Ticker

6/recent/ticker-posts

Asibitin Farko A Garin Birnin Magaji

"Birnin Magaji an yi mata Asibiti,
Amma na ji  Malamin ya na hwaɗin ba aiki, ba aiki.. 

Haka☝️ Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi ke cewa a cikin faifansa na Ɗan Tauri Ibrahim Twasshi Birnin Magaji, Jihar Zamfara. Wannan☝️ ita ce Asibitin da ya ke nufi.

An gina ta a cikin shekarar 1963 a matsayin ƙaramin ɗakin shan magani (Dispensary), ita ce cibiyar kiyon lafiya ta farko da Gwamnati ta fara ginawa a garin Birnin Magaji. Duk da samuwar babbar Asibiti a garin (General Hospital) da ta soma daga Cibiyar Kiyon Lafiya ta karkara(PHC) ya zuwa yau ana amfani da wannan wuri domin gudanar da wasu ayyuka na kiwon lafiya da ma wasu lamurra na rayuwar al'umma.

Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara.
08149388452, 08027484815.
birninbagaji4040@gmail.com
Alhamis, 20/02/2025.

Post a Comment

0 Comments