Cite this as: Ɗangulbi, A. R. (2024). Zuga Da Habaicia Wakokin Zamani: Nazari a kan wasu waƙoƙin siyasa na Muhammadu Buhari a Jumhuriya ta huɗu [Kundin digiri na uku wanda ba a wallafa ba]. Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria.

ZUGA DA HABAICI A WAƘOƘIN ZAMANI: NAZARI A KAN WASU WAƘOƘIN SIYASA NA MUHAMMADU BUHARI A JUMHURIYA TA HUƊU

NA

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

A THESIS SUBMITTED TO THE SCHOOL OF POST GRADUATE STUDIES, AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA IN PARTIAL FULFILMENT OF THE REQUIREMENTS FOR THE AWARD OF DOCTORATE DEGREE IN AFRICAN LITERATURE (HAUSA) DEPARTMENT OF AFRICAN LANGUAGES AND CULTURES, FACULTY OF ARTS AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA, NIGERIA

SATUMBA, 2024

BABI NA HUDU

HABAICI A WASU WAƘOƘIN SIYASAR MUHAMMADU BUHARI A JUMHURIYA TA HUDU

4.1. Gabatarwa

Babu shakka nazarin habaici cikin waƙoƙin siyasa, musamman waɗanda aka yi wa Muhammadu Buhari, wani fage ne da yake buƙatar a faɗaɗa bincikensa don ƙara fayyacewa tare da fitowa da irin fasaha da hikimar da Allah ya albarkaci wasu zaɓaɓɓun mutane ta fuskar bunƙasa adabi, da harshen Hausa. Masana da manazarta sun yi bayanai daban-daban dangane da ma’anar habaici.

Masana sun tabbatar da cewa, amfani da habaici a cikin waƙa wata dabara ce da mawaƙan Hausa ke amfani da ita wajen jawo hankalin masu sauraro domin isar da saƙon waƙoƙinsu cikin hanzari da nishaɗi. Domin kuwa, shi habaici salo ne da ke ƙara fayyace fasahar mawaƙi, tare da jawo hankalin masu saurarensa su fahimci saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Wannan dalili ne ya sa ake cewa, habaici shi ne adon waƙa, domin kuwa duk mawaƙin da ba ya amfani da habaici, to sai a ɗauke shi ba shi da fasaha ko dabarar jawo hankalin masu sauraren waƙarsa (Yahya, 2001, P.34). Akan ce, wannan mawaƙi ba shi da fasaha. wato ba shi da dabarar jawo hanlkalin masu saurarensa, har su gamsu da saƙon da yake isarwa gare su. Mutane sun fi sha’awar waƙar da ke cike da habaici bisa ga wadda ba ta da habaici. Haka kuma duk mawaƙin da ke amfani da habaici a cikin waƙarsa jamaa sun mai da hankali ga sauraren waƙarsa. Sannan habaici yana taimakawa masu saurare su fahimci cewa, ba ana yin habaici domin samar da nishaɗi kawai ba, a’a habaici hikima ce ta fasaha da ke saka masu sauraren waƙa su ƙara zurfafa tunaninsu wajen warware kowace irin matsala ta tunkare su a bangaren zamatakewar al’umma ta yau da kullum da sauransu. Da wannan dalili ne ya sa manazarta irin su (Leech, 1969, P.47], yake ganin ba wani abu ne ke sanya waƙa ta yi armashi ba, ta kuma sanya mawaƙa su shahara, illa amfani da habaici a cikin waƙa da kuma a maganganun yau da kullum. Habaici yana daga cikin zantuttuka na hikima da mawaƙan siyasar zamani suke amfani da shi wajen jawo hankali da faɗakar da al’umma su san wani abu da ba kasafai za su san shi ba,sai lokacin da mawaƙa suka faɗakar da su cikin waƙoƙinssu.Wannan shi ne ke sanya mawaƙi ya zamo fitacce a cikin sana’ar waƙarsa,har ya sa masu sauraro su riƙa shauƙin sauraren waƙoƙinsa, tare da duba da idon zuciyarsu, su riƙa jin cewa abin da mawaƙi ya faɗa, za a iya kallon sa da idon nazari, kamar haka:

4.2. Habaici a Matsayin Salon Faɗakarwa

Habaici wani salo ne da mawaƙan siyasar zamani ke amfani da shi mai ƙunshe da jigon faɗakarwa da ilmantarwa da kuma nishaɗantarwa ga masu sauraren waƙoƙinsu. Habaici yana ƙara wa waƙa armashi da ɗauaka darajar mawaƙan Hausa, musamman na siyasa (Ɗangulbi 1996:). Ya ƙara da cewa, duk waƙar da ba ta da habaici a cikinta, tamkar miya ce ba gishiri. Mawaƙa suna amfani da habaici domin su isar da wani muhimmin saƙo zuwa ga alumma a kan wani sabon abu da ya ɓullo da ake buƙatar a wayar masu da kawunansu. Habaici shi ne furta magana ta ɓatanci ko ɓaci a kaikaice domin a muzanta ko ƙasƙanta wani ko wasu mutane a ba su shiri tsakaninsu da mai waƙa ko zuwa ga wasu abokan hamayya. An nazarci habaici ta waɗannan fuskoki kamar haka. Misali,

4.2.1.Habaici ta Fuskar Mulkin Siyasa

Da yake ana magana ne a kan habaici, za mu ga abin da mawaƙa suka ce a cikin waƙoƙin da suka yi wa Muhammadu Buhari dangane da yabon gwagwarmayarsa ga samar da mulkinsiyasa mai ɗorewa a Nijeriya. Kamar yadda aka sani, mulkin siyasa (dimokuraɗiyya) wani salon mulki ne da ke bai wa ‘yan ƙasa ‘yancin walwala da damar faɗar albarkacin bakinsu.Wato, talakawa suna da damar su faɗi ra’ayinsu game da yadda shugabanni suke gudanar da harkokin mulkinsu.Mulkin duk da ba a sami ‘yancin walwala da damar faɗar albarkacin baki ba,to ya zama mulkin kama-karya ko salon mulki irin na soja. Misali, a cikin waƙarsa ta A.P.C., Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana cewa:

Jama’a a gare ku na yi kira,

Ga kanya kar ku ɗau ɗinya.

 (Kamilu koko: Waƙar APC 2015).

 

Wannan ɗan waƙa yana ɗauke da habaici mai jigon faɗakarw game da muhimmancin mulkin farar hula,wanda ya bambanta da salonmulkinsoja.Mulkin farar hulasalon mulki ne da mutane ke zaɓen wanda suke so ya jagorance su a gwamnatance.Mulki ne da ke bai wa kowane ɗan ƙasa damar faɗin albarkacin bakinsa. Mawaƙin ya yi wa salon mulkin soja habaici inda ya ce ‘ga kanya kar ku ɗau ɗinya’. Ya yi ƙoƙarin kamanta abubuwa biyu masu alaƙada juna ta fuskar ɗanɗano domin ya bambanta mulkin farar hula da na soja ta fuskar ‘yanci da walwala.Bishiyarkanya da ɗinya, dukkansu itatuwa ne da sukan yi ‘ya’ya masu zaƙi, sai dai na kanya sun bambanta da na ɗinya wajen launi da ɗanɗano.

