1.
Wai me ya sa ne shi so in ya shiga,
2.
Duk ƙoƙarinka na son ka dakushe-
Shi, sai ya ƙara fure da jijiya.
3.
Ko da an sare har bishiya tasa,
Kwana kaɗan ya dawo kamar jiya.
4.
Duk yadda kasso ka bilƙiye masa,
Ya fi ka naci jure wa bibiya.
5.
Gurbi yake yi a cikin zuciya,
Ko za a korai sai ya yi dagiya.
6.
In ma an toge an ka ƙi maida shi,
Kufansa dai yana nan a zuciya.
7.
Dole ne sai an nemi madadi nai,
Kana ai samun zama na lafiya.
8.
To a nan kuma saƙar gizon take,
Zai wuya ya zamo cif da naj jiya.
9.
Ko dai ya kasa ko fin na baya ɗin,
Duk biyun matsala ne ga zuciya.
10.
Bai kai na farkon ba taƙ ƙi gamsuwa,
In ya fi wancan girma ta sha wuya.
11.
Wuyar ciko gurbin ko ko buɗuwa,
Kun ga dai an wahalshe ta gaskiya.
12.
Shi ya sa ni dai kam nake ganin,
Kan shiga ruwa zai kyautu a tsaya.
13.
A gane yaya zurfinsa don gudun,
Abin da ka je kuma yai waiwaya.
14.
Don kar buƙatar ceto ta bijjiro,
A inda masu fito ba mutum ɗaya,
15.
Ga ruwan kuma har ya wuce wuya,
To kun ga ya zam tilas a dulmiya.
16.
Ga dan misali da za ni baku shi,
Ciki da tarin darussa ku bibiya.
17.
Ku marmatso, kusa ku tsaya ku ji,
Zan baku labarina na gaskiya.
18.
Da ni ya faru silar masoyiya,
Da mukka yi soyayyar ƙuruciya.
19.
Shekaru ashirin yanzu an kusa,
Tun ban fi sha bakwai ba a duniya.
20.
Ita ko ba ta zarce wa sha biyar,
A shekaru ba, kusan kanmu ma ɗaya.
21
Kamar da wasa sai mukka tsunduma,
Kogi na so ƙauna mun yi sulmiya.
22.
Muna ta ninƙaya babu ji gani,
Ba ma tunanin gaɓa mu waiwaya.
23.
Mun sakankance babu fargaba,
Mun aminta da junanmu bai ɗaya.
24.
Ba mu jin da akwai wanda zai raba,
So muke yi wa juna da gaskiya.
25.
Ruwan wasiƙu safe da yammaci,
Tunda loton duka ba mu da waya.
26.
Haɗuwa ba ta yi mana wahala,
Aji guda muke a islamiya.
27.
Wataran ma a tare mu ke zuwa,
In za mu dawo hanyarmu dai ɗaya.
28.
Ni nake a tudu ita gangare,
In na fito kan hanya nake tsaya.
29.
Na yo jira, ta zo don tarar da ni,
Kana in ta iso sai mu rankaya.
30.
Alhamis da juma'a sukaz zamo,
Ranakunmu na zance ku zam jiya.
31.
In na aika ba a taba yin hanin,
Ta zo garan mu zanta ba ko ɗaya.
32
Babban gida da ya tare bangaro-
Ri, irin namu na 'yan gargajiya.
33.
Kofar gidansun nan ne muke zama,
A ƙarƙashin bishiyar darbejiya.
34.
Ni da aminan nan nau Muddassiru,
Ko Harisu wanda muke gida ɗaya.
35.
Iya sanina ban je ba ni kaɗai,
Sai dai aboki yai mini rakiya.
36.
Cikin nishaɗi hirarmu mui ta yi,
Goman dare kadadarmu gaskiya,
37.
Mui sallama, ta shige cikin raha,
Muma mu kamo hanya ta tafiya.
38.
Kafin mu kwanta hirar mu bibiya,
Da tsokanar juna mui ta dariya.
39.
Kwatsam ana haka rannan sai na ji,
Abin da ban tsammani ba ko ɗaya.
40.
Ƙiris in yanke jiki in fadi ƙas,
A take na ji yanayin hajijiya.
Cigaban na nan zuwa....🖊️
A dakace mu!
© ALIYU USMAN KURINGAFA.
AL'USKUN WAƘA.
Juma'a 06/12/2024.
Imel: alusku12@gmail.com
Lambar Waya: 07067717013/08024502520
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.