Ticker

6/recent/ticker-posts

Kunne Ya Girmi Kaka: Waiwayen Tarihi da Al’adun Jalla Babbar Hausa a Wakar ALA ta Mashigan Kano

Citation: Yakasai, M.G. (2024). Kunne Ya Girmi Kaka: Waiwayen Tarihi da Al’adun Jalla Babbar Hausa a Waƙar ALA ta Mashigan Kano. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 242-246.

www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.029.

KUNNE YA GIRMI KAKA: WAIWAYEN TARIHI DA AL’ADUN JALLA BABBAR HAUSA A WAƘAR ALA TA MASHIGAN KANO

Murtala Garba Yakasai

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano

Tsakure:

Daga tarihin harshe ne ake samun cikakken bayanin tarihin al’ummar, da ta yi amfani da harshen a shekarun da suka gabata. Wannan tsari yana tafiya ne a bisa doron adanawa a matsayin wata kafar kimiyyar harshe, ta waiwayen abin da ya gabata. Saboda haka, ana amfani da harshe a matsayin wata madogara ta adana tarihi da al’adun al’umma. . Wannan kafa ta fi maida hankali ga samar da bayanan da suka keɓanta ga ci gaban al’umma, wato bibiyar al’amuran da tarihi ya adana a lokaci da ya gabata. Bugu da ƙari, wannan bayani ya ƙunshe al’adun al’umma kamar yadda suka auku daga lokaci ko zamani zuwa wani. Ƙunshiyar  wannan maƙala, tsokaci ne a kan tarihi da al’adun Jalla Babbar Hausa a waƙar Dakta Aminu Ladan Abubakar (ALA) ta Mashigan Kano. Domin cimma manufar wannan maƙala, an karkasa takardar zuwa gida biyar. Kashi na farko shimfiɗa ce, sai kuma taƙaitaccen bayani a kan mawaƙin a kashi na biyu. Kashi na uku tsokaci ne a kan matsayin harshe a waƙe, a yayin da kashi na huɗu ya kawo nazarin waƙar Mashigan Kano.

Fitilun Kalmomi: multi-word verbs, meanings, undergraduate students, deficiencies

Gabatarwa

Tarihi ya tabbatar da irin gudummawar da mawaƙa suke bayarwa a wajen adana harshe da al’adu. Wannan ya nuna cewa, tun a wasu zamuna da suka gabata, ana amfani da waƙa domin wayar da kai da kuma ilimantar da al’umma. A matsayin mawaƙi na wanda aka aminta da cewa ya naƙalci harshe, yana isar da  saƙonsa ta amfani da waƙa domin ilimantarwa da kuma wayar da kan al’umma dangane da dukkan wani abu da zai cutar da su. Saboda haka, mawaƙi ƙwararren mutum ne da ya naƙalci harshe, kuma waƙoƙin da yake shiryawa suke da tasiri a zahirin rayuwa ta duniyar da yake rayuwa (Woolger, 1978).

Ta ɗaya haujin kuma, waƙa wata fasaha ce da take ɗamfare da zuciya domin gina mutum da rayuwarsa. Tana ba da nishaɗi, kuma a ƙarshe ta zama jagora wajen faɗakarwa dangane da yadda za a gina al’umma gaba ɗaya. Kowace irin waƙa tana da tasiri ga rayuwa ta hanyar nuni cikin nishaɗi, tamkar dai yadda masana falsafa suke faɗakar da  al’umma. Gaskiyar magana dai ita ce, tasirin waƙa ya fi na ayyukan masana falsafa, musamman  idan aka yi la’akari da cewa, tana ba da gudummuwa wajen gina al’umma. Waƙoƙi suna samar da muhimman tasire-tasire, kamar yadda masu ƙananan muhimmanci suke samar da ƙananan tasire-tasire a rayuwar al’umma (Dennis, 1704).

