WAƘAR ZUWA BIRNIN KANO TA SARKIN ZAZZAU ALU ƊANSIDI
Ka rarra, ka Kabra, ku san tumkiya
Bata iya kabra ba Kano
Da tauri da tsauri idan anka goga
Guda sai shi yanke guda a Kano
Ba'an gwada karfe ba, sai inda karfe
Duwatsu fashewa su kai a Kano
Ka zaga Kano har kasan dan Kano
Na birnin Kano wanda yasan Kano
Ka kau tambaye shi tsakani da Allah
Ya bayyana maka taron Kano
Na yawata Kano gani ga dan Kano
Dada har nasan anguwa a Kano
Akwai anguwan madawkin Kano
Da sunanta Yola a birnin Kano
Daneji, da Soron dinki akwai su
Akwai Lungunawa da Sheshe Kano
Da Marmara duk unguwa ce duka
Da Kunduke Kwankwaso duk a Kano
Akwai Wudilawa akwai Na'ibawa
Da Ibadi Fasa-keya a birnin Kano.
Caranci, Gudundi, akkwai Jarkasa
Makankari, Garko duk a Kano
Kusura, Kudancin Kano da Wazirci
Da Siradi akwai ta Kano
Karofi na Wanka da Shuni akwaisu
Madatai da Daushi akwai su Kano
Karofi na Sudawa, Zangon Ciki
Da Dandago, Diso akwai su Kano
Akwai unguwar Durunmin Kaigama
Da Bulbulas, Guntu akwai su Kano
Da Yalwa da Dala, Madaboo duka
Suna nan Arewa da Kurmin Kano
Akwai wata ko unguwa Masaka
Da Sarari da Sagagi Birnin Kano
Awai unguwa Waitaka a Kano
Akwai Durumin Dakata min Kano
Mahanga, Kutumbawa duk unguwa ce
Da Damtsenka Tsage a Birnin Kano
Akwai Cediya ta Kuda unguwa ce
Akwai Kalaman Dusu duk a Kano
Da Lallokin Lemu, da kau Makwarari
Makwalla fa duk unguwa ce Kano
Dabinon Awansu da Mandawari
Da Alfindiki Kwalwa duk a Kano
Tsaya in gajarta guda don kau yawaita
In kawo wurinta da niyyi Kano
Fa har muka kare naje Nasarawa
Garin makarantan su Sambon Kano
Akwai makaranta karatun Bature
Acan Nasarawa ta kofar Kano
Akwai yara masu Karatu na allo
Akwai masallaci ginanne Kano
AKwai Makaranta ta al Kur'ani
Da litattafanmu a birnin Kano
Akwai wani dakin zaman masu ciwo
Akwai matsarinsu a kofan Kano
Masaka, madunka, da mai Sassaka
Gidansu guda makarantan Kano
Makera, Badukai da masu kudi
Cikin makaranta ta kofar Kano
Cikin shekara goma sha dai ga daula
Aliyu binu Sidi zuwanshi Kano
Ya wake ta yan baya domin su ji
Su san wakacin tafiyanshi Kano.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.