mai kurya
ya haife
shi. Kenan Sa’idu Faru shi ne ɗan Abdu da Alu mai kurya. Amma mahaifiyarsa
mutuniyar Banga ta cikin ƙasar Ƙauran-Namoda ce. An kuma yi masa laƙabi da ‘Ɗan’umma’
wanda matar ƙanen ubansa ta sanya masa, saboda ba ya faɗin sunanta, sai dai
yana kiran ta
da Umma. Sai dai wannan laƙabi bai
yi fice a cikin al’umma ba, ballantana ya shafe sunansa na yanka. Shi kansa
yakan yi wa kansa kira da wannan suna ‘Ɗan’umma.
Sa’idu Faru kamar sauran makaɗan fada, ya gaji kiɗa daga wajen mahaifinsa. Domin kakansa makaɗa Alu, makaɗin kurya ne. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi
yawancin ƙuruciyarsa a garin Banga ta Ƙauran-Namoda inda aka
haifi mahaifiyarsa, amma daga
bisani ya koma wajen mahaifinsa makaɗa Abubakar a Faru. Sai dai bai samu ilmin
Muhammadiya da yawa ba. Ba a kuma saka shi a makarantar boko ba. Duk da haka,
an saka shi a makarantar allo, inda ya samu karatun Alƙur’ani mai tsarki.
Duk da sha’anin kiɗa da waƙa sun rinjaye
karatun. Sannan ya koyi waƙa a wajen mahaifinsa, tun yana ɗan shekara goma aka
fara yawon kiɗa da waƙa da shi gari-gari.
Da ya kai wasu shekaru ya fara karɓi, tare da ƙanensa Mu’azu, wanda
shi ne Ɗangaladimansa a halin yanzu. Bai koyi kiɗa da waƙa daga wajen kowa ba,
da mahaifinsa ya rasu, shi ne ya ɗauki gabatar waƙa. Waƙar farko da ya fara
ita ce wadda ya yi wa sarkin Yamman Faru Ibrahim. Daga nan ya ci gaba da yi wa
sarakuna da ‘ya’yan sarakuna waƙoƙi har zuwa lokacin da
ya haɗu da sarkin Kudu
Muhammadu Macciɗo (Gusau, 1996).
2.1 Makaɗan Baka na Hausa
An jima ana yi wa
makaɗa da waƙoƙinsu hidima a ƙasar Hausa. An yi ta
wannan ƙoƙari a jami’o’i a, a matakan digiri daban-daban. Har ta
kai ana shirya manyan taruka na ƙasa da ƙasa kan wasu
shahararrun makaɗa da waƙoƙinsu. An yi irin waɗannan taruka a
jami’ar Bayero ta Kano. Alal misali, irin wannan taro da
aka gabatar a taron ƙasa-da-ƙasa kan Ibrahim Naramabaɗa. Wanda Sashen Koyar
da
Harsunan Nijeriya da Nazarin Ilmin Harsuna na Jami’ar Bayero suka
shirya daga ranar 15 -17 ga Satumba, 2019.
An kuma yi irin wannan taro don tunawa da gudunmawar
Alhaji Musa Ɗanƙwairo ga Waƙoƙin Hausa. Wanda
Sashen Ilmin Kimiyyar Harshe da Harsuna Ƙetare Haɗin Gwiwa da Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya suka gabatar ranar 12 zuwa 15 Ga watan Satumba, 2021.
An kuma yi irin wannan taro kan gudunmawar Alhaji Mammam Shata Katsina har Amin
(2011:120) ya
nuna ayyana cewa (Furniss, 1996:132) ya jaddada cewa Alhaji Mamman Shata
Katsina ba ɓoyayye ba ne kusan
duk wani Bahaushe ko ma-ji Hausa, a ƙasar Hausa ko wajenta
duk an san shi ko ma a ce ba a yi fitaccen mawaƙi a ƙasar Hausa kamar
Shata ba.