Bargery (1993:558), ya bayyana ‘Kanya ko kaiwa’{African ebony tree}da cewa, itaciya ce mai ‘ya’ya masu zaki, kuma ‘ya’yanta sukan kasance masu launin rawaya,idan ta nuna. Ita ɗinya {The spur-winged goose},wata itaciya ce mai yin ‘ya’ya kamar kanya. Sai dai ya’yanta sukan kasance da launin baƙi, wanda shi ne alamar ƙosawarta ko nunarta. Mawaƙin ya yi amfani da waɗannan itace ne, ya gina habaicinsa don ya yabi mulkin farar hula a idon jama’a; a lokaci guda kuma yake sokar salon mulkin kama-karya irin na soja.Yadda ya nuna banbancin da ke tsakanin tsirrai masu amfani ga ɗan Adam, haka ya nuna wa jama’a bambancin mulkin farar hula da na soja..Wato ko a cikin itace wani ya fi wani daraja, balle ma a tsarin shugabancin al’umma. Wannan habaici faɗakarwa ce zuwa ga mutane don su fahimci irin alherin da mulkin siyasa yake kawowa ga al’umma wajen kawo cigaba ta kowane fanni, idan aka zaɓi shugaba nagari mai gaskiya da riƙon amana.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kamancen fifikodomin ya jawo hankalin masu saurare su fahimci alfanun mulkin siyasa wajen samar da ‘yanci da walwala da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da na al’umma.Ya kamanta itace biyu masu kama da juna da kuma amfani ga ɗan adam domin ya nuna ma talakawa muhimmancin mulkin farar hula a ƙasa. Wato,kanya da ɗinya, waɗanda suka bambanta ga daraja duk da kasancewarsu itace ne masu amfani ga ɗan adam.Don haka, kowane lokaci jama’ar ƙasa suna maraba da mulkin da ke ba su damar faɗar albarkacinbakinsu domin nuna wa shugabanni kurakuransu don su gyara.Wannan dabara ta isar da saƙo da mawaƙin ya yi amfani da ita, ta taimaka wajen isar da saƙon jamiyyar APC ga talakawa cikin sauƙi.Haka kuma Kamiluya ƙara da kawo kwatankwacin wannan habaici dangane da fifikon mulkin farar hula bisa ga mulkin soja ta fuskar ‘yancin faɗar albarkacin baki. Mawaƙin yana cewa:

Sikari da rake akwai zaƙi,

Wata kalma naku talakawa.

(Kamilu koko: Waƙar APC).

Bisa ga yanayin jin daɗin rayuwa, baki yana son ya ɗanɗani abi mai daddaɗan ɗanɗano kamar sikari. Domin duk daɗin rake ba ta kai sikari ba.Shi Sikari (sugar) ana samar da shi daga ruwan rake, wadda ake dafa tata koma maɗi, sannan, a yi amfani da wani sinadarin canza launi (Bleaching Chemicals),a canja launinsadaga maɗi (brawn suger) zuwa farin suga ko sikari da ake amfani da shi yau da kullum, (Ɗangulbi da wasu, 2022,P. 56) da Hira da Rilwanu Anka tsohon ma’aikacin kamfanin Sabana suga,a ranar Lahadi 26/2/2023). Ita kuwa rake ana shan ta ba tare da an tace ta ba. Sai dai zaƙinta ya banbanta da na sikari, kuma bata da wata illa mai cutarwa ga jikin ɗan adam. Wannan habaici da mawaƙin ya kawo a cikin waƙarsa ya nuna fifikon daɗin mulkin farar hula bisa ga na soja, kamar yadda ya bambanta zaƙin sikari da na rake. Don haka mulkin farar hula ya fi mulkin soja ta fuskar ‘yancin magana da walwalar al’umma.

A siyasance mawaƙin ya nuna cewa, komi daɗin mulkin soja, mulkin farar hula ya fi shi amfani ga jama’a, domin akwai ‘yancin magana da walwala. Saboda haka.mawaƙin ya yi wa mulkin soja habaici hannunka –mai- sanda, wato habaici gargaɗau domin ya faɗakar da su, muhimmancin mulkin farar hula ga talakawa. Mawaƙin ya yaba wa shugabanni masu gaskiya da riƙon amana, musamman Muhammadu Buhari dangane da irin jajircewarsa ga tabbatar da an tsayar da mutanen kirki a zaɓukan da suka gudana a lokacin da ya tsaya takarar shugabancin Nijeriya.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kamancen fifiko domin ya jawo hankalin ‘yan Nijeriya su iya rarrabewa tsakanin sukari a rake, duk da kasancewasu na kirki ne amma ɗaya ya fi ɗaya..Mawaƙin ya kamanta sukari da rake don ya fayyace bambancin zaƙinsu da kuma ɗanɗanonsu a baki da kuma amfaninsu a jikin ɗan adam.Wannan habaici da ya yi amfani da shi wata dabara ce ta isar da saƙo cikin sauƙi da saurin fahimta. Mawaƙin ya yi haka ne don ya nuna wa mutane irin bambancin da ke tsakanin mulkin siyasa da mulkin soja.

Shi kuwa Yusuf Fasaha a cikin waƙarsa dayayi wa jam’iyyar APC da Muhammadu Buhari, ya soki aƙidar wasu yan siyasa marasa kishin ƙasa.Ya ce, masu yaudara da matsayinsu ko addini wajen jawo ra’ayin talakawa su amince da su idan zaɓe ya zo,mutane ne da ba su gaskiya.Yana cewa:

“Tuni mu kam mun ƙara hankali,

Mahaukata ba sua yaudare mu ba”.

(Yusuf Fasaha: Waƙar Maja).

Mawaƙin ya yi amfani da habaici keɓantau inda ya ce,’mu kam’don ya nuna irin shirin da talakawa suka yi na ƙauracewa mulkin jari-hujja ko na kama-karya da soja suke yi.Ya soki ‘ya’yan jam’iyya mai mulki da ke da aƙidar mulkin kama-karya ko jari- hujja irin na soja alhali kuwa mulkin siyasa ne suke yi.Ga tsari irin na mulkin soja, ko jari-hujja duk wata doka da aka tsara mutane na ƙoƙarin bin ta sau da ƙafa domin kauce wa fuskantar hukumci mai tsanani. Saboda haka, sai shugabanni su riƙa amfani da matsayinsu su cilasta wa talakawa yin abin da ba zai yi masu daɗi a rai ba. Don haka, mawaƙin yana faɗakar da jama’a cewa, yanzu sun yi hankali shugabanni ba za su yaudare su da matsayin da suke da shi ba, su tilasta masu yin abin da ransu bai so ba. A siyasance dole ne a bar su, su zaɓi wanda suke ra’ayi. Mulkin siyasa, mulki ne da ke bai wa kowa damar ya bi ra’ayinsa ba tare da ƙuntatawa ba ko rashin tausayi,da walwala. Mulki ne da ke ba wa mutane damar tofa albarkacin bakinsu cikin harkokin mulki, inda talakawa za su faɗi ra’ayinsu. Amma mulkin soja ko na kama-karya yana takura wa al’umma don haka talakawa su yi watsi da tunaninsu na neman soja su karɓi mulki. Jama’a su zaɓi farar hula su ci gaba da mulki ta yadda talakawa zasu sami ‘yanci su faɗi ra’ayinsu, idan shugabanni ba su yi masu adalci ba.

