Ticker

6/recent/ticker-posts

Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Birbishin Kore a Cikin Wakokin Makada Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Maccido

Citation: Lawali, B. & Aminu, N. (2024). Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 103-108. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.014.

JIRWAYE MAI KAMA DA WANKA: ƁIRƁISHIN KORE A CIKIN WAƘOƘIN MAKAƊA SA’IDU FARU NA SARKIN KUDUN SAKKWATO ALHAJI MUHAMMADU MACCIƊO

Daga

Buhari Lawali

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,

Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sakkwato
08140134145
buharilawal1984@)gmail.com 

Da

Dr. Nasiru Aminu
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato

07067706006

Tsakure

Wannan maƙala ta karkata ne a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, musamman waɗanda ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Aikin an yi shi ne a kan al’ada domin ya fito da ɓirɓishin kore da Sa’idu Faru ya yi amfani da shi wajen bayyana wa al’umma matsayi da daraja da nagartar da Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo yake da wadda ta fifita shi a cikin sauran jikokin Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Da nuna ya fi kowa cancantar ya gadi mahaifinsa Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar na uku, idan mai rabawa ta raba. An ɗora aikin a bisa karin maganar Hausawa da ke cewa: “Ko kana da kyau ka ƙara da wanka”. Ganin yadda Makaɗa Sa’idu Faru ya yaba ɗabi’u da halaye na Sarkin Kudun Sakkwato duk da ya san jama’a suna da masaniya game da abubuwan da ya ambata a kan Alhaji Muhammadu Macciɗo na nasaba da kyawawan ɗabi’u. Sakamakon binciken ya gano cewa saƙon Sa’idu Faru ya isa a wurin da ya dace ya isa, kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Sarkin Kudun Sakkwato ya gadi mahaifinsa a matsayin Sarkin Musulmi. Sai dai Allah bai kai rayuwar Sa’idu Faru wannan lokaci ba.

1.1 Gabatarwa

Ba kowane lokaci kore yake zama yaudara ko cutarwa ba. Ibrahim (2002: 374) ya bayyana cewa: “Shi kansa koren, in an dube shi ta wata fuska, sai a ga kamar talla ne wanda ake yi don a faɗakar da mutane game da maganin da yake bayarwa da kuma amfanin maganin”. Kore talla ce ta dabara a yi amfani da wayo a durmuye mutum ya yi abin da bai shirya wa yi ba.

Wannan ya ja hankalina wajen tunanin cewa makaɗa ma suna iya amfani da kore domin nuna wa mutane matsayin wanda suke yi wa waƙa da tasirinsa a cikin al’umma don cimma wata manufa a gaba. Kore a nan shi ne jawo hankalin mutane ta dabara su yarda da wanda ake yi wa koren, ko a samo masa kwarjini da ɗaukaka a cikin al’umma. Kore ba kore ingancin abin da ake sayar wa jama’a yake yi ba, amfaninsa fito da ingancin abun da ake sayar wa jama’a domin su gamsu da shi su saya (Lawali, 2023: 66). Sa’idu Faru ya san cewa babban burin kowane ɗan sarki ya gaji kujerar gidansu. Kuma ya san idan sarauta ta faɗi akwai waɗanda aka aza wa nauyin zaɓen sabon sarki (king makers). Kuma ya san wasu daga cikin abubuwan da suke la’akari da su wajen zaɓen sabon sarki, kamar nasabarsa da masarauta da karɓuwarsa ga jama’a da dattakonsa da riƙo ga addini da amana. Sa’idu Faru ya yi amfani da waƙoƙinsa wajen yin kore don faɗakar da jama’a da ‘yan majalisar zaɓen sabon sarki cewa Sarkin kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo ya cika duk waɗannan sharuɗɗa. Idan sarauta ta faɗa ya fi duk sauran ‘yan galadimomi cancantar ya hau karagar sarautar Sarkin Musulmi.

