Citation: Bashir, R. (2024). Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 163-171. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.021.
SALON JERIN SARƘE A WASU WAƘOƘIN MAKAƊA SA’IDU FARU
Daga
Rabiu Bashir PhD
Department of Nigerian
Languages and Linguistics,
Kaduna State University,
Kaduna
rabiubashir86@gmail.com
08035932193/08094378162
Tsakure
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin
jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai
burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sauraro. Da wannan ne ya
sa fasihai kan dage su ga sun zaɓo salailan da za su dace da su, su kuma ba su dama su ga
sun sace zuciyar masu sauraren su, domin ganin haƙarsu ta cim ma ruwa na neman samu karɓuwa ga abokan hulɗarsu. Salon jerin sarƙe (Parallelism) shi ne dabarar tsarawa da jera kalmomi ko
jumloli iri guda a cikin ɗiyan waƙa da nufin jaddadawa ko ƙarfafawa ko nuna wata danganataka ko alaƙa a tsakanin gunduwoyin ɗiyan waƙa. Wannan maƙala ta ƙudiri aniyar zaƙulowa tare da nazartar salon jerin sarƙe daga cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, inda za a bi wasu ɗiyan waƙoƙnsa a nuna yadda ya sarrafa salon, ta
hanyar jerowa da tsara kalmomi da jumloli iri guda ko masu alaƙa da juna domin ya isar da wani saƙo. Maƙalar ta ginu ne
a kan nau’in bincike bi-sharhi, inda aka zaƙulo wasu waƙoƙin makaɗin
waɗanda ake ganin suna ƙunshe da salon jerin sarƙe a cikinsu, sannan a warware yadda ya ƙunshe tunanin nasa ta hanyar yin sharhi ga ɗiyan
waƙoƙin. Maƙalar ta tattara bayanan da ta yi amfani da su ne ta
hanyar bibiyar tahirin makaɗin da sauraron waƙoƙinsa domin ganin an tace waɗanda
suke ƙunshe da wannan salo
a cikinsu. Sannan kuma aka juye su a takarda. A ƙarshe maƙalar
ta tabbatar da harsashenta na cewa waƙoƙin
Makaɗa Sa’idu Faru cike suke da salailai mabambanta, wanda
salon jerin sarƙe ɗaya
ne daga cikinsu, inda ta tabbatar da hakan ta hanyar kawo misalai na yadda makaɗin
ya sarrafa salon, tare da yin sharhi a kan ɗiyan
waƙoƙin nasa.
1.1 Gabatarwa
Babu shakka cewa salo shi ne dokin jigo kuma asirin waƙa, domin kuwa da shi ne ake isar da duk wani saƙo na adabi.
Haka kuma da salo ne makaɗa ke iya isar da duk wani saƙon da suka ƙunso a waƙa har ta kai ga ta samu karɓuwa wurin masu sauraro. Wannan dalili ya sa idan salo ya kasance mai gwaɓi da karsashi sai manufa da saƙon waƙa su zama masu gwaɓi da armashi. Idan kuma suka
kasance raunanan ko kuma lami, sai a iske cewa komai na waƙar ya gaza
biyan buƙata, kuma ta kasance mai gundura. (Yahya 2001 da Ɗangambo 2007). Haka kuma Garba
(2011) ya jaddada cewa iya zaɓin salo babbar alama ce ta shaidar basira da ƙwarewar
fasihi a fagen adabi, musamman waƙa. Hakan wani tabbaci ne cewa
iya girman fasahar da mawaƙi yake da ita, tana ta’allaƙa ne a kan gwanancewa da ƙwazonsa wajen iya sarrafa salo
a waƙa.
Makaɗa Sa’idu
Faru wanda ake kira “Malamin waƙa”, ɗaya ne daga cikin fitattun makaɗan fada da aka yi a ƙasar Hausa wanda ya ɗauki dogon zamani yana kiɗa da waƙa. An haife
shi ne a garin Faru Ƙaramar Hukumar Maradun ta jahar Zamfara a yanzu a shekarar 1916. Ya yi
karatun addini bakin gwargwado,
kuma ya gaji kiɗa ne daga
wurin mahaifinsa wanda kuma a wurinsa ne ya koyi kiɗan fada. Kenan a iya cewa, Sa’idu Faru mawaƙi ne na gado, na kuma ƙungiya,
yana shirya waƙoƙinsa bisa sahu na ƙire
tare da ɗora
su kan awo kamar haka: + ƙungiya
(+ jagogara
+ ‘Y/Amshi (+Ciko + G/waƙa)
+ kaɗaita
(+ƙulli-ƙari) + takidi + kwaikwaye.
1. 2 Ma’anar Salo
Masana da manazarta
adabi sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen bayyana fahimtarsu game da ma’anar salo, duk
da cewa akwai kaɗan
daga cikinsu kamar su Yahya (2001), da Adamu (2002), da suke kallonsa a
matsayin wani abu da ke da wahalar fayyacewa musamman ta fuskar ma’ana.
Stephen (2000), ya
bayyana ma’anar salon fasihin waƙa
da cewa shi ne yadda fasihin ke ƙullawa
da sarrafa hikomomin harshe, da kuma ƙoƙarinsa wajen zaɓen kalmomi, da amsa-amo, da karin waƙa, da raujinta, da kuma irin yadda yake sarrafa su daidai
da tunaninsa a waƙe. Wato dai salon
sarrafa sifofin harshen asali gwargwadon zurfin tunanin fasihi da kuma bunƙasarsa.
Sa’id (1981), cewa ya
yi salo shi ne yadda mawaƙi
ya zana tunaninsa a takarda. Za a dube shi a gani, shin yana da manufa, kuma
bayaninsa yana da ƙarfi ko rarrauna ne,
ana kuma fahimtarsa cikin sauƙi
ko sai an yi lalube a gane manufarsa? Haka kuma za a dubi gwanintarsa wajen
sarrafa harshen da ya yi amfani da shi.