Shi mulkin siyasa,wato farar hula, wani salon mulki ne da ke bai wa talaka ‘yanci ya faɗi ra’ayinsa, muddin bai gamsu da yadda ake gudanar da mulkin ba. Saboda haka mawaƙin ya yi wa sojoji habaici cewa, lokaci ya yi da za su koma bariki su bai wa jama’a dama su zaɓi mutanen da za su tausaya masu. Wannan ya nuna ma jama’a cewa, mulkin farar hula, mulki ne da jama’arƙasa suke maraba da shi; domin shi ke ba su dama, a dama da su. Mawaƙin ya ƙara da kawo wani ɗan waƙa don ya kare kansa ga maganar da ya yi game da banbancin mulkin kama-karya da sunan na farar hula (dimokuraɗiyya).Yana cewa:

 

“Har mu kauda ‘yan kama- karya,

A ƙasarmu an daina shan wuya”.

 (Yusuf Fasaha Kano: “Mu bi APC al’ummar ƙasa”.)

 

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Aminu Abubakar Ladan Alan waƙa, yana ganin ai a mulkin dimokuraɗiyya ake hauka. Wato a mulkin dimokuraɗiyya jama’a ke bin son rai har suna wuce gona da iri, wanda ya kwatanta shi da hauka. Ga abin da yake cewa:

“Cikin dimokuraɗiyya ake son rai, ake hauka”.

Son rai yana nufin son kai, ita kuma hauka tana nufin gushewar hankali. Alan waƙa ya danganta son rai da hauka a cikin mulkin soja ko na dimokuraɗiyya don ya bayyana irin illar da ‘yancin da dimokuraɗiyya ke ba wa mutane na faɗar albarkacin bakinsu har su wuce gona-da iri, su zama marasa biyayya ga hukumomi ko shugabanni. Wato dai mulki ne da ke sa talakawa su zaƙe ko su wuce gona-da- iri wajen maganganu har su kasance suna keta rigar mutuncin masu mulki, wanda Alan waƙa ya ce “hauka ne”.

Duk yadda mulkin soja ya faye tsanani da rashin bai wa talaka ‘yancin Magana, ya fi mulkin dimokuraɗiyya a fagen ladabtarwa da kariyar mutuncin masu gudanar da mulkin da sauran jama’ar ƙasa. Hausawa suna faɗin wata karin magana cewa, “Talaka zuma ne sai da wuta”, domin su yi masa habaic da cewa, bai wa talaka ‘yancin faɗar albarkacin bakinsa kan kawo ya wuce gona da iri, har ya zama tamkar mahaukaci a wajen faɗar ra’ayinsa ko yin maganganu da babu kai, babu gindi, wai shi yana da ‘yancin yin haka. Mulkin farar hula,yana da muhimmanci ga ƙasa don ta hanyarsa ne talaka kan san ‘yancinsa, sai dai kuma idan sanin ‘yanci ya yi yawa, to son rai da hauka kan biyo baya kamar yadda Alan waƙa yake hasashe.Airin wannan salon mulki na dimokraɗiyya ne Alan waƙa yake habaici ga masu mulki dangane da ‘yancin faɗar albarkacin baki,wanda yake, ga talakawa suna ne kawai, domin babu wani ‘yanci da ake ba talakawa da ake tunani suna da shi.Wannan ‘yanci da ake hasashe babu shi domin da zarar talaka ko ‘yan adawa ya faɗira’ayinsa, sai ka isko masu mulki sun sa jami’an tsaro sun yi awon gaba da shi.Wato, idan ka ga wani abu daba ka gamsu da yadda ake gudanar dashi ba, ka faɗi ra’ayinka, sai a yi amfani da ƙarfin mulki a musguna maka ko a kame ka a jefa ka gidan maza (kurkuku) har sai ka tagayyara ko ka nemi afuwa, sannan a sako ka, ka koma ga iyalanka.A nan ‘yancin magana bai yi amfani ba.

A nan mawaƙin ya yi amfani da salon sifantawa, inda ya sifanta mulkin kama-karya da mulkin siyasar zamani.Wato, salon mulkin da ya bai wa talaka’yanci da damar walwal a harkokin rayuwarsa ta yau da kullum, amma da zarar ya faɗi wani abu na ra’ayin kansa ga gwanati, sai ya zama abin farautar jami’an tsaro.Wannan sifantawa da mawaƙin ya yi wa mulkin siyasar wannan zamani da mulkin kama-karya, wata dabarar isar da saƙo ce ya yi amfani da ita don ya jawo hankalin mutane su fahimci cewa, shugabannin da suke mulki da sunan dimokuraɗiyya ba tsarin dimokuraɗiyya ne na gaskiya suke aiki da shi ba.Wato, akwai birbishin tsanantawa ga talakawa kamar yadda mulkin kama-karya yake a can baya.Ya yi amfani da wannan salo domin ya faɗakar da talakawa, ko masu kaɗa ƙuria su san cewa ana yi masu karan-tsaye, wato, kama-karya ne a wannan mulki da sunan dimokuraɗiyya,amma ba dimokuraɗiya ba ce;mulkin soja ne ko na jari-hujja da sunan dimokuraɗiyya.Har wa yau, Aminu Alan waƙa ya cigaba da cewa:

“A mulkin nan na al’umma

Na zaɓen ra’ayin kanka.

Mulki daga al’umma ake

Cikin zaɓe na son ranka

Ana yi don mutane ne

Misalin ba ka ‘yancinka

Amma kuma ko mulikiya

Ba ta yi kama haka hauka.

Ko tsarin gurguzu malam

Ya kai haka ba a tauye ka

Nm jari-hujja ake yi muna

Muƙami na saman doka.

(Alan waƙa: Guguwar sauyi ta zo).

 

Mulkin siyasa, salon mulki ne da ‘yan ƙasa ke samun dama su yi abin da suke so babu tsangwama da wulaƙanci. Amma in ya zama ba a bai wa talaka damar faɗar ra’ayinsa to fa ya koma tamkar mulkin jari-hujja yake irin na ƙasar sin (China) ko mulkin sojoji. A tsarin mulki irin na siyasa, mutane sun yarda da cewa, ‘yancin faɗar albarkaci baki da ake bayarwa ga ‘yan ƙasa wani abu ne da ya wajaba ga shugabanni.Wannan hasashe na ‘yan Nijeriya ya saɓa wa tunanin masu mulki: domin ‘yan siyasa suna laɓewa ga karsana su harbi barewa’. Ma’ana suna fakewa da ‘yancin da tsarin mulkin siyasa ya baiwa‘yan ƙasa,sucuta wa al’ummada rashinbasu‘yancin da tsarin mukin ya ba su.