An daɗe ana yi wa waƙoƙin baka na Hausa
hidima, tun daga kundaye da takardu da bugaggun litattafai. Madalla da ayyuka
irin na su
Gusau (1988) da Gusau (2003) da Ɗangambo (2008) da
Gusau (2008) da Gusau (2008) da Bunza (2009) da Satatima (2009) da Gusau (2010)
da Gusau (2010) da Gusau (2011) da Gusau (2013) da Gusau (2013) da Funtua
(2015) da Gusau (2019) da sauransu. Sun duba abin da ya shafi asalin waƙar baka da tarihin kiɗa a ƙasar Hausa. An nuna
yanayin makaɗan baka na Hausa da
halayya da nau’o’in waƙoƙin tare da bayyana yanayin turke da
hanyar nazarin waƙar baka. Saboda haka, waƙoƙin baka sun sha
hidima daga hannun malamai da manazarta Hausa, har da ma masu sha’awar harshen
Hausa.
3.1
Mata
Mata sun daɗe suna
rubuce-rubuce da suka shafi mata ‘yan uwansu a waƙoƙi da finafinai har
da sana’o’i da tallace-tallace da sauran batutuwa da suka shafi
harshe da al’ada da adabi. A ciki irin waɗannan
ayyuka sukan bayyana matsalolin mata da nufin shawo kansu kamar yadda ya zo a ayyuka
irin na su Yaro (2008) da Bugaje (2011) da Muhammad (2011) da suka
yi bincike a kan mata marubuta waƙoƙi da gudunmawarsu
da duba ɗabi’un mata a bakin mawaƙan baka na Hausa. Yaro (2008) ta yi nazarin rubutattun waƙoƙin mata a Kano
daga 1954-2004. Bugaje
(2011) ta yi bincike a kan rubutattun waƙoƙi na wa’azi na mata
na ƙarni
na ashirin. Daga farko ta yi bayanin mata a ƙasar Hausa, ta yi
waiwayen yadda rayuwar mata ta kasance a cikin al’ummar Hausawa, tun daga
lokacin maguzanci da Jihadi da bayan zuwan Turawa, domin fito da gudunmuwarsu
wajen bunƙasa adabi da kyautata tarbiyya. Ita kuwa Muhammad (2011)
ta yi bincike a kan ɗabi’un mata a bakin
mawaƙan baka na Hausa. Daga farko ta duba mata a ƙarƙashin inuwar al’ada,
ta nuna cewa kafin zuwan musulunci ba a yi wasu ayyuka masu yawa a kan mace ba,
inda aka samu an yi za a ga cewa a kan al’adar bori ne.
Ammani (2008) da
Bagudo (2010) da Sanda (2011) da Bibi Faruk (2011) da Hausawa (2012) da Ingawa
(2012) sun yi bincike a kan sana’o’i da tallace-tallacen mata. Muhammad (2002)
da Hassan (2012) sun duba matsayin mata a cikin fina-finan Hausa. Dunfawa
(2004) ya yi magana a kan matsayin mata a idon ‘yan boko da gargajiyar
Bahaushe. Ya yi ƙoƙarin dubin matsayin mata a wajen Bahaushe a gargajiyance
da kuma yadda Hausawa ‘yan boko suke dubinsu. Ya yi bayani yadda Bahaushe ke
dubar mace kafin zuwan addini musulunci da kuma bayan zuwansa kafin zuwan boko. Ya
kuma duba mata a lokacin samuwar ilmin boko, musamman ga mata wanɗanda suka samu ilmin.
Haka mata suka ci gaba da hidimta wa mata a cikin
ayyukan adabi. Ana cikin haka maza suka fara yunƙurowa wajen taya mata
koken matsalolinsu a cikin ayyukan adabi na ƙagaggun labarai. An
samu Muhammed Umar da ya rubuta littafin Amina
(2009).