A wannan gaɓa, kunne ya girmi kaka yana share fagen yin waiwayen tarihin al’umma. Hususan dai, al’umma na tuna abubuwan da aka adana kuma masu muhimmanci, daga nan kuma tarihin al’umma ya ginu. A wasu lokuta ma, waiwayen al’amuran da suka gabata yana zama wata kafa ta ƙulla zumunta. Wato mutanen da suka rarrabu su suke haɗuwa a matsayin al’umma guda mai rayuwa a bisa doron harshe da al’ada. Ƙunshiyar wannan maƙala, waiwaye ne na tarihi da al’adu na Jalla Babbar Hausa (Birinin Kano) a waƙar Dakta Aminu Ladan Abubakar (ALA) ta Mashigan Kano. Sashe na farko shimfiɗa ce, sai kuma taƙaitaccen bayanin mawaƙi a sashe na biyu. Sashe na uku tsokaci ne a kan matsayin harshe a waƙe, da kuma nazarin waƙar Mashigan Kano a sashe na huɗu.

Wane ne Aminu Ladan Abubakar (ALA)?

A lokuta da waƙoƙi daban-daban, Aminu Ladan Abubakar (wanda aka fi sani da ALAN WAƘA), ya bayyana tarihin rayuwarsa (Waƙar CTV), ya kuma kawo bayanin yadda siffarsa take domin mutane su fahimta a cikin sauƙi (Waƙar Sufiyanu Makaho). An haifi Aminu Ladan Abubakar (ALA) a ranar 2nd ga watan Oktoban 1973 a Unguwar Yakasai ta ƙaramar hukumar birni da kewaye. Ya taso ne a hannun kakarsa da take zaune a Unguwar Ƙofar Wambai, sannan daga baya ya koma wajen mahaifansa bayan sun koma Unguwar Tudun Murtala da zama. Kamar kowane ɗan Musulmi, ALA ya taso a bisa doron neman ilimi na Isilama da kuma na boko har matakin Difloma.

Laƙabin ALA haɗaka ce ta sunansa da na mahaifinsa. A tsakanin kakanni da kuma iyayen ALA babu wanda ya gaji waƙa, to amma kuma ga duk masu sauraron waƙoƙinsa za su tabbatar da yana da waƙoƙi da yawa, kamar dai yadda yakan bayyana da kansa. A waƙarsa ta Alfiyya mai taken SHAHARA, mawaƙin ya kawo salsalarsa. Asalin mutum yana daga cikin ma’aunai da ke tabbatar da ƙima da martabarsa. Aminu ALA yana da martaba a idanun mutane, kuma ga shi ɗan sarauta ne. A buɗewar wasu ɗiyan waƙa, mawaƙin yana cewa:  

Godiya ga Ubangijina da ya tsarma dare a rana,

Hikima ta Ubangijina ta buwayi alam su zana,

Baiwarsa Ubangijina ta wuce ƙalami su tona,

Zan bayyana ra’ayina ga batun rayuwa ta kaina,

Ɗan Malam Sani ALA Ladan baba a guna,

Sani Ladan Habu ne Abubakari kaka a guna,

Shi Bukari kuwa ɗa ne ga Mijinyawa bincikena,

Mijinyawa kure Jarmai Baba a gun kakana,

Ɗan Sarki Dambuwa ne Gobir Tsibiri garina,

            Dambuwa ɗa ne ga Gunke Gunkawa assalina.

Masarutar Bawa Gwarzo ku ji salsalar ubana,

Sunana Al-Aminu da shi aka raɗa suna,

Alhaji Ladan ubana da Abubakari kakana,

Sunan da na sa wa kaina Alan waƙar yabona,

Saƙandamai na sunayena na cire ciki laƙabina,

Asali na garin ubana Jega Kebbi State garina,

Asali na garin uwata Dabo ta Kano garina,

Gari kuwa na haihuwata birni na Kano garina,

Shekarar ran haihuwata ƙirgen shari’ar Nabina,

             Hijira ta alif dubu ɗaya da ɗari uku da ɗuguna.

Ma’anar  manufar ɗuguna casa’in da huɗu nufina,

Ƙirge kuma na nasara 1973 ne,

A Municipal Kanawa Yakasai garina,

Nan ne aka haihuwata labarin assalina,

Nai ilimin zamanina boko dan zamanina,

Gwargwado dai Diploma nai domin kare kaina,

Nai kan Art & Design ƙirƙirar zane fununa,

Duka dangogin fasaha na fi ƙarfi lamurana,

             Nai rubutu na hikaya Fiction shi ne ƙarin bayana.