Alan waƙa ya yi wannan tunani a cikin ɗiyan waƙa da suka gabata a sama. Ya kwatanta salon mulkin siyasar Nijeriya da mulkin kama-karya ko na jari-ujja, waɗanda ba su ba talaka damar faɗaralbarkacin bakinsa. Ko ma an ba shi dama, to idan ya faɗi wani abun da ya saɓa wa ra’ayin shugabanni, sai a saka jami’an tsaro su yi awon gaba da shi zuwa gidan yari ko wani wuri daba a san inda yakeba. Wannan ya nuna wa ‘yan Nijeriya cewa, ‘yancin magana da baki kawai ake cewa, amma babu wani abu ‘yancin magana, musamman ga ‘yan adawa da sauran jama’ar ƙasa. Masu mulki kawai ke yin yadda sukeso,kuma ba su bin abin da doka ta gindaya masu sai dai bin son zuciyarsu.Kaga a nan salon dimokuraɗiya ya koma mulkin kama-karya. Saboda haka ne mawaƙin yake faɗakar da al’ummar Nijeriya da su fahimci abin da dimokuraɗiyya take nufi domin su jajirce wajen nema wa kansu ‘yanci ta hanyar zaɓen mutumin da ya cancanta.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kamantawa ta hanyar kamanta salon mulkin siyasar Nijeriya da mulkin gurguzu ko na jari-hujja.Duk da kasancewa mulkin ya ba da damar talaka ya faɗi ra’ayinsa, hakan bai sa masu mulkin siyasar Nijeriya sun kula da wannan haƙƙi ba. A sanadiyar haka mawaƙin ya yi amfani da wannan salo don ya faɗakar da ‘yan Nijeriya su ɗauki matakin nema wa kansu ‘yanci; domin su tsira daga azabar mulkiirin na kama-karya ko na ‘yan jari-hujja ko na gurguzu da shugabannin Nijeriya ke yi wa talakawansu.Wato, mawaƙin ya kamanta mulkin da jamiyyar PDP take yi da na kama-karya ko jari-hujja.Don haha, sai mawaƙin ya yi amfani da salon kamantawa a cikin ɗan waƙarsa domin ya jawo hankalin talakawa su iya rarrabewa tsakanin mulkin siyasa da mulkin kama-karya irin na soja ko ‘yan jari-hujja

4.2.2. Habaici ta Fuskar Shugabanci da Shugabanni

Bargery{1993:944}, ya bayyana shugabanci da cewa, wani matsayi ne na wakilci da ake ɗora wa mutum bata hanyar yaƙi ba. Wato kowane irin matsayi aka ɗora wa wani mutum don ya wakilci al’umma, ko ya jagorance su ga tafiyar da al’amurransu na yau da kullum, shi ne ake kira shugabanci. Idris (2016:147), ya ce, shugabanci wani abu ne da ya shafi mu’amula ta yau da kullum, a inda mutum zai nemi taimako da goyon bayan sauran mutane domin ya sauke nauyin da aka ɗora masa.Shugabanci wani jagoranci ne da aka ɗora wa wani mutum ko wasu gungun mutane. Shugabanci na iya kasancewa na gargajiya, wato ta hanyar sarakunan gargajiya. Haka kuma yana iya kasancewa a kan tsarinsiyasa,wanda Turawan mulkin mallaka suka zo da shi (Ɗangulbi 2003:56). Wannan salon mulki shi ne wanda ke bai wa ɗan ƙasa damar ya zaɓi shugabansa da kansa, wanda zai ba shi dama ya faɗi ra’ayinsa a harkokin gudanar da shugabancin ƙasa.Wato, talaka ya faɗi albarkacin bakinsa wurin da yake ganin an yi ba daidai ba.Ko kuma yake ganin an yi abin da ya kamata.Wannan faɗar albarkacin baki kan iya zama kushewa ko yabo.Kushewa tana nufin ‘nuna aibu ko laifi game da wani abu’, Ƙamusun Hausa (2006:257).

 Tsarin shugabanci na kowace irin al’umma ya zama wajibi domin shi ne ke tabbatar da zaman lafiya da zai bai wa mutane damar su tafiyar da harkokin rayuwarsu ta yau da kullum cikin sauƙi da walwala. Idan babu shuganci a cikin al’umma, to akwai rikici da ruɗami da hargitsi a tsakanin mutane. Haka kuma dole a sami tashin hankali da cutar juna da zalunci, inda mai ƙarfi zai danne haƙƙin maras ƙarfi. Idan haka ya faru, sai al;umma ta shiga wani halin ni- ‘ya- su. Hakan zai sa talakawa su kasa samun walwala da ‘yancin fita su nemi abinci da arzikin ƙasa {Yakasai: 2012:51}. Dalilin haka kan sa mutane ko mawaƙan siyasa su riƙa kushe salon mulkin masu mulki ta hanyar yi masu habaici domin su faɗakar da su ga kurakuran da suke tafkawa don su gyara.

A cikin duniya, kowace al’umma tana da irin nata tsarin shugabanci. Wannan ya nuna cewa shugabanci wani nauyi ne da ake ɗora wa mutum domin ya taimaka wa al’umma wajen ƙwato masu haƙƙoƙansu. Shugabanci yana buƙatar cancanta da ƙwarewa kafin mutum ya zama shugaba. Cancanta tana nufin dacewa ga zama bisa wani matsayi, ko yin wani abu na al’ada ko shugabanci da mutane suka ɗora wa wani mutum.

Aminu (1987:), ya ce,.mulkin siyasa wani jagoranci ne na al’umma da ake zaɓen wakili daga cikin al’umma domin ya shugabanci mutanen da suka zave shi. Wannan salon mulki yana gudana ne a ƙarƙashin jam’iyun siyasa waɗanda ke da haƙƙin tsayar da mutanen da suka cancanta su wakilce su a muƙamai daban daban Ana la’akari da dacewar wanda aka zaɓa ga muƙami ko matsayi ko wakilcin da ake so ya yina jama’a. Da zarar an fahimci cewa, mutum yana da munanan ɗabi’u ko wata illa da mutane ke ƙyama, to a nan take sai a ƙi amincewa da waƙilcinsa. Daga cikin munanan ɗabi’u ko halaye da ke saka a ƙyamaci mutum har a ƙi zaɓensa, akwai rashin dangana da cuta da ƙeta da rashin cika alƙawari da kuma bayyanar da ayyukan baɗala a fili. Haka kuma akwai zamba da cin amanar ƙasa da ha’inci da sauransu.Ta hanyar duba da irin waɗannan halaye ne ake gane rashin cancantar wanda ake so a tsayar takara don ya wakilci al’umma a matakin kansila ko shugaban ƙaramar hukuma ko majalisardokoki ta jaha ko ta waklai ta ƙasa da ta dattijai da kuma muƙamin shugaban ƙasa.

Shugabanni su ne waɗanda aka ɗora wa nauyin jagorancin jama’a ta hanyar zaɓe ko naɗi. Wato shugaba shi ne wanda ke kula da al’amurran rayuwar al’umma. Ƙamusun Hausa, (2016,P. ), ya bayyana shugaba a matsayin mutum wanda ke kula da al’umma ko jagorar mutane, wanda aka zaɓa ko aka naɗa shi (ba a fagen yaƙi ba). Shugaba a taƙaice shi ne, wakilin jama’a ko jadani ko jami’i wanda mutune suka ɗora haƙƙin kula da al’amurransu nayau da kullum a kansa. Shugaba shi ne jadani da ke kula da kare lafiya da dukkan abin da zai cuta wa al’ummarsa. Ana buƙatar shugaba ya kasance mai kyawawan ɗabi’u da suka haɗa da gaskiya da riƙon amana da tausayi da sauransu.

