GARIN BABBAR RUGA, KATSINA
Garin Babbar Ruga Katsina, ya kafu tun wajen karni na goma Sha tara ( K19). Ruga Kalmar Fulatanci ce da take nufin wurin zama ko matsugunni na Dan lokacin, wanda ba na dindindin ba. Asalin wurin da ya zama babbar ruga Fulanine suka kafa tun wajen shekarar 1900. Amma suna babbar ruga ya samo asline daga Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944). Kamar yadda Tarihi ya nuna Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, Yana da Gona a Kauyen Kurmjya Dake Karamar Hukumar Batsari ta yanzu. To duk lokacin da zaije Gona shi yakan yada Zango a dai dai wannan Rugar ta Fulani yasha Madara da Nonon Shanu, ta haka sai ya sanya ma Rugar suna Babbar Ruga, saboda babbar ruga ta samo aslin sunantane daga Sarkin Katsina Muhammadu Dikko a wajen shekarar 1928.
Babbar Asibin babbar Ruga tana daya daga cikin manyan wuraren da suka fiddo Garin babbar Ruga. Asalin wannan Asibitin Turawan Mishan ne suka budeta a cikin shekarar 1931. Lokacin da Turawan Mishan sukazo Katsina sun fara Bude Makarantar Mishan ta farko a Modoji Dake a Unguwar Turawa ko kuma GRA ta yanzu, wanda itace a halin yanzu ta koma Modoji Primary School. Daga baya Sarki Dikko tare da Turawan mulkin Mallaka suka basu wurin zama na dindindin, a wurin da babbar Ruga take yanzu. Acikin shekarar 1931 ne Turawan Mishan suka tare a babbar Ruga inda suka Gina Gidajesu, da Makarantar Mishan ta biyu a Katsina, a nan babbar Rugar. Sannan kuma suka Gina Asibiti domin ba mutane magani kyauta. Cutar Kuturta data Tibi, da Tarin huka sune suka fi maida hankali a kansu. Sun fara wannan aiki tun daga shekarar 1931 har zuwa 1972. Mafi yawan mutanen da suka warkar sun mayar dasu Kiristoci, sannan kuma yayansu da suka zo dasu sun sanyasu a ( Mission School ) Dake a nan Babbar Ruga, wadda su Mission din suka Gina. Wannan dalilin yasa aka samu Kiristoci da dama a makwabtan babbar Rugar Misali Yar,Shanya da Sabon Garin Alhaji Yahuza da sauran Garuruwan Dake makwabtaka da ita babbar Rugar.
A cikin shekarar 1972 Gwamnatin Jihar Arewa ta Tsakiyav( North Central State) ta karbe duk Makarantun da Asibitocin Dake hannun Mishan, ta mayar dasu karkashin kulawarta, wanda wanda wannan doka ta shafi Asibitin babbar Ruga da Makarantar Mishan ta babbar Ruga. A halin yanzu Asibitin babbar Ruga ta koma karkashin ( Federal Ministry of Health) da sunan National Ostetric Pasula Centre.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.