RAMZI NA ABAJADA MAGHRIBI
Daga
A.B. Yahya
ABAJADA
NA HARSHEN LARABCI
Haruffan Harshen Larabci su ne ake kira Abajada na Larabci. A makarantun allo na ƙasar Hausa a da da su ne ake fara koyar da ‘yan makaranta karatu da rubutun Arabiyya/Larabci da Alƙur’ani. Karatun akan yi shi ne musamman da Harshen Hausa ko Fulfulde da yake su ne suka fi ƙarfi a ƙasar Hausa, amma wannan bai hana yin karatun da wani harshe kamar Zabarmanci ba idan wurin da ake yin karatun harshen ya fi ƙarfi. Waɗannan harsuna an ambace su don su ne suka fi daɗewa a wannan ƙasa. Babu matsala idan ‘yan makaranta ba su iya harshen da ake kiran Abajadan saboda ƙanana ne kuma muhimmin abu shi ne yaro ya fahimci harafin da ake nufi idan aka ambace shi ko aka rubuta shi ya kuma iya rubuta shi. Ga dai harufan a tsarin da ake kira Maghribi wanda kuma ake amfani da shi a ƙasar Hausa da ma faɗin Afirka ta Yamma
ب أ
ص ن م ل ك ي ط ح ز و ه د ج ش غ ظ ذ خ ث ت س ر ق ض ف ع
Ga kuma yadda ake rubuta waɗannan
haruffa cikin rubutun Boko:
b ʾ
ṣ n m l k y ṭ ḥ z w/u h d j
sh gh ẓ dh kh th t s r ƙ ḍ f ʿ
Su kuma waɗannan
haruffa, wato Abajada, da aka rubuta alƙalamin
ƙidaya a ƙarƙashin kowane harafi, ana nufin adadin
kowane harafi ne. Misali, alifi adadinsa ɗaya
ne, ya
adadinsa goma ne, har dai zuwa sha wadda take da adadin dubu.
To da wannan adadi ne mawaƙa kan yi amfani su ƙirƙiri
abin da ake kira ramzi. Ramzi fannin ilmi ne da ake iya ambaton tarihi ko yawan
abu musamman waƙa ko
yawan baitocinta. A cikin waƙar
Daliyya wadda Shehu Usmanu ya rubuta ya yi amfani da ramzi a baitin waƙar na ƙarshe
(da Laraci) wato na 63, ya ce ƙasshin
ba’ada
fahhin
. A rubuce cikin Larabci haruffa ‘ƙ’, da ‘sh’, da ‘fa’, da ‘h’ su ne za a gani. Idan aka tattara
adadinsu, wato, da 100 da 1000 da 80 da 8, za a samu 1188, wato ke nan lokacin
da Shehu ya rubuta waƙar
shi ne Hijira tana 1188 wadda ta yi daidai da shekara ta 1774 Miladiyya. Wato
Shehu yana ɗan shekara ishirin ya rubuta waƙar domin an haife shi a 1754. Ramzi na
tarihi ke nan.
Haka kuma mawaƙa kan yi amfani da ramzi domin su faɗi yawan baitocin da waƙarsu ta ƙunsa. Misali, Alhaji (Dr.) Aliyu Namangi a baitin waƙarsa, Tsarabar Madina’ y ace,
150. To adadin baitin
kau naƙin
Hamsin ne da ɗari tak kwana
Wato da
nunu, ‘n’ da ƙa ‘ƙ’ ne ramzin abin da
ke ba da 50 da kuma 100, wato 150. Mai karatu ko saurare ko da ɗangon farko na wannan
baiti ya ji zai gane cewa baitocin waƙar 150 ne.
Ga
jadawali wanda ke nuna adadin kowane harafi:
ل |
ك |
ي |
ط |
ح |
ز |
و |
ه |
د |
ج |
ب |
أ |
30 |
20 |
10 |
9 |
8 |
7 |
6 |
5 |
4 |
3 |
2 |
1 |
خ |
ث |
ت |
س |
ر |
ق |
ض |
ف |
ع |
ص |
ن |
م |
600 |
500 |
400 |
300 |
200 |
100 |
90 |
80 |
70 |
60 |
50 |
40 |
ش |
غ |
ظ |
ذ |
1000 |
900 |
800 |
700 |
Mawaƙa kan ƙirƙiri kalmomi masu ma’ana ko marasa ma’ana cikin amfani da ramzi. A zamanin Shehu Usmanu ɗan Fodiyo, har ma a yau, mawaƙa kan ƙirƙiri kalmar da za ta bayar da ma’ana mai dangantaka da Musulumci. Misalin kalmar da aka fi amfani da ita a matsayin wani ɓangaren ramzi ita ce, ‘rushdu’, wadda ke nufin ‘shiryuwa’. Wato ko bayan adana tarihi da mawaƙi ya yi cikin baitin waƙarsa, ya kuma yi nuni da zamanin hidimar da suke yi ga Musulumci, domin wannan Kalmar Fannu ce da ke nufin Addinin Musulunci.
Wani tsari ko salo mai
dangantaka da asalin ramzi shi ne yadda wasu mawaƙa
kan ambaci sunansu ta hanyar tsara harufa ko gaɓoɓin
suna. Misali idan sunan mawaƙi
shi ne Umaru, sai mawaƙin
ya kawo gaɓoɓi
ukun da sunan ya ƙunsa,
kamar yadda Alhaji Dr. Umaru Wazirin Gwandu ya yi cikin wannan baiti:
50.Wanda
yay yi waƙa sunanai
‘U’ da ‘Ma’ da ‘Ru’ ga mazamninai
Sai ka zo ka ‘Bi Ke’ birninai
Nasarawa can kaka komawa
(Wazirin Gwandu: Zaɓaɓɓiya).
.
Shi kuwa Alƙali Alhaji Haliru
Wurno da zai faɗi sunansa sai ya yi
amfani harufan sunan kamar yadda ake faɗar su cikin Larabci kamar haka:
49
Mai biɗat sanin ma’ajin waƙa
‘Ha’u’
‘Dadu’ ‘Ra’ shi yas sarƙa
Wurno
ag garinsu gida haƙƙa
Fassararsa
Alhaji Ishraƙa
Ko da yaushe bai rasa shiryawa
(Alƙali Alhaji Haliru
Wurno: Tura Ta Kai Bango).
Ɗangaladiman Wazirin
Sakkwato Junaidu, Alƙali Bello Giɗaɗawa ya yi amfani da tsarin ramzi ya bayyana
yawan baitocin da waƙarsa ta ƙunsa:
24. Daɗa waƙag ga ta cika na
tsaya nan
Yawan baiti KADA don
kak ka dabke
(Alƙali Bello Giɗaɗawa: A BI GASKIYA AD
DAIDAI)
Kalmar sunan naman ruwa, wato kada, mai harafi biyu, k da d su su ne adadinsu da 20 da kuma 4, wato 24.
MANAZARTA
Giɗaɗawa, A. M. B. (2006) Bargon Hikima. Sokoto: Cibiyar Nazarin
Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, sh. 45, bt. 24, ɗg. 2.
Gwandu,
U. N. W. (2006) Wa’azu Gonar Malam. Sokoto:
Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, sh. 50,
bt.50, ɗg. 2.
Hiskett,
M. (1975), A History of Hausa Islamic Ɓerse, London.
Wurno, A. A. H.Diwanin Waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno wanda mai muƙalar nan ya mallaka.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.