1.2 Waiwayen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru

An haifi makaɗa Sa’idu Faru ta cikin ƙasar Maradun, a wajajen shekara ta 1932. Ana kuma yi masa laƙabi da “Ɗan Umma” wanda matar ƙanen ubansa ta sanya masa, saboda ba ya faɗin sunansa, sai dai yana kiran sa Ɗan Umma. Shi ya sa ita kuma ta dinga kiran sa Ɗan Umma, amma wannan laƙabi bai shahara a tsakanin mutane ba, balle ya danne sunansa na yanka watau Sa’idu. Sunan mahaifin Sa’idu Faru shi ne makaɗa Abubakar ɗan Abdu, shi kuwa makaɗa Abdu, Alu mai Kurya ya haife shi. Ashe Sa’idu Faru shi ne ɗan Abubakar ɗan Abdu da Alu mai Kurya. Dukkan waɗannan makaɗa an yi su ne a garin Faru, sai dai mahaifiyar Sa’idu mutumiyar Banga ta cikin ƙasar Ƙaura-Namoda ce, kuma a can ne aka haife ta. Makaɗa Sa’idu Faru ya koyi waƙa wurin mahaifinsa makaɗa Abubakar, waƙoƙinsa suka daɗa kyautatuwa ta hanyar fasaha da hikima tare da ƙwaƙwalwar da Allah ya ba shi. Tun Sa’idu Faru yana da shekaru goma aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gari-gari. Bayan da ya cimma shekaru goma sha shida ya soma karɓi, a wannan lokaci ne kuma aka haɗa su tare da ƙanensa Mu’azu wanda shi ne Ɗangaladimansa. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi waƙoƙi da yawa amma waƙoƙin da ake jin sun fito da shi a sarari aka san shi a duniya su ne na Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo, musamman wannan waƙa mai gindi:

Gindi: Kana shirye babban ‘yanruwa,

Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

Sa’idu Faru yana da matan aure da ‘ya’ya maza da mata da kuma jikoki da dama. Ya kuma rasu a shekarar 1987 (Gusau, 2009: 170). Allah Ya jiƙansa da rahma, Amin.

1.3 Ɓirɓishin kore a cikin waƙoƙin Sa’idu Faru na Sarkin Kudun Sakkwato, Muhammadu Macciɗo

Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da kore ta hanyar dabara da wayo wajen isar da saƙonsa ga jama’a da kuma masu zaben Sabon Sarki idan sarauta ta faɗi, ba tare da an ankara ba. Ya bayyana matsayin Sarkin Kudu Sakkwato da nuna shi ne mafi cancanta a cikin masu gadon sarautar Sarkin Musulmi bayan Abubakar na uku ya wuce. Ya kuma kawo wasu halaye kyawawa da sifofi waɗanda sai mai su ne ya kamata ya zan sarki, ya danganta su ga Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Domin nuna cancantarsa fiye da sauran ɗiyan sarki. Kamar haƙuri da kyauta da riƙo da addini da martaba da ilimi da ɗaukaka da farin jini.

Sanin ma’anar kore zai fito da ɓirɓishin kore a fili a cikin waƙoƙin Sa’idu Faru waɗanda ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo.

Bunza (1999: 163) ya ce: “Kore shi ne dabarun taimaka wa mai siddabaru ko boka ko malami ko makaɗi ko duk wanda ya bayyana a bainar jama’a cikin wayo domin tabbatar da abin da yake da’awa”.

Shi kuma Ibrahim (2002: 367) “Kore wata hanya ce ta jawo wa magani kasuwa da gaskatawa ta kuma samo wa mai magani shahara da amincewa da maganinsa”.

A tawa fahimtar, kore na nufin wata hanyar dabara ko wayo da ake amfani da ita don isar da saƙo a cikin al’umma domin a gamsu, kuma a aminta da wanda suke yi wa koren ko abinda ake wa kore. a kuma kau da kai ga raunin wanda ake yi wa kore ko abinda ake yi wa kore ba tare da an ankara ba.

Sa’idu Faru malamin waƙa ne, saboda haka ba zai fito fili ya nuna kore yake son ya yi ba. Wannan ya sa ya ba Sarkin Kudu haƙuri a kan koren da zai yi masa don ya ɓad da hankalin mai wayo. Ga yadda Sa’idu Faru ke cewa a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu.