4.1 Taƙaitaccen
Tarihin Mai Babban Ɗaki Hajiya Hasiya
An haifi Hajiya Hasiya
a unguwar Darma, da ke cikin birnin Kano. Mahaifinta Babarbare ne, mai suna
Muhammadu Kabir. ‘Ya’yansa suna kiransa da Abba Kabir, wanda suke zuriyar gidan
Sallaman Kano ne. Mahaifiyarta kuwa sunanta Ummu Kaltume Shuwa Arab ce, daga
wani gari da ake kira Wadai ta Fallomin ƙasar Chadi, gaba da ƙasar Borno. ‘Ya’yanta
suna kiranta da Tadiye. Hajiya Hasiya tana daga cikin ‘yaya huɗu da suka rayu ga
mahaifanta. Ana kiranta da Asabe, sunan ranar da aka haife ta. Ana kiranta da
Maiturare ko ‘yar Tadiye a gidan mai martaba sarki. Daga baya Abba Kabir da
iyalensa suka koma unguwar Maraɓa (Durumin Iya), a nan iyayenta suka rasu. Mahaifinta ya
rasu a zamanin sarkin Kano Abbas Maje Nasarawa. Mahaifiyarta ta rasu a zamanin
sarkin Kano Abdullahi Bayero (Bayero, 2007).
5.1 Hoton
Mata a Bakin Makaɗa Sa’idu Faru
Makaɗa Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin shahararrun makaɗan fada na ƙasar Hausa. Ya yi wa sarakuna da hakimai da ‘ya’yan sarki
waƙoƙi da dama.
Wata fitacciyar al’ada game da waƙoƙin fada na ƙasar Hausa, da wuya a
ji wani makaɗin fada ya yi wa mace
waƙa,
ya bayyana wata daraja da gudunmawar da take bayarwa
kamar yadda wasu mazan suke yi. Ba za a ce ba a taɓa yi ba,
sai dai a ce kunnuwa ba su kai ga ji ba sai a bakin Ɗan’umma
Rungumi, Ɗantumba Rungumi, ɗan Abubakar ɗan Abdu da Alu mai
kurya. Sannan kamar yadda tarihinsa ya nuna, yawancin ƙuruciyarsa ya yi ta a
Banga, tare da mahaifiyarsa. Ya rayu da uwarsa da farko, kafin ya koma wajen
mahaifinsa.
A waƙar ‘Mai Babban Ɗaki, waƙa ce makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Hajiya Hasiya
mai babban ɗaki wato mahaifiyar sarkin Kano Ado
Bayero. A
cikin waƙar, makaɗin ya yabi mai babban
ɗaki, ya nuna
muhimmancin mata a cikin al’umma da irin gudunmawar da za su iya bayarwa. Duk
da makaɗi ne na dauri,
hakan bai hana shi ganin kima da darajar mata ba ta hanyar waƙe su da fito matsayinsu
ta hanyar nuna irin gudunmawar da za su iya bayarwa a cikin al’umma. A wani ɗan waƙar, makaɗin yana cewa:
Jagora:
Kanawan Dabo kuna da kyauta,
: Kanawan
Dabo kuna da yaƙi.
A wannan ɗan waƙa makaɗin ya yabi Kanawa da
kyauta. Son kyauta ko a ce roƙo ga makaɗan baka, abu ne
fitacce wanda da wahala a ce an yi waƙa ba tare da yabon
wanda aka yi ma waƙar ba. Yawanci ma yabon yake sa a yi waƙa, har a yi roƙon wata kyauta. Duk
da akwai turaku da dama da maƙaɗa suke amfani da su wajen
aiwatar da waƙoƙinsu. Kodayake Gusau (2008:376) ya nuna yabo yana ɗaya daga cikin manyan
turakun da makaɗan baka suka fi
yawan amfani da shi wajen aiwatar da waƙoƙinsu. Ya ayyana
fitaccen turke ne a waƙoƙin baka na Hausa don yawancin waƙoƙin sukan kasance
yabon wanda aka yi ma waƙar ne. A wannan ɗan waƙar mai zuwa, makaɗa Sa’idu faru ya nuna
cewa:
Jagora:
Ta ɗara gwamnati kowace
iri,
Ta ɗara gwamnati kowace
iri,
Ke taimaki talakawa,
talakawa sun taimake ki.
