Ticker

6/recent/ticker-posts

Taken Marubuta

Taken Marubuta

TAKEN MARUBUTA
Tare da waƙar:
ALƘALAMI DA RUBUTU

Mu ne marubuta muke yi a karanta,
Alfaharinmu rubutu don mu faranta zukata,
Raya al'adarmu ta Hausa da ɗaukakar darajarta,
Umbreller adabi ga mu cikinta, mazanmu da mata,
Bunƙasar harshenmu har ya yi wa na saurarata,
Uku ga uku kai har ma ka ƙure lambata,
Tasirin marubuta, ya wuce 'yan tatata,
An yanka ta tashi a duk sabga in ba marubuta. 

Allah ga Marubuta ka ƙara shiga lamuranmu,
Allah ga Marubuta Ka yi riƙo da hannayenmu,
Allah ga Marubuta Ka yi ƙarfafar guiwarmu,
Allah ga Marubuta ka ƙara harhaɗa kanmu,
Allah ga Marubuta ƙara mana son junanmu,
Allah ga Marubuta kare sharrin maƙiyanmu,
Allah ga Marubuta ka kasance jagoranmu,
Allah sa Haske nasarka a alƙaluman Marubuta.

WANENE MARUBUCI KU ZO KU JI AMSAR GATA, TASIRIN MARUBUTA KU JI SHI CIKIN WAƘATA, ALƘLAMI DA RUBUTU DARAJA TASU ZAN SHELANTA.

1.
Da sunan rayayyen Sarkin da shi Ya kaɗaita a bauta,
Bai da iyaye ba Shi da dangi balle ɗa ko mata,
Gwanin hikimar da ya ƙago alƙalami farko a halitta,
Bayan samar da shi kuma Yai masa umarnin ya rubuta,
Ƙaddarar kowa da ta komai tun asali haka nan ya ƙadarta

2. 
Ka ƙara daɗin tsira da aminci masu yawa ya Allah,
Ga zaɓaɓɓen Bawan nan ɗan Aminatu ɗan Abdullah,
Shugaban duk Annabawa tare da manzanni duka jumla,
Har alaye da sahabbai nai a saka su ciki ya Jallah,
Tabi'ai da dukkan mabiya nasa ban ware ba cikin sabga ta,

3. 
Wane ne marubuci ku matso ku ji amsa ga ta,
Tasirin marubuta za ku ji shi cikin waƙata,
Ku san girmansu da tarin gudummawarsu ga Al'ummata,
Alƙalami da rubutu daraja tasu zan shelanta,
Aliyu usman al'usku za ku ji su cikin muryata.

4. 
Marubuci shi ya kasance mahadi mai dogon zaman,
Shi ne kan sanya tabarau da tunani don ya yi hangen,
Nesa ko ya waiwayi baya shekaru dubunnai kenan,
Rayuwar da ka iya zowa ko ko wadda akka yi da can,
A yanzu ko zuwa wani ƙarni wassu al'umma su karanta.

5. 
Lokacin da wassu ka bacci shi ko marubuci na can,
Za ya je ya hau kan tsauni domin hango ƙasa can-can,
Ya bi duhun dare ya bi rana sai da ransa domin neman,
Duk abin da zai amfanar warware dukkan matsalolin,
Al'umma ya tara bayanai kana yai zama ya nazarta.

6. 
Yayin da wassu kan zuba jari har su zam cire ribarsu,
Wassu leburanci don samun rufin asiran kansu,
Shi ko marubuci na can na taya su sauke haƙƙinsu,
Yadda za su sam sassauci har da cigaban sana'arsu,
A rubuce ya taskance ran da suka so su karanta.

7. 
Alƙalam kira shi hukuma wanda dole sai rarrashi,
Don ko har idan ya ɗaure ba mawarwari sai dai shi,
A silar shi ne na ji rannan wane kyautuka an ba shi,
Sanadinsa ne na ji cewa kuma wani ya sha kashi,
Shi makamashi na wuta ne kuma ya zam ruwa na kashe ta.

8. 
Alƙalam cikin bulali ya ɗarar wa dorina zafi,
Babu mai musu in na ce ya fi ma takobi kaifi,
Ya wuce kibau tsini har ya fi bindiga ma kaifi,
Makamai na ƙare dangi in ka tattare duka ya fi,
In kace da shi sha kundum alƙalam fa ya cancanta.

9. 
Wanda duk ya rayu a duniya ya ci arziƙi na rubutu,
Ko a kasuwa ko ofis gwamnati zuwa masarautu,
Duk isar ka duk girmanka dole dai da shi ka buƙatu,
Yai silar talauta waɗansu wasu sanadin su rabautu,
Matsayi isa alfarma dukiya a zam tara ta.

10. 
Marubuci jagora ne mai jan ragamar tarihi,
Sannan kuma shi ne goga ko ana tuma ko ahi,
Mai gwalangwason labari mai mayar da sanyi zahi,
Shi ka ɗaura auren dole ba mai iya ce masa ihi,
Zai tsayar da kai daga aiki, kuma zuciya ya faranta.

11. 
A taƙaice dai marubuci ya zamo kamar fitila ne,
Yunƙurin dukan marubuta don su zam kawar da duhu ne,
Su ko alƙalam da rubutu jagororin shiriya ne,
Wanda duk ya so bin haske kishiyar hakan ra'ayi ne,
Mai zuwa gari ko daji duk mu miƙi hanyar zata.

12. 
Tare da malam Nura Abu Uthaymin ne muka tsaro,
Baitocin waƙar nan muka zam yin karo-karo,
Har ya zam ta samu zuwa kunnen dukkan mai sauraro,
Magogin ƙarfe shi ne kan iya gurje mazajen goro,
Ga toro ga zaki dole a yi tafiyar ƙasaita.

13.
Nan zani taƙaita don bani nufin na tsawaita,
Rabbi ga Marubuta ayyukanmu kar ka taƙaita,
Aikin mu rubutu ba mu zamba ko ko mugunta,
Adabi gatanmu kuma ya ɗare mana gata,
Godiya muke maka Allah da muka zam cikin marubuta.

Alhamdu Lillah.
25/06/2022

Haƙƙin Mallaka:
Aliyu Usman Kuringafa (Al'usku).
Nura Isma'il Abubakar (About Uthaymin).

Za a iya tuntuɓarmu ta waɗannan hanyoyi da ke ƙasa:
07067717013, 07036080441, 08024502520, 08139502982.
alusku12@gmail.com, aluskunwaka@gmail.com,

Post a Comment

0 Comments