Citation: Bashir, R. (2024). Salo Ruhin Waƙa: Nazarin Salo a Waƙar ‘Salo’ Ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 261-269. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.032.
SALO RUHIN WAƘA:
NAZARIN SALO A WAƘAR ‘SALO’ TA ALHAJI SANI SABULU
KANOMA
Rabiu Bashir
Department of
Nigerian Languages and Linguistics, Kaduna State University, Kaduna
Tsakure:
Waƙa kamar yadda masana suka yi ta ƙoƙarin bayyanawa zance ne da ya saɓa da zance na yau da kullum
domin ita shiryayyiyar magana ce mai ƙunshe da saƙo wadda ake aiwatarwa cikin hikima da
balagar harshe ta hanyar zaɓen
kalmomi da shirya su tare da sadar da su a kan wasu ƙa’idoji. Salo a cikin ayyukan adabi yakan kasance wata
gada ce wadda ta kanta ne fasihi ke bi ya gwada ƙwanjin fasaharsa da baiwarsa ta mallakar
harshe tare da samun damar isar da saƙonsa cikin sauƙi da burgewa. Masana irin
su Leech (1968) da Yahaya (2001) da Garba (2014) sun tabbatar da cewa iya
sarrafa salon fasihi shi zai ba shi dama ya samar da waƙa mai daɗi da armashi kuma har
mutane su kwaɗaitu da
waƙar
tasa. Masana irin su Mukhtar (2001) da Yahaya (2001) da Adamu (2002) suna
kallon salo a matsayin wani faffaɗan
fage na nazari wanda kusan a iya cewa ba shi da iyaka amma duk da haka ana
nazarinsa ta fuskar harshe da kuma adabi.Wannan maƙala ta yi nazarin yadda
Alhaji Sani Sabulu Kanoma ya sarrafa salailai mabambanta ne a cikin waƙarsa
ta ‘Salo’ musamman ta fuskar adabi,
domin kuwa ba ta taɓo
abin da ya shafi harshe ba. Maƙalar ta yi dubi ne na ƙwaƙƙwafi
tare da ƙwanƙance ɗiyan waƙar da ƙoƙarin
fayyace su a kan wani nau’i
na salo. A wajen tattaro bayanai, maƙalar ta juyi wannan waƙa ta ‘Salo’ a rubuce, sannan ta bibiyi bayanan masana a kan salo
da hanyoyin nazarinsa waɗanda
suka zamar mata matashiya wajen ganin an zaƙulo nau’o’in
salalai da makaɗin ya
sarrafa a cikin waƙar. A ƙarshe maƙalar ta tabbatar da cewa makaɗin
gwani ne wajen iya sarrafa salo wanda hakan ya sa waƙoƙinsa suka samu karɓuwa a wurin mutane kuma har
duniya ta sansa a matsayin fitaccen makaɗi
mai ɗimbin hikima
sannan kuma waƙoƙin nasa suka ɗauki
tsawon lokaci ana sauraren su ba tare da sun ɓace
ba duk kuwa da cewa makaɗin
ya daɗe da barin
duniya.
Fitilun Kalmomi: Adabi, waƙa, Salo Sani Sabulu
Gabatarwa
Idan aka
duba matsayi da aikin salo a cikin waƙa
ba zai zama kuskure ba idan aka fayyace shi a matsayin ruhin waƙa, domin kuwa da shi ake gina harshen duk wata waƙa, kuma samuwar harshe a cikin waƙa shi ne samuwar waƙar.
Haƙiƙa
iya amfani da salo da sarrafa shi ne ke sa waƙa ta zama rayayyiya wadda za ta ɗauki
tsawon lokaci ana saurarenta da amfanuwa da ita. Haka kuma a lokacion da makaɗi
ya rasa samar da gwaggwaɓan salo a waƙa shi kan
sa waƙar ta gaza kai bantenta a cikin waƙoƙi
ballentana har ta rayu a tsakanin al’umma, don haka a ƙarshe ba abin da zai rage illa ta mutu a daina jin ta
gaba ɗaya. Alhaji
Sani Sabulu Kanoma fitaccen makaɗi ne wanda ya yi tashe a ciki da
wajen ƙasar
Hausa da ma maƙwabtanta.
Duk da cewa Allah ya yi masa rasuwa tun wurin shekaru ashirin da uku
(19/8/2000) da suka wuce, amma har yanzu waƙoƙinsa na
rayuwa kasancewar ya sadar da su cikin kyakkyawan salo mai gamsarwa da armashi
ta yadda mutum zai iya ɗauka jiya ko shekaran jiya aka
rera su.
