Ticker

6/recent/ticker-posts

Taron Farfado Da Al'adun Hausa

Taron Farfaɗo Da Al'adun Hausa
Taron Farfaɗo Da Al'adun Hausa
Assalamu alaikum da fatan muna lafiya. Kamar yadda muka sani cewa" haɗaɗɗiyar wannan ƙungiyarta mu ta shafin Wasof mai suna Ƙungiyar Masu Ƙishin Harshen Hausa Da Al'adunta Ta Nijeriya, Reshen Jihar Jigawa wanda mai martaba Sarkin Gumel HRH Ahmad Muhammad Sani II yake jagorantarta.

Ƙungiyar tana sake sanar da jama'a cewa" za ta gudanar da gagarumin taronta a karon farko domin farfaɗo da al'adun Hausawa tare da ɗabbaka harshe da adabi.

Wannan taron kamar yadda wasu daga cikin mu suka sani, ba kamar sauran karabitin taro ba ne don an riga an tanadi manyan maliman ɓangarorin Hausa waɗanda za su jagaranci taron kamar haka;
Ɗan galadiman Farfesa: Assoc. Prof. Sa'adu Mu'azu Kudan da ke Jami'ar Kafin Hausa ta nan Jigawa da Dr. Binta Umar Usaini da Dr. Musa Isah Abubakar duka sun biyun daga JSCOE Gumel sai kuma Dr. Hassan Dauda Kwalam daga JSCILS Ringim, duk domin su gudanar da jabawai tare da muƙalolin da za su yi laccoci akansu a wannan lokacin sannan kuma za a aiwatar da wasannin gargajiya ga ɗaliban makarantun Sakandire da na Firamare da kuma takwarorin ƙungiyoyin Hausa a wajen taron.

In sha Allahu za a yi taron kamar haka;
Rana: Asabar 22/2/2025
Lokaci: 10:00 Na marece na safe daidai ban ruwan dawakai.
Wuri: Gumel Emirate Foundation, Ɗakin Taro Na Sarkin Yaƙi.

Daga ƙarshe muna farin cikin gayyatar kowa da kowa, kama daga kan Iyayen ƙasa Sarakuna da Hakimai da Dandalamu da Malimai da ɗalibai da abokan karatu da na abokan arziki da shugabanni da jagororin ƴan siyasa da Jami'an tsaro da ƴan kasuwa da masu gidajen Rediyo da sauran al'umma masu sha'awar koyo da jin harshen Hausa da al'adun domin su amsa gayyata. Allah ya ba da ikon zuwa ya sa albarka a cikin wannan taron namu.





Post a Comment

0 Comments