Ticker

6/recent/ticker-posts

Ibrahim Narambaɗa Bagargajiye: Nazari Kan Ra’in Falsafar Rayuwa (Life Course Theory)

Citation: Aminu, N. (2024). Ibrahim Narambaɗa Bagargajiye: Nazari Kan Ra’in Falsafar Rayuwa (Life Course Theory). Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 247-253. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.030.

IBRAHIM NARAMBAƊA BAGARGAJIYE: NAZARI KAN RA’IN FALSAFAR RAYUWA (LIFE COURSE THEORY)

Nasiru Aminu

Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto

Tsakure:

Wannan maƙala tana magana ne a kan tsarin rayuwar makaɗa Narambaɗa, ta yi ƙoƙarin kawo hujjoji da ke tabbatar da cewa shi dai bagargajiye ne, wato mutun wanda ya zama garkuwa ta hanyar fake ɗabi’u da halaye da tsarin rayuwa ta gargajiya a zamunnan rayuwarsa. Tunanin wannan take ya tuzgo ne bayan ganin an yi ayyuka da suka kawo tarihi da halaye da zubi da tsarin waƙoƙinsa masu yawa, amma manazarta ba su mayar da hankali a kansa ba, da yadda lokutta da rayuwa suka yi tasiri a kansa ba, kamar yadda ya ratsa hazon zamunna a tsawon shekaru 73 a duniya. Manufar ita ce bin tarihi da matakan rayuwar Ibrahim Narambaɗa, a yi nazarin wasu keɓaɓɓun halaye da ɗabi’unsa domin ƙara tabbatar da cewa shi mutun ne na gargajiya mai fake da daɗaɗɗun al’adun Hausawa. Bincike zai yi nazarin yaranci da samartaka har zuwa tsufansa. Za a iya yin haka ta hanyar duba suturarsa da kalamansa da mu’amalarsa da jama’a. Bayan haka an duba irin ayyuka da sana’arsa ta kiɗa da kayan kiɗansa. Za a cimma wannan manufa ta amfani da sharuɗɗa ko jagorancin ra’i mai bayyana matakai na ‘Falsafar Tsarin Rayuwar Mutun’ wato Life Course Theory. An haɗa da dabarun tarihi da na al’adun al’umma a wannan bincike. Daga ƙarshe, bincike ya yi hasashen samun hujjoji da dalilai da ke tabbatar da marigayi na Narambaɗa a matsayin wanda ya fake tsarin rayuwa ta gargajiya a kusan dukan ayyukansa na rayuwa.

Fitilun Kalmomi: Ibrahim Narambaɗa, falsafa, matakan rayuwa, tarihi

Gabatarwa

Kowace irin al’umma a duniyar nan tana da nata keɓaɓɓun ɗabi’u da al’adu da ke iya tantance matsayinta, mai amfani da aƙidojin zamani ko kuma na kaka da kakanni. Wannan tunani ne ya tayar da magana a kan rayuwa ta gargajiya da ta lokaci domin kowace irin al’umma ta yi lokutta mabambanta, har zuwa wannan ƙarni na ashirin da ɗaya (21st Century). Duk da haka, akan samu wasu mutane da ke riƙe da al’adu da ɗabi’u irin waɗanda suka gada na gargajiya. Wannan dalili ne ke sa ana ambaton al’adun Hausawa na gargajiya ko sarautun gargajiya ko magunguna da sana’o’i ko abincin gargajiya. Ko bayan al’umma, akan samu ɗaiɗaiku ko keɓaɓɓun mutane da ke riƙe da tunani da ɗabi’u da al’adu ko halaye irin na gargajiya da suka tashi a ciki, duk kuwa da fadi-tashin da suka shiga na haɗuwa da wasu baƙin al’adu, sukan bijire musu su fake ga waɗanda suka gada, ko ga aƙidarsu. Rayuwa ko ɗabi’a da halaye na gargajiya na tsokaci ne a kan tsarin rayuwa da al’umma ko wani mutum ya gada daga kaka da kakanni, ko tsarin rayuwar da al’umma ta saba da su tun kafin ta haɗu da wata baƙuwar alumma, ba tsarin rayuwa da ya shafi wayewar kai ko zamananci ba. Don haka irin wannan na nuni ne ga ɗabi’a ta asali da mutun ya gada ko ya saba aiwatarwa tare da iyaye ko wasu magabatansa a cikin al’umma, ba tare da gurɓatawa ko hautsinawa da wata sabuwar al’ada ba. Don haka, wannan takarda ta mayar da hankali wajen duba tsarin rayuwar Ibrahim Narambaɗa Tubali a matsayin wani keɓantaccen mutum kuma mawaƙin baka a ƙasar Hausa da bai taɓa miƙa wuya ga lokacin zamananci har ya yi tasiri a cikin rayuwarsa ba. Wannan takarda ta fahimci wasu mawaƙan bakan Hausa sun sunkuya a rayuwar zamani aka tafi tare da su, amma a tunanin wannan bincike, Marigayi Narambaɗa tun daga muhallinsa da yarantakarsa har zuwa girma da wayonsa bai raja’a ga abubuwa ko rayuwa ta zamani ko duniyanci ba. Ba ma a nan kaɗai ba, a’a har a tsarin abinci da sutura da salon kiɗansa duk suna tafiya ne bisa tsarin gargajiya. Bincike ya yi amfani da bin diddigi rayuwa da wasu waƙoƙin Narambada ta bitar wasu ayyukan magabata da tattaunawa da jama’a da sauraren lafuzza jama’a a kansa, domin fitowa da hujjoji da ke ƙara tantance Narambaɗa a matsayin Bahaushe na gargajiya.

Dabarun Bincike

An yi amfani da wasu hanyoyi domin cimma manufar bincike. Wannan ya zama wajibi domin kowane irin aiki yana bukatar jagora da kuma matashiya daga wasu ayyukan magabata, a matsayin hannunka mai sanda domin cimma burin bincike. Daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su akwai duba ayyukan da masana suka gabatar game da Marigayi Narambaɗa. Waɗannan ayyuka sun haɗa da litattafai da Maƙalu ko wani sharhi game da rayuwa da ayyuka ko waƙoƙin Narambaɗa. An kuma tattauna da jama’a kan batutuwan da maƙala ta sa a gaba, wato kallon Narambaɗa a matsayin mutum mai riƙe da al’adu da halaye ko ɗabi’u irin na gargajiya a tsawon rayuwarsa.

Bayan haka an yi amfani da ra’in bincike da ake ganin ya dace da manufa ko matakan aiki. Ra’in da aka yi amfani da shi ya samo asali daga sassan ilimin nazarin rayuwar bil’adama (Sociology) da ilimin nazarin al’adu da aƙidun al’umma (Anthropology) da ilimin nazarin halayyar Dan’adam (Psychology) sai ilimin nazarin tarihin rayuwa (Social Historians). Wannan ra’i shi ne Life Course Theory, wato falsafar nazarin halaye da dabi’un mutane a matakan rayuwa. Hausance, ra’i ne mai kama da abin da Bahaushe ke ce wa “ Hali zanen Dutse”, kuma “Kowa ya bar gida, gida ya bar shi”. Ya samo asali daga wani masani mai suna Glen Elder Junior, 1960. Ra’in ya ta’allaƙa a kan nazarin halaye da ɗabi’un gargajiya a bisa tafarkin rayuwa daban – daban, tun daga haihuwa har zuwa tsufa. Ra’in ya yi amanna da cewa tarihi da lamurran rayuwa da al’adu da zumuncin mutun da al’umma ko lokaci, na da tasiri a rayuwar bil’adama, kamar yadda ake iya samun irin wannan dangantaka a rayuwar tauraron wannan bincike.

Ra’in ya shata wasu matakai da ke da tasiri ko hannunka-mai-sanda ga wannan bincike. Na farko, shi ne bukatar nazari ko duba yadda mutun ya tashi, ya rayu tun yana ƙarami har zuwa tsufansa, ta la’akari da abubuwan da suka faru na halaye da ɗa’bi’u da wasu abubuwa da ya fuskanta. Wannan na nuna cewa girma da rayuwa ba su tsaya a shekaru goma sha takwas ba kacal. Babban mutun na iya fuskantar wasu sauye - sauye na girma da tunani, musamman zuwa neman abin da ya ci, ya sha, (Johnson, 200lb). wannan tunani da mataki ya shafi rayuwar Narambaɗa, domin bayan yarantaka, ya zama matashi har ya shiga hadahadar kiɗa da waƙa domin rayuwa.

Haka kuma, ra’in ya nuna cewa kowane mutun yana da dama da ‘yanci na tsara wa kansa rayuwa daidai yadda yake bukata a cikin al’ummarsa. Wannan sharaɗi yana nuni ga cewa, bai dace a samu tasirin tunanin wani a kan wani mutum ba. Mutun yana da damar zaɓa wa kansa abubuwan da suka fi dacewa da shi. Ashe idan Marigayi Narambaɗa ya kaɗaita kansa ga aƙidojin rayuwa irin ta al’ummarsa, na gargajiya tun yana matashi, ba wani abin mamaki ne ba, musamman a lokacin da yake matashi zuwa girmansa. Wannan ya nuna cewa Narambaɗa bai ba da dama tunanin rayuwa da zamantakewa da abokan zama, ko ta abokan waƙa suka sauya tunaninsa ba.

 A wani sharaɗi da ra’in ya gabatar, ya ce “The life course of individuals is embedded and shaped by the historical times and places they experience over their lifetime. Gieryn (2000). Wannan na nuni da cewa, a rayuwar mutun, zamunna da sauye – sauyen lokaci da tafiye- tafiyen na da tasiri a rayuwarsa. Falsafar da ke tafiya da wannan tunani ta dogara a kan abu uku. Waɗannan sun haɗa da wuri ko muhallin da mutun ya sami kansa da arzikinsa na rayuwa da kuma aƙidoji da al’adun al’ummarsa da na wasu wurare da ziyarta duk suna da matsayi a gare shi. Domin, idan ba yana da matsayi da ya zauna a kansa ba, waɗannan abubuwa guda na iya kawo canji a rayuwa da tunaninsa a zamunna da ya yi. Duk da haka, Marigayi Narmbaɗa da ya yi zamunna daban – daban, ya zauna da mutane iri – iri, ya fuskanci samu da rashi a arzikinsa na rayuwa da al’adun al’ummarsa, amma bai aminta daɗin duniya ya shige shi har ya ɗauki baƙin aƙidu ba, ya zauna daram a kan tsarin rayuwa da ya gada daga kakanninsa da ta addininsa.

Bayan haka faɗi tashin da Narambaɗa ya yi a sana’arsa ta kiɗa da waƙa na da matuƙar tasiri a rayuwarsa. Dalili kuwa shi ne ya fuskanci mutane (sarakuna da abokan sana’a) masu halaye da ɗabi’u daban – daban a lokuta mabambanta. Duk da haka bai yarda ra’ayinsu ko halaye ko wata dangantakar da ke a tsakaninsu ta juya masa ra’ayi game da rayuwa ba. Kamar yadda ra’in ya fasalta a sharaɗi na huɗu ya nuna fita daga shekarun samartaka zuwa girma na da matakai da suka haɗa da barin gida daga ido ko kulawar iyaye zuwa wasu wurare. Shiga rayuwar aure na kawo barin gida zuwa neman abinci, ko kuma zama magidanci mai iyali na sa mutun cikin wani yanayi da halin rayuwa, duka abubuwa ne da ke iya kawo canjin tunani da aƙida ga wani mutum, amma marigayi Narambaɗa ya riƙe al’adu da aƙidojin rayuwarsa ta gargajiya a dukan waɗannan matakai da mu’amala ko cuɗanyar da ya shiga da al’ummomin zamani, musamman hada-hadar kiɗa da waƙa da ta zama sana’a ta zama sanadin haɗa shi da rukunonin mawaƙa da mutane daban – daban da aka yi ma’amala ta rayuwa.

Babban sharaɗi da wannan ra’i ya kawo wanda ke da matsayi a wannan bincike, shi ne cewa, sauye – sauyen lokaci da tsarin rayuwa da kafuwar wasu ƙungiyoyi na zamani masu tunani daban da na gargajiya, na iya kawo tasiri a rayuwar wani mutum. Sai ga shi marigayi Narambaɗa ya shiga zamunna da yin alaƙa da ƙungiyoyi makaɗa da wasu masu zaman kansu masu aƙida ta zamani, amma ya ci gaba da kare al’adu da ɗabi’unsa na gado.

Waɗannan sharuɗɗa da matakan tunani da aka yi bayani a sama, abubuwa ne da ke da tasiri a rayuwar kowane mutun tun yana ƙarami har zuwa girma da tsufansa. Su ne ke ba mutun damar yin zaɓi na irin abubuwan da suka dace da shi, ko kuma su ba shi damar sauyawa zuwa wani tunani, ganin ba yadda za a iya keɓance mutun daga yin ma’amala ta rayuwa a cikin al’umma. Waɗannan sharuɗɗa ne ke taimakawa a san mutun, a san ko shi wane ne, a san halinsa da sana’arsa. Wannan ne ya sa ake ganin cewa ra’in yana da dangantaka da tunanin bincike, ya kuma taimaka wajen fayyacewa da tabbatar da cewa marigayi Narambaɗa keɓaɓɓen mutum ne wanda ya tashi, ya girma ya kuma rayu da al’adunsa na gargajiya har ya bar duniya.

Narambaɗa a Matakan Rayuwa

Manufar wannan sashe shi ne yin bitar ko wane ne Narambaɗa, ta yin la’akari da tarihin rayuwarsa tun daga haihuwa zuwa girma da tsufansa, kamar yadda wasu masana da magabata suka gabatar da bincike a kansa. Wannan ya ba da dama domin fito da wasu halaye da ɗabi’u da kuma kamanni da siffofin Narambaɗa da wannan takarda ke gani a matsayin hujja na tabbatar da shi a matsayin shahararren Bahaushe mai riƙe da al’adunsa na gargajiya, duk da cewa mutun ɗan tara ne, bai cika na goma ba. Wato ba a rasa wasu wurare ‘yan ƙalilan da ake iya ganin yana da kasawa. Ko da akwai ta, mizaninta (kasawar) ba ta taka kara ta karya ba, wato ba ta yi wani tasiri a kan rayuwarsa ta gargajiya ba.

Masana da dama sun yi rubuce – rubuce game da rayuwa da sana’ar kiɗa da waƙa ko wasu ma’amaloli da tsarin rayuwa ta marigayi Narambaɗa. Alal misali;

A wata takarda da ya gabatar, Bunza (1998) ya bi diddigin jirwayen rayuwar Narambaɗa ta amfani da falsafar yadda makaɗa ke luguden kalmomi a cikin waƙoƙinsa, ya yi kirdadon tushe da asalin abubuwan da suka taimaka wa marigayi Ibrahim Narambaɗa wajen sarrafa hikimominsa. A ƙoƙarin cimma manufar da ya sa a kan gaba, Bunza ya kawo taƙaitaccen tarihin marigayi Narambaɗa, wanda tarihi ne da wannan takarda ta yi amfani da shi matuƙa. Haka kuma a cikin wannan aikin bincike Bunza, (1998:4) ya jeranta wasu ɗabi’un Ibrahim Narambaɗa waɗanda za su taimaka wa wannan aiki wajen tantancewa da tabbatar da makaɗa Narambaɗa a matsayin mutum mai al’adu da ɗabi’a na gargajiya har bayan rasuwarsa. Haka ma a nazarin Kimiyyar Walwalar Harshe, ire – iren kalmomin da mutun ke amfani da su a maganarsa ta yau da kullum, na iya tantance matsayinsa da muƙaminsa da kuma aƙidojinsa na rayuwa, Yakasai, (2018). Don haka, tarin luguden kalmomin da Bunza ya fitar daga waƙoƙin Narambaɗa sun amfani wannan takarda wajen tantance dangantakar harshe da matsayinsa a rayuwar Narambaɗa.

Akwai jawabin da Bunza, (2009) ya gabatar wajen ƙaddamar da littafin Narambaɗa ƙarƙashin jagorancin Farfesa Dandatti Abdulkadir. Marubucin ya gutsara tarihi da wasu siffofi da ake iya bayyana Narambaɗa, kamar haka, malami ne da ya karanci jiya. Narambaɗa ya fahimci yau, ga bakin mazajen jiya. Ya daidaita wa mutanen zamaninsa tafarkin da za su ƙyallaro gobe domin su samu tsira jibi.

A wata siffantawa da masanin ya yi wa Narambaɗa ya kwatanta shi a matsayin malamin duniya, abokin hirar manyan duniya, kuma masoyin masu abin duniya, bukkar mazauna duniya, kuma alƙali ga waɗanda duniya ta rabsuwa da waɗanda suka kai mata lehe na ƙulla sabon aure.

Haka kuma domin nuna cewa Narambaɗa cikakken malamin addini ne, ya ce:

Idan kuwa aka lugudi nassoshin zantukan waƙoƙinsa babu malamin da ba ya iya takin - saƙa da shi.

Ba a nan wannan jawabi ya tsaya ba, Bunza, (2009) ya ƙara da bayyana marigayi Narambaɗa a fagen waƙa a matsayin malagi leza, ya kuma taƙaita kimar rayuwar Narambaɗa da cewa; haka har ya bar duniya da mamakin gurɓacewar zamani, ƙarami ya kurɗa babba da barazanar maye gurbinsa,

A nan za a fahimci cewa Narmbaɗa na mamaki kan yadda tarbiyya ta fara taɓarɓarewa tun a cikin shekarun 1960. Da yana nan har a wannan zamani, da ba a san irin fasalin da zai ba duniyarmu ta yau ba, game da koma bayan tarbiyyar matasa. Zan kammala bitar wannan jawabi da kawo yadda Bunza ya dunƙule falsafar rayuwar makaɗa, inda yake cewa:

dukkanin rayuwar Narambaɗa falsafar Waƙarsa abu biyu ne ta mayar da hankali a kai: koɗa gaskiya da zuguguta ta da martaba ta. Kushe ƙarya da tozartar da ita da mizaninta.

Dukkan waɗannan abubuwa na nuni da yadda Narambaɗa ya ƙi shiga cikin zamanin rashin gaskiya, ya fake kan abubuwan da ya gada na gargajiya waɗanda suka fake martaba da mutuncin Hausawa.

Wannan ne ya zo daidai da tunanin Amfani, (2011) inda yake bayyana Bahaushe a matsayin mutun mai riƙon al’adunsa, mai haƙuri da gaskiya da son lahira maimakon duniya. Shi ma Aminu, (2003) a wani aikin bincike ya fito da wasu siffofi da ya kwatanta Bahaushen dauri da su, daga ciki akwai ilimi, wato sani da haƙuri da juriya da gaskiya da taka-tsantsan. Sauran kuwa su ne ƙwazo da kirki da biyayya da mutunci da zumunci, waɗanda halaye ne da ake ganin marigayi Narambaɗa ya mallaka. A irin wannan kamance na halayen Hausawa da ɗabi’unsu na gargajiya, Bunza (2015) ya bayyana wasu fitattun halayen Bahaushe na gargajiya da ya gada tun kaka da kakanni daga ciki kuwa akwai fake gaskiya da ƙwazo da zumunci da riƙon amana.

A wani fitaccen bincike game da Narambaɗa, Bunza (2009) ya gabatar da sakamakon bincikensa game da tarihin marigayi Narambaɗa, wanda kusan a ce ba ya da na biyu a duniyar adabin waƙa game da Narambaɗa. A cikin littafin ne ya kallaci Narambaɗa ciki da waje, ya binciko tarihinsa, ya kawo turaku da falsafa da salon waƙoƙinsa da mutanen da ya yi mu’amala tare da su da duk wasu halaye da suka shafi rayuwar makaɗa. Ba shakka wannan aikin bincike da malam ya rubuta shi ne mafi yawancin abin dogaro ga wannan maƙala wajen kafa hujjoji da ke tabbatar da Narambaɗa a matsayin mutun wanda ya fake halaye da ɗabi’u irin na gargajiya da ya gada.

Gusau, (1987, da 1990) ya gabatar da ayyuka a kan Narambada, inda a shekarun farko ya tara wasu waƙoƙin Narambaɗa, amma a shekarun gaba ya zo da taƙaitaccen tarihin makaɗa. Dukan waɗannan ayukkan bincike suna da matukar muhimmanci ga wannan aiki domin tauraron nasu iri guda ne.

Daga bayanan da suka gabata, za a iya fahimtar cewa an yi ayyuka masu ma’ana da fa’idoji kan Ibrahim Narambada. An yi bincike kan tarihinsa, an yi a kan rayuwarsa da turakun waƙoƙinsa da aka tattara. Dukan waɗannan ayyuka suna da muhimmanci ga wannan takarda domin irin bayanan da suka bayyana ne ta dogara a kansu domin fito da wani sakamako game da rayuwa da halayen Ibrahim Narambaɗa

Narambaɗa Bagargajiye a Rayuwarsa

 A wannan sashe an kawo misalai da hujjoji daga wasu sassan rayuwar da aka yi nazari ta Narambaɗa da ke nuna cewa shi bagargijyen Bahaushe ne. Idan aka ce gargajiya ana magana ne a kan tsarin rayuwa na asali na kaka da kakanni da al’umma ko wani mutun ya tashi tare da su tun bai haɗu da wata baƙuwar al’ada ba. Tun da farko yana da kyau a fara duba shi kanshi muhallin da Narambaɗa ya tashi a cikinsa.

Kamar yadda masana, Gusau, (1996) da Bunza, (2009) suka ruwaito tarihin marigayi Narambaɗa an haife shi a garin Tubali cikin ƙasar Shinkafi a yankin Zamfara. Wannan ƙauye yana a ɓoye sosai cikin karkaru, kuma a nan ne Narambaɗa ya tashi. Al’adun jama’ar wurin dukansu na yankunan karkara ne. Bunza, (2009: 42) ya ce “Da ba don Narambaɗa ba abu ne mai wuya tarihin Tubali ya tsallake Shinkafi”. Ke nan tun daga wuri ko muhallin da Narambaɗa ya tashi, ya rayu ashe wurin da ba zamananci a cikinsa. Manyan sana’o’in mutanen Tubali su ne noma da kamun kifi. Irin horon da ya samu a lokacin da yana yaro ya dogara a kan tsarin rayuwa ta gargajiya, ta ƙauye. Idan muka kalli muhallin da Narambaɗa ya tashi, ba shakka za mu iya aminta da samar da naso a rayuwar da hankali ko ɗabi’un Narambaɗa. Nazarin da wannan bincike ya tabbatar da haka a inda Bunza, (2009:45) ya ƙarfafa matsayi da yanayin inda Naambaɗa ya yi rayuwarsa da cewa “A zamanin Narambaɗa fadama ake ratsawa a yi subba idan za a shiga Tubali.”don haka da irin waɗannan hujjoji ne ake iya tabbatar da gargajiyanci a rayuwa da tunanin marigayi Narambaɗa. Bayan haka mutun ne mai son wasannin gargajiya (kokawa) da sana’o’in gargajiya da suturar Hausawa da farauta da son masarautu da malama gargajiya da Alkalai na Hausa. Game da sutura, wato tufafin jikinsa, Rambo (2023) ya bayyana cewa koyaushe shigarsa ta gargajiya ce babbar riga da wando da rawani. Ya kara da cewa lafuzzan Narambaɗa suna nan a kan harshen Hausa da aka gada ba ka samun zamananci a ciki, said a muhallan da aka inganta shi cikin hikima da fasaha irin ta mawaka.

Dukkan abubuwan nan da aka bayyana suna da tasiri da ra’in fasalin rayuwar wani mutum ko wata al’umma, musamman idan aka yi la’akari da falsafarsa da ke bayanin cewa muhallin da mutun ya tashi da mu’amalarsa da jama’a da nasa ginannun halaye suna da babban tasiri a rayuwarsa tun yana ƙarami har zuwa tsufansa.

Game da hulɗarsa da jama’a kuwa an fahimci cewa marigayi Narambaɗa yana girmama jama’a da shi da yaransa baki-ɗaya, ga shi kuma da kamun kai. Wannan ya sa har mawaƙan zamaninsa ke girmama shi. Masu gidajensa, sarakuna su ma suna girmama shi saboda kyawawar ɗabi’u da halayensa. Bunza (2019:22) ya ce “Dattakonsa ya tabbata na kamun kai da nisantar banna da mabannata balle ashararu da ya ƙi raga wa hakin susa”. A irin wannan yanayi da mu’amala daidai da fahimtarsa game da rayuwa ya keɓanta rayuwarsa kusa ga jama’arsa da kuma sarakunan gargajiya da ya yi wa waƙa, kuma mafi yawancin darussa da saƙannin waƙoƙinsa abubuwa ne da suka shafi gargajiya a fadojin sarakuna.

Akwai kalaman masana da magabata game da rayuwar Narambaɗa da suke iya zama hujja wajen tabbatar da rayuwar wannan mawaƙi. Alal misali, a wurin wani taro game da Narambada a Jami’ar Bayero, Farfesa Isma’il Junaidu Adamu, a jawabinsa ya bayyana Narambada a matsayin mawaƙi da ba irinsa a duniyar waƙar baka, musamman idan aka yi la’akari da irin hikima da fasaharsa wajen gabatar da lamurrar rayuwa da suka shafi al’umma a cikin lafuzza masu sarƙaƙiya da saƙonni masu gamsarwa, (Adamu, 2019). Wannan ya nuna cewa mutum ne wanda ke tare da al’ummarsa ta gargajiya, ya kuma san matsalolinsu da yadda ake iya warware su gargajiyance. Watakilan a irin wannan fahimtar ne Bunza (2019), a gabatarwarsa, ya kwatanta Narambada da cewa, ‘Kamar kumbu kamar kayanta’. Wato kamar yadda rayuwar iyaye da kakanni ta gabata, haka ma rayuwar Narambaɗa da halayensa suka kasance har zuwa rasuwarsa. Ba rayuwa irin ta zamani ba.

Idan aka dubi tafiye-tafiyensa, bai ta~a zuwa Turai ba, ko wata ƙasa ta Afirka ba, kamar yadda Bunza, (2009:20) ya kawo wasu garuruwa na Hausa da suka haɗa da Badarawa da Shinkafi da Katuru da Galadi da Tsibiri da Sabon birni da makaɗa ya ziyarta. Haka a yankin Zamfara ma ya yawata a wurare kamar Tsafe da Kotorkwashi da Maradun da Mafara da Gusau.

Kamar yadda aka bayyana, marigayi Narambaɗa, mutum ne da ya yi sha’awar abubuwan da suka shafi gargajiya a cikin al’ummar Hausawa. Wannan ya ba shi damar sha’awar wasan kokawa, wadda wasa ce ta gargajiya a zamanin da, Ana iya tabbatar da haka a cikin wata waƙa da shi kansa ya ambato kokuwa a ciki, mai suna ‘Ibrahim na Guraguri’, inda yake cewa:

Jagora: Bamin kokuwa koyaushe

Shi aka shammata

Bai iya ba

Amshi: Ga wata kokuwa

An wuce da shi

Karsannai kakkabe mishi kasa

Game da jin dadin rayuwa, abubuwan duniya da na more rayuwa ba su taɓa bude wa Narambada ido ba, domin nazari ya tabbatar da cewa har kusa da lokacin rasuwarsa yana zaune ne a gidan kara. Irin gidan nan na Hausawa da ake amfani da kara a zagaye ko’ina a matsayin gina, duk da cewa ya kusanci manyan mutane da sarakuna masu mulki da arziki. Ga abin da (Bunza, 2019:17) yake cewa “Ga alama marigayi Narambada shi ya makaro a gidan, kuma a gidan gadon ya rayu har ya bar duniya. Tun asali gidan, gidan kara ne irin na talakawan zamaninsa”.

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata kamar yadda masana suka gabatar da su game da marigayi Ibrahim Narambaɗa, kuma kamar yadda wannan takarda ta yi taciya ta bi diddigin rayuwarsa, an tabbatar da cewa Narambaɗa mutun ne da ya tashi a cikin al’ummar mai riƙe da al’adun gargajiya, ya rayu a cikinta. Ya samu ilimin addini ta hanyar al’adun gargajiya da addinin Musulunci. Ya kuma yi samartakarsa kamar yadda matasan ƙauye ke rayuwa. Ya yi farauta da kokawa da wasanni na gargajiya. Da ya girma ya kama sana’ar kiɗa da waƙa a gargajiyance. Narambaɗa ya fara yi wa kokawa kiɗa kafin ya koma wa sarakuna, waɗanda dukansu wasu muhimman abubuwa ne da suke da tasiri a rayuwar al’ummar Hausawa na gargajiya. A lokacin girmansa, a tabbatar da cewa mutun ne mai nuna bijire wa zamani da mamakin zamananci, duk da cewa ya rasu a lokacin da zamananci ya fara kutso kai bagatatan a muhallin Hausawa. Wannan ya ƙara tabbatar da shi a matsayin gangariyar Bahaushe. Abincinsa da suturarsa duk irin na gargajiya ne. hatta ma yadda yake kula da yaransa a yawon waƙa ba ya sakaci. Bincike ya tabbatar da cewa Narambaɗa mutun ne mai gaskiya da riƙon amana, mai tsoron Allah. Don haka, yana da kyau ɗalibai da wasu masu bincike a nan gaba su yi amfani da waƙoƙinsa, su fahimci al’adun gargajiya na Hausawa da yake bayyanawa a cikin waƙoƙinsa, musamman kamar yadda suka shafi tsarin rayuwa a fada da kuma zamantakewa a tsakanin jama’a.

Manazarta

Abubakar III (1966) Hali Zanen Dutsi. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

Adamu, A. (2019) “Keynote Speech” Presented at the Conference on Narambada, Organised by the Centre for Research in Nigerian Languages and Folklore, in collaboration with the Department of Nigerian Languages and the Department of Linguistics and Foreign Languages, in honour of General Ibrahim Badamasi Babangida, September 15-17, Bayero University, Kano.

Amfani, A. H. (2012) “Hausa Da Hausawa: Jiya Da Yau Da Gobe” in Champion of Hausa Cikin Hausa, a Festschrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad. Zaria: Ahmadu Bello University, Press Limited.

Aminu, M. L. (2003) “The Hausa Code of World - Life: A Paremiological Exposition”, in African Studies Association of Australasia and the Pacific 2003 Conference Proceedings - African on a Global Stage.

Bunza, A. M. (1998) “Naƙalin Diddigin Jirwayen Rayuwar Narambaɗa Cikin Falsafar Luguden Kalmomin Waƙoƙinsa”, Takarda Sokoto: Jami’ar Usmanu Danfodiyo

Bunza, A. M. (2009) “Taƙaitaccen Bayanin Narambaɗa daga Cibiyar Binciken Adabi da Al’adu Sakkwato”. A Jawabin da aka Gabatar a Taron Кaddamar da Littafin Narmbaɗa, Arewa House, Kaduna, ranar 16/08/2009.

Bunza, A. M. (2009) Narambaɗa. Lagos: Ibrash, Publications.

Bunza, A. M. (2015) A ji Bahaushe, A Ga Bahaushe, A San Bahaushe: Tsakuren Ficen Bahaushe da Tasirinsa a Duniyar Кarninsa. Paper Presented At Academic Forum in Honour of Dr. Ibrahim S. S. Kontagora For Being Promoted to the Rank of Associate Professor. Venue- PTF Hall, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto 8th August, 2015.

Bunza, A. M. (2019) “Wane ne Naranbaɗa? Ibrahim Narambaɗa Buhari Maidangwale Abdulƙadir Tubali (1890-1963)”. Presented at the Conference on Narambaɗa, Organised by the Centre for Research in Nigerian Languages and Folklore, in collaboration with the Department of Nigerian Languages and the Department of Linguistics and Foreign Languages, in honour of General Ibrahim Badamasi Babangida, September 15-17, Bayero University, Kano.

Furstenberg, F., Cook, T., Eccles, J., Elder, G. H., Jr., & Sameroff, A. (1999). Managing to make it: Urban families and adolescent success. Chicago: University of Chicago Press.

George, L. K. (1993) Sociological perspectives on life transitions. Annual Review of Sociology, 19, 353-373

Gieryn, T. F. (2000). A space for place in sociology. Annual Review of Sociology, 26, 463-496.

Gusau, M. S. (1987) “Jerin Wasu Waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa Tubali”, Kano: Jami’ar Bayero.

Gusau, S. M. (1996) Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kaduna: FISBAS Media

Johnson, M. K. (200lb). Job values in the young adult transition: Stability and change with age. Social Psychology Quarterly, 64,297-317.

Shinkafi, S. I. (1998) “Shahararrun Waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali (1975-1960)” Kundin digirin B.A Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Amsoshi

Post a Comment

0 Comments