Jagora: Maganag ga da za ni hwaɗa maka,

Y/Amshi: Gagarau ɗan Alu kai man gahwara,

Wada duk aka gadon ɗaukaka,

Wada duk aka gadon ƙasura,

Wada duk aka gadon ci gaba,

Mamman ka gadi Abubakar,

Ko da sayen halin nan akai,

Baba halin da ka kai kuɗɗi ya kai.

 

Gindi: Kana shirye babban ‘yanruwa,

Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Macciɗo)

A nan Sa’idu Faru yana son ya nuna cewa duk irin halayen da aka san Sarkin Musulmi Abubakar yana da, shi ma Sarkin Kudun Sakkwato yana da su. Hausawa sun ce: “Kyawon ɗa ya gadi ubansa”. Kuma Sa’idu Faru yana son ya nuna cewa Sarkin Kudu yana da wasu halaye masu tsada da ba kowa ya san su ba, sai wanda ya zauna da shi, Kuma yana son ya nuna cewa samun kyawawan halaye irin na Macciɗo ba abu ne mai sauƙi ba, domin ba a iya sayensu da kuɗi.

Ɓirɓishin kore a nan shi ne, Sa’idu Faru ya san mutane sun ɗauki Sarkin Musulmi Abubakar a matsayin waliyi kuma mai daraja wanda samun irinsa yana da wuya. Sa’idu Faru yana son ya ce wa mutane su kwantar da hankalinsu, in dai an zaɓi Sarkin Kudun Sakkwato a matsayin Sarkin Musulmi, to har gobe Bubakar na uku yana nan. Inda kore ya fito a cikin ɗan waƙar shi ne cewar Sa’idu Faru:

Mamman ka gadi Abubakar,

Ko da sayen halin nan akai,

Baba halin da kakai kuɗɗi yakai.

A nan Sa’idu Faru yana son ya nuna cewa cikin ɗiyan sarki ba wanda ya ɗauko halayen Sarkin Musulmi Abubakar na uku sai Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Ya kuma ce a wani ɗan waƙar kamar haka:

Jagora: Halin ga da Bubakar yar riƙa,

Y/Amshi: Macciɗo ɗai ka shirin gado haka.

1.4 Imani da Allah

Sa’idu Faru yana son ya nuna cewa Sarkin Kudun Sakkwato mumini ne, wanda ya yi imani da Allah kamar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, sai ya ce:

Jagora: Duba ƙafarka zuwa bisa hannuwa,

Y/Amshi: Kamas Shehu na ba wata za’ida,

Sarkin Musulmin wata ran kake,

Da imani da mu’uzzija,

Na nan ga Mammam Macciɗo,

Tun ga Alu mai saje nij jiya.

 

Gindi: Kana shirye babban ‘yanruwa,

Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Macciɗo)

Idan aka lura da kyau za a fahimci cewa, bayan siffa irin ta Mujaddadi da Sa’idu Faru ya ce Muhammadu Macciɗo yana da. Ya kuma nuna cewa Macciɗo mutum ne mai imani kamar kakansa Mujaddadi Shehu Usmanu. Kuma an yi ishara da cewa nan gaba wani zai zo mai irin siffa da halaye waɗanda ke nuna wanda ya yi imani da Allah, tamkar Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Kuma zai gadi kujerar Sarkin Musulmi. Ga yadda Sa’idu Faru ke cewa:

Sarkin Musulmin wata ran kake,

Da imani da mu’uzziza,

Na nan gun Mamman Macciɗo,

Tun ga Alu mai saje nij jiya.

A nan Sa’idu Faru ya yi amfani da kore wajen kore sauran jikokin Mujaddadi daga tsayawa takarar neman sarautar Sarkin Musulmi. Kuma abinda ya faɗa game da Sarkin Kudun Sakkwato ya yi tasiri a zukatan al’umma, har suna ganinsa tamkar wani waliyyi.