Mawaƙan siyasa suna amfani da habaici domin su yi gargaɗi ko faɗakar da al’umma cewa, duk mutumin da bai mallaki irin ɗabi’un da aka ambata a sama ba, to bai dace a zaɓe shi ya wakilci jama’a ba. Aminu (1987:54), ya ce “Kyawawan ɗabi’u su ne makamin tabbatar da zaɓen wakilin jama’a nagari ga kowane irin muƙami na shugabanci”. Misali a cikin waƙarsa da ya yi wa Buhari a jam’iyar APP/ANPP, a shekara 1999 da 2003, Ibrahim Yala Hayin Banki, ya yi wa wasu shugabannin jam’iyar PDP habaici yana gargaɗin su dasu ji tsoron Allah a wajen gudanar da shugabancin jama’a.Jin tsoron Allah kan sa shugaba ya yi adalci tsakaninsada waɗanda yake shugabanta.Tsayar da gaskiya da adalci kan sa waɗanda ake mulki su ji tsoron shugabanni su kuma yi masu ɗa’a da biyayya ga umurnin da suka ba su. Ga abin da yake cewa kamar haka:

Duk wani wanda ba ya jin tsoron Rabbana

To mun daina girmama shi ya cuta mana

Mai rawani da jiniya Allah isar mana

Za mu buga da ku bana faɗin Nijeriya.

 (Ibrahim Yala:Waƙar APP/ANPP )

Tsoron Rabbana, wato Ubangiji wanda ya halicci kowa da komi, shi ne tushen jagoranci na gari. Rashin jin tsoron Allah shi ke kawo aikata cuta da ƙeta, saboda babu tunanen akwai ranar da za a yi hisabi.Idan shugaba ya cuta wa talakawansa, ko ya zalunce su lokacin da yake mulki, sai Allah ya cire wa mutane jin kunya da tsoron shugaban. Don haka ko ya shata doka ba a bin ta.Saboda haka mawaƙin yana ganin shugabannin jam’iyar PDP,da masu sarautun gargajiya a lokacin mulkin ‘yan jam’iyar PDP, sun zalunci al’ummar ƙasa ta fuskoki da dama. Saboda haka yanzu sauyi suke so don ƙasa ta zauna lafiya da ci gaban tattalin arziki.Ana buƙatar shugabanni su kasance masu tsoron Allah, wanda zai taimaka su fahimci cewa, duk abin da mutum ya aikata mai mulki ne ko ma maras mulki, to ya sani cewa, zai fuskanci sakamako ranar da shugaba ba shi da mafita, sai idan ya yi adalci a mulkinsa, wato ranar lahira. A siyasance mawaƙin yajawo hankalin shugabanni su saka tsoron Allah wajen gudanar da mulkinsu. Wato jin tsoron Allah shi kaɗai ne zai sa su gudanar da mulki cikin nasara tare da jawo wa kansu mutunci a idon talakawa; su riƙa girmama su. Saboda haka sai mawaƙin ya ƙara da cewa, to, a wannan zaɓe da za a yi sun rantse ba za su sake zaɓen shugabannin da ba su jin tsoron Allah ba. Rashin jin tsoron Allah ga shugabanni shi ne ummulhaba’isin aikata zalunci da cin amanar ƙasa. Don haka,abin so ga masu neman muƙami ko shugabanci na jama’a su kasance mutane masu tausayi da tsoron Allah, wanda zai sa mutane su zaɓe su, su kuma cigaba da girmama su.Ya cigaba da cewa:

Bana ƙarya kuke ku sake rubuta mana

Kuma kun daina sanya kowa musguna mana

Mun rantse da wanda yai Ka’aba Rabbana

Kun gama murɗiya yau a duk Nijeriya.

 (Ibarahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya)

 

Mawaƙin ya yi amfani da habaici keɓantau tare da salon aron kalmomi daga harshen Larabci da Turanci don ya jawo hankalin masu saurarensa su fahimci saƙon da yake isarwa gare su.Wato, ya yi amfani da habaicin keɓantau don ya nuna wa mutane shi ma yana da ilimin addini da na zamani. Kalmomin da ya aro su ne,Rabbana, da ka’aba da jiniya da sauransu.Yin amfani da waɗannan kalmomi cikin waƙarsa wata dabara ce ta isar da saƙo ga mutane masu ilimin addini ko Larabci da kuma masu jin harshen Turanci.Mawaƙin ya nuna wa jamaa cewa, shi ƙwararre ne ga sarrafa harshen Hausa.Kamar yadda ya gabata ,a ɗan waƙa na farko yana ɗauke da habaici, inda mawaƙin ya yi amfani da lamirin jami na waɗanda ake yi wa magana ‘ƙarya kuke ku sake rubuta mana.Waɗannan kalmomi su suka tabbatar da habaici da mawaƙin yake yi ga wasu shugabanni domin ya nuna masu damuwarsa da ta yan Nijeriya game da mulkin kama karya da suke yi wa alummar Nijeriya.

Shi ma, da yake yi wa shugabanni habaici dangane da halaye na gari, Dauda Kahutu Rarara, yana cewa:

Wanda zai yi siyasa da gaskiya, Shi ab babba.

Sabon abu dai na shaida, Darajarsa ta zarce gyauro.

 (Dauda Kahutu: Waƙar Muhammadu Buhari).

 

Gaskiya tana daga cikin kyawawan ɗabi’u da ake la’akari da ita wajen zaɓen shugabanni. Idan mutum ya kasance mai rashin gaskiya ne ga gudanar da al’amurransa, to, yana da wuya a amince masa ga kowace irin hulɗa da zai yi da mutane. Saboda haka koyaushe mutum mai gaskiya yakan zama babba a idon jama’a. Wannan baiti yana faɗakar da al’umma cewa su zaɓi mutum mai gaskiya a lokacin da suka zo wurin jefa ƙuria domin a samu kyakkyawan jagoranci a ƙasa. Mutane suna alfahari da shugaba, idan ya zama mai gaskiya, domin shi ake sa ran ya riƙa amanar dukiyar al’umma ba tare da ya salwantar da ita ba, ko ya handame wa kansa da ‘ya’yansa. Muhammadu Buhari yana a sahun gaba a wajen bin ƙa’ida da tsare gaskiya a cikin tafiyar siyasarsa. Saboda haka ne ya sa Dauda Rarara ke yi wa masu mulki na waccan jam’iyya habaici game da rashin gaskiya da suka nuna a lokacin da suke gudanar da mulkinsu. Ya ƙara shaida wa jamaa cewa sabuwar jamiyya da Muhammadu Buhari yake neman shugabanci a ƙarƙashin inuwarta tana da daraja. Saboda haka ta fi tsohuwar jamiyya, wadda ya kira da gyauro.