Matsayin Harshe a Waƙe

Tun a tsakiyar ƙarni na sha tara ne, masana masu nazari da bincike a fannin kunne ya girmi kaka, suka tabbatar da cewa ana amfani da harshe a waƙe wajen adanawa da yaɗawa. Hanyar yaɗa bayanai ta kunne ya girmi kaka, tana da tasiri a kowane zamani, saboda haka kiɗa da waƙa da labarai ana adana su a tsawon zamani ba tare da sun kasance a rubuce ba (Rubin, 1995). Dalilin da ya sa ake amfani da hikima ta kunne ya girmi kaka shi ne, hanyar tana wakiltar wani muhimmin tsari ne na kimiyar harshe cikin yaɗawa da adanawa, da za a iya waiwaya a kowane lokaci. Wato hanyar tana da tasiri mai ɗorewa a rayuwar al’umma. Wani tuntuɓe gushin gaba ma shi ne, ɗaiɗaikun mutane na iya waiwaye domin tuna al’amuran da suka gabata a rayuwarsu a cikin ƙanƙanin lokaci.

Sakamakon nazarce-nazarce ya bayyanar da cewa, hanyar kunne ya girmi kaka tana da matakai daban-daban da suka ƙunshe ma’ana da kuma ƙa’idojin waƙa. Waɗannan ƙa’idoji sun haɗa da hawa da sauka na murya da karin sauti da tsawon wasali da ƙarfafawa da suransu. Saboda haka, a fili take cewa, hanyar kunne ya girmi kaka tana amfani da zubi da tsari na waƙa domin samun sakamakon da ake bukata. Ta haka ne ake sarrafa harshe a waƙe a matsayin dabarun isar da saƙonni a waƙe. Bugu da ƙari, masana amfani da ra’o’i a wannan hanya sun yi ittifaƙin cewa waƙa ta kasance hanya mafi inganci wajen adana bayanai. Amfani da harshe a waƙe na kuma ƙara taimakawa wajen tabbatar da ɗorewar  ƙima da martabar al’umma a tsarin zamantakewa.  A wannan gaɓa ana iya cewa, amfani da wannan hanya (musamman sarrafa waƙoƙi), na taka muhimmiyar rawa a ƙasar Hausa.

Waƙar Mashigan Kano a faifan nazari

Masu hikimar magana suna cewa, idan kana so ka zama bahari, to ka naƙalci ƙa’idojin zubi da tsarin waƙa. Idan kuma kana son dacewa, to ka bibiyi  dokokin  hawa da sauka na murya a cikin waƙa. A wannan gaɓar ne za mu bijiro da nazarin waƙar Mashigan Kano, domin ganin yadda harshen waƙa yake yin tasiri wajen riƙewa da tunawa da kuma adana tarihi da al’adun al’ummar Jalla Babbar Hausa. Harshe a matsayinsa na wata baiwa da take ɗamfare a tare da ɗan’Adam, ana amfani da shi domin sadarwa. Wato a tare da shi akwai tasarrufi na sautuka a cikin tsari da kuma ma’ana. A gaskiya ma wani tsari ne na alamomi da yake samar da dama ga majiya harshe su yi mu’amala mai ma’ana (Yalwa, 2014). Saboda haka, da harshe ne ake samar da bayanan da ai’umma take bukata domin sadarwa.

A zamanin mulkin mallaka, mawaƙan Hausa na wannan lokacin sun fi maida  hankali ga bayyana bukatun mutane na samun ‘yancin mulkin kai. Da tafiya ta yi tafiya aka samu ‘yanci, sai kuma mawaƙa suka koma ga ƙalubalantar juna cikin al’amuran tafiyar da mulki da ƙabilanci da ɓangaranci da kuma gazawar shugabanni wajen inganta rayuwar al’umma (Muhammad, 2014). Haka kuma waɗannan mawaƙan na Hausa sun taɓo batutuwa irin na kunne ya girmi kaka. A wannan sashen na wannan maƙala, za a kawo bayanan yadda Aminu ALA ya ƙalubalanci waɗansu halaye da tadojin al’umma marasa kyau da kuma tasirinsu ga ci gaban al’ummar Hausawa (musamman a wannan birni na Kano)

Ta ɗaya haujin kuma mawaƙin ya faɗakar da al’umma muhimmancin adana tarhin al’umma. Wannan waƙa ta Mashigan Kano, an tanade ta ne domin bayyana hujjoji na tarihi dangane da muhimman ƙofofin birnin Kano da kuma dalilan samuwar su. A mabuɗin waƙar, mawaƙin ya bayyana manufarsa ta bayyana tsarin ƙofofin birnin Kano na dauri (wato na gargajiya kamar yadda suke a zamanin iyaye da kakanni). Ga abin da ya ce:

Rabbana ƙadiran Allah abin girmamawa,

Wanda ikonsa ne na buɗe bakin ga nawa,

Nai nufin ambato abubuwan kambamawa,

Tarihin Kano jaha abar girmamawa.

