Kalmar Sai-Baba-ta-gani ta shiga bakin al’umma musamman a wannan zamani na yawaitar yajin aikin ‘yan kwadago. Amma kun san yadda ta samu shiga harshen Hausa?
Ku karkade kunnawanku ku ji tarihin wannan batu kamar yadda
Jarman Kano Isah Hashim ya shaidawa marigayi Tijjani Ado Ahmad, mai gabatar da
shirin Barka da hantsi na Freedom Radiyo Kano.
Tushen maganar dai ya taso ne daga zamanin yakin duniya na
biyu, wanda Hausawa ke kira yakin Hitila ko yakin Burma.
Da yake a shekarun yakin, 1939-45, Najeriya na karkashin
mulkin Burtaniya sai Turawa suka yi ta yada farfaganda don neman matasa da za
su shiga aikin soja.
Daya daga cikin farfagandar da aka yada a lokacin, ita ce
cewar duk wanda ya je yaki ya dawo za’a nada shi sarkin garinsu.
Hakan ta sa matasa da dama su ka yi ta shiga aikin soja
saboda kwadayin sarauta. Amma inda gizon ke saka shi ne, matasan arewacin
Najeriya da dama sai su ka fi sha’awar a nada su sarkin Kano maimakon sarakunan
garinsu. Don haka masu irin wannan kudirin sai su ka yi ta shiga aikin soja da
sunan mutanen Kano. Sai ka ga Ali Kano, Idi Kano, Mamman Kano amma ko ‘zo nan’
basa ji a harshen Hausa.
Bayan dawowa daga yaki, sai Turawa suka maye gurbin wacce
farfagandar karya da samawa wadanda su ka dawo aikin ‘yan doka. To wadannan
‘yan doka marasa Hausa da suka kama aiki a Kano sai Allah ya yi su, masu
gaskiya ne da rashin karbar cin hanci.
Saboda haka duk lokacin da suka kama mai laifi, in ya fara
ba su hakuri ko ya yi yunkuri ba da na goro, sai su cukuikuye shi su ce
‘sai-Baba-ta-gani’. Ma’anarsu, ba za su sake shi ba sai wakilin doka – wanda su
ke kira Baba – ya gan shi kuma ya dauki mataki a kansa.
Daga nan harshen Hausa ya karu da Sai-Baba-ta-gani, wato ba
zamu bari ba sai mai iko a kan lamarin ya Gani.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.