Shugabanci nauyi ne da Allah (S.W.A) yake ɗora wa wanda ya so, domin ya jaraba shi.Idan shugaba ya yi gaskiya wajen tafiyar da mulkinsa, to, zai kasance abin so ga al’ummarsa. Idan kuwa akasin haka ya faru,to sai shugaba ya zama abin zargi ga mutanen da yake yi wa jagoranci. Don haka mawaƙin yana zargin shugabani da suke mulki da cewa, ba su da gaskiya. Saboda haka ga sabuwar jam’iya wadda ke da mutum mai gaskiya, wato Muhammadu Buhari. Ya ce, sabon abu duk yadda yake ya fi gyauro. Gyauro na nufin tsohon abu. Wato, wani tsiro ne da kan fito idan aka sare amfanin gona daga baya ya sake tartsewa ya sake yin ‘ya’ya idan damina ta sauka. Wato abin daya fito na amfanin gonar da aka samu ba tare daan sake shuka shi ba. Wato idan aka zaɓi Buhari ya fi wancan shugaba da aka ga kamun ludayinsa a mulki. Dauda Kahutu Rarara ya yi wa shugaba Johnathan habaici ne, don ya soki salon mulkinsa, ya kuma jawo hankalin ‘yan Nijeriya su fahimci cewa, Buhari mai gaskiya ne. Don haka shi kaɗai zai iya mulkin adalci a samu ci gaban ƙasa ta fuskar tattalin arziki da zaman lafiya a duk faɗin Nijeriya.

A nan mawaƙin ya sifanta Buhari da sabuwar shuka wadda ta fi gyauro, wato tsohuwar gwamnati.Mawaƙin ya yi amfani da salon sifantawa a waƙarsa domin ya isar da saƙonsa ga jamaa ta hanyar kawo sunan abin da suka sani.Wato, ya abunta shi, inda ya ba shi darajar abu maras rai don ya bayyana wa jama’a bambancin sabuwar shuka da gyauro da kuma sabuwar jam’iyya da waccan mai mulki.Wannan dabarar isar da saƙo da mawaƙin ya yi amfani da ita, ta yi matuƙar tasiri ga siyasar Muhammadu Buhari wajen jawo hankalin alumma su zaɓi jam’iyyar da Muhammadu Buhari yake takarar kujerar shugaban ƙasa a inuwarta. a zaɓen 2015 zuwa 2019.

Ibrahim Yala Hayin Banki ya yi amfani da habaici mars ƙaidi cikin waƙarsa don ya jawo hankalin ‘yan Nijeriya su zaɓi mutum mai gaskiya domin a sami tsaro da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Yana cewa:

Aye ga wasiƙa nan buɗaɗɗiya,

A je a kai wa mai malfa,

Bara ta riga ta wuce,

Bana ƙarfa-ƙarfa ba za ai ba,

Ya mutum yana da gida,

A ce ya je ya kwana cikin rumfa,

Zalunci ƙarya ce mai ita,

Taka bi Bai tsere ba.

Zaɓen bana ba zan ba

Ba za a yi rinto ba

Mu Buhari muke fata

Shi ne da gaskiya dokin ƙarfe.

 (Ibrahim Yala: Waƙar CPC)

Kamar yadda bayani ya gabata mawaƙin yana faɗakar da al’umma ne, a kan muhimmancin zaɓen mutum mai gaskiya. Ya kamata duk wata hulɗa da ɗan Adam zai yi, ya tsare gaskiya domin zalunci ƙarya ce. Ita kuma, “ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya”, inji Hausawa. Rashin gaskiyar da shugabanni ke tabkawa ita ke jawo ra’ayin talakawa har su nemi sauya masu mulki. Mawaƙn ya yi wa gwamnatin PDP, da shugabanninta habaici don ya jawo hankalin al’umma da su sa ido idan zaɓe ya zo su zaɓi Buhari don shi ne mai gaskiya.Mawaƙin yana yi wa shugaba Johnathan da gwamnatinsa habaici don ya naƙasa shi, ya kuma tallata Buhari ga mutane.Wato, mutane su dawo da hankalinsu wuri ɗaya su zaɓi mutum mai gaskiya.Kamar yadda mawaƙin ya bayyana cewa, su Buhari suke fata ya ci zaɓe, domin shi mutum ne mai gaskiya. Shugaba mai gaskiya shi kaɗai zai iya kawo wa ƙasarsa cigaba ta kowane hali.Don haka talakwa su zaɓi Muhammadu Buhari mai gaskiya, don ceto ƙasa daga halin da ta faɗa ciki na taɓarɓarewar al’amurran rayuwar ‘yan Nijeriya.Rashin samun mutum mai gaskiya ga mulki yana iya haifar da taɓarɓarewar ilimi, da kiyon lafiya, da sauran fannoni daban-daban na cigaban ƙasa.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kamantawa ne ta hanyar kawo kalmomi biyu masu alaƙa da juna, sai dai ɗaya ta fi ɗayan daraja. Wato,ya kawo kalmar gida da kuma rumfa. Dukkansu wurin zama ne,amma rumfa ba ta kai gida daraja ba. Wannan dalili ne ya sa mawaƙin ya nuna cewa, kuskure ne mutum da ya mallaki gida a ce, ya tafi cikin rumfa ya kwana.A nan mawaƙin ya yi amfani da salon kamancen kasawa ne, inda ya nuna cewa rumfa ba kai darajar gida ba, duk da cewa, wuri ne da mutane ka iya zaunawa su kwana.Amma babu cikakken natsuwa ga wanda ya kwana cikin rumfa, kamar wanda ya kwanta cikin aminci a gida.Haka kuma, mawaƙin ya yi amfani da kalmar Rinto wadda ke nufin ƙari a wajen ƙirga wani abu. Wato, maimakon ya ce ba su yarda da maguɗin zaɓe ba,ko ƙarin ƙuriu, a lokacin zaɓe ko wajen ƙirga ƙuriu,sai ya ce,‘rinto’, don ya nuna ƙwarewarsa ga harshen Hausa. Haka wata dabara ce ta jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da ake son isarwa gare su cikin sauƙi.

Kamilu ɗan almajrin mawaƙa ya kalli matsayin gaskiya da idon basira musamman a fagen gudanar da jagorancin al’umma. Ya bayyana cewa halacci wani mataki ne da sai mutum na ƙwarai ake halatta wa mulkin jama’a da amanar dukiyarsu. Yana cewa:

Shi halacci sai ga ɗa na ƙwarai,

In ruwa ne sai ka je gulbi.

Ɗa na ƙwarai shi ne, wanda yake gudanar da al’amurransa cikin gaskiya. Ana sa ran cewa duk lokacin da ake buƙatar a yi mu’amala ta jagoranci, to a yi ta da mutum na ƙwarai, mai gaskiya da riƙon amana. Mai gaskiya kamar gulbi da ruwa yake, wanda idan aka je za a ɗebo wadatattu a sha a yi sauran aikace-aikacen gida da sauransu. Don haka mai son ya sha ruwa, ya yi wanka sai ya je gulbi; ya ɗiba ya sha ya yi wanka. Haka idan ana son aiki na gaskiya to a nemi mutum na ƙwarai, wanda zai iya riƙe amanar nauyin da aka ɗora masa na jama’a da dukiyoyinsu. Wannan shi zai saka a sami zaman lafiya a cikin al’umma.Wannan habaici wani jigon gargaɗi ne da mawaƙin yake ƙoƙarin isarwa ga yan siyasa domin su aminta su zaɓi Muhammadu Buhari don a sami ingantacciyar gwamnati mai gaskiya da kowane ɗan ƙasa zai amfana da mulkinta. Wannan habaici gargaɗau ne mawaƙin ya yi amfani a shi domin ya gargaɗi ‘yan siyasa su kasance masu gaskiya a riƙon mana kafin su nemi yardar jamaa su zaɓe su a muƙamin siyasa.