A yayin da shi kuma Ɗangambo (1981), ya
bayyana salo a matsayin hanya ko dabara ta isar da saƙo.
Sannan ya ƙara da cewa lallai ne
salo ya ƙunshi zaɓi, kuma kyan salo ko
muninsa ya danganta ne da yadda kowane mutum ya zaɓi abubuwan da ya yi
amfani da su a cikin rubutunsa, ko furucinsa don ya isar da saƙonsa.
Har wa yau Gusau
(1975 da 2003), ya bayyana salo a matsayin wata dabara da ake yi wa harshen waƙa kwalliya da ita. Wato akan zaɓi kalmomi ne a
zayyana waƙa, a ƙawata ta sosai ta yadda za a burge mai saurare a kuma
jawo hankalinsa.
Shi kuwa Yahya
(2001), cewa ya yi salo na nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi domin isar da saƙo.
Ita wannan hanya tana yi wa waƙa
kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar.
Baldick (2004), ya
bayyana salo ne a matsayin hanya ta musamman da wani fasihi ko zamani ko wata
mazhaba ko wani fannin ya shahara da shi wajen sarrafa harshe.
Dunfawa (2002), cewa
ya yi kalmar salo tana nufin azanci, wato dabara da mutum kan yi amfani da ita
wajen samun nasarar aiwatar da abubuwa. Sannan ya ci gaba da cewa, a
fagen nazarin waƙa kuwa, salo na nufin
hanyoyi da dabarun da mai shirya waƙa
yake amfani da su domin sadar da saƙon
da yake ƙunshe a cikin waƙarsa ga masu saurare ko karatu (Dunfawa,
2002: 270).
A ƙarshe idan muka kalli yadda manazarta suka bayyana
ma’anar salo, ma iya cewa wata dabara ce ko hanya da wani fasihi kan yi amfani
da ita don ya zaɓo kalmomi da kalamai
waɗanda
za su dace da saƙonsa, ta yadda zai
isar da shi cikin burgewa da jan hankalin mai sauraronsa, kuma ita irin wannan
dabarar ta sha bamban a tsakanin mawaƙa,
kuma da ita ce
akan yi wa waƙa hukunci a matsayin
mai daɗi
ko akasin haka.
Nazarin salo ba sabon abu ba ne a fagen waƙa, duk da cewa wasu masanan suna kallonsa a matsayin wani
fage faffaɗa
kuma mai wahalar ƙididdigewa, amma duk
da haka ba a bar shi a baya
ba, don kuwa an yi ta bibiyarsa ta kowace fuska. Misali;
Leech (1968), ya
nazarci salon sarrafa harshe da lalurar waƙa
da kuma sauran hanyoyin ƙwanƙwance harshen waƙa.
Ya bayyana lalurar waƙa a matsayin ‘yancin
da mawaƙi yake da shi wajen
karya ƙa’idoji da dokokin
harshe saɓanin masu amfani da
harshen na yau da kullum. Ya ƙara
da cewa irin wannan ‘yancin ne kan kai wasu mawaƙa,
musamman na wannan lokaci su wuce iyaka, wadda yake kaiwa ga gurɓata harshe. Haka nan
malamin ya kawo nau’o’in lalurar waƙa
daban-daban, waɗanda
suka haɗa
da na tsarin sauti, da na gundarin kalma, da ta karin harshe, da lalurar
rajista, da ta tarihi, da ta ƙa’idojin
rubutu sai kuma larurar waƙa
ta ma’ana, sannan ya tabbatar da cewa mawaƙi
na da damar amfani da kowane nau’i daga cikin nau’o’in larurar waƙar a kowane lokaci yake shirya waƙa.
1.3 Bitar Salon Jerin Sarƙe
Salon jerin sarƙe wata hikima ce ko dabarar shirya waƙa ta hanyar saƙa
zantuka masu alaƙa da juna ta fuskar
ma’anoninsu ko tsarin gini ko kuma saƙonni.
Kuma akasari ana sarrafa irin wannan dabara ne da nufin ƙarfafawa
ko nanata alaƙar da ke tsakanin
zantukan da aka jero. Wani lokaci kuma ana amfani da
ita ne domin a kwanta bambancin da ke tsakanin wasu abubuwa ko kuma a jaddada
wani tunani ko wani batu da aka yi.
Manazarta da dama sun
yi rubuce rubuce a kan salon jerin sarƙe,
kama tun daga ma’anarsa har zuwa nau’o’i ko ire-irensa. Misali Unger (1951) ya bayyana ire-iren jerin sarƙe da dama tare da fayyace ma’anar
su. Daga ciki akwai jerin sarƙe na kalmomi masu ma’ana iri guda (Synonymous
parallelism) wanda ya bayyana shi da cewa layi na farko yana ƙarfafa na biyu ne sannan
kuma ya fayyace ma’anar zancen. Sannan ya ƙara da cewa yana nuna daidito ne da
dangata tsakanin kalmomi ko yankin jumla ko kuma jumla a dalilin maimata
manufar layin farko a cikin layi na biyu ta hanyar kawo kalmomi mabambanta amma
masu ma’ana iri guda. Ya jaddada cewa irin wannan jerin sarƙe yana faruwa ne a waƙa lokacin da kalmomin layin farko suke da ma’ana iri guda
da kalmomin layi na biyu (Unger, 1951).