A ƙoƙarin yabon Mai Babban
Ɗaki,
makaɗin ya kai ta matsayin
da ake ganin mata ba za su iya kaiwa ba. Duk da cewa musulunci ya daidaita
matsayin mace da na namiji wajen daraja. Aliyu (1980:13) ya ayyana babu shakka,
musulunci ya tabbatar da matsayin mace daidai yake da na namiji wajen daraja da
kasancewarta cikakkiyar mutum, duk asalinsu ɗaya ne. Makaɗa Sa’idu Faru ya burge, ya nuna mace
tana iya yin kwatankwacin abin da namiji zai iya yi. Bayan haka, ya ƙara nuna matsayin
mata da irin aikin da suke iya yi, a wannan ɗan waƙa:
Jagora:
In rancen galmar shanu kake so,
ka zo
mai babban ɗaki ta ba ka,
In kana
son galmar shanu,
Ka zo
mai babban ɗaki ta ba ka,
In kana
son bashi ka yi noma,
Ka zo
mai babban ɗaki ta ba ka,
In kana
son babbar riga,
Zo
babban ɗaki ta ba ka,
In kana
son bashin kuɗɗi,
Zo
babban ɗaki ta ba ka,
In kana
son kyautar mota,
Zo
babban ɗaki ta ba ka,
Kowaz
zo nan birnin Kano,
Kowaz
zo birnin Kano,
In yaz
zo babban ɗaki,
Ya iske aikin gabata.
Makaɗa Sa’idu Faru ya ci
gaba da nuna amfanin mata da irin gudunmawar da za su ba al’’umma ta hanyar
taimako ko kyauta ko bashi. Kyauta a wajen Bahaushe abu ne mai kyau, don yakan
ce, “Alheri mai hana mugun suna”.
Cin bashi ma yana daga cikin ɗabi’un Hausawa, yakan ce,
“Bashi
hanji ne yana cikin kowa”. Wannan jan hali da
makaɗin ya rattabo,
kyawawan halaye ne da aka fi jin maza suna aikatawa,
musamman a lokacin da aka aiwatar da waƙar. Duk ba a samu
ainihin lokacin ba, ana sa ran waƙar ta jima. Ko daga
lokacin da Sa’idu Faru ya rasu a shekarar 1987 a ce a shekarar aka yi waƙar, ai ta girma
sosai. A shekaru talatin da bakwai da suka wuce a samu mace da aiki irin na
maza, abun burgewa ne. Ko ba ta yi abin da namiji
ya yi ba, ai ta kamanta. Musulunci ya ba mace damar kyauta da aikata ayyukan
alheri kamar maza. Al’adar Bahaushe ba ta hana mace aikata alheri ba. Ya nuna
kamata ta bayyana darajar mata da matsayinsu a cikin al’umma, tunda ɗan waƙar ya nuna yadda makaɗan faɗa ba su cika yi wa
mata waƙa ba kamar yadda ya yi, sai dai su ambata su jefi-jefi
cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsu.
Ba a ce ba a taɓa yi ba,
watalila kunnuwa ba su ji ba ne. Wannan wata karramawa ce sosai da Sa’idu Faru
ya yi wa mata.
Jagora:
Na shekara talatin daidai maza su nay yi ma waƙa,
Yau
mata nika yi wa waƙa,
Na zo ‘yar malam
Muhamman.
Haka makaɗin ya ci gaba da
yabon mata da nuna su cikin matsayi mai kima, mai daraja. Bayan haka, bai gaza
ba wajen jaddada matsayin mata, ya ce:
Jagora:
Matan nan tahi maza duka, don iko gare ta,
Amshi:
Matan nan tahi maza duka, don na san hairan gare ta,
Matan
nan tahi maza duka, don na san hairan gare ta,
Matan
nan tahi maza duka, don na san hairan gare ta.
Ba
a gwada maki iko, Asabe tun farko iko gare ki,
Ba
a gwada maki yaƙi, tun farko yaƙi gare ki,
Ba a gwada maki ilmi,
tun farko ilmi gare ki.
A wannan ɗa, ya nuna fifikon
mata a kan maza yayin wannan yabo na Mai Babban Ɗaki. Ko a ƙoƙarin mata na neman
‘yanci ba su cika nuna matan sun fi maza ba, sun fi neman ‘yancin daidai komai
tsakaninsu da maza, shi ya sa matan kan ce: “Duk
abin da namiji zai yi, mace ta za iya”. Ya nuna ta mai yaƙi, mai ilimi kamar
maza. Da ma musulunci bai hana mace neman ilmi kamar maza ba,
sai dai sharuɗɗan fitar mace da kuma
nuni da wasu ayyukan da sukan fi dacewa da mata. Aliyu (1980) ya nuna a kan
ilmi, musulunci bai nuna bambanci tsakanin namiji da mace ba.
Musulunci ya yi kira ga mace kamar yadda ya yi bisa ga namiji. A fagen yaƙi da iko ne musulunci
ya nuna matsayin kowa. Sannan makaɗin ya dai sha yi wa maza waƙa, yanzu fagen mata
ne, ya ce:
Jagora:
Na gaji da kiɗi na maza,
Mata nika zuba ma waƙa.
Wannan ɗa ya nuna Sa’idu Faru
ya nuna mata suna da rawar da suke takawa da har ya gaji
da kiɗin maza, ya fara na
mata. Watakila da makaɗin bai ga abin yabo
ga matan ba, da bai yaba ba. Hakan ma wani fito da matsayin
mata ne a idon al’umma. A wani ɗan kuma cewa ya yi:
Jagora: Tunda maza ma
na da iko,
Amshi: Ko mata ma na
da iko.
Jagora: Tunda maza
duka na sarauta,
Amshi: Ko mata ma na
sarauta.
Jagora: Tunda maza
dai na da ilmi,
Amshi: Ko mata ma na
da ilmi.
Jagora: Tunda maza
mulki gare su,
Amshi: Ko mata ma na
da mulki.
Jagora: Tunda maza
iko gare su,
Amshi: Ko mata ma na
da iko.
Jagora: Tunda maza
noma sukai Sa’idu,
Amshi: Ko mata aiki gare su.
A wannan ɗa, ya bayyana duk
abin da namiji yake iya yi, mata suna iya kwatankwacinsa. Maza na iko mata ma
suna yi, maza na noma mata ma suna yi, maza na sarauta, mata ma suna yi. Wannan
ɗa ya nuna ba a bar
mata a baya ba wajen kawo ci gaba a cikin al’umma. Ci gaba mai kyau tunda ya
shafi noma da iko da ilmi da sarauta.
6.0 Kammalawa
Wannan bincike ya
nuna ashe makaɗan fada ma ba a bar
su a baya ba wajen waƙe mata ta yabon baiwar da Allah Ya yi masu. Abun ya burge
da aka ji wannan makaɗi ya wasa mata, ya
nuna irin gudunmawar da su ma suke iya badawa. A baya nan da suka gabata, sun
nuna lallai wannan waƙa ta zama wata taska ta adana muhimmancin mata a waƙoƙin fada. Makaɗin ya yabi mai babban
ɗaki, ya koɗa ta sosai da sosai. Bayan
yabo, makaɗin ya kawo maganar
tauhidi, a wani ɗan da ya nuna komai
Allah ke yi. Kenan a iya cewa, waƙar “Mai
Babban Ɗaki” ta makaɗa Sa’idu Faru ta zama
wata taska ta nuna muhimmancin mata a waƙoƙin fada. Tunda a iya ɗan bincke, ba a samu
wata waƙa da makaɗan faɗa musamman na dauri suka yi wa mata kacokam ba. Hannun
mai bincike bai kai gare ta ba. Shi ya sa wannan waƙa
ta burge matuƙa.