A tsari na shugabanci kowane iri ne, dole a nemi wanda yake mai mutunci, wanda ke da ɗabi’u na ƙwari. Samun haka zai sa a yi mulki cikin adalci domin a bunƙasa ƙasa ta ɓangarori daban daban, da suka haɗa da; ilimi, kiyon lafiya da samar da wadataccen abinci da ingantattun ruwan sha, da kuma bunƙasa aikin gona. Saboda haka, wannan mawaƙi ya yi wa shugabanni habaici don su kasance mutane na gari. Amma shi a nasa tunani, Muhammadu Buhari shi ne gulbin da za a je a sami ruwa, wato shi ne mutum nagari wanda ya cancanta a zaɓa ya yi mulkin Nijeriya, saboda a sami wadata da zaman lafiya da cigaban ƙasa.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kamance, inda ya kamata ɗa na ƙwarai da gulbi.A mawaƙin ya amfani da salon baubawan burmi,inda ya kamanta abubuwa biyu masu bambancin maana domin ya isar da saƙonsa ga alumma, su sani cewa, kamar yadda ake zuwa gulbi a sami ruwa masu yawa, haka shi ma ɗa na ƙwarai ake samun riƙon gaskiya da adalci idan aka zaɓe shi ya yi shugabanci.Wannan wani salo ne da mawaƙin ya yi amfani da shi, yakamanta Muhammadu Buhari da mutum nagari da ‘yan Nijeriya za su yi alfahari da zaɓensa a matsayin shugaba. Sai dai wannan salo shi ake kira da baubawan burmi kamar yadda aka fadomin ɗabi’un abubuwan biyu sun bambanta. Ɗa na ƙwari yana nufin mutum,yayin da gulbi na nufin wurin da ruwa ke taruwa su riƙa gudana zuwa wani wuri na kusa ko na nesa. Mutane da dabbobi da sauran halittu suna amfani da ruwa don su rayu. Mawaƙin ya yi amfani da wannan salo domin ya jawo hankalin masu saurare su san matsayin Muhamadu Buhari, cewa shi mutum ne mai nagarta.

Haka yake a tunanin Kamilu ɗan almajirin mawaƙa. Shi yana ganin biyayya wata abu ce mai mahimmanci a sami shugaba wanda yake a tarihinsa, shi mutum ne mai biyayya da ɗa’a ga iyaye da shugabanni ,wanda idan har aka zaɓi irin wannnan mutum ya yi shugabanci za a sami kyakkyawan jagoranci.. Kamilu yana cewa:

Kuma duk haɗamar mai haɗama,

Wallahi bai iya ɗaukar duniya,

Mai yawan bacci in ya sha hura,

Ku duba kar ku yi tambaya,

Wanda ya yi biyayya haƙƙin uwa,uba,

Ya zauna lafiya

Akasin haka illa ce ‘yan ƙasa,

Ku duba ‘yan Nijeriya.

 (Kamilu: Waƙar APC 1).

Handama da babakera ɗabi’a ce ta wasu mutane a cikin al’umma, Sai dai irin waɗannan ɗabi’u na sata da handama da babakere da dukiyar jama’a ko ƙasa suna faruwa ne a lokacin da mutane suka sami riƙa shugabanci. Biyayya ga iyaye kan sa mutum ya yi albarka ga dukkan abin da ya shafi rayuwarsa. Irin waɗannan mutane ake alfahari da su idan sun sami wani shugabancin jama’a, wanda kan taimaka masu su gudanar da gaskiya a cikin harkokin mulki.Saboda haka albarkar iyaye kan sa shugaba ya ji tsoron Allah ya kaucewa handamar dukiyar al’umma da aka ba shi amana.Rashin biyayya ga uwaye babbar illa ce ga ɗa.Waɗannan ɗiyan waƙa suna ɗauke da jigon gargaɗi ne ga al’umma, musamman ‘ya’ya. Idan ya kasance mutum bai girmama iyayensa ba, to ko ya zama shugaba ba zai darajanta mutanen da yake shugabanta ba. Biyayya ita ce nagartar ɗa, duk ɗan da ba shi da biyayya ya rasa matsayi a idon mutane.Saboda haka, kafin a zaɓi mutum a matsayin shugaba, dole sai an yaba da kirkinsa.

Kamar yadda aka sani wasu mutane musamman ‘yan siyasa sukan jefa kansu cikin ɗabi’ar yin sama da faɗi ga dukiyar talakawa idan suka hau kujerar mulki.Rashin biyayya ga uwaye illa ce domin yakan hana wa mutum tsoron Allah, balantana ya iya kiyaue amanar da aka ɗora masa ta dukiyar al’ummar ƙasa.Sai dai ga irin yawan albarkatun arzikin ƙasa da Allah ya ba Nijeriya, komi yawan zaluncin da shugabanni suka yi; ba za su iya ƙare arzikin ƙasa ba. Wannan habaici ya shafi shugabanni mahandama, waɗanda suka mai da dukiyar ƙasa tamkar tasu. Amma duk haɗamarsu ba za su iya ɗaukar duniya ba.Mulkin gaskiya da adalci shi ke kawo zaman lafiya a ƙasa. Samun haka sai an zaɓi shugaba mai gaskiya da riƙon amana.

Mawaƙin ya yi amfani da dabarar isar da saƙo ta hanyar amfani da salon aron kalmomi masu jan hankalin masu saurare. Ya yi amfani da kalmar haɗama, da duniya da kuma akasi.Waɗannan kalmomi ya aro su ne daga harshen Larabci kuma ya bar su kamar yadda Larabci yake faɗar su.Idan aka fassara waɗannan kalmomi da harshen Hausa za su ba da ma’ana kamar haka: haɗama tana nufin zwari/zri, wato daukar abin da ya fi ƙarfin mutum. Ita kuma duniya kamar yadda Alƙurani yake faɗar ta, tana nufin sararin da ɗan adam da sauran halittu suke rayuwarsu. Kalmar akasi tana nufin saɓini ko rangwane ga abin da aka saba da shi.Kawo irin wadannan kalmomi da mawaƙin ya yi cikin waƙarsa wata dabarar isar da saƙo ce da mawaƙin ya yimamfani da ita don ya nuna ƙwarewarsa ga harshen Hausa.Shi ma malam Ibrahim Yala yana cewa:

Allah wadaranku tun da ba kwa ƙaunar mu,

Tun da kuna ta mulkin mu ba ku kula da mu,

Don Allah Buhari mu zo ka fitar da mu,

Yau kai ne muke so a nan Nijeriya.,

 (Yala:yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

Shugabannin jam’iyar PDP sun ƙuntata wa ‘yan Nijeriya, wanda hakan ya bayyanar da ƙiyayyar talakawazuwa gashugabanni.Wato, rashin kula da talakawa ba ƙaramar illa bace ga shugabanni, musamman kamar yadda masu mulki na PDP suka nuna. Talakawa suna son shugaba ya kula da su ta fuskoki da dama, kamar ta fuskar ilimi da kiyon lafiya da abinci da sauransu.Idan talakawa suna cikin irin waɗannan yanaye-yanayen, to abin da suke nema shi ne su sami mutum mai gaskiya wanda zai ceto su daga wannan ƙangi da suke ciki. Mawaƙin ya yi wa waɗannan shugabanni habaici saboda rashin iya tafiyar da mulki yadda ya kamata.

A nan manufar mawaƙin ita ce ya faɗakar da talakawa illar da masu mulki na waccan jam’iya suka yi, sannan ya tallata ɗan takararsa a idon duniya cewa shi mai gaskiyar da ya cancanta ‘yan Nijeriya su zava. Don haka sai mawaƙin ya haxa Buhari da Mahaliccinsa, wato, Allah (S.W.A.) cewa ya zo ya fitar dayan Nijeriya daga mawuyacin halin da suke ciki a sanadiyar mulkin mayaudara azzalumai. Yala ya yi magiya wajen neman Buhari ya amince da buƙatar yan Nijeriya ta hanyar karɓa kiransu ya fito ya nemi kujerar shugabancin Nijeriya don talakawa su sami sauƙin rayuwa.

Har wa a wani baiti, mawaƙin ya yi habaic ga duk wanda ya nuna ba ya son Buhari ya neman kujerar shugaban ƙasa. Yana cewa:

Wanda ya ja da kai Buhari zai sha wuya,

Domin ka fi wane mai halin ‘yan giya,

Mai fuska kamar ana murjin taliya,

Kai hango shi ba ya ƙaunar Nijeriya.

 (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya)

 

Mawaƙin ya yi amfani da habaicin shaguɓau don ya soke salon mulkin ‘ya’yan jam’iyyar P.D.P da suka jefa talakawa cikin halin wahala tare da yi wa talakawa hannunka-mai-sanda su guji jayayya da Buhari a fagen siyasa.Wahala, ita ce a shiga wani hali na shan wuya wadda Bahaushe ke cewa, ‘wuya ko da magani ba daɗi’. Wato mawaƙin ya yi habaici ne ga masu nuna ƙiyayyarsu ga Buhari don ya jawo hankalin mutanen Nijeriya a kan alfanun zaɓen Buhari.Sannan kuma ya nuna cewa,Buhari ya fi wani ɗantakara, wanda mawaƙin ya ɓace shi dangane da wata siffa da kuma ɗabi’a maras kyau da yake aikatawa. Ya ce fuskar shi kamar ana murɗar taliya, sannan ɗabi’arsa irin ta mashaya giya ce. Taliya wani nau’in abinci ne da ake sarrafa shi daga fulawar alkama. Ana kwaɓa garin fulawar alkama a saka ta cikin injin ana marɗa injimin sai taliya ta riƙa fitowa. A lokacin da ake sarrafa taliya za ta riƙa fitowa murɗe ginit-ginit saboda matsar da injin yake yi mata. To haka fuskar wancan mutum da ake yi wa habaici take. Sannan kowa ya san mashayin giya ba shi da ɗabi’a mai kyau domin mutum ne wanda ba shi da kunya.

Wannan habaici da mawaƙin ya yi wa wancan shugaba, yana ƙoƙarin tozartar da shi ne a idon yan Nijeriya don ya nuna masu cewa ba ya da fara’a. Saboda haka, yadda fuskarsa take murɗe, to haka mulkinsa yake murɗe, ba komai sai wahala.Wato talakawa suna shan baƙar wuya saboda rashin wadata da rashin tsaro a ƙasa.Ƙarshe mawaƙin ya kira mutane da su kalle shi da kyaucewa, shi maƙiyin Nijeriya ne.Don haka su zaɓi Buhari don ya fitar da su daga wahalar da suke ciki.Mawaƙin ya yi amfani da salon kamance, inda ya kamanta fuskar wanda yake yi wa habaici da taliya da ake murɗawa daga injimin murɗar taliya. Wato, ya kalli yadda fuskarsa take, sai ya kamanta shi da taliya domin ya naƙasa shi a idon jamaa. Haka kuma ya sifanta shi yan giya domin ya gargaɗi al’umma da su ƙaurace wa zaɓen mashayin giya saboda ka da ya zo ya yi masu shirme a mulkinsa.Idan ɗan giya ya sha ya bugu sosai, to ba zai san abin da yake yi ba. Yana iya yanke ɗanyen hukunci ko kuma sa ma wata yarjejeniyar da ba ta bisa ƙaida hannu.Wannan wata dabara ce ta isar da saƙo ga mutane domin a jawo hankalinsu su gujewa zaɓen duk mutumin da ba shi hankali ko wanda ba shi da fara’a da nan-nan da mutane. Mawaƙin ya gargaɗi ‘yan Nijeriya su sa ido ga kowane mutum wanda ba shi ƙaunar ci gaban Nijeriya don kaucewa zaɓen shi a matsayin shugaban ƙasa.

4.2.3. Habaici ta fuskar Jam’iyya

Siyasa salon mulki ne da ake aiwatarwa ta hanyar kafa jam’iyyu daban-daban a ƙasa.Jam’iyyu suna kafuwa ne ta hanyar haɗin kan mutane masu ra’ayi da manufofi iri ɗaya. Kowace jam’iya tana da manufofi na raya ƙasa da take niyyar aiwatarwa idan aka zaɓe tata kafa gwamnati.Misalin manufofin kowace jam’iya basu wuce samar da ilimi kyauta, dakiyon lafiya, da ruwan sha ingantacce da bunƙasa harkokin noma don samar da wadataccen abinci ga al’umma, da samar da hanyoyin sufari da na sadarwa da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.Mawaƙan siyasa suna taka rawar gani wajen jawo hankalin jamaa su fahinci abin da ake son su sani. Habaici salo ne da mawaƙan siyasa ke amfani da shi domin su isar da wani muhimmin saƙo zuwa ga mutane.Misali, a cikin waƙoƙin da mawaƙan da suka rera wa Buhari waƙa don su tallata shi ga alummar Nijeriya sun yi amfani da habaici domin su jawo hankalin mutane su yarda da manufofin Muhammadu Buhari ga mulkin Nijeriya. Da yake yi wa jamiyar PDP habaici Alan waƙa yana cewa:

Baƙar jamiya mai malfa

Tana son kada bayinka.

Baƙar malfa baƙar jarfa

Mai shanye jinin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar karab da gari.

 (Aminu Alan Waƙa: Guguwar sauyi).

Duk lokacin da aka kira wani abu da kalmar baƙi,to za ka ga an danganta shi da abu mai muni ko maras haske. Alan waƙa ya ambaci launin baƙi don ya jawo hankalin masu saurare su iya banbancewa tsakanin abu mai kyau da maras kyau.Ba duka launin baƙi mutane ke sha’awar ba, sai idan lalura ta tusgo. Amma farin abu koyaushe mutane na ribibin samun shi don su amfana da shi. Wannan ɗan waƙa da mawaƙin ya kawