Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Turakun Zambo a Bakin Makada Sa’idu Faru

Citation: Rabeh, H. & Nalado, N. (2024). Nazarin Turakun Zambo a Bakin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 92-97. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.012.

NAZARIN TURAKUN ZAMBO A BAKIN MAKAƊA SA’IDU FARU

Daga

Hassan Rabeh
08069612112
rabehassan26@gmail.con 

Da

Nuhu Nalado
Sashen Hausa na Tsangayar Ilimin Harsuna,
Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita, Dutsinma, Jihar Katsina
08067762873
naladonuhu@gmail.com

Tsakure

Muƙalar ta yi nazarin tubalan da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a matsayin gina turken zambo a cikin waƙoƙinsa. Manufar wannan muƙala ita ce yin nazarin kalaman zambo a waƙoƙin Sa’idu Faru tare da bayyana abubuwan da mawaƙin yake amfani da su domin ƙulla zambo a waƙoƙinsa. An yi amfani da dabarar sauraren waƙoƙimsa da nazarce-nazarcen masana a matsayin hanyoyin da aka bi domin tattara bayanan da aka yi amfani da su a wannan muƙala. Don cim wannan manufa, an yi amfani da mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya wadda ta bayyana hanyoyin da ake yin nazarin yadda ake nazarin waƙar baka Bahaushiya. Wanda ya jagoranci wannan mazhaba shi ne Farfesa Sa’id Muhammad Gusau. Bayan kammala wannan muƙala, an gano turakun da mawaƙin yake la’akari da su a yayin samar da zambo a cikin waƙoƙinsa da suka ginu a kan ɗabi’a a gurabun wasu dabbobi da tsuntsaye da mutane. Tare da yin amfani da turakun ƙarangiya da na ba’a da wasu turakun da ke nuna matsayin mutum a rayuwa.

1.0 Gabatarwa

Waƙar baka, zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaituwa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da amshi (Gusau, 2023: xix). Haka kuma, ta fuskarsiga da zubi da tsarinaiwatarwa, Bahaushiyar waƙar baka ba ta zuwa a shimfiɗe ko ta zo gaba ɗaya, takan zo ne gutsure-gutsure tare da maimaituwar gindinta a tsakaninsu. Gutsure shi ne ‘ɗa’. A waƙar baka ba a ƙayyade yawan layuka a ɗan waƙa, musamman ga makaɗan da suke cikin ƙungiya, suna maimaita gindin waƙa a ƙarshen kowane ɗan waƙa.

Waƙoƙin baka na Hausawa suna daga cikin hanyoyin da Hausawan suke nuna fasaharsu ta baka. Waƙar baka tana daga cikin hanyoyi daban-daban na isar da saƙonni da kuma samar da nishaɗi. Haka nan suna taskace abubuwa da dama, daga ciki akwai tarihi da al’adu da sarauta da kalmomi. Don haka ne makaɗa da mawaƙa suke da matuƙar muhimmanci a rayuwar Hausawa, musamman ta gargajiya. Kowane fannin a rayuwar Hausawa yana da mawaƙa na musamman da waƙoƙinsu suka shafi wannan ɓangaren.

Daga cikin mayan rabe-raben makaɗa da masana. Gusau (2008:137) ya raba su zuwa makaɗan jama’a da na maza da kuma na fada. Makaɗan fada su ne makaɗa (ko mawaƙan) da ba su yi wa kowa waƙa sai jinin sarauta ko masu riƙe da muƙamai na sarauta. Sa’idu Faru yana daga cikin irin waɗannan mawaƙa, domin shi da kansa yana cewa:

Jagora: Sa’idu Faru ka waƙar iko,

‘Y/Amshi: Komi kaj jiya ƙarya akai,

Jagora: Sa’idu Faru ka waƙam Mulki,

‘Y/Amshi: Kami kaj jiya ƙarya akai.

(Waƙar Ɗan Hashim).

Makaɗan fada suna yin tasiri ƙwarai a harkokin sarauta. Baya ga kasancewar masu samar da nishaɗi sukan yaɗa manufofin sarakuna da bayyana salsalarsu. Haka nan kuma sukan zama wata garkuwa ga masauta da sarakuna. Daga cikin hanyoyin da suke zama garkuwa ita ce sukan mayar da raddi ga maƙiyan masarauta da kuma sarakuna, wani lokaci ma sukan zama kanwa uwar gamia wajen assasa yaƙe-yaƙe a tsakanin masarautu. Ana iya ganin misalin haka a wasu ɗiyan waƙar Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Ƙauran Namoda, Abubakar inda yake cewa:

Jagora: Ni kiɗin yaƙi nay yi ma Abu na Isau,

Ba ni son kana zamnawa banza

Ka ɗauki takobi da bindigogi da bakunkuna

Ka sa surdi ba mu sansani sai baki Tsauri

Kano da Katsina, Kwantagora

Hab Barno riƙon Namoda na

Shi na ac can

Garba ka amshe riƙon dud da Ummarun Ummaru

Yab bar ma.

(Waƙar Sarkin ƘauranNamoda, Abubakar).

A wannan ɗan waƙar mawaƙin ya ambaci irin kiɗin da ya yi wa sarkin nasa wato kiɗin yaƙi ne ba wai don sarautarsa kurum ya yi masa ba. Dubi farkon ɗan waƙar, ya kuma cigaba da nuna masa wasu wuraren kamar Kano da Katsina da Kwantagora har Borno duk riƙon kakansa ne.da yake ganin a da duk nasu ne don ya yi niyyar kwato su ta hanyar yaƙin.

Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin shahararrun mawaƙan fada da ƙasar Hausa ta samar. Daga cikin ƙunshiyar waƙoƙinsa akwai zuga da yabo da nuna salsala da gwanintar harshe, idan kuwa maganar zambo ce makaɗa Sa’idu ba shi da na ɗaya. A matsayinsa na makaɗin fada zambo yana daga cikin batutuwan da makaɗin yake gwarzant agwarzayensa da kambamasu. Haka kuma ya kankushe abokan hamayyar sarakunansa don kare martabarsu (Gusau, 2008:147). Ganin haka ne ya sanya wannan muƙala ta yi nazarin turakun da Sa’idu Faru ya yi amfani da su domin gina zambo a cikin waƙoƙinsa.

Manufar wannan muƙala ita ce, yin nazri a kan turakun da makaɗa Sa’idu Faru yayi amfani da su domin gina ɗiyan waƙoƙinsa masu nasaba da zambo. za a yi haka ne ta hanyar gabatar da turken sannan a kafa hujja ta hanyar kawo ɗiyan waƙa ko waƙoƙi da suka nuna tueken da aka ambata, sannan a kawo sharhi a kan ɗiyan waƙar da aka gabatar.

2.0 Taƙaitaccen Tarihin Sa’idu Faru

Gusau (2005:117) ya bayyana cewa an haifi makaɗa Sa’idu Faru a ƙasar Maradun a shekarar (1932). Sunansa na yarinta shi ne Ɗan’umma. Wannan suna ya samo asali ne daga matar ƙanen ubansa, wacce baya kiran sunanta naasali sai dai ya kira ta da Umma. Sunan mahaifinsa makaɗa Abubakar ɗan makaɗa Abdu. Wannan yana nuna cewa makaɗa Sa’idu Faru ya yi gadon kiɗa ya yi daga wurin mahaifinsa da kakansa. Makaɗa Sa’idu ya yi ƙuruciyarsa a garin Banga ta ƙasar Ƙauran Namoda. Sa’idu ya koyi waƙa daga wurin mahaifinsa. A lokacin da Sa’idu ya fara cin gashin kansa, sai fasaha da hikimarsa ta ƙara fitowa a fili.

3.0 Ra’i

An ɗora muƙala a bisa Mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya. Mazhaba ce da ta samo asali a shekarun (1993), a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau. Manufar mazhabar ta ƙunshi bayyana tarihi da asali da salsalar waƙar baka ta Hausa, da kuma zurfafa bayani a kan turke da abubuwan da waƙa ta ƙunsa. Ita wannan mazhaba ta tarken waƙar baka Bahaushiya ta jinginu da wasu Ra’o’i na wasu mazhabobin da suka haɗa da Mazhabar Gargajiya. Daga cikin ayyukan da aka samu sun ginu ta yin amfani da wanna mazhaba suna da yawa. Kaɗan daga cikinsu akwai aikin Garba (1998) da Satatima (2008) da Abubakar (2011) (Gusau, 2023:23). Dangantakar wannan Mazhabar da wannan muƙala ita ce, aikin ya ginu ne a kan nazarin turakun waƙoƙi masu nasaba da zambo a waƙoƙin Sa’idu Faru. Mazhabar kuma tana magana ne a kan nazarin waƙar baka Bahaushiya. Wannan dalili ne ya sanya aka zaɓi gudanar da wannan muƙala a bisa wannan Mazhaba.

3.1 Hanyar Gudanar da Bincike

An yi amfani da hanyoyi biyu a yayin tattara bayanan da aka yi amfani da su a wannan gudummawa da ta yi nazarin turakun da Sa’idu Faru yake yin amfani da su a yayin gina zambo a cikin waƙoƙinsa. Hanya ta farko ita ce ta sauraron waƙoƙin tare da tattara wuraren da yake yin zambo a cikinsu.

Hanya ta biyu kuwa, ita ce, ta hanyar yin nazarin rubuce-rubucen masana masu nasaba da waƙoƙin baka na Hausa. Har ila yau, an samo waɗannan bayanai daga wallafaffun littattafai da kundayen bincike da aka gudanar daga jami’o’i daban-daban da muƙalu da aka gabatar a tarurruka daban-daban na ƙara wa juna sani. Haka kuma an yi amfani da kafar sadarwa ta yanar gizo wajen samu da tattara bayanan da aka yi amfani da su a yayin gudanar da wannan bincike.

4.0 Turakun Gina Zambo a Bakin Sa’idu Faru

Kalmar zambo kishiyar yabo ce. Ma’ana tana nufin bayyana mutum da wasu munanan siffofi waɗanda za su muzanta mutum tare da jawo masa rashin ƙima da mutunci a idanun sauran al’umma. A yayin gina zambo a waƙoƙin baka akan lura da halaye da siffofin mutum na zahiri ko kuma a yi masa siffofin ƙage. Daga cikin hanyoyin da akan bi domin yi wa mutum zambo akwai duba kamanni da nuna halin rashin kirki da kamanta mutum da halayen dabbobi ko tsuntsaye marasa kyau da ɓata asali da nasaba da kuma ƙaga wa mutum mummunar siffa ko da kuwa bay a da ita (Gusau, 2008:382).

Makaɗa Sa’idu Faru yana amfani da wasu tubula a yayin da yake ƙulla ɗiyan waƙa masu nasaba da zambo. Daga cikin waɗannan tubula akwai:

4.1 Ɗabi’u

Sa’idu Faru yakan yi amfani da ɗabi’a a matsayin tubalin gina zambo a cikin waƙoƙinsa. Waɗannan ɗabi’u sun haɗa da na dabbobi da na tsuntsaye da munanan ɗabi’u waɗanda Hausawa suke ƙyamata a rayuwa.

4.1 Turken Ɗabi’ar Dabbobi

A nan mawaƙin yakan yi amfani da ɗabi’u masu kyawo a yayin zuga ko kwatanta gwarzayensa sannan ya yi amfani da ɗabi’u masu rauni ko muni waɗanda Hausawa suke ta’allaƙawa ga wasu dabbobi domin yin zambo ga waɗanda yake nufin yi wa zambo. a lura da abin da yake faɗa a cikin waɗannan ɗiyan waƙoƙin:

Jagora: Alibawa kuna ganin hwansakku wurin Sule babu dama

Giwa ta sha ruwa tai miƙa ta taushegurbi

Kuma ‘yan ɗiyanta sun shiga sun sha sun hwara ƙarfi

Sai ‘yan namu suna jin ƙisa ba damas su ɗebo

Sai bil’amu ubandubara

Shi ɗai yaz zo ga giwa

Albarkacinki niz zaka in samu ruwan da nis sha

Giwa ta ba shi hili, ya samu ruwan da yas sha

Ya sha ya kuma ba ɗiyanai

Yaw wa dangi kirari yac ce ya ƙwato da ƙarhi

Zomo yac ce tsaya shege lallashin ta kay yi

In ƙarhi gaskiya na koma ɗebo gabana.

(Waƙar Sule, sarkin Zurmi)

A ɗiyan waƙoƙin da suka gabata mawaƙin ya yi amfani da ƙarfin da giwa take da shi a matsayin fifiko a kan sauran dabbobi. Haka nan ya yi amfani da wayo ko dabarun dila da kuma kaifin hankali da Zomo ya yi amfani da shi domin tona asirin Bil’amu (Dila).

Haka kuma, a wani wurin ya kawo irin wannan:

Jagora: Na zo na ishe ‘yan sarki naz zaɓi guda

Komi za mu yi da shi mukai

Ihihiya da kunkuru shawara guda sukai

Buƙuƙuwa da jinjimi shawara guda sukai

Da bisshiya da beguwa shawara guda sukai

Da kurciya da hazbiya shawara guda sukai

Duk babu wanda yaz zo haji babu mai nuhwaz zuwa.

(Waƙar Sarkin Tudu)

A nan makaɗa ya kawo dabbobi masu kusancin ɗabi’a da juna domin kwatanta waɗanda yake yi wa zambo. a cikin ɗiyan waƙar ya nuna yadda ihihiya da kunkuru suna da kammanu da ɗabi’u iri ɗaya ta yadda wasu ma ba su iya bambance su. Shi ya sa ya ce shawara guda suke yi. haka ma bubuƙuwa da jinjimi suna da kamannu da ɗabi’u iri ɗaya kamar yadda bushiya da beguwa kowannensu yana da ƙaya a jikinsa. Kurciya da hazbiya ma suna da kamannu da ɗabi’a iri ɗaya. Dukkan waɗannan halittu ya nuna babu wanda yaz zo haji babu mai nufin zuwa, wato waɗanda ya kwatanta da waɗancan halittu babu wanda ya yi sarauta kuma babu mai alamar yin sarautar.

4.2 Turken Ɗabi’ar Tsuntsaye

A nan kuma, Sa’idu Faru yana amfani da ɗabi’un tsuntsaye kamar yadda yake yi ga dabbobin a nuna fifiko da ƙarfin halin wasu tsuntsaye a kan masu rauni ko waɗanda ake ta’allaƙa wa wayo a kan waɗanda ake nuna wa rashin wayo. Dubi waɗannan ɗiyan waƙoƙi:

Jagora: Duk tsuntsun da ka daji

Ko babba ko ƙarami duka na gane nuhinai

Jemage ga halinai ba mu san wanda shike so ba

Ga shi mai haƙora na, Ga shi kunnuwa na

Ga ya ba ya sabka ƙasa balle a ga dama tai

Don munahukin Allah kai munka naɗa babba.

(Waƙar Amadun Sambo)

A nan mawaƙin ya yi amfani da halittar jemage wanda yana tashi kamar tsuntsu, kuma yana da haƙora da kunnuwa kamar dabba a matsayin munafunci. Domin ya kasance da kamannu na abubuwa biyu. Ke nan ya kwatanta wanda yake yi wa zambo a matsayin munafuki kamar yadda halittar jemage take.

4.3 Turken Ɗabi’un Mutane

Akwai waɗansu ɗabi’u da al’ummar Hausawa suke ɗauka a matsayin na ƙwarai, wasu kuma munana. Daga cikin munanan akwai sata da maita da daudu da karuwanci. Sa’idu ya yi amfani da mummunar ɗabi’ar ɗandaudu domin ƙulla ɗiyan waƙarsa mai nasaba da zambo. Ya yi haka ne kuwa domin yana sane da cewar ɗabi’ar ‘yandaudu tana daga cikin daɗaɗɗaun munanan ɗabi’un da Hausawa suke ƙyama (Rabeh da Darma, 2016:239). Greenberg (1946:42 da Bosmer (1993:18) sun bayyana cewa ɗabi’ar ‘yan daudu ta samo asali ne daga wani iska da ake kira Daudu wanda yake yin ɗabi’un mata. Sanin kowa ne cewar ɗan daudu mutum ne namiji mai nuna sha’awa da yin ɗabi’un mata, wani lokaci ma harsunan mata yake amfani da su. Haka nan yakan yi kwalliya irin ta mata da ɗaura zane da kuma kallabi, har ma a wani lokaci akan danganta su da kawalci da luwaɗi (Gaudios, 1988:19). Mawaƙin ya yi amfani da wannan ɗabi’a da Hausawa suke ƙyamata domin yin zambo a cikin waƙarsa ta Sarkin Zurmi Sule. A cikin waƙar yana cewa:

Jagora: Ko can zamanin ana yaƙi kakan Sule ad da hwama

Mai yanke mutane Ummaru ba wargi ag garai ba

Kakan wani ba shi da yaƙi

Ko can ɗandaudu na shi

In da dai shahwa kwalli na da kaka nai ka suna

Da madibinai da hoda

Da hwarar riga da kore

Da gani nai ka ga kure geme cinjim da shuni

(Waƙar Sarkin Zurmi Sule)

Haka nan, a wasuɗiyanwaƙaryayiamfani da mummunarɗabi’ar karuwanci don gina ɗiyan waƙar, inda yake cewa:

Jagora: Baicin kokuwa akwai maraba

Ɗan Arkuma ya bah hwaɗa maka Muhammadu

Ko wurin uwaye mata kuna da tsettserai

Ɗan mara abun wuya

Ɗan karuwa duɓ ɓaci kaj jiya da kai muke.

Karuwanci abin ƙyama ne ga al’ummar Hausawa. Don haka ake ƙyamar karuwa da ma duk zur’ar da ta tsira daga jikinta. Saboda wannan dalili ne Sa’idu ya kwatanta wanda yake yi wa zambo da Ɗan karuwa watau wanda ba shi da nagartaccen asali. Sa’idu ya yi haka ne kuma domin ya muzanta wanda yake yi wa zambo domin ya ɗauke shi abokin hamayyar ubangidansa.

4.4 Turken Ba’a

Makaɗa Sa’idu Faru yakan yi amfani da ba’a ya ƙulla zarensa a yayin da yake yin zambo. Sa’id (2006) ya bayyana da zolaya ko muzantawa cikin wasa. Akan kalli sifa ko surar mutum a danganta shi da halittar dabba ko wani abu mai muni. A irin wannan yanayi Sa’idu yakan kalli siffar jiki ya kwatanta mutum da wani abu da zai zamo ba’a a gare shi kamar yadda za a gani a ɗiyan waƙar da yake ƙasa:

Jagora: Sharrin da an ka ƙulla ma Ƙaura duka ya kwance

Mai kamab buhun garin kwaki aka wa yanzu

Akuɗunɗun-akuɗunɗun

Ɗan sarki da wuyan gora

Zamna mu ji labarin ƙaryad da kakai soto.

A nan mawaƙin ya kwatanta wanda yake yi wa zambo da buhun garin kwaki. Daga jin wannan kwatance za a fahimci cewar duk wanda ake yi wa zambon mutum ne mai jiki, sannan mutum ne mai dogon wuya. Haka kuma ya nuna cewa akwai wani ɗan sarki mai gajeren wuya ta yadda ya kamanta shi da wuyan gora.

4.5 Turken Bayyana Matsayi

A irin wannan yanayi Sa’idu yana amfani da rashin wadata wacce ba a cika danganta sarauta da ita ba domin ya yi zambo. Yakan nuna talauci ya kuma danganta shi da sarki ko ɗan sarkin da yake yi wa zambo. Dubi abin da yake cewa a waɗannan ɗiyan waƙa mai amshin Koma shirin daga na Bubakar, gamda’aren alƙali wan maza’:

Jagora: Ga wani sarki ba shi da zagi.To kuma sannan bai da guzuri.

Garin rogo ɗai suka ta ci da guru kowane na aza ruwa

Amma shi kau had da dama-dama

Y/Amshi: Ga wani sarki na ta kumburi da yaranai sun sha mashi hura

Ga wani santolon uban ƙasa da yaranai wajjen guda huɗu

Ba kau mai suturar kwabo huɗu

Ya hita mota ya yi tagumi da kwandon ɗunya yay yi guzuri.

Idan aka lura za a ga cewa mawaƙin ya nuna tsananin talauci, ya kuma danganta shi da sarki (uban ƙasa) wanda ya nuna ba shi da zagi kuma ba shi da guzuri don nuna rashin wadata sai ya nuna cewar garin rogo suke ci da guru. Haka nan ya nuna cewar wannan ma yana da dama a kan uban ƙasar da yake fushi da yaransa da suka sha masa fura. Haka nan dukan yaran guda huɗu babu mai suturar kwabo huɗu. Wannan yanayi ya yi muni ga sarki ko uban ƙasa komai lalacewarsa.