Shi kuwa ya bayyana salon jerin sarƙe da cewa ɗaya ne daga cikin ƙunshiyar salon sarrafa harshe wanda ya haɗa salailai da makaɗa ke amfani da su (Muhammad, 1977). Da waɗannan salailai ne makaɗa suke nuna gwanancewarsu wajen iya sarrafa harshen da
suke shirya waƙa da shi, kuma da haka ne sukan nuna lallai sun laƙanci wannan harshe don haka sukan
sarrafa shi irin yadda suke buƙata. Ya kuma bayyana salon jerin sarƙe a matsayin fitaccen salo da ake
iya samu a cikin waƙoƙin Hausa musamman rubutattu, da haka ne ya nazarci nau’o’insa guda biyu waɗanda ya kira salon jerin sarƙe na ma’ana (semantic parallelism)
da kuma salon jerin sarƙe na layantawa (line linking parallelism). Sai kuma ya bayyana ma’anarsa a
matsayin wata hikima ko dabara da mawaƙa ke amfani da ita su jero wasu batutuwa ta hanyar amfani
da kalmomi ko jumloli iri ɗaya, ko masu dangantaka da juna ta fuskar ma’ana.
Baldick (2002) ya bayyana salon jerin sarƙe a matsayin wata muhimmiyar hikima
da ta yi tashe a cikin adabin Ingilishi a wuraren ƙarni na sha takwas. Sannan kuma ya
bayyana ma’anarsa da cewa ya ƙunshi shirywa ko jera jumloli ko yankin jumloli ko layuka
iri guda a cikin waƙa waɗanda suke da alaƙa da juna kuma suna nuna
wata dangantaka a tsakanin su. Ya ƙara da cewa ana iya ganin tasirin salon a fili ta yadda
aka jera kalmomi ko jumloli tare da maimaita su ko maimaita wani ɓangaren su a cikin waƙa.
Gwammaja (2014) ya nazarci salon jerin sarƙe daga cikin karin maganar Hausa. Ya
ɗora binciken ne a kan nau’o’in jerin
sarƙe guda uku waɗanda suka haɗa da na kalmomi masu ma’ana iri ɗaya (synonymous) da na kalmomi kishiyoyin juna
(anttithetic) sai kuma na ginin jumla (synthetic). Ya bayyana cewa jerin sarƙe na kamomi masu ma’ana
iri ɗaya da cewa shi ne ya fi kowane sauƙin sarrafawa a cikin
ayyukan fasaha. Sai ya bayyana ma’anarsa da cewa wata hikima ce ta jera zance a
cikin layuka guda biyu ta hanyar amfani da kamomi mabambanta amma masu isar da
ma’ana iri ɗaya (Gwammaja 2014). Haka kuma ya
bayyana cewa jerin sarƙe na kalmomi kishiyoyin juna kamar kishiya ne na jerin sarƙe na kalmomi iri ɗaya, inda shi akan jero kamomi ne masu kishiyoyi a cikin
layuka. Ya ce shi yana samuwa ne a lokacin da kalmomin layukan farko suka saɓa da kalmomin layuka na biyu. A wajen jerin sarƙe na ginin jumla kuma ya
nuna cewa, sau tari jumlar da ke biye ita ce ke ƙara fito da bayani na tunanin da ke ƙunshe cikin jumla ta biyu da nufin
jaddadawa ko ƙara yayyace batun da ke cikin jumlar farko.
A taƙaice dai a iya cewa salon jerin sarƙe wata hikima ce ko dabara da fasihai kan yi amfani da
ita a cikin ayyukan adabi musamman waƙa domin su isar da wani saƙo ta hanyar jero kalmomi ko jumloli
iri ɗaya a cikin ɗiya ko layukan waƙar, kuma waɗannan kalmomi ko jumloli su kasance
suna da alaƙa ko dangantaka da juna game da saƙon da suke ƙoƙarin isarwa. Haka kuma za a iya cewa salon jerin sarƙe na nufin amfani da kalmomi ko
jumloli ko yankin jumloli a cikin waƙa da nufin nuna wani tunani ko dangantaka ta wasu
abubuwa. Iya sarrafa jerin sarƙe a waƙa kan sa ɗiyan waƙa su tafi a tsare tare da maimaita wasu kalmomi ko jumloli a cikinsu da
nufin jaddada saƙo ko burge mai sauraro.
1.4 Salon Jerin Sarƙe a Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Sa’idu Faru
Makaɗa Sa’idu Faru na ɗaya daga cikin fitattun makaɗan fada na Hausa waɗanda Allah ya yi wa baiwa da fasaha ta iya sarrafa harshe, inda yakan ƙulla waƙoƙinsa ya kuma sadar da su ta hanyar
sarrafa salailai daban-daban domin ganin ya burge kuma ya isar da saƙonsa cikin sauƙi. Salon jerin sarƙe ɗaya ne daga cikin salailai da makaɗa Sa’idu Faru ke amfani da su a cikin waƙoƙinsa, wanda kusan a iya cewa zai yi
wahala a samu wata waƙarsa guda ɗaya da bai yi amfani da irin wannan
salon a cikinta ba. Sarrafa salon na jerin sarƙe da makaɗin yake yawan yi a cikin waƙoƙin nasa, bai rasa nasaba da irin kiɗan da waƙoƙin da yake yi na fada, domin kuwa waƙoƙin fada waƙoƙi ne na iko waɗanda suke tafiya da tsarin mulki da gudanarwa na al’umar Hausawa. Shi kuma
irin wannan tsarin mulkin ya yarda da biyayya da kuma ƙarfafa bajinta da tausayi da kuma
kyautayi na masu gudanar da tsarin (sarakuna). Don haka sarrafa salon jerin sarƙe na ba makaɗin dama ya jaddada waɗannan batutuwa a cikin waƙoƙin nasa, domin al’uma su ci gaba da
tsayuwa a kan su.
A cikin waƙar Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo, mai gindin “Kana shire Baban ‘Yan ruwa”, Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da salon
jerin sarƙe domin ya zayyano nau’o’in mutane da Allah ya halitta, inda ya ce:
J : Kai duk ran da Allahu yai duniya,
: Duk randa Allahu yai duniya
: Shi yay yi mutum mai ƙoƙari,
: Sannan yay yi mutum mai kyawo,
: Kuma yay yi mutum mummuna,
: Sai
yay yi mutum mai haske,
: Kuma yay yi mutum mai dauni,
: Sai yay yi mutum mai samu,
: Kuma yay yi mutum busasshe,
: Sai
yay yi mutum ɗan
Sarki,
: Kuma
ya aza bawan Sarki,
: Sai
yay yi mutum mai iko,
: Kuma
ya aza mai roƙo nai,
‘Y/A: Albarkar Nana Uwar Daji
: Ba
mu mato Muhamman Sarkin Kudu.