1.5 Kyauta da Ilmi

Kyauta abu ce mai muhimmanci a cikin al’umma. Kuma jama’a suna mutunta mai kyauta, kamar yadda suka tsani mai rowa. Al’ummar Hausawa suna mutunta malami musamman na addini, wannan ya sa Sa’idu Faru ya nuna Muhammadu Macciɗo mutum ne mai kyauta da ilimi. Kuma duk jikokin Mujaddadi ba wanda ya kai shi kyauta. Ga yadda Sa’idu Faru ke cewa:

Jagora: Faɗi gaskiya Bello kai Shehu yac ce,

Bari masu son duk su maishe ka yaro,

Da kyauta da ilmi da neman dalili,

Da gode wa Allah da Istingifari,

Da su Bello ɗan Shehu yat tsar ma kowa,

Ka kai kamab Bello ka gadi Moyi,

Y/Amshi: Saura ka kai inda mai Hausa yak kai.

Jagora: Da mutum da dabba datsuntsu da ƙwaro,

Y/Amsa: Mutum da dabba da tsuntsu da ƙwaro,

Da ƙasa da abin da duk ag bayanta,

Komai na duniya na Almuɗɗafa na,

Garai Shehu yas sami girma da yarda,

Komi na gun Shehu shi ag ga Bello,

Komi na gun Bello shi ag ga Garba,

Komi na gun Garba kai ad da shi Bello,

Ko lahira ko muna taƙamatai.

 

Gindi: Bajinin gidan Shehu Mamman na Yari,

Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.

(Sai’idu Faru: Waƙar Sarkin Musulmi Macciɗo)

Ɓirbishin kore a cikin wannan ɗan waƙa shi ne, Sa’idu Faru ya san cewa ba Muhammadu Macciɗo kaɗai ba ne mai son gadon sarautar Sarkin Musulmi, kuma duk nasabar su ɗaya. Yana son ya nuna Muhammadu Macciɗo ne kawai ya ke bisa turbar waɗannan magabata bai kauce ba. Kowab bi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo a cewar Malamin waƙa zai tsira duniya da lahira. Saboda horo yake a yi daidai, a kuma daina abin da ba daidai ba, tamkar dai Mujaddadi na nan raye. Ya kuma nuna cewa Sarkin Kudu yana da wasu halaye da suka sa ya yi wa ‘yan uwansa zarra, kuma duk mai waɗannan halaye ba mai iya jayayya da shi. Sa’idu Faru ya nuna Macciɗo a matsayin mutum mai kyauta, kullum bayarwa ya kai. Kuma malami ne wanda ya tara ilimi mai yawa. Idan an zo wurin Macciɗo da wata magana ko ƙara ba nan take yake yanke hukunci ba sai ya yi bincike, ya samu dalili. Bugu da ƙari, Macciɗo mutum ne mai yawan gode Allah a kan ni’imomin da Allah Ya masa. Shi mutum ne mai neman gafarar Ubangiji, kullum aikinsa kenan. Da irin waɗannan halaye na Sarkin Kudu Sakkwato, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya tsere wa kowa a cikin ‘ya’yan Shehu. Shi ma Sarkin Kudu da su ne ya tsere wa kowa a cikin jikokin Mujaddadi Shehu Ɗanfodiyo.

Ɓirɓishin kore a nan shi ne, ba lalle ba ne Muhammadu Macciɗo kaɗai ke da irin waɗannan halaye, amma Sa’idu Faru ya tsantsame Macciɗo cewa shi kaɗai ne ke da irin waɗannan halaye a cikin jikokin Ɗanfodiyo, kuma shi ne mafi cancantar ya gaje shi a cikin jikokinsa. Kamar yadda Sa’idu Faru ke cewa:

Da kyauta da ilmi da istingifari,

Da gode wa Allah da neman dalili,

Da su Bello ɗan Shehu yat tsar ma kowa,

Ka kai kamar Bello ka gadi Moyi,

Saura ka kai inda mai Hausa kak kai.

(Bajimin gidan Shehu Mamman na Yari)

1.6 Ɗaukaka

Makaɗa Sa’idu Faru ya yi ƙoƙarin nuna wa duniya cewa ɗaukakar Muhammadu Macciɗo ta kai ko’ina, ba inda labarinsa ba kai ba. Sauran mazan da ke jayayya da shi sun yi da-nasani, sun gane cewa ba su iyawa, har suna ganin ɗaukakar da Muhammadu Macciɗo ya samu ikon Allah ne kawai, mai jayayya da shi kamar yana jayayya da ikon Allah. Ga yadda Sa’idu Faru ya ce:

Jagora: Ƙarya ba magana ba ce yanzu gidan Bani ba kamar Macciɗon Hausa,

Y/Amshi: Girmanka ya kai misalinka ya kai riƙon duniya, wada Bubakar yak kai.