4.4 Turken Ƙarangiya

Wannan yana ɗaya daga cikin azancin magana. Ƙarangiya tana nufin yin lugudenkalmomi ko sautuka a cikin zance. Hakan yana samuwa ne ta hanyar maimaita wata ko wasu gaɓoɓi ko sautuka iri ɗaya ko masu kusancin furuci masu tafiya bai ɗaya (Gusau 2023:70). Makaɗa Sa’idu Faru gwani ne na amfani da ƙarangiya a cikin waƙoƙinsa. A yayin ƙulla zambo ma bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen amfani da wannan azancin magana. Lura da abin da yake cewa a waɗannan ɗiyan waƙa:

Jagora: ‘Yan banza da ac cikin garin Maru

Yam maidama nan suke ga Mamman

Na ishe raggo da rangama da ragagge

Garkam marar ragowa

Katako da kattako da mai kanta da katanga da kanta karya

(Waƙar Alƙali Muazu)

A yayin ƙulla zambo mawaƙin ya yi amfani da salon Magana inda ya yi amfani da sautukan /r/ da /g/, sannan ya yi amfani da sautin /k/ da na /t/. Kodayake salon magana ya yi amfani da shi, za a iya fahimta ɓurɓushin zambo, musamman a kalmomin raggo da ragagge da mai kanta.

4.5 Turken Batsa

Batsa tana nufin maganar banza, musamman wadda ta danganci ambaton al’aurar mace ko namiji (Sa’id, 2006). A irin wannan ɗiyan waƙa mawaƙin ya yi amfani da batsa a kaikaice domin ƙulla zambo, za a iya ganin haka a cikin wasu ɗiyan waƙar Alƙali Mu’azu inda yake cewa:

Jagora: Wani Alƙali wanda bai kashe amre

Wai sai ya ji wada tac ce

Yarinya ke ji wadda nic ce

Ke ko sai na ji wadda kic ce

In na koma gida ki koma

Sai in binciki ƙasas shari’akki

In ji daɗin riƙa dalili.

(Waƙar AlƙaliM u’azu).

A ɗiyan waƙar da suka gabata mawaƙin ya nuna cewar wani alƙalin yana neman matan aure a matsayin cin hanci daga baya ya kasha masu aure. A nan mawaƙin ya yi amfani da kalmomi na batsa a kaikaice a inda ya ambaci Sai in binciki ƙasas shari’akki, In ji daɗin riƙa dalili.. Wannan ba ya rasa dalili da cewar mawaƙin dattijo ne don haka bai fito fili ya yi batsa kai tsaye ba domin duk da yana son ya aibunta abokin adawar alƙali, a ɓangare ɗaya kuma yana taka tsantsan da kare mutuncinsa na dattijo.

5.0 Kammalawa

Wannan muƙala ta kamala wadda a cikinta an lura da cewa makaɗa Sa’idu Faru yakan yi amfani da munanan ɗabi’u na mutane da dabbobi da tsuntsaye a yayin da yake shirya ɗiyan waƙoƙinsa masu nasaba da zambo. haka nan an lura da cewar ya yi amfani da ƙasƙantar da darajar mutane, musamman ‘yan sarki a yayin da yake yin zambo a waƙoƙinsa. Haka kuma, yana amfani da ƙarangiya da batsa. Don haka ana iya cewa waɗannan batutuwa da aka ambatasu ne ƙashin bayan turakun da mawaƙin yake ƙulla zarensa na zambo a cikin waƙoƙin da ya aiwatar a lokacin rayuwarsa.

Manazarta

Bosmer, F. E. (1983). Horses, Musicial& Gods. The Horses Cult of Possession. Trans. Massachasetts: Bergin & Gaerney Publishers.

Gaudio, R. P. (1998). Male Lesbians and Other Ƙueer Notions in Hausa. Murray. Stephen O. A. & Roscoe, Will (eds), Boy Wiɓes and Female Husbands. Studies of African Homosexualities. New York: St Martins Press.

Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (2023). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: WT Press Printing & Publishing.

Rabeh, H. da Darma, A. Y. (2016). “Munanan Ɗabi’un Hausawa: Waiwaye a kan ‘Yan Daudu da Yanayin Rayuwarsu”. Argungu Journal of Language Studies. Vol. II. Pp. 239-243.

Sa’id, B. (2006). Ƙamusun Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Sa'idu Faru

Post a Comment

0 Comments