 

Mawaƙin ya jaddada manufarsa da cewa abin da zai gabatar na al’ummar mutanen Kano, ya aza shi ne a bisa doron tarihi musamman domin adanawa da kaucewa salwanta. Tuni dai an lura cewa an yi watsi da waɗannan abubuwa na tarihin al’ummar Kano. Ganuwar Kano da ta kewaye cikin birnin, ta daɗe tun wasu zamunna da suka wuce. Saboda haka, sai ya tunasar da al’umma cewa babu wani ci gaba da ya wuce na tafiya tare da abubuwan tarihinmu. A ta bakin mawaƙin yana cewa:

Zan batu kan ababen Kanawa,

Wasu an banzatar wasu an bi an adanawa,

Mai yiwa yin hakan zai tinzirar da Kanawa,

A gurin kariya da abin da zan ambatowa.

Farko ganuwa ta Kano da ta kekewayewa,

Wacce tau wanzu tun zamanin Annabawa,

Hikimar Farisi Salmanu ɗan Farisawa,

Mutanen Kano muna ta rurrugujewa.

Wasu na iƙirarin zamani ya sauyawa,

Wai sun ci gaba kawunansu ya zam wayewa,

Ni kuwa sai na ce tuna baya shi ne yabawa,

Tozartar da tarihi ya zai zam wayewa.

Aminu ALA ya nuna takaicinsa dangane da tasirin lalacewa da kuma salwantar ganuwar birnin Kano. A wannan waƙa, ya bayyana yanayin da abin kaico, sannan ya nemi gwamnati da ta ɗauki matakai na gaggawa wajen magance taɓarɓarewar abubuwan tarihi. Ya ƙara da cewa, tunda waɗannan abubuwa na tarihi suna fuskantar barazana, to ya zamo wajibi a kare tadoji da al’adun mutanen Kano. Ga yadda ya bayyana ɓacin ransa:

Wai ina gwamnati tarihi zai gushewa,

Martabobinmu ne fa ake ta ballagazawa,

Tarihinmu Sarki amma fa ya zam gushewa,

Mu ne kariya ga martabobin Kanawa.

A ra’ayin Abdulƙadir (1975), baya ga bayar da nishaɗi ga al’umma, mawaƙi yana kuma faɗakar da al’umma dangane da abubuwan da ke faruwa a yanzu da kuma al’amura na tarihin dauri. Ta haka ne yake ilimantar da matasa dangane da al’adu da tadoji da tarihi da kuma hikimomin magabata. Daga bayanan da suka gabata da kuma ƙunshiyar waƙar, mawaƙin ya kambama waɗannan ƙofofi na birnin Kano, musamman ma waɗanda suke a kewaye da ganuwar birnin Kano. A nazarin mawaƙin, Allah ya albarkaci Kano da muhimman abubuwa. Ga abin da ya ce:

 

Sarkin Kano Gijimasu sarkin Kanawa,

Shi ne sila da ya fara ƙaƙƙarowa,

Ƙofofi goma guda huɗu ka zam daɗawa,

Tafiyarsa Rumfa ya maye gurbi Kanawa.

Shi ne ya rushe guda takwas ba daɗawa,

Ya ƙara nasa guda huɗu a kai sanarwa,

Kafin zuwan Bayero sha ukkun sun cikewa,

Ya ida sha shida wanda zan bayyanawa.

Gado-ƙaya wani malami ne Kanawa,

Mai taƙƙawa zuhudu abin ba shi faɗuwa,

Sam ba shi bacci bisa abin shimfiɗawa,

Shi ne ya furta gado ƙaya ba musawa.

A ci gaba da waiwayen tarihi kamar yadda ya danganci ƙofofin Kano, baitoci sha ɗaya zuwa na sha uku sun bayyana musabbabin samuwar ƙofofin Dukawuya da Ƙofar-ruwa. Wannan waƙa tana da muhimmanci wajen adana abubuwa na kunne ya girmi kaka. A wurare daban-daban ALA ya bayyana sunayen sarakunan da suka yi mulki da ushen zuriyarsu. Ta haka ne masu sauraronsa za su san adadin sarakuna da kuma yadda suka yi mulki ɗaya bayan ɗaya. Haka kuma al’umma za ta san waɗannan ƙofofi da kuma dalilan samuwarsu da kuma wuri ko bagiren da suke, kamar yadda ya bayyana a waɗannan baitoci:

Dukawuya suna ne ba musawa,

Na wani sadaukin jarumi mara ƙwawa,

Gidansa anka biɗa ya ce ba shi baiwa,

Sarki ya zo da ƙafarsa don faɗɗakarwa.

Ya ce da bawan nan ni na izo fadawa,

Gidanka za ai maka wani abin yabawa,

Sannan fa ƙofar sunansa za a sawa,

Kun ɗan ji tarihi gwanin armasawa.

Ƙofar-ruwa da ake faɗi kun ji Kanawa,

Sunan ɗiyar sarkin Kano ce Kanawa,

Sunanta Lunƙui babu ja ba musawa,

Shi ne fa sunan ƙofar tunda daɗewa.

Ƙofofi na gaba su ne waɗanda suka haɗa Mazugal da Ƙofar Wambai da Ƙofar Fagge. Irin abin da ya faru ga Ƙofar-ruwa shi ne ya faru ga Ƙofar Mazugal, musamman ma da yake ƙofar ta samu sunanta ne daga sunan ɗiyar sarkin Kano. Ga abin da ya ce:

Ƙofar Mazugal ma disem ‘yan Kanawa,

Sunan ɗiyar sarkin Kano ce ‘yar baiwa,

Jika gurin Suntilma mai martabawa,

Shi ne fa sunan ƙofar da daɗewa.

Ƙofa ta Wambai zan faɗo don sanarwa,

Ƙofar Daggaci da ake ambatawa,

Sarki uban Abdu Rumfa nak Kanawa,

Shi yai naɗin Wamban da ba tumɓukewa.

Ƙofar Fagge da a yanzu aka tumɓukewa,

Ƙofa ta mata da haka ake sanarwa,

Wani hatsabibi na mata kira shi wawa,

Shi ne dalili ko akwai mai musawa.

Babu shakka martabar al’umma tana ƙunshe ne a cikin tarihi da al’adunta, wato zubi da tsarin zamantakewar rayuwarsu. Wannan shi ya ƙara jaddada muhimmancin gudummawar waɗannan ƙofofi a bisa doron tarihin al’umma

A baitoci na gaba, mawaƙin ya bayyana sauran ƙofofin da suka haɗa da Nasarawa da Agundi da Waika da Nadilƙe da Na’isa. Mawaƙin ya bayyana yanayi da taɓarɓarewar rayuwar al’umma a sanadiyar irin salon mulkin Turawa. Ga misali, kirari irin su Nasara mai idon Kyanwa da Azzalumai masu halin ɓatarwa duk suna bayyana ruɗani da matsananciyar wahalar da al’umma suka fuskanta.Wato su ne masu mulkin mallaka da ya kai al’umma ga taɓewa. Ga abin da mawaƙin ya ce:

Ke Nassarawa abu abin ƙayatarwa,

Ita ce ƙofa ta Nasara mai idon kyanwa,

Sunansa ne aka sa wa ƙofar Kanawa,

Azzalumai masu halin ɓatarwa.

Agundi sunan wata ɗiyar Maguzawa,

Wacce dalilin ɗanta ne anka sa wa,

Ƙofar fa suna Ɗan-Agundin Kanawa,

Shi ke tsaron ƙofar gari ‘yan Kanawa.

Ƙofa ta Waika ba abin rikitarwa,

Wani ɗan’Adam ne mai kashi da tsarewa,

Sunansa ne aka bai wa ƙofar Kanawa,

Saura kaɗan sha shida in zam kammalawa.