Manazarta
Ammani, Z. (2008). Tasirin Al’adu Baƙi a kan Sana’o’in Gargajiya na Mata Hausawa a Kano da Katsina.
Unpublished
Master’s Thesis. Kano:
Department of Nigerian Languages, Faculty of Arts and Islamic Studies,
Bayero University.
Aliyu,
I, A. (1980). Matsayin Mata Da Rayuwar
Aure a Musulunci. Kano: Rukhsa Publications.
Bagudo, F. A. (2010). In Ba Ku Ba Ƙasa: Gudunmuwar Mata ga Bunƙasar Sana’o’i a Sakkwato. Unpublished Master’s Thesis. Sokoto: Department
of Nigerian Languages, Faculty of Arts, Usmanu Ɗanfodio University.
Bayero,
S.K. (2007). Rumfa Sha Shirgi: Hajiya Hasiya Bayero (Mai Babban Ɗaki).
Bibi Faruk, S. I. (2011). Tasirin Aikin
Gwamnati a kan Matan Aure Hausawa a Jihar Kano. Unpublished
Master’s Thesis. Kano: Department of Nigerian Languages, Faculty of Arts and
Islamic Studies. Bayero University.
Bugaje,
H. M. (2011). Wa’azi a Rubutattun Waƙoƙin Mata na Ƙarni na Ashirin.
Unpublished Master’s
Thesis. Zaria: Department of Nigerian and African Languages, Ahmadu
Bello University.
Bunza,
A. M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash
Islamic Publications Centre Limited.
CNHN
(2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello
University Press Limited.
Dunfawa,
A. A. (2004). Matsayin Mata ga Idon ‘Yan Boko da Gargajiyar Bahaushe. Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies. Vol. 1, no.1. Sokoto: Department of
Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University.
Ɗangambo, A. (1987). Rabe-raben
Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Gidan Sa’adu Zungur.
Ɗangambo, A. (2008). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon Tsari). Zaria: Amana Pulishers Limited.
Funtua,
A.I. (2015). Nazari Akan Waƙoƙin Makaɗan Baka Na Hausa A
Jihar Katsina Daga 1987-2012.
Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Gusau,
S.M. (1988). Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu Da Yanayinsu Musamman A Ƙasar Sakkwato.
Kundin Digiri na UKu. Kano: Sashen Harsuna Nijeriya, Jami’ar
Bayero.
Gusau,
S.M (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Gusau,
S. M. (1996). Makaɗa Da Mawaƙan
Hausa.
Kaduna: Fisbas Media Services.
Gusau,
S. M. (2008). Waƙoƙin Baka
A Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Gusau,
S. M. (2008). Dabarun Nazarin Adabin
Hausa. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Gusau,
S. M. (2010). Rawar Da Ta Kamata Marubuta Waƙoƙin Hausa Su Taka Ga
Kyautata Rayuwar
Al’umma. Takarda Wadda Aka Gabatar A Taron Bita Wadda Hukumar Bunƙasa Harkokin Matasa
Ta Jihar Kano Ta ShiryaWa Marubuta Da Makaɗa Waƙoƙin Hausa A Gidan
Mambayya Na MalamAminu Kano, Kano. Daga Juma’a 19/02/2010 Zuwa Lahadi
21/02/2010.
Gusau,
S.M. (2010). Hanyar Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya A Taƙaice. Takarda Wadda
Aka Gabatar
A Taron Ƙara Wa Juna Ilmi Tsakanin Malamai Da Ɗalibai, Sashen Hausa,
Jami’ar Bukar Abba Ibrahim, Damaturu, Jihar Yobe. Laraba 10/12/2010.
Gusau,
S.M. (2011). Ga Fili Ga Mai Doki: Wata Mahanga Ga Mawaƙa Da Makaɗan Hausa. Takarda Wadda Aka Gabatar a Taron Ƙara Wa Juna Sani Na Haɗin Gwiwa Tsakanin Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano Da Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i Ta Jihar Kano. Alhamis 07/04/2011.
Gusau,
S.M. (2011). Adabin Hausa A Sauƙaƙe. Kano: Century
Research and Publishing Limited.
Gusau,
S.M. (2013). Bayani Kan ‘Ranar Mawaƙan Hausa’. Takarda
Wadda Aka Gabatar
A Taron ‘Ranar Mawaƙan Hausa’ Na Farko Wanda Aka Yi a Taskar
Ala Global, Guda Abdullahi Street, Farm Centre, Near Country Mall,
Kano. Talata 01/01/ 2013.
Gusau,
S.M. (2013). Mizani Tsakanin Waƙoƙin Hausa Na Baka Da
Rubutattu. Takarda Wadda Aka Gabatar A Taron Ƙara Wa Juna Ilmi Na Ƙasa Kan Harshe
Da Adabi da Al’adun Hausawa Na Farko Wanda Cibiyar Nazarin Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano Ta Shirya A Gidan Mambayya, Kano. 14-19 Ga
Janairu 2013.
Gusau,
S.M. (2019). Diwanin Waƙoƙin
Baka: Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun
(1909-1991) Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun Jihar Zamfara (Juzu’i Na Huɗu). Kano: Century
Reseach & Publishing Limited.
Hassan, B. M. (2012). Takaicin Mata a
Fina-Finan Hausa. Unpublished
Master’s Thesis.
Zaria: Department of African
Languages and Cultures, Ahmadu Bello University.
Hausawa, M. H. (2012). Gudunmuwar Mata
Hausawa a Tallace-Tallacen Zamani a Jihar Kano.Unpublished Master’s Thesis. Kano: Department
of Nigerian Languages and Linguistics, Faculty of Arts and Islamic
Studies,
Bayero University.
Ingawa, Z. S. (2012). Tasirin
Sauye-Sauyen Zamani a kan Rayuwar Matan Hausawa a Katsina Daga
1960-2010. Unpublished
Phd Thesis. Kano: Department of Nigerian Languages and Linguistics,
Faculty of Arts and Islamic Studies, Bayero University.
Muhammad, N. A. (2002). Mata a Cikin
Fina-Finan Hausa (1995-2002). Unpublished Master’s Thesis. Kano: Department
of Nigerian Languages, Faculty of Arts and Islamic Studies,
Bayero University.
Muhammad,
R. (2011). Ɗabi’un Mata a Bakin Mawaƙan Baka na Hausa.
Unpublished Master’s Thesis.
Zaria: Department of African Languages and Cultures, faculty of
Arts, Ahmadu Bello University.
Sanda, F. U. (2011). Gudunmuwar Turawa
a kan Wasu Sana’o’in Gargajiya na Mata Hausawa. Unpublished
Master’s Thesis. Kano: Department of Nigerian Languages, Faculty of Arts and Islamic
Studies,
Bayero University.
Satatima,
I. (2009). Waƙoƙin Ɗarsashin Zuciya Na Makaɗan Hausa. Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Yaro, M. I. (2008). Nazarin Wasu
Rubutattun Waƙoƙin Mata a Kano Daga 1954-2004.
Unpublished
Master’s Thesis. Kano: Department of Nigerian Languages, Faculty of Arts and Islamic
Studies,
Bayero University.
Umar,
M. (2009). Amina. Zaria: Ahmadu Bello
University Press Ltd.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.