Idan aka yi la’akari
da wannan ɗan
waƙa, za a ga cewa Makaɗa
Sa’idu Faru ya fayyace nau’o’in mutane ne da Allah ya halitta kuma suke
mu’amala da juna a cikin duniya. Makaɗin ya yi haka ne da
nufin tabbatar da tunanin Bahaushe a kan tsarin rayuwar duniya cewa,
Allah bai halicci mutane kai ɗaya ba, kamar yadda
‘yan yatsunmu ba su kasance kansu guda ba. Watau dai abin nufi a tsari na
halittar Allah ya halicce mutane daban- daban, kuma kowa da yadda ya ga dama ya
yi shi. Da makaɗin
ya tashi lissafo ire-iren mutane da kuma nau’o’insu sai ya yi amfani da salon
jerin sarƙe ya jero su ya nuna
cewa cikin halittar Allah ne ya yi wasu mutanen masu ƙoƙari. Haka kuma Allah ya halicci
wasu mutanen kyawawa, sannan ya halicci wasu munana. Haka kuma ya halicci wasu
farare, ya kuma halicci wasu baƙaƙe. Haka zalika Allah ya halicci
masu arziki, sannan kuma ya halicci talakawa. Sannan kuma a cikin mutane ne dai Allah ya halicci sarakuna, sannan ya
halicci masu yi musu hidima. A ƙarshe sai ya nuna cewa cikin
halittar Allah ne ya halicci masu mulki, sannan kuma ya halicci maroƙa duk domin duniyar ta
tafi bai ɗaya.
Haka kuma dai a cikin waƙar ta Sarkin Kudun Sakkwato ya yi amfani da Salon jerin
sarƙe, ya jero wasu tagomashi na rayuwa da basaraken yake da su, inda ya
ce :
J: Maganag ga da zani whaɗa
maka,
Y/A:
Gagarau ɗan
Alu kai man gahwara,
: Wadda
dud aka gadon ɗaukaka,
: Wadda dud aka gadon ƙasura,
: Wadda dud aka gadon ci gaba,
: Mamman ka gaji Abubabakar,
: Ko
da sayen halin nan akai,
: Baba
halin da kakai kuɗdi
shi kai.
A cikin wannan ɗan waƘar, Saidu Faru ya zuga Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo ne ta hanyar zayyano wasu darajoji da martabobi da yake
da su a matsayinsa na mai sarauta, waɗanda ba kowa Allah yake haɗa wa su ba sai zaɓaɓɓun mutane irinsa. A
wannan gaɓar makaɗin sai ya sarrafa salon jerin sarƙe ya jero fa’idojin da suka haɗa da ɗaukaka da ƙasura da ci gaba. Sannan ya nuna cewa duk waɗannan halayen ya yi gadon su ne daga wurin mahaifinsa
Sarkin Musulmi Abubakar na uku. A ƙarshe sai makaɗin ya nuna cewa ire-iren waɗannan ɗabi’u da halayen, ko da cewa aka yi
ana sayar da su a kasuwa, to fa halayen Sarkin Kudun Sakkwato masu tsada ne ba
kowa ne zai iya sayen su ba.
Har wa yau dai a cikin waƙar ta Sarkin Kudun Sakkawato mai gindin Kana shire Baban
‘Yan Ruwa, ya yi amfani da salon jerin sarƙe a lokacin da ya tashi zai zayyano
ire-iren kyaututtukan da ake yi masu, inda ya ce:
Jagora: Ko ni makaɗinka Uban Zagi
‘Y/Amshi: Don na gadi a ba mu garuruwa,
: Na gadi a ba mu jukunkuna,
: Na gadi a ba mu dawakuna,
: Mamman in Allah yai nuhi,
: Ba mu gari da mutane nai duka.
A cikin wannan ɗan waƙar, makaɗin ya nuna ire-iren kyaututtukan da
aka saba yi masu ne a matsayinsu na makaɗan iko, ta hanyar sarrafa salon jerin sarƙe ya jero su a cikin jumloli iri
guda. Makaɗin ya nuna cewa a matsayinsa na makaɗin sarakuna ya gaji a yi masa kyauta ta garuruwa da ta
jakunkunan kuɗi da kuma kyautar dawakai. A ƙarshe sai ya nuna cewa
idan akwai wata kyauta da mai gidan nasa zai yi masa, to ita ce ya ba shi
kyautar gari da kuma mutanen cikin garin duka. Haƙiƙa irin wannan kyautar da Makaɗa Sa’idu Faru yake roƙon Sarkin Kudun Sakkwato da ya yi
masa, kyauta ce ta isa da ƙasaita wadda ba kowa ke iya yin ta ba sai manyan sarakuna. Haka kuma ba kowa ake iya yi wa ita
ba sai manyan makaɗa irin shi Sa’idu Faru ɗin.
Haka kuma dai, da makaɗin ya tashi yana ƙoƙarin kwatanta irin farin jini da soyuwar Sarkin Kudun Sakkwato sai ya yi
amfani da salon jerin sarƙe ya ce :
Jagora: Babban daji kake ɗan
Abu,
‘Y/Amshi: Ko icce ko namun dawa,
: Ko manya ko ‘yan ƙanƙane,
: Da
mutum da dabba da itatuwa,
: Kowa
ƙamnam Mamman ya kai,
: Mamman
jikan Attafiru,
: Baba
na Sidi,
: Mamman
gwarzon Cika.
