1.0 Shimfiɗa
An haifi Alh. Haruna Uji a Unguwar Gandun sarki dake cikin garin Hadejia, a shekarar (1946). Sunan Mahaifinsa Mallam Ibrahim, Malami ne kuma shine Limamin Gandun sarki. Sunan Mahaifiyarsa Zainabu itama mutumiyar Unguwar ce. Anan ya tashi yayi wayo. Yana kimanin shekara shida mahaifinsa ya sakashi a makarantar Allo dake kofar gidansu, a gun wani Malami da ake kira Mallam Alhaji.
Haruna Uji ya shafe wajen shekaru uku yana wannan Makaranta
a Gandun sarki, daga nan suka tashi da malaminsa zuwa garin Birniwa wanda take
gabas da Hadejia, mai nisan kilo mita 45. Sun kwashe shekaru kamar biyu suna
karatu da sauran Almajirai, anan Uji ya samu karatu mai dama.
Bayan nan suka bar Birniwa suka dawo Hadejia suka ci gaba da
karatu a Gandun sarki. Wannan yasa ya samu karatu mai dama fiye da sauran yara
musamman wadanda suka zauna a gida basu fita wani guri neman Ilmi ba. A wannan
lokaci Mallam Alhaji yakan sa Uji ya kula da yara tare da koya musu karatu.
Haruna Uji ya bar makarantar Allo yana dan shekara goma sha biyu, bayan ya samu
karatu mai dama.
Hadejia A yau!
1.1 Asalin Inkiyar Haruna Uji
Sunansa na yanka Haruna, yaci sunan wan Mahaifinsa, wato
Mallam Haruna. Mallam Haruna mai sunan Uji yana da mata mai suna IYA KURA,
Lokacin Uji yana karami matan kanin Babansa suna masa wasa suna ce masa Mijin
Iya Kura, Mijin Iya Kura’ A wannan Lokacin yara kannensa basu da baki, sai suke
ce masa, Ujin Iya Kura. Maimakon Mijin Iya Kura. Wannan shine Asalin inda
Haruna Uji ya samo Inkiyar Uji. Tun ana danganta sunan da Iya Kura har aka
daina ake cewa Uji.
1.2 Siffar Haruna Uji
Haruna Uji baki ne, mai matsakaicin tsawo, yana da jiki
matsakaici, ga farin hakora da bakin gashi, yana yawan barin gashin baki, ga
magana (Idanu) haka kuma, ma’abocin barin suma ne, yana da Murya mai zaki da
kauri kadan, kuma Gwanin Ado ne, da manyan kaya na sarauta. Kuma yakan saka
‘yar shara, musamman lokacin zafi.
Alh. Haruna Uji mutum nd mai fara’a da kyauta, domin abin
hannunsa bai rufe masa ido ba. Yana da raha sannan kuma bashi da wata nakasa a
fili.
2.0 Sana’oin Haruna Uji
2.1 Farauta Da Noma
Bayan Haruna Uji ya bar makarantar Allo, ya fara zuwa Daji
da nufin farauta. Wadda itace sana’arsa ta farko, wanda ya fara, kuma ta
sanyashi jarunta inda ya zama bashi da tsoro. Kuma a nan ne ya samu tambaya
wato lakani na tsare kai.
Bayan farauta Haruna Uji Manomi ne, ya fara aikin gona ne da
taya mahaifinsa, domin neman tabariki, wannan tasa yasan harkar noma wanda har
yake noma gonar kansa.
2.2 Sana’ar Tukin Mota (Direba)
Alh. Haruna Uji yayi Sana’ar Tukin mota, wanda ya fara da
Yaron mota a gun Mai gidansa wanda ake kira da suna Jibrin Dan Amingo. Jibrin
Dan Amingo dan Asalin Danbatta ne ta Jihar Kano. Haruna Uji ya shafe shekaru da
dama yana sana’ar yaron mota. Tukin mota ne sana’arsa ta farko da ta fara fitar
dashi wani gari da nufin zama. Suna aiki ne tsakanin Kano da Hadejia.
Kuma a wannan lokacin suna zaune ne a garin kano a Tudun
wada. Amma duk abinda ya taso a gida dashi akeyi, musamman aikin gona da
bukukuwa da sauransu.
2.3 Sana’ar Waka
Haruna Uji bai gaji waka ba, domin Mahaifinsa Malami ne,
kuma ko a waƙarsa
ta Gurmi ba Haramun ba yana cewa:-
“Ni Haruna dan Mallam nake, Waka ta ba ta gado bace”
Saboda haka tun farko Haruna Uji ya riki waka ne a matsayin
nishadi, domin ba wanda ya koya masa waka a matsayin Sana’a.
Haruna Uji ya fara ganin Gurmi ne a gun wani ma’aikacin titi
wanda sukayi aiki a hanyar Mallam madori zuwa Gumel, wanda ake kira Dan-mato, a
gun Dan-mato Uji ya fara ganin Gurmi da kidansa, shi Dan-mato yana kada Gurmi
ne a yayinda suka samu hutun aiki. Yana kadawa yana waka, lokacin Uji yana
Matashi, duk lokacinda sukaje kallon aiki sai su tsaya suna ganin kidan Gurmin
Dan-mato, wannan tasa kidan Gurmi ya shiga ran Haruna Uji, idan ya dawo gida
sai yakan nemi gwangwani da tsirkiya ya hada Gurmi yana kadawa. Har Dan-mato
suka hada aikin hanya bai koyawa Uji Gurmi ba, sai dai Uji yana zuwa yana ganin
yanda yake kadawa. Wannan tasa Uji ya dinga kwaikoyon Dan-mato tun bai iya ba
har ya koya.
Wannan yasa idan yana gurmi yara sukan tsaya suna ji da
kallonsa, Wannan shine Asalin koyon Gurmin Haruna Uji. Daga nan sai ya fara
tunanin ya samu sanda, da lilo da butar Duma da fatar Damo da Zobe domin ya
hada bubban Gurmi.
Farkon lokacinda ya fara Gurmi idan an bashi abu baya karba,
don yanayi ne saboda Nishadi. Kuma sau da yawa idan ya fito hira ko ana wani
biki na samari da ‘yan mata, yakan kada Gurminsa yana waka, samari da ‘yan mata
suna kallo.
A wancan lokacin yana Gurmi yana aikin Mota, wannan yasa ya
fara Gurmi a garuruwa daban daban na Arewacin Nigeria.
Daga nan Uji ya bar tukin mota ya koma kidan Gurmi Kuma ya
nemi mataimaka don sunayi su biyu.
A lokacin Gwamnan Kano Abdu Bako, sai yaji labarin Haruna
Uji, sai yasa aka nemoshi domin yayi masa waka akan wayar da kan Al’umma akan
Noma. Saboda haka Gwamna Abdu Bako sai ya hadawa Haruna Uji kayan wasa, kamar
Amsa Kuwwa (Loud speaker) da Abin Magana wato (Microphone) da Injin wuta, wato
Generator.
Wannan shine lokaci na farko da Haruna Uji ya fara waka da
kayan wasa na zamani, kuma ya kama yin waka gadan gadan a matsayin sana’a.
Waƙar da yayi a lokacin Itace waƙar Noma. An yiwaƙar ne da nufin wayar da
kan Talakawa su koma Aikin gona.
3.0 Waƙoƙin Haruna Uji Na Farko
Alh. Haruna Uji yayi waƙoƙi masu tarin yawa, kuma a cikin Jerin waƙoƙinsa
ga wasu daga cikin waƙoƙin da ya fara yi.
1. Waƙar Naira da kwabo sabon kudi.
2. Waƙar Gudaliya.
3. Waƙar Shamuwa.
4. Waƙar Noma.
5. Waƙar Bakar Rama.
Waɗannan
sune kusan Shahararrun waƙoƙin da ya fara yi.
3.1 Ajin Haruna Uji a tsakanin Mawakan baka.
A cikin wani Littafi da Ibrahim Yaro Yahya da Abba Rufa’i
suka tsara, Mamuda Aminu ya kawo rabe-raben Mawakan baka zuwa rukunai kamar
haka:
1. Mawakan Sarakuna
2. Mawakan ‘yan mata
3. Mawakan Jama’a
4. Mawakan Mafarauta. Da sauransu.
Ya kawo misalin Mawakan Jama’a shine wanda zai yiwa Sarakuna
da ‘yan kasuwa da ‘yan mata da Masu kudi da talakawa waka. Misali Mamman shata
da Haruna Uji da sauransu.
Hakan ta nuna cewa Haruna Uji ya kasance a cikin Mawakan
Jama’a, domin ya tabo duk abinda aka zayyana a sama. Wato yakan yiwa kowa waka.
3.1.1 Dangantakar Haruna Uji da Mawakan Baka
Alh. Haruna Uji yana da kyakkyawar dangantaka da sauran ‘yan
uwansa mawakan baka, yana girmamasu shima suna girmama shi, sannan ya hori wasu
suma sun zama shahararrun mawaka a kasar Hausa. Yayiwa wasu waka kuma shima
wasu sunyi masa. A cikin mawakan da suka masa waka har da Alh. Mamman shata,
kuma shima Haruna Uji yayi wa Alh. Garba sufa waƙar Ta’aziyya bayan ya mutu.
3.1.2 Jerin wasu daga waƙoƙin
Haruna Uji
Bayan rukunin waƙoƙinsa na farko, ga wasu daga cikin waƙoƙin da
ya yi.
1. Waƙar Dankabo
2. Waƙar Alh. Sani Likori
3. Waƙar Direban Chiyaman
4. Waƙar (Air vice marshal) Ibrahim Alpha
5. Waƙar (kwamishinan ‘yan
sanda) Daudu Gwalalo
6. Waƙar Haruna karamba
7. Waƙar Adamu Hassan Abunabo
8. Waƙar Ahmed Aruwa
9. Waƙar Asabe Madara
10. Waƙar Amadu koloji makwallah
11. Waƙar Bako Inusa kano
12. Waƙar Balaraba
13. Waƙar Jimmai Aljummah
14. Waƙar Birgediya Abdullahi shalin.
15. Waƙar Dankamasho
16. Waƙar Fulanin Jebbi fulato
17. Waƙar Idiyo Mai kayan Babur
18. Waƙar Kainuwa.
SAURAN WAƘOƘIN KU DUBA LITTAFIN
Reference Haruna Uji mobile app
A.H Rasheed
27/06/2019
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.