A cikin baitocin ƙarshe, mawaƙin ya bayyana ƙofofin Nadilƙe da Dawanau. Ita Nadailƙe sabuwa ce kuma an yi ta ne domin ɗalibai, a yayin da ƙofar Famfo aka yi ta domin samuwar ruwa. Ƙofar Dawanau ita ce cikon ta ƙarshe, kamar yadda mawaƙin ya tsaro a waɗannan baitoci:

Ƙofar Nadilƙe da ta zam ana cewa sabuwa,

Don ɗalibai aka yi ta don sauƙaƙawa,

Ƙofa ta Famfo kuma dalilin zuwan ruwa,

Sauran Dawanau Na’isa in kammalawa,

Ƙofar Dawanau asalinta Kanawa,

Maje Karofi da Abdullahin Sikawa,

Kullum idan ya rako mahaɗa ta rabuwa,

Zai ce a nan Malam mu ɗan dawayawa.

Wasu sunka ce Bafulatani ne Kanawa,

Ya taho da garken shanu wai zai wucewa,

Sarki na ƙofa ya hana musu wucewa,

Da yai fushi yai wa kansa hanyar wucewa,

Sarki Sulaimanu ya aika ya zuwa,

Yat tambaye shi dalilin ruggujewa,

Wai sai ya ce Sarki isa ce ta sawa,

Daga nan akai masa lamunin tabbatarwa.      

Naɗewa

Abin da ya gabata tsokaci ne a kan muhimmancin waƙoƙi da kuma tasirinsu, kamar yadda ya bayyana a rayuwa da al’adun Hausawa. Harshe da tarihin al’umma tamkar jini da tsoka suke, wato suna da alaƙa makusanciya ta yadda ba za a iya raba su ba. Dalili kuwa shi ne, daga tarihin harshen kowace al’umma ne ake samun tarihin al’ummar da suka yi amfani da wannan harshen a zamunna da suka gabata. A taƙaice, ana amfani da harshe wajen adana dukkan abin da ya gabata, kamar dai yadda ya bayyana a waƙar Aminu ALA ta Mashigan Kano. Haka kuma harshe a waƙe yana bayyana alaƙar harshe da waƙa cikin kunne ya girmi kaka. Maƙalar ta kuma kawo yadda aka sarrafa harshe a cikin waƙar, ta hanyar adanawa da tunawa da musanya  abin da ya shafi tarihin al’umma. Wato wannan waƙa ta Mashigan Kano, ta kuma fito da aikin harshe a cikin zamantakewar al’umma.

Manazarta

Abdulƙadir, D. (1975). “The Role of an Oral Poet in Hausa/Fulani Society”, Unpublished PhD Thesis, Bloomington & Indiana University.

Abubakar, A. L. (2015). SHAHARA: Alfiyar Alan Waƙa (Shahara Sanadin Sanina), Kano: Taskar Ala Global Ltd

Barista, M. L. (2011). Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), Vol. 1 Kano: Iya Ruwa Publishers.

Dennis, K. (1704). Available at Literature of the 20th Centuryto the present (2008) “English Literature”, Microsoft R. Encarta R. (DVD) Redmond WA, Microsoft Corporation.

Muhammad, A. (2014). “Nigerian Poetry and Women Consciousness: A Study of Three Nigerian Poets” In JALAL, Journal of Language and Literatures, Vol.5, No. 1

Rasheed, A. & S. A. Aliyu (2014). Current Perspectives on African Folklore: A Festschrift for Professor Ɗadatti Abdulƙair, Zaria: ABU Press.

Rubin, D. C. (1995). Memory in Oral Tradition: The Cognitive Psychology of Epic, Ballads and Counting out rhymes, New York, OUP.

Woolger, D. & Ogungbeson, K. (1978). Images and Impressions: An Oxford Senior Poetry Course, Oxford University Press.

Yakasai, S. A. (2014). “Some Major Themes in Hausa Responsorial Songs in Aminu Ala’S Performance” In Current Perspectives on African Folklore, A Festschrift fo Professor Ɗandatti Abdulƙadir, Zaria: ABU Press

Yakasai, S. A. (2014). “Nazarin Harshen Farfaganda Cikin Siyasar Kudanci da Arewacin Nijeriya a Waƙar ALA ta Rajista” In Garkuwan Adabin Hausa: A Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo, S. M. Gusau (ed) Zaria: ABU Press

Yakasai, S. A.  Jagoran Ilimin Walwalar Harshe, Sokoto: GARKUWA Media Services.

Hausa

Post a Comment

0 Comments