A cikin wannan ɗan
waƙar, Makaɗa
Sa’idu faru ya fayyace irin farin jinin gwaninsa ne, da kuma yadda ya zama abin
so a wurin mutane har da wasu halittun ma da ba mutane ba. Wurin kawo halittun
da suke ƙaunar basaraken ne
sai ya yi amfani da salon jerin sarƙe
ya jero su cikin ɗan
waƙar, waɗanda
suka haɗa
da mutane da tsirrai da itatuwa da dabbobi da namun dawa manya da ƙanana. A ƙarshe
sai ya jaddada cewa duka waɗannan nau’o’in
halittar da ya
zano dukkansu ƙaunar basaraken suke
yi.
Haka kuma dai a cikin
wata waƙar ta Sarkin Kudun
Sakkwato mai gindin “Bajinin gidan Bello Mamman na Yari” ya
yi amfani da salon jerin sarƙe a
wurare da dama, kamar haka:
Jagora: Na Magaji mai martabad ɗan Mu’azu,
‘Y/Amshi: Irin nassabab
Bubakar baba yay yo.
Jagora: Tsari gaskiya Bello kai Shefu yac ce,
‘Y/A: Bari masu son dus su mai she ka yaro,
: Da kyauta da ilmi da neman dalili,
: Da gode ma Allah da istangafari,
: Da su Bello ɗan Shehu yatc tcarma kowa,
: Ka kai kamab Bello,
: Ka
gaji moyi,
: Saura ka kai inda mai Hausa ya kai.
Haka kuma a wani ɗiyan
dai, duk a cikin wannan waƙar
sai ya ce :
Jagora: Da mutum da dabba,
: Da
tsuntsu da ƙwaro,
: Da
mutum da dabba,
: Da
tsuntsu da ƙwaro,
: Da ƙasa da abin da duk ag ga bayanta,
: Komi
na duniya na Almusɗaha na,
: Manzon
Allah abin so gare mu,
: Garai Shefu yas samu girma da yarda,
: Komi na gun shefu shi ag ga Bello,
: Komi na gun Bello shi ag ga Garba,
: Komi na na gun Garba Kai ad da shi Bello.
Idan aka duba waɗannan ɗiyan waƙa, za a ga cewa makaɗin ya yi ƙoƙarin bayyana girma da martabar basaraken ne, tare da kawo wasu kyawawan
halaye da ɗabi’u waɗanda ya riƙe kuma ya tsayu a kansu. Haka kuma ya nuna irin yadda ya
gado wasu kyawawan ɗabi’un daga tsatson zuriyar da ya fito, inda ya nunu cewa duk wasu halayen
da yake da su masu kyawu, ya gado su ne tun daga Shehu Uman Ɗanfodiyo, wanda shi kuma
duk waɗannan halaye sun kasance koyarwa ce
Manzon Allah. Daga Ɗanfodiyo sai suka biyo tsatson Sarkin Musulmi Muhammadu Bello wanda kaka ne
ga Muhammadu Macciɗo, sannan kuma suka gangaro ga Sarkin Musulmi Abubakar, wanda shi ne
mahaifinsa. Duk waɗannan abubuwan da Makaɗa Sa’idu Faru ya zayyano, ya yi amfani ne da salon jerin sarƙe ya kawo su a cikin
jumloli mabambanta. Daga cikin irin ɗabi’un da ya jero na Sarkin Kudun Sakkwato sun haɗa da kyauta da ilmi da neman dalilin faruwar wani abu
kafin a yi masa hukunci, da godiyar Allah da kuma neman tuba zuwa ga Allah.
Haka kuma sai ya jero abubuwa da yawa na halittar Allah, waɗanda ya nuna cewa duk waɗannan abubuwa duk Allah ya halicce su ne don darajar
Manzon Allah (SAW). Cikin su ya jero mutum da dabba da tsuntsu da ƙwaro da ƙasa da kuma duk wani abu
da Allah ya halitta a doron ƙasar.
Haka kuma dai a cikin wannan waƙar, da ya tashi zayyano irin kyaututtukan da Sarkin Kudun
ya yi masu na bajinta, sai ya yi amfani da salon jerin sarƙe ya jero su kamar haka:
Jagora: Baba ya ba mu bandur guda dun na lailai,
: Ya ba mu bandur guda dud na yadi,
: Ya ba mu fam goma ya ce mu ɗunka,
: Ga takalumma na fan shidda shidda,
: Hula
kalabus guda goma yab ban,
: Doki
da kaya da kuɗin
ciyawa,
: Kyauta
irin taka jikan Mu’azu,
: Don
ba a cewa mutun ba kamatai.
A nan makaɗin
ya yi amfani da salon jerin sarƙe
ne ya jero ire-iren kyaututtuka na girma da Sarkin Kudun Sakkwato (Muhammadu
Macciɗo)
ya yi masu, wadda ta haɗa da bandur ɗin
lailai da bandur ɗin
yadi da kuɗin
ɗinki
da takalma masu tsada da hula irin ta sarakuna (kalabus) har guda goma. Haka
kuma ya ba shi doki ɗauke da kaya, bai kuma tsaya a nan ba,
har da kuɗin
ciyawar da za a
riƙa ciyar da dokin sai
da ya ba su.
A ƙarshe sai ya nuna
cewa ba kowa ke iya yin irin wannan kyautar ba idan ba irin gwanin nasa ba.
Har wa yau dai a
cikin wanan waƙar, da makaɗin
ya tashi kawo ire-iren abincin Larabawa, waɗanda
yake ganin sun bambanta da namu, sai ya sarrafa salon jerin sarƙe ya zano su a cikin ɗa
guda. Waɗannan
nau’o’in abincin da ya jero sun haɗa da biskit da taba
sigari da lemu da soda da kwlbar giya (sitawut). A ƙarshe
ya nuna cewa waɗannan
abincin ba fa irin namu ba ne, don haka ba abu ne da aka yarda mutum ya yi
amfani da su ba. Inda ya ce:
Jagora: Da biskit da minti da taba sigari,
: Da biskit da minti da taba sigari,
: Da lemu da soda da kwalbas sitawut,
: Bai yarda aza su ko sau guda ba,
: Ya ɗau wasicin
da Usumanu yac ce,
: Ya ce abincinsu ba namu ne,
: Yawancin abincinsu daɗi
gare shi,
: Kowam
mami yay rashi ba ruwa nai.
‘Y/Amshi: Wancan na ci an naci bai ci can ba,
: Bajinin gidan Bello Mamman na Yari,
: Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.
A wata waƙar kuma dai ta Sarkin Kudun Sakkwato da yake ƙoƙarin bayyana irin baiwa da ɗaukakar da Allah ya yi wa Muhammadu macciɗo sai ya yi amfani da salon jerin sarƙe ya jero wasu martabobi
da darajojin da gawanin nasa ke da su fiye da sauran ‘ya’yan sarki. Makaɗin ya nuna cewa, Muhammadu Macciɗo ya kwashe kaso mafi rinjaye na duk wanin abu da ake buƙatar mai sarauta ya
mallaka na daga halaye da ɗabi’u na gari, inda ya jero su waɗanda suka haɗa da gadon gidan da ya fito wanda
abu ne da ake buƙatar kowane ɗan sarki ya kasance. Sanna ya nuna
cewa daraja gadon ta ya yi tun daga mahaifa. Haka kuma, shi jika ne ga mujaddadi Shuhu Usmanu wanda mutum ne da duk wani Musulmi zai so a alaƙanta shi da shi. Sannan ya nuna cewa
shi mutum ne mai gudun duniya, don haka sai kai tsaye ya kira shi da (kurɗabi). Haka kuma sai ya kira shi da sarkin nasara, malami
kuma mummuni. Duk waɗannan halaye da ɗabiu na daraja da martaba, makaɗin ya jero su ne cikin jerin jumloli masu alaƙa da juna ta sigar salon jerin sarƙe kamar haka:
Jagora: Kashi bakwai kak kwasa,
: ’Yan Sarki na kallo,
: Gidan
bani kai kak kai,
: Ga
irin wagga maslaha.
‘Y/Amshi: Dud gidan bani kai kak,
: Kai da irin wagga maslaha.
Jagora/’Y/Amshi: Ga ka ɗan mai daraja,
: Ga ka jikan Usumanu,
: Kurɗabi
na Fodiyo,
: Ga
ka Sarkin nasara,
: Ga
ka Alhaji Macciɗo,
: Ga jikka ta yi dubu,
: Ga ka mallami kake,
: Ga
ka mummuni kake,
‘Y/Amshi: Abin da Allah duk kai ma mutum,
: Baba yai maka.
A cikin wata waƙa mai turken “Gogarman gidan Moyi ci fansa NiƘatau”. Makaɗa Sai’du Faru ya yi amfani da salon jerin sarƙe a cikin wasu ɗiyan waƙar domin ya nuna irin yadda gwanin nasa ya shahara kuma
ya samu karɓuwa a tsakanin ‘yan’uwansa sarakuna da kuma manyan jami’an gwamnati inda ya ce :
Jagora: Sa Amadu Bello Sardauna ya yaba ƙoƙarinai,
: Tafawa Ɓalewa Bubakar ya yaba ƙoƙarinai,
: Da Gwamna Janar da Gwamnan Jaha sun ba ka
girma,
Jagora/’Y/Amshi : Kuma ya samu yardi ga
ab Lamiɗo babba
: Kuma ya samu yardi ga ab Lamiɗo
babba.
J: Wani
taro da anka zo Ikko na bariyac can,
: Da
Turawa da kuma Ministoci had da Kansiloli,
: Sarkin
Musulmi da Amadu Bello sun zo,
: Wurin
dus sun ziyar tai,
: Tafawa
Ɓalewa
ya sauka ga Lamiɗo
Barno,
: Nan
kudu Shehu Talba,
: Sarkin
Bidda ya sauka ga Sarkin Ilori,
: Kulluhinsu Sarakunan majalisa sun taru Ikko,
: Muhammadu Bello jikan Hassan kai sun ka zaɓa,
: Don ka hi su kyawon shirin kawo dalilai.
A cikin wannan ɗan waƙar makaɗin ya sarrafa salon jerin sarƙe ne ya jero wasu manyan
jami’an gwamnati waɗanda ake taƙama da su a duk ƙasar Hausa, tare da jiga-jigan sarakunan arewa. A cikin ɗan waƙar sai ya nuna cewa dukkansu sun yaba wa gwanin nasa kuma
sun yarda da shi da kuma irin yadda yake gudanar da harkokinsa na rayuwa. Daga
cikin manyan jami’an gwamnatin da makaɗin ya jero ya fara ne da Amadu Bello
(Sardaunana Sakkwato), wanda shi ne Firimiyan Arewa gaba Ɗaya. Sai Abubakar Tafawa Ɓalewa, wanda shi ne Firan
Minista a lokacin. Sai kuma ya kawo Gwamna Janar da kuma Gwamna na jahar Arewa, sannan sai ya ambato
Lamiɗo. Bayan haka sai ya nuna cewa a
lokacin wani taro da aka yi a garin Ikko, kusan duk mahalarta taron tun daga
kan Turawan da suka zo, waɗanda su ne wakilan mulkin mallaka, da Ministoci, da Kansiloli da Sarkin
Musulmi, da Sarkin Borno, da Sarkin Bidda da kuma Sarkin Ilori duk sun haɗu sun nuna cewa babu kamar shi. Haƙiƙa saƙa zantuka cikin irin waɗannan jumloli ya isa ya nuna wa mai saurare irin naƙaltar harshe da kuma iya
sarrafa salo da makaɗin ke da shi.
A cikin wata waƙa ta marigayi mai girma Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda Abubakar Garba, makaɗa Saidu Faru ya yi amfani da salon jerin sarƙe a wasu ɗiya. Makaɗin ya jero sunayen wasu fitattun makaɗan ƙasar Hausa ne, ya nuna cewa duk da sun yi wa Sarkin waƙa yana ganin waƙarsa ta ɗarar ma tasu wadda ya yi masa. Inda ya ce :
Jagora: NaƊa mani Sarkin kiƊi,
: Ka ba mu gida.
‘Y/Amshi: Kuma ka ba mu mata mui amre,
: Garba ka ba mu Rifenin da za mu ci,
: Tare da matana.
Jagora: Narambaɗa,
‘Y/Amshi: Waƙad da yay yi ma,
: Ba ta yi kamat tau ba.
Jagora: Auta Daɗi,
’Y/Amshi: Waƙad da yay yi ma,
: Ba ta yi kamat tau ba.
Jagora: Bawa Dabci,
‘Y/Amshi: Waƙad da yay yi ma,
: Ba ta yi kamat tau ba.
Jagora: Ɗandodo Alu,
‘Y/Amashi : Waƙad da yay yi ma,
: Ba ta yi kamat tau ba.
Jagora: Waƙa Ɗancana ya yi ma,
‘Y/Amshi: Ba ta yi kamat tau ba.
Jagora: Jankiɗi waƙad da yay yi ma,
‘Y/Amshi: Na ishe tai daɗi,
: Amma in an yi bincika ba ta yi kamat tau
ba.
Jagora: Ni kiɗin yaƙi niy yi ma Abu na Isau,
‘Y/Amshi/Jagora: Ba ni son kana zannawa banza,
: Ka ɗauki takobi da bindigogi da bakunkuna,
: Ka sa sirdi,
: Ba mu sansani sai bakin Tsabre,
: Kano da Katcina Kwantagora hab,
: Barno
riƙon Namoda na shi na
an can,
: Garba
ka anshe riƙon dud da
: Ummarun
Ummaru yab bar ma.
Waɗannan
ɗiyan
waƙar da suka gabata,
makaɗin
ya shirya su ne da nufin ya bugi ƙirjinsa,
ya nuna wa duniya cewa indai a fagen kiɗan fada ne to fa sai
dai a biyo bayansa wajen iya tsara waƙa.
Haka kuma ya zuga gwanin nasa da yake waƙewa
tare da nuna masa irin ƙarfin mulkin da ya gada
wurin magabatansa. Haƙiƙa yin hakan wata hikima ce ta sa basarake ya ƙara jin cewa lallai fa shi ɗin
ba kanwar lasa ba ce ko a tsakanin sarakuna ‘yan uwansa. Buƙatar Makaɗa Sa’idu Faru ta kai
ga cika ne ta hanyar amfani da salon jerin sarƙe,
inda ya jero sunayen wasu fitattun makaɗan ƙasar Hausa a cikin mabambanta jummloli masu kama da juna,
sai ya nuna cewa duka waɗannan makaɗan
ba su kai gare shi ba a wajen shirya wa sarkin kiɗa
da kuma sadar da ita gare shi. Cikin makaɗan da Sai’du Faru ya
jero, ya fara ne da makaɗa Ibrahim Narambaɗa sai
ya ambato Bawa Dabci da
Auta Daɗi
da Alu Ɗandodo mai taushi da Ɗancana da kuma Saluhu
Jankiɗi
(Sarkin Taushin Sarkin Musulmi). Bayan ya jero sunayen waɗannan
makaɗa,
sai a ƙarshe ya nuna cewa
duk waƙoƙin da suka shirya wa basaraken babu wadda waƙarsa ta kai kamar tasa. Bayan haka sai ya bayyana irin kiɗan
da yake yi masa na jaruman sarakuna ne tare da jero masa irin shirin da ya
kamata ya yi na fuskantar abokan gaba, da haka ne ya gaya masa irin shirin da ya
kamata ya yi ya kuma jero masa irin makaman da ya dace ya riƙe ya waɗanda suka haɗa
da bindigogi da takobi da bakunkuna na harbi sannan kuma sai ya hau dokinsa.
A cikin waƙar Sarkin Ƙayan Maradun Amadu,
makaɗa
Saidu Faru ya yi amfani da salon jerin sarƙe,
inda ya jero wasu sarakuna waɗanda manyan sarakuna
ne a ƙasar Hausa, waɗanda
suka haɗa
da Sarkin Kano da na Ikko da Sarkin Zazzau da Sarkin Barno da Sarkin Funtuwa da
na Bauci da na Bunguɗu da Sarkin Gobir da Sarkin Ƙayan Maradun da
Sarkin Yawuri da na Gwandu. Haka kuma sai ya Ambato wasu sarakunan da sunayen
sarautunsu waɗanda
suka haɗa
da Arɗon
Shuni da Banaga na Maru. Sai kuma a ƙarshe
ya cikashe waƙarsa tasa da ambaton
Sarkin Yamai wanda babban sarki ne a ƙasar
Nijar, sai ya nuna cewa duk waɗannan sarakun da ya
lissaffo ba sa iya aiwatar da wani abu sai sun jiraci zuwansa. Amfanin da makaɗin
ya yi da wannan salon yana ƙoƙarin ya jaddada irin girma da daraja ne da basaraken yake
da ita a tsakanin sarakuna ‘yan uwansa, wanda hakan ya sa suke mutunta shi.
Jagora: Ga Sarkin Kano gami da Sarkin Ikko sun
kammale ɗiya,
: Ga
Sarkin Zariya gami da Sarkin Barno sun kammale ɗiya,
: Ga
Sarkin Funtuwa da Sarkin Bauci sun kammale ɗiya,
: Ga Sarkin
Bunguɗu
da Sarkin Gobir sun kammale ɗiya,
: Ga
kuma Sarkin Ƙayan Maradun Maikuɗin ɗan
Shehu ya iso,
: Ga
Sarkin Yawuri da Sarkin Gwandu sun kammale ɗiya,
: Ga
Sarkin Yamai Gami da Arɗon Shuni,
: Banaga ya shigo,
‘Y/Amshi: Su duka sun taru,
: Ba su yin magana sai ran da yay iso.
1.5 Kammalawa
Wannan takarda ta yi nazarci salon jerin sarƙe ne a wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Kamar yadda aka gani an yi nazarin ne
ta hanyar duba ɗiyan wasu waƙoƙin makaɗin tare da duba
irin yadda ya saƙa wasu jumloli ko kalmomi masu alaƙa da juna domin ya jaddada wata manufa ko saƙo a cikin waƙar tasa. Bayan
haka an kawo misalai daga cikin ɗiyan waƙoƙi daban-daban tare da yi masu sharhi
domin a nuna irin yadda makaɗin ya sarrafa fasahar salon jerin sarƙe. Bincikenmu ya gano cewa, Sa’idu Faru na yawan amfani
da salon jerin sarƙe a cikin waƙoƙinsa. Haka kuma ya ƙara tabbatar da cewa makaɗin gwani ne wurin
sarrafa salailai da dama wadda hakan ce ta sa ya yi suna sosai a tsakanin makaɗan fada na Hausa
har kuma ya samu karɓuwa matuƙa a wurin al’umar Hausawa da ma sauran masu sha’awar waƙoƙin baka na Hausa waɗanda ba Hausawa ba,
kuma hakan ya dace da harsashen su Leech (1968 da 2008) da suka nuna cewa iya
sarrafa salon makaɗi na sa ya yi fice a san shi sosai kuma
ya samu karɓuwa a wurin abokan hulɗarsa.
Manazarta
Andrea,
C. (2000). AShort GuideTo Imagery, Symbolism and FigurativeLanguage.
Andrew,
O. (1980). Understanding Metaphor.
Illinios: Urbana-Champaign.
Baldick,
C. (2004). Oxford Concise
Dictionary of Literary terms. New York: Oxford University Press.
Bargery,
G.P. (1993). A Hausa-English Dictionary and English Hausa Vocabulary. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.
Bartolomeo,
P. (2015). VisualImagery. French: Institute
Of Health and Medical Reseach.
Bashir,
R. (2014). Salon Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Shata. Unpublished M.A. Thesis. Zaria: Department of
African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University.
Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Zaria: Fisbas Media Service.
Ɗangambo, A. (2008). Rabe-Raben Adabin Hausa. Kaduna: Amana
Publishers Ltd.
Dumfawa,
A.A. (2002). Waƙa a
Tunanin Yara. Unpublished Ph.D Thesis. Sokoto: Department of Nigerian
Languages, Usman Ɗanfodio University.
Dumfawa, A.A. (2005). Zambo da Habaici A cikin
Rubutattun Waƙoƙin Addini, Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol.1. No.1, Department of Nigerian Languages, Sokoto, Usmanu Ɗan Fodiyo University, Sokoto.
Garba,
S. (2011). Salon Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aƙilu
Aliyu. Unpublished Ph.D. Thesis. Zaria: Department of African Languages and
Cultures, Ahmadu Bello University.
Garba,
S. (2013). Tsokaci kan Nahawu a Waƙoƙin Aƙilu
Aliyu. Sokoto: In Zauren Waƙa,
Journal of Hausa Poetry Studies. Department of Nigerian Languages, Usman Ɗanfodio University.
Gusau,
S.M. (1985). Salo da Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: in Studies of Hausa Language,
Literature and Culture.
Gusau,
S.M. (1988). Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da
Yanaye-Yanayensu. Unpublished Ph.D. Thesis. Kano: Department of Nigerian
Languages, Bayero University.
Gusau,
S.M. (2002). Saƙo a waƙoƙin Baka: Tsokaci kan
Turke da Rabe-Rabensa. Kano: In the Studies of language, Literature and
Culture, Bichi A.Y. da Wasu (edit), Centre for the study of Nigerian Languages,
Bayero University.
Gusau,
S.M. (2002). Salihu Jankiɗi SarkinTaushi. Baraka Press and Publishers Limited.
Gusau,
S.M. (2003). Jagoran Nazarin WaƙarBaka. Kano: Benchmark
Publishers Ltd.
Gusau,
S.M. (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark
Publishers Ltd.
Gwammaja,
I. G. (2014). Parallelism in Hausa Proverbs. In Folklore, Integration and Natioanal Development In Nigeria. A Festschrift
for Professor Ɗandatti Abdulƙadir,
OFR.
Kugel,
J. (1998). The Idea of Biblical Poetry: Parallelism and its History. New York: John Hopkins Press.
Leech,
G.P. (1968). A Linguistics Guide to
English Poetry. London Longman.
Leech,
G.P. (2008). Language in Literature: style and Foregrounding. Harlow England:
Pearson Longman.
Muhammad,
D. (1977). The Individual
Talent in the Hausa Poetic Tradition: a Study of AƘilu aliyu and His
art. Unpublished Ph.D. Thesis. London SOAS.
Muhammad,
D. (1978). Structural Tension in Poetry: Case Note on Enjambmernt and Run-on in
Hausa Poetry. Kano, in Harsunan Najeriya. Center for the Study of Nigerian
Languages.
Muhammad,
D. (1978). Waƙa Bahaushiya. Kano:
In Study of Hausa Language and Literature. Kano: Centre for the Study of
Nigerian Languages.
Muhammad,
D. (1979). Interaction between the oral and the literate tradition of Hausa
Poetry. In Harsunan Nijeriya IX.
Kano: Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero.
Muhammad,
D. (1990). Hausa Metalanguage (edit).
Ibadan: University Press Limited.
Mukhtar,
I. (2004). Introduction to Stylistics Theories, Practice and Criticism. Abuja: Countryside
Ltd.
Simpson,
P. (2004). Stylistics: A resource book for students. New York:
Routledge, Abingdon.
Unger,
M. F. (1951). The Nature of Hebrew Poetry. Bibliotheca Sacra 108: 282-285.
Yahya,
A.B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.
Yahya,
A.B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.