Asalin mahaifin Sani Sabulu
mutumin ƙasar
Borno ne, kuma sunansa Garba, wanda ya zo garin Kanoma da nufin ci-rani na
farauta. Da ya zo garin Kanoma ya zauna a garin tsawon lokaci kuma a cikin haka
ne sai mahaifiyar Sani ta fito daga gidan mijinta, don haka bayan ta gama idda
sai suka yi aure kuma a sanadiyar auren ne aka haifi Sani Sabulu a garin Kanoma
a shekarar Alif da ɗari tara da hamsin da ɗaya (1951). Kuma mahaifinsa ya laƙaba masa sunan ‘Sabulu’ a
lokacin da aka haife shi. A lokacin da Sani Sabulu ya kai kimanin shekara
bakwai, sai mahaifinsa ya kai shi Gusau domin neman ilmin addinin musulunci,
inda ya zauna a hannun malam Shehu Mai Almajirai har ya yi sauka kafin daga bisani
ya dawo gida Kanoma inda ya sa karatun littattafai a hannun kawunsa malam
Haruna. Waƙar
“Kurkunu mugun ciwo”, ana harsashen ita ce waƙarsa ta farko, wadda ya rera ta a sanadiyyar kamuwa da ya yi
da ciwon na kurkunu, kuma ya yi ta ne da kiɗan
gambara wanda shi ne abin kiɗan da yake amfani da shi a
farkon da ya fara waƙa, duk da
cewa daga baya ya kuma rera waƙar
da kiɗan kalangu. Alhaji Sani Sani
Sabulu ya shahara matuƙa
a waƙa kuma ya samu karɓuwa sosai har a tsakanin makaɗa
da mawaƙa domin
kuwa har sai da Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina ya naɗa shi Sarkin yaƙinsa
a fagen kiɗa da waƙa kuma ta dalilin hakan ya kai
shi Makka ya sauke farali sannan ya yi masa kyautar mota.Ta fuskar aiwatarwa da
sadar da waƙoƙinsa kuwa a iya cewa makaɗi ne na ‘jibiliyya’ domin kuwa bai gaji waƙa ba kuma bai koya ba. Sannan
kuma duk da cewa yana aiwatar da waƙar
tasa ne a cikin ƙungiya a
matsayin jagoran ƙungiyar
amma ba shi da ‘yan amshi, sai dai masu yi masa kiɗa kawai sai kuma sanƙira.
Kenan a iya cewa yana aiwatar da waƙa
ne a kan tsarin +Ƙungiya
+Jagora – ‘yan amshi + Masu kiɗa + Sanƙira.
Waƙar ‘Salo’ ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma waƙa ce mai daɗin saurare da burgewa wadda makaɗin ya gina ta a kan turken bugun gaba da koɗa kai ta hanyar amfani da salailai daban daban domin ya nuna
matuƙar ƙwarewarsa wajen iya sarrafa
harshensa a yayin sadar da waƙa.
Haka kuma waƙar ta
amsa sunanta domin Alhaji Sani Sabulu ya yi nasarar gwada zalaƙarsa ta sarrafa salo da harshe
tare da nuna cewa ba baya ba ne shi wajen ƙullawa
da sadar da waƙoƙin baka.
Ma’anar Salo
Masana da manazarta adabi sun yi
iya bakin ƙoƙarinsu wajen bayyana fahimtarsu
game da ma’anar salo, duk da cewa akwai kaɗan daga cikinsu kamar su Yahya
(2001), da Adamu (2002), da suke kallon sa a matsayin wani abu da ke da wahalar
fayyacewa musamman ta fuskar ma’ana.
Stephen (2000), ya bayyana
ma’anar salon fasihin waƙa
da cewa shi ne yadda fasihin ke ƙullawa
da sarrafa hikomomin harshe, da kuma ƙoƙarinsa wajen zaɓen kalmomi, da amsa- amo, da karin waƙa, da raujinta, da kuma irin
yadda yake sarrafa su daidai da tunaninsa a waƙe. Wato dai salon sarrafa sifofin harshen asali gwargwadon
zurfin tunanin fasihi da kuma bunƙasarsa.
Sa’id (1981), cewa ya yi salo
shi ne yadda mawaƙi ya zana
tunaninsa a takarda. Za a dube shi a gani, shin yana da manufa, kuma bayaninsa
yana da ƙarfi ko
rarrauna ne, ana kuma fahimtarsa cikin sauƙi
ko sai an yi lalube a gane manufarsa? Haka kuma za a dubi gwanintarsa wajen
sarrafa harshen da ya yi amfani da shi.
Shi kuwa Ɗangambo (1981), ya bayyana salo
ne a matsayin hanya ko dabara ta isar da saƙo. Sannan ya ƙara
da cewa lallai ne salo ya ƙunshi
zaɓi, kuma kyan salo ko muninsa ya
danganta ne da yadda kowane mutum ya zaɓi abubuwan da ya yi amfani da su
a cikin rubutunsa, ko furucinsa don ya isar da saƙonsa.
Har wa yau Gusau (1975 da 2003),
ya bayyana salo a matsayin wata dabara da ake yi wa harshen waƙa kwalliya da ita. Wato akan zaɓi kalmomi ne a zayyana waƙa, a ƙawata
ta sosai ta yadda za a burge mai saurare a kuma jawo hankalinsa.
Shi kuwa Yahya (2001), cewa ya
yi salo na nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi domin isar da saƙo. Ita wannan hanya tana yi wa
waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko
karatun waƙar.
Baldick (2004), ya bayyana salo
ne a matsayin hanya ta musamman da wani fasihi ko zamani ko wata mazhaba ko
wani fannin ya shahara da shi wajen sarrafa harshe.
Idan muka yi dubi zuwa ga
ma’anonin salo da masana suka bayar, za mu iya cewa salo ya ƙunshi duk wata hikima ko dabara
wadda fasihi ko wata mazhaba suka yi amfani da ita wajen ssarrafa harshe domin
yi wa waƙa ado da
kwalliya don nuna naƙaltar
harshe da burge mai karatu ko sauraren waƙa.
Masana wannan fanni na nazarin
suna kallon fannin ne tare da nazarinsa ta fuska biyu, watau nazarin salo ta
fuskar adabi da kuma nazarin salo ta fuskar harshe wanda kuma yake da wahalar
bambancewa saboda kusancin da ke tsakaninsu. Amma duk da haka sun bayyana wasu
‘yan sifofi da za a iya bambance tsakaninsu kamar haka: Olusegun (2008) ya ce
nazarin salon adabi yakan fi mayar da hankali ne a kan sigar bayar da labari
don haka aka fi amfani da shi wajen ƙwanƙwance salon ƙagaggun labarai. Masanin kuma ya
ƙara da cewa, shi kuwa nazarin
salon sarrafa harshe ana lura ne da sifofin harshe (tsarin sauti, da ginin jumla, da gundarin kalmomi) da ke cikin
matanin da kuma irin gudunmuwarsu wajen bunƙasawa da kyautata ma’anar matani. Sannan kuma ana ƙwanƙwance adon harshe ne ta fuskar
saɓaninsu da kafaffun dokokin
harshe da kuma ƙirƙirarrun ma’anoninsu gwargwadon
yadda suka bayyana a wani muhalli a cikin matani.
Shi kuwa Olusegun (2008) ya
ruwaito cewa Freeman (1973) ya ce, ana amfani da salon sarrafa harshe ne domin
yana taimakawa wajen fahimtar da mai karatu sifofin harshe da na adabin da ke
tattare a cikin matanin da ake nazarta, domin kuwa ba salon matani kawai ake
nazarta ba har da nahawunsa. Wannan dalili ya sa masana irin su Leech (1968) da
Leech da Short (1981) da Muktar (2004) da Olusegun (2008) da Lawal (1997) da
kuma Garba (2014) duk suka gwada cewa an fi amfani da irin wannan salon sarrafa
harshen ne wajen ƙwanƙwance salon sarrafa harshen waƙa, musamman domin fito da
ire-iren bambance- bambancen da ke tsakanin matanin waƙa da sauran matanoni.
Salo a Cikin Waƙar ‘Salo’
Alhaji Sani Sabulu Kanoma mutum
ne mai yawan hikima da basira, wannan ya sa ya kira wannan waƙa ‘salo’ da bakinsa da nufin ya
gwada cewa lallai ya iya sarrafa salo tare da wasa da harshe a waƙa. Haƙiƙa manufar makaɗin ta cika kuma haƙarsa ta cimma ruwa domin kuwa waƙar tana ƙunshe da salailai mabambanta a
cikinta. Kamar yadda bayani ya gabata na yadda masana suka fayyace fagen
nazarin salo ta fuska biyu, watau ta fuskar adabi da kuma ta fuskar harshe idan
aka nazarci waƙar za a
tabbatar ta amsa sunanta domin kuwa ko ta ina aka nazarce ta za a sami salai
lai kala-kala a cikinta. Za a iya ganin misalai kamar haka :
Salon Zuga
Salon zuga salo ne da ke cicciɓa mutum tare da ƙoƙarin ɗaga matsayinsa da nuna cewa wanda ake zugawa ɗin ya shahara kuma karansa ya kai tsaiko a fagensa. Makaɗi kan sarrafa salon zuga ne ya don ya nuna wa duniya isa ta
wani, shi kuma wanda aka zuga ɗin ya rinƙa jin lallai fa ya isa kuma har
zugar ta sa ya iya aikata wani abu na bajinta. Masana da dama sun bayyana salon
zuga misali:
Bello (1976), ya bayyana cewa
zuga tana kama da yabo wajen faɗin abubuwa na ƙwarai da mutum ya yi, sai dai a
wajen zuga ana ƙara
gishiri a faɗi abin da ba haka nan yake ba,
amma babu wanda zai damu tun da an san niyyar ta a kumbura kan mutum ne. Ya ƙara da cewa babban harsashin da
aka gina zuga a kai shi ne a nuna wa wanda ake zugawa cewa ya fi kowa, babu
kamar shi kuma yana iya yin abin da kowa ba zai iya yi ba. (Bello 1979: 29).
Shi kuwa Gusau (2002), cewa ya yi zuga wata magana ce da ke ɗauke da wasu kalmomi da ake amfani da su a koɗa wani a cicciɓa shi, a nuna fifikonsa kan
wasu.
Alhaji Sani Sabulu ya sarrafa
salon zuga a cikin waƙarsa
ta salo domin ya cicciɓa yaransa na waƙa waɗanda ke yi masa kiɗa inda ya ce:
J: Musa ɗan Garewa mai kaɗa fata na Nana, Mamman mijin
Ayashe da Dela,
Baban Abdul’aziz
ina tambura.
Birgediyan mutan
Jangebe na Abu mai kaɗa fata, Sani Yabo na Saudi
Mamman,
Da Audu Waziri,
eh, Angon Rabi Mijin,
Ya mijin Aminatu
Audu,
Dalla dalla ku ba
ni wamba wamba, Don hannu ya iya jiki ya saba, Tafiya sannu sannu kwana nesa,
In magana ta salo
ce,
Kai ba ni ba
Sabulun sallaye, Ko ku ko kuna iyakar naku,
Tunda kuna kiɗa kamar harsashi, Akuya ta gane ku ta aje fata, Tunda tana
gudun azabar Allah.
Makaɗin ya zuga yaran nasa tare da nuna musu cewa in dai batun kiɗa ake yi to su fa ba baya ba ne, domin kuwa sun iya shi kuma
sun saba. Tun a farkon ɗan waƙar makaɗin sai da ya yi amfani da basirarsa da Allah ya hore masa ya
kira sunayen makaɗan nasa ɗaya da ɗaya yana alaƙanta su da matayensu, wanda yin
hakan wani salo ne na zuga mutum a ƙasar
Hausa. A lokacin da ake so a tsuma mutum kuma a zuga shi domin ya ji ƙarfin aikata wani abu sai mutane
su kururuta shi ta hanyar haɗa shi da matarsa ko kuma wata
wadda aka tabbatar yana ƙauna,
wanda yin hakan zai sa mutumin ya aikata abin da ake buƙata yadda ya dace ko da kuwa bai
yi niyyar hakan ba. Bayan makaɗin ya kwarzanta yaran nasa ta
hanyar haɗa su da masoyansu bai tsaya haka
ba, sai da ya nuna musu cewa idan fa ana magana a fagen kiɗa to su fa ba kanwar lasa ba ce, domin kuwa sun riga sun iya
shi kuma sun san yadda ake yinsa. Alhaji Sani Sabulu bai tsaya haka ba sai da
ya kai ƙarshe
wurin zuga yaran nasa ya nuna cewa saboda irin yadda suka iya kiɗa kuma suke bugun kalangu da gaske to fa da zaran akuya ta
hange su sai ta jefar da fatar da ke jikinta. Haƙiƙa wannan
zuga ta kai zuga, domin kuwa a zahiri babu ruwan akuya da kiɗan yaran Sani Sabulu duk kuwa da cewa ana haɗa kalangu ne da fatar akuya. Sai dai salon zugar da ya yi
amfani da shi ya sa yaran nasa sun zage sun yi masa kiɗa irin yadda ya dace a cikin waƙar,
Salon Bugun Gaba
Salon bugun gaba ko salon koɗa kai wata hikima ce ko dabara a cikin waƙa wadda makaɗi ke amfani da ita domin ya zuga ko zuzuta kansa ko ya yi
alfahari ya nuna wa duniya cewa shi fasihi ne kuma karansa ya kai tsaiko a
fagen hikima da balaga da kuma sarrafa harshe. A irin wannan fasaha makaɗi na ƙoƙarin ya gwada irin matsayinsa ne
da ƙwazonsa a wannan fage sannan ya
gwada ya isa kuma ya cika mai fasaha, a wasu lokutan har da ƙalubalantar sauran makaɗa da idan suna jin sun isa to su kwatanta ko su yi abin da
ya yi na fasaha. Bunza ya bayyana salon bugun gaba a matsayin ‘Furuci da wani
mutum zai yi a cikin zancensa ko waƙarsa
ko rubutunsa yana ƙoƙarin fito da irin martabarsa ko ƙwazonsa. Galibi idan fagen
fasaha ne, mai bugun gaban zai yi bugun gaba ne da fasaharsa da ya yi fice da
ita’. Mujaheed ya bayyana salon bugun gaba da cewa ‘Shi ne furucin mawaƙi na alfahari ta hanyar cika
baki musamman ta fuskar ƙwarewa
da hikima da baiwa ko asali ko gogewa ko bayyana ficensa da zarce tsara don
nuna fifiko da mawaƙin yake
da su kain saura’.
Alhaji sani Sabulu ya yi amfani
da salon bugun gaba ko salon koɗa kai a cikin waƙarsa ta ‘salo’ inda ya ce :
J: Duk mai son
salo,
:Ya zo ga Haji
Sani Sabulu,
:Tunda salo ga
sabulu yat tashi.
:Ga alama ina
zaton,
:Ni as shugabn ƙasar masu salo,
:Cikin musulmin
Allah.
:Sani Sabulu
Kanoma Dutsi,
:Ashe Sani Sabulu
Kanoma guda ne,
:Angon Haja,
:Mijin Amina
Mamman,
:Sani uban su
Jamilu,
:Manya manya wane yaro, wurin
wuya sai manya.
A cikin ɗan waƙar
makaɗin ya bugi gabansa ne tare da koɗa kansa ya gwada wa duniya cewa duk mai buƙatar waƙa cikin tsantsar hikima da
azanci to ya neme shi, domin kuwa duk wata hikima da basirar waƙa da iya sarrafa harshe daga
daga gare shi ta samo asali. Sani Sabulu bai tsaya nan ba sai da ya gwada cewa
shi fa a fagen fasahar kiɗa da iya sarrafa harshe yana
kallon kansa ne a matsayin shugaban ƙasa,
watau yana jin yana gaba da kowa a tsakanin dukan makaɗan ƙasar
Hausa.
Salon Ƙarangiya
Salon ƙarangiya wata hikima ce ko
dabara da mawaƙa ke
amfani da ita a cikin waƙa
ta hanyar wasa da harshe da luguden kalmomi ko sauti na baƙi ko wasali. Mawaƙa kan zaɓo wasu kalmomi ne ko sautika na wani baƙi ko wasali su yi ta maimaita
shi a cikin kalmomi musamman a goshin kalmomin ko a ƙeyarsu wani lokacin har a
tsakiya a cikin layukan waƙa.
Masana sun tofa albarkacin bakinsu wajen fayyace ma’anar ƙarangiya. Misali Gusau (2002) ya
ce ‘Ƙarangiya dabara ce ta luguden
harrufa ko kalmomi ko wasa da harshe cikin baƙaƙe da
kalmomi. Haka kuma akan iya maimaita wata gaɓa
ko ƙwayar sauti, sautinsu ya dinga
tafiya bai ɗaya a cikin kalmomi da saɗarun ɗan waƙa’. Shi kuwa Ɗangambo (2008) cewa ya yi ‘Ƙarangiya dabara ce ta luguden
sautukan harrufa a cikin ɗango ko baiti, inda za a ji wasu
saituttuka masu kama da juna suna hawa da sauka suna maimaita kansu’. Shi kuwa
Garba (2014) cewa ya yi ‘Wannan salo ne wanda ya shafi luguden wasu sautuka-
musamman a goshi ko ƙeyar
kalmomi, mafi yawanci a tasassun gaɓoɓi
kuma masu maƙwabtaka
da juna’. Baldick (2004) ya nuna cewa akwai salon ƙarangiya har nau’i uku, watau
akwai luguden wasali wanda ya ce shi ne maimaita sautin wani wasali ko
makamantan juna a cikin tasassun gaɓoɓin
kalmomi masu makwabtaka da juna. Sai kuma luguden baƙi wanda ya bayyana cewa shi ne
maimaita sautin wani baƙi
ko makamantan juna a cikin kalmomi masu mabambantan wasali kuma a muhallin da
ke bayyanar da maƙwabtaka a
tsakaninsu a cikin matani, musamman idan sautin baƙaƙen ya daidaita. Sai kuma nanatau (luguden ma’ana) wanda ya
bayyana cewa, ta ƙunshi
maimaita wata kalma ko wani rukunin nahawu a goshin ɗangaye. A wannan muhalli saƙon ake maimaitawa ko riɓanyawa domin ƙara fito da shi fili.
Waƙar ‘salo’ ta Alhaji Sani Sabulu na cike da salon ƙarangiya a cikinta, inda za a
iya ganin misalai a cikin wasu ɗiya kamar haka:
J: Ado ɗan mutan Kano sanƙira,
:In kana da salo,
:Sai Salame ta sa
Maisallah,
:Ya yi salla,
:Ya sallame yana
ta salati,
:Cikin musulmi,
:Ya sami salsalar
bisimillah,
:Saboda son
Musulunci.
J: Bara cikin
sallar layya,
:Sa’ilin da ina
sallama,
:Salamatu taz zo
da Saliha,
:Sule na sassabe
cikin saura,
:Ya ga Sulluɓawa sun sa salo,
:Ga sallar lufa
yab bi salsala,
:Ya bi Salamu har
masallaci,
:Don ya sa Musulmi
sallah,
:Da sallama da salati.
J: Cikin salati,
:Muka sami
salsalar, sa sabon salo,
:Ka san so, ke sa
a sa ma soko riga,
:Yana suka ran
sallah,
:Cikin suka yas
sato sulen masunta,
:Suka so su
sussuke shi su soke,
:Sai masunta suka sami susuwa
sai suya.
J: Salamatu mai
salak,
:Salamatu mai
salak,
:Da tas so ta ji
salsalar salo,
:Ta yo sammako da
assalatu ta ishe Sani,
:Sabulu ta ce mani
ya salsalar salo,
:Shi asalin salo ana samu nai ga
sabulu koyaushe.
Idan aka duba misalan ɗiyan waƙar
da aka jero za a tabbatar da cewa waƙar
na ƙunshe da salon ƙarangiya sosai inda makaɗin ya nuna gwanintar wasa da harshe matuƙa ya yi ta maimaitawa da sassarƙa sautin /sa/ a cikin kalmomi
mabambanta, wani wurin a goshin kalma wani wurin a tsakiyar kalma wani wurin
kuma a ƙeyar
kalma. Haka kuma akwai kalmomi da dama da ya yi ta jujjuya su da nanata su a
wurare daban-daban, wanda yin hakan yana cikin salon ƙarangiya da masana suka
tabbatar.
Salon Adon Harshe
Masana irin su Shifly (1970) da
Muhammad (1973) da Cuddon (1977) da Ɗan’iya
(1997) da Gusau (2003) da kuma Muhammad (2011) sun yi gamayya kan cewa adon
harshe wata kwalliya ce da ake yi wa harshen waƙa. Sai dai Shifly (1970), ya ƙara da cewa ya shafi karkatar da wani abu daga sifarsa ta
asali ya zuwa wata sifar ko wani abu, kuma yin hakan kan kasance ne ta hanyar
kamantawa ko mutuntarwa, ko tamka ko jurwaye ko kuma kwalliya. Yayin da shi
kuma Cuddon ya ƙara da
cewa shi adon harshe, shi ne kan fito da kowace irin magana (zance) ko waƙa, kana ya bayyana manyan
rukunansa da suka haɗa da kwalliya, da tamka, da kuma
alamci. Ɗan’iya
(1997) ta ƙara da
cewa da adon harshe ne ake yi wa waƙa
kwalliya don ƙara mata
armashi da daɗi, kuma shi ne ma’auni na gwada
hikimar zance da balaga da ɗan Adam yake da ita a harshensa.
Bashir (2019) ya bayyana cewa
adon harshe wata hanya ce ko dabara wadda makaɗa
kan bi ta kanta domin su yi wa harshen waƙarsu
ƙawa, ta yadda za su sami damar
koɗa wanda suke waƙewa cikin harshe mai kwalliya da
burgewa, gami da kambama shi cikin sifofi daban- daban. Su kuwa ginshiƙan adon harshe ko sigoginsa sun
haɗa ne da kwalliya da tamka ta
mutuntarwa da alamtarwa da kambamawa da sauransu.
Kwalliya da Tamka suna daga
cikin ginshiƙan
sigogin adon harshe, wanɗanda makaɗa kan yi amfani da su a cikin waƙoƙinsu domin su ƙara
jin daɗi da sauƙin isar da saƙo ga mai saurare. Masana sun
fayyace fahimtarsu a kan salon adon harshe na ‘Kwalliya’ da ‘Tamka’. Alal
misali Yahya (2001), ya ce’Tamka, wani ɓangare ne na babban salon
siffantawa, wanda ke bayyana sifar wani abu ta fuskar kwatanta shi da wani abu
daban tare da amfani da kalmomin mizani’. (Yahya 2001:07). Malamin ya bayyana
cewa, da za a kwatanta salon tamka (‘kamance’), da kwalliya (‘kinaya’), sai a
ga cewa yayin da tamka kan siffanta mutum da cewa ya yi kama da wani abu, amma
ba shi ne abun ba, to shi salon kwalliya yakan siffanta mutum da cewa shi ne
abin kacokan. Har wa yau masanin ya nuna cewa, su waɗannan ‘kalmomin mizani’ da tamka kan yi amfani da su, sun
kasu zuwa gida uku ne, wato akwai mizani na ‘daidaito‘ waɗanda suka haɗa da, awa da kamar da i da ya,
da kake da sauransu. Sai ‘mizani na fifiko’ wanda ya ƙunshi kalmomi irin su wuce da
zarce da fi da gota da furce da tsere da kuma ɗara.
Na cikon ukun su ne kalmomin ‘mizani na kasawa’, waɗanda suka haɗa da kasa da gaza da wane da
kuma kalmomi masu soke samuwa kamar bai da kuma ba. Shi kuwa Gusau (2002) ya
bayyana cewa kwalliya kwatancen kai tsaye ne inda ake ba wani abu darajar wani
abu ba tare da amfani da wani mahaɗi ba. Yayin da ita kuma tamka
kwatance ne, inda makaɗi kan auna darajojin abubuwa
daban-daban, ta hanyar daidaitawa ko bambantawa, ko fifitawa ko naƙasarwar wani kan wani.
Kasantuwar Alhaji Sani Sabulu
Kanoma makaɗi mai tsara waƙoƙinsa cikin harshe mai sauƙin fahimta da burgewa gami da ƙawa, tare da saka karsashi da annashuwa ga mai saurare, ya
sa ya gwanance wajen sarrafa salon adon harshe kamar yadda ya bayyana a cikin
wannnan waƙar tasa
ta salo, inda ya ce:
J: Ni waƙa nake kamar tamsiri,
:Ni waƙa nake kamar alburda,
:Wasu in sun jiya
su ce wa’azi ne,
:Wasu in sun jiya
su ce tamsiri,
:Duk maganar ta salo ce.
A cikin ɗan waƙa
guda na ‘Salo’, Sani Sabulu ya yi amfani da Salon adon harshe na ‘Tamka’ da
kuma na kwalliya duk domin ya nuna yadda ya mallaki harshensa ya kuma iya wasa
da shi. A layi na farko da na biyu ya yi amfani tamka ne inda ya sarrafa
kalmomin mizani na daidaito ya kwatanta irin yadda yake yin waƙa da yadda malamai suke yin
tafsiri (Karatun Alƙur’ani da
fassara tare da sharhi). Abin da yake so ya nuna shi ne in dai a fagen waƙa ne to fa shi gwani ne kuma
gangaran, domin kuwa ko a cikin malamai ba kowa ba ne yake yin tafsiri, sai
wanda iliminsa ya kai kuma ya san fannonin ilimi daban-daban. Don haka a nan
sai ya daidaita waƙarsa da
tafsiri. A layi na biyu na ɗan waƙar sai ya sake kwatanta yanayin
waƙarsa da ‘alburda’. A wannan gaɓar, makaɗin ya sarrafa salon adon harshe
ne na tamka ta hanya amfani da kalmomin mizani na daidaito, inda ya daidaita
yanayin waƙarsa da
‘Alburda’. Wadda fitacciyar waƙa
ce ta yabon Manzo (S.A.W), wadda wani babban malamin sufanci ɗan ƙasar
Masar mai suna Imam al-Busiri ya rera tun a wurin ƙarni na sha uku. Sani Sabulu ya
yi ƙoƙarin daidaita waƙarsa
da waƙar alburda ne don ya san
fitacciyar waƙa ce a
wurin Musulmi, wadda take da matuƙar
tarihi da kuma tasiri. Har wa yau dai a cikin wannan ɗan waƙar,
makaɗin bai gushe ba sai da ya yi
amfani da adon harshe na kwalliya inda kai tsaye ya kamanta waƙar tasa da ‘wa’azi’ da kuma
‘tamsiri’. A waɗannan layuka guda biyu na ɗan waƙar
makaɗin ya nuna matsayin waƙar tasa ne da irin yadda yake
aiwatar da ita, don haka sai kai tsaye ya kira ta da wa’azi da kuma tamsiri
domin ya kwatan ta da su ya nuna cewa matsayin su guda ne.
Salon Yabau
Kalmar Yabau ‘Euloƙues’ kalma ce ƙirƙirarriya a Ingilishi, kuma wanda ya fara ƙirƙirar kalmar shi ne wani masani da ake kira Kunene (1971)
inda ya ce “Daga yau za a riƙa
amfani da ƙirƙirarriyar kalmar ‘Yabau’ domin
bayyana dukkan kalmomin da suka shafi yabon wani gwarzo, ko da kuwa sun kasance
suna ne ko dangantawa”. Wato a nan ‘Yabau’ za ta kasance baddalawa ne ko faɗaɗawa a kan kalmar yabo ko yaba,
ko yabi, ko yabe, ko kuma yabawa, da nufin bayyana ko dai Kalmar yabo, ko
yankin yabo ko kuma yabo a cikin jumla gaba ɗaya.
Yabau a cikin waƙa shi ke
siffanta jarumi da ayyukan jarumtarsa ta hanyar amfani da kwalliya ko alamta
shi da wasu abubuwa, haka kuma akan yaba wa gwarzo tsurarsa, a wani lokaci kuma
a danganta shi da wasu mutane. Irin muhimman kalmomi da aka kwarzanta barde da
su a cikin waƙa su ne
ake nufi da ‘Yabau’ ba yabo ba. (Tsoho, 2002 Shf:2-143).
Tsoho ya jaddada cewa yabau a
Hausa ya ƙunshi
kalma ko yankin magana ko jumlar da aka yi amfani da ita wajen yaba wa gwarzo
cikin kwalliya ko alamci, musamman danganta shi da ƙarfafan dabbobi ko abubuwa ko
yanayi mai tsoratarwa da ake yi. Ya ƙara
da cewa yabau kan siffanta zatin jarumi ya cicciɓa
shi, ya kuma ɗaga kimarsa a idon duniya, haka
kuma yabau kan fayyace kimar sarakuna da manoma, ya bayyana kyawawan halayensu
da ɗabiu’nsu, saɓanin yabau a waƙoƙin ‘yan tauri da ‘yan dambe da ɓarayi, (Tsoho 2002, Shf:145-146). Haka kuma ya ce za a iya
raba yabau a ƙalla zuwa
gida biyar, inda ya ce a kwai yabau na kwalliya da yabau siffantau, da yabau
aikatau da yabau dangantau da kuma yabau na yankin magana ko na jumla. (Tsoho
2002, Shf: 150-159 da 159-202).
A taƙaice dai a iya cewa yabau wata
hikima ce ko salo da ake amfani da shi a cikin waƙa ko a kirari domin a kwarzanta ko kuma a koɗa wani mutum ta hanyar sarrafa kwalliya ko alamci ko kuma a
danganta shi da wasu mutane masu kima da daraja, domin shi ma girmansa da
martabarsa gami da jarumtakarsa da kuma asali da muhibba su bayyana tare da ɗaukaka a idon duniya. Haka kuma akan haɗa mutum da waɗanda mutane da ke da daraja da
kima a idonsa kuma yake jin yana son su misali kamar iyaye da matan mutum da
kuma ‘ya’yansa domin a ƙara
masa ƙaimi a kuma yaba shi a cikin waƙa. Za a iya ganin misalin salon
yabau a cikin waƙar salo a
cikin ɗiya da dama. Misali :
J: Na tuna da
Garba Mabera Ɗ 2,
:Baban A’i,
:Baban Balkisu na
yaba maka hairan,
:Abu na Ma’inna,
:Bari wannan mutum
yana kaɗa tifa,
:Dogo ɗan Magaji mai kaɗa ƙarfe,
:Bala mai roka
Bala na Babban Rami Ɗ 2,
:Ya angon Amina,
:Bari wannan
direba na kaɗa ƙarhe,
:Sani ɗan babanai na Tambuwal mai mota,
:Ya Allah jiƙan musulmi Mamman,
:Don na tuna
Amadun tasha ya hwaɗi,
:Bari wannan
direba na kaɗa ƙarfe,
:Sani Sabulu yana gaishe shi.
Idan muka duba wannan ɗan waƙar,
za mu ga cewa Sani Sabulu ya yi amfani ne da salon yabau musamman na dangantau,
inda ya yi ta jero sunayen masoyansa waɗanda yawancinsu direbobin mota
ne yana yaba musu tare da nuna shaharar su a fagen sana’arsu ta tuƙin mota. Makaɗin ya yi ta amfani da iyali musamman mata da ‘yayan waɗanda yake yabawa da kuma abokan arzikinsu wani lokacin har
ma da iyayensu yana yaba musu, tare da fayyace shahararsu da bajintarsu a kan
sana’arsu ta tuƙi, wanda
masana suka tabbatar da cewa yin hakan a cikin waƙa salo ne na yabau dangantau.
Kammalawa
Haƙiƙa salo da
iya sarrafa shi a cikin waƙa
shi ke ba makaɗi dama ya fayyace duk wani saƙo da yake da buƙata ba tare da tasgaro ba, kuma
shi ke sa waƙa ta
burge ta yi daɗi sannan kuma ta rayu tsawon
lokaci ana yayinta ko da kuwa makaɗin da ya yi ta ya mutu. Haka
kuma idan aka rasa shi a cikin waƙa
takan kasance lami mai saurin gundura kuma hakan kan sa takan ɓace gaba ɗaya a daina jin ta cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ko da kuwa makaɗin da ya yi ta yana nan a raye. Bisa la’akari da kima da
daraja da salo ke da ita a cikin waƙa
ya sa nake ganin ba a yi kuskure ba idan aka ayyana shi a matsayin ruhin waƙa, wanda a kansa waƙa ke rayuwa. Sannan kuma rasa
gwaggwaɓan salo a waƙa yakan sa ta mutu murus. Waƙar ‘Salo’ ta Alhaji Sani Sabulu
Kanoma waƙa ce da
makaɗin ya baje kolinsa a cikinta ta
hanyar wasa da harshe da sarrafa salo yadda ya ga dama, don haka ta kasance ɗaya daga cikin waƙoƙin makaɗin da har yanzu ake saurare tare da yayi a duk lokacin da
aka kunna ta. Wannan maƙala
ta nazarci salailai ne mabambanta waɗanda Sani Sabulu ya yi amfani da
su a cikin waƙar
‘Salo’. Maƙalar ta
gano cewa makaɗin ya yi amfani da salailai da
dama wajen gina saƙon waƙar kuma haka ya sa waƙar ta amsa sunan da aka kira ta
da shi kuma hakan ya sa ta rayu tsawon lokaci duk kuwa da cewa shi makaɗin ya daɗe da rasuwa. Haka kuma maƙalar ta tabbatar da cewa iya
sarrafa salo na makaɗin ya sa ya shahara ya kuma sami
karɓuwa, wanda hakan ya dace da
harsashen masana. A ƙarshe maƙalar ta tabbatar cewa Alhaji
Sani Sabulu Kanoma makaɗi ne da ya gwanance wajen iya
sarrafa harshe da salo tare da gina waƙa
cikin tsari mai ban sha’awa da armashi.
Manazarta
Amin, M.L. (19193) .Sake leƙa Adon Harshe; Nazarin kwalliya
a rubutattun wakokin Hausa, Kungiyar Habaka Hausa, Ahmadu Bello University, Zaria.
Ayuba A. (2012). Zuga da Yabau:
Matakan Yabo a Bakandamiyar Abubakar A kwara. A cikin Champion of Hausa
Cikin Hausa, A Festcrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad, Zaria: Department of African
Languages and Cultures, Ahmadu Bello University.
Baldick, C. (2004), Oxford
Concise Dictionary of Literary Terms, Oxford University Press, New York.
Bashir, R. (2000). Zuga da Yabau
a Bakandamiyar Ibrahim Narambaɗa. A cikin YOJOLAC.
Bashir, R. (2014). Salon Sarrafa
Harshe A Waƙoƙin Shata. Zaria. M.A Thesis,
Ahmadu Bello University.
Bello, G. (1976). “Yabo Zuga Da
Zambo a waƙoƙin Fada” A Cikin Harsunan
Nigeriya VI, Kano Bayero University.
Bunza, A. M. (2003). Kashin Baƙi sai Taro: Riwayar Bakandamiyar
Gambu a Zaren Tunanin Manazarta Al’ada. A Seminar Paper, Sokoto, Usman Ɗanfodio University.
Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa.
Lagos: Ibrash
Islamic Publication Center Ltd.
Cuddon, J. A. (1977). A
Dictionary of Literary Terms. Andre Doustsch, London.
Dunfawa, A. A. (2004). Zuga A
Cikin Waƙoƙin Fada. A cikin Algaita
Journal of Current Hausa Reserch in Hausa Studies No. 3 Volume 1, Kano: Department of Nigerian Languages Bayero
University.
Ɗan’iya, D. (1997) .Adon Harshe a
cikin Rubutaccen Adabin Hausa. M. A. Thesis, Bayero University, Kano.
Ɗangambo, A. (1973), Shata Da Waƙoƙinsa. B.A. Project, Abdullahi Beyero College, Kano.
Ɗangambo, A. (1978), Rikiɗar Azanci: Siddabarun Salo da Harshe Cikin’ Tabarƙoƙo’, Tahamisin Aliyu Ɗansidi Sarkin Zazzau. Published in Hausa Language,
Literature and Culture, the first Hausa International Conference, Bayero
University, Kano.
Ɗangambo, A. (2007), Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Fisbas Media Services, Zariya.
Ɗangambo, A. (2008). Rabe-Raben
Adabin Hausa. Amana Publishers Ltd, Kaduna.
Funtua, A.I. (2011), Mamman
Shata a Fagen Saka Karsashi a Rayuwar Al’umma, in Waƙoƙin Baka Na Hausa, Katsina, Federal College of Education.
Funtua, A.I. and Gusau, S.M.
(2011). Wakokin Baka na Hausa. Centuary Research and Publishing Ltd,
Kano.
Garba, S. (2011). Salon Sarrafa
Harshe A Waƙoƙin Aƙilu Aliyu. PhD Dessertation,
Department of African Languages and Culture, Ahmadu Bello University, Zaria.
Gusau, S.M. (1985), Salo Da
Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Baka Na Hausa. Wadda aka
gabatar aa taron ƙarawa
juna ilimi na uku kan harshe da adabi da al’adun Hausa, Bayero University,
Kano.
Gusau, S.M. (1996), Dabarar
Alkunya a waƙoƙin Makaɗan Baka. In Mujallar Afrika ta Yamma kan harshe da adabi da
sharhi Volume I, Bayero University, Kano.
Gusau, S.M. (2003), Jagorar
Nazarin Waƙar
Baka, Benchmark
Publishers Ltd, Kano.
Leech, G.P. (1968). A Linguistic
Guide to the Study of Poetry, London.
Muhammad, D. (1990), Hausa
Metalanguage, (edit) University Press Ltd, Ibadan.
Sa’id, B. (1978). Salo da tsarin
Rubutacciyar Waƙar Hausa
Ta ƙarni na 19: A cikin Yahaya, I.Y.
da Rufa’I, A. (eds), Studies of Hausa
Language, Literature and Culture, First Hausa International Conference, Centre for the Study of Nigerian
Languages, Bayero University, Kano.
Umar, M. B. (1984).Symbolism in
oral Poetry; A Study of Symbolical Indices of Social status in Hausa Court
Songs. M. A. Thesis, Department of Nigeria and African Languages, Ahmadu Bello
University, Zaria.
Yahya, A.B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.
Yahya, A.B. (2001). Salo Asirin Waƙa, Kaduna, Fisbas Media Servi
ces.
Yakawada,
M. T. (2002). Eulogues: The building Blocks of Hausa Praise Songs. PhD. Thesis,
Zaria: Department of Nigerian and African Languages. Ahmadu Bello University.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.