Jagora/Amshi: Girman da duk ba na Allah ba mun san zubewa shi kai, totogiiyar banza,

Jagora: Da kai ake gobe da kai ake jibi,

Y/Amshi: Balaraben Hausa Mamman na ɗan Dikko,

Sauran mazan yanzu duk sun ɓace sun saki godabe,

Sun dangana sun yi da-nasani,

A yanzu Mamman na Ɗanfodiyo,

Ba su san nuhi nai ba.

Jagora: Farin wata ko’ina ka isa Bello,

Y/Amshi: Ba inda ba naka ba Modibon Hausa,

Babbar inuwa na Amadun Macciɗo gamji,

Ba kamar ‘yan itace ba.

 

Gindi: Bajimin gidan Bello ɗan Abdu jikan Hassan maganin wargi.

(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kudu Macciɗo)

Ɓirɓishin kore a nan shi ne, cewar da Saidu Faru ya yi duk gidan Bani ba kamar Muhammadu Macciɗo, wannan magana kore ce. Kuma Muhammadu Macciɗo ba Sakkwato ba har duniya matsayinsa ya kai yana iya riƙawa domin girman da Allah ya ba shi. Ga yadda Sa’idu Faru ya ce:

Jagora: Ƙarya ba magana ba ce yanzu gidan Bani ba kamar Macciɗon Hausa,

Jagora/Amshi: Girmanka ya kai misalinka ya kai riƙon duniya, wada Bubakar yak kai.

Jagora: Girman da duk ba na Allah ba mun san zubewa shi kai, totoshiyar banza.

A cikin wata waƙa Sa’idu Faru ya fito fili ya tallata Muhammadu Macciɗo, ya kuma nuna bambancinsa da sauran ‘ya’yan Sarki. Kamar yadda ya cewa:

Jagora: Bajimi ɗan gagara gasa Amalen Sarakuna,

‘Y/Amshi: Toron Giwa ɗan Abdu ƙanen Ali ɗan Iya,

Mu’azu: Wada ɗan Sarki yak kammala bai kai ga Macciɗo,

Jagora: Wada ɗan Sarki yah harzuƙa bai kai ga Macciɗo,

‘Y/Amshi: Girma Allah yai ma da yawa Baba duniya,

Jagora: Wada ɗan Sarki yac ciccika bai kai ga Macciɗo,

‘Y/Amshi: Girma Allah yai ma da yawa Baba duniya,

Jagora: Kashi bakwai kai kwasa ‘yan Sarki na kallo,

‘Y/Amshi: Gidan bani kai kak kai ga irin wagga maslaha,

Ga ka ɗan mai daraja,

Ga ka jikan Usmanu ƙurdabi na Fodiyo,

Ga ka Sarkin nasara,

Ga ka Alhaji Macciɗo, ga jikka ta hi dubu,

Ga ka Mallami ka ke,

Ga ka Mummuni ka ke,

Ga ka ba ka za’ida,

Abin da Allah duk kai yi mutum Baba yai maka.

 

Gindi: Bajimin Ɗan gagara gasa Amalen Sarakuna.

(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kudu Macciɗo)

Abin da Sa’idu Faru ke son ya nuna a nan shi ne, girma gaba ɗaya na gidan Mujaddadi Macciɗo ya kwashe shi, saboda haka ‘yan Galadimomi su yi haƙuri. Macciɗo shi ne Ƙurɗabi, ma’ana wanda ya bi hanyar Ɗanfodiyo ba kaucewa. Sa’idu Faru ya yi kore a nan na tallata mai gidansa. Kuma da yawan mutane sun ɗauki maganarsa, har suna ganin Macciɗo ya fi kowa cancantar ya gadi mahaifinsa. Lawali (2023: 66) yana cewa: “Amfanin kore shi ne fito da ingancin abin da ake sayar wa jama’a domin su gamsu da shi su saya”. Jama’a sun gamsu kuma sun yarda da Muhammadu Macciɗo ya zamo sabon sarkin Musulmi, wanda takai a shirye suke su bayar da rayuwarsu domin tabbatuwar haka.

1.7 Farin-jini

A wurin Sa’idu Faru ba a taɓa yin wani ɗan Sarki mai farin-jini kamar Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo ba. Farin jinin sa ya kai duk halittun Allah suna ƙaunar Mamman Macciɗo. Sa’idu Faru ya nuna haka inda yake cewa:

Jagora: Babban daji kake ɗan Abu,

Y/Amshi: Ko ice ko namun dawa,

Ko manya ko ‘yan ƙanƙane,

Da mutum da dabba da itatuwa,

Kowa ƙamnar Mamman ya kai,

Mamman jikan Attahiru,

Baba na Sidi Mamman gwarzon Cika.

Gindi: Kana shirye baban ‘yan ruwa.

(Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo).

Ɓirɓishin kore a nan shi ne, cewa kowa yana ƙaunar Mamman Macciɗo, tun daga mutane da ke da hankali da dabbabi marasa hankali har itatuwa da ba su motsi irin na tashi daga nan zuwa can suna ƙaunar Macciɗo. Kamar yadda yake cewa:

Da mutum da dabba da itatuwa,

Kowa ƙamnar Mamman yakai.

1.7 Sakamakon Bincike

Sakamakon muƙalar ya gano cewa, burin Sa’idu Faru ya cika, domin Sarkin Kudun Sakkwato ya gadi mahaifinsa a matsayin Sarkin Musulmi. Sai dai Allah bai kai rayuwar Makaɗa Sa’idu Faru zuwa wannan ranar ba, domin ya rasu shekarar 1987 Sarkin Kudun Sakkwato ya zamo Sarkin Musulmi a shekarar 1996. Dukkansu Allah Ya jiƙan su, Ya yi masu rahma, Ya sa Aljanna ce makomarsu.

1.8 Kammalawa

Kamar yadda aka ambata tun a gabatarwa cewa, ba kowane lokaci kore ke zama yaudara ba. Kore a wannan maƙala yana nuna matsayin karin maganar Hausawa da ke cewa “Ko kana da kyau ka ƙara da wanka”. Idan aka kalli dalilan da aka kafa masu tabbatar da ɓirɓishin kore a cikin waƙoƙin da Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato za a tabbatar da haka. Makaɗin ya yi ƙoƙari wajen nuna martaba da daraja da kyawawan halayen Sarkin Kudu, har sai da mafi yawan mutane suka tabbatar da haka, ta hanyar dabara da wayo da fasahar da Allah Ya hore masa ta waƙa. Cikin dabara ya nuna cewa kar mutane su yi sake a yi masu sakiyar da ba ruwa, a yi masu zaɓen tumun dare idan sarautar Sarkin Musulmi ta faɗi. Su tabbatar Ƙurɗabi aka zaɓar masu (wato wanda bai kauce bisa hanyar Mujaddadi ba).

Manazarta

Bunza, A.M. (1999). “Kore ɓad da Hankalin mai Wayo: Tsokacin Rawar Ɗankore a Siddabarun Dandali”. The West African Journal of Language, Literature and Critisicism (A multi-Lingual Bi-Annual), Vol.1,Pp. 163-166. Kano: Bayero University.

Gusau, S.M. (1987). Makaɗa da Mawaƙan Hausa, Kano: Usman Al-amin Publishing Company.

Ibrahim, M.S. (2OO2). “Dangantakar Kore da Maganin Gargajiya”. In Bichi, A.Y., Kafin Hausa, A.U., Yalwa, L.D. (Eds) Studies in Hausa Language, Literature and Culture, the Fifth Hausa International Conference. Center for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano: Benchmark Publishers Ltd.

Lawali, B. (2023). “Gurbin Kore a Sana’o’in Bahaushe”. Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto.

Sa'idu Faru

Post a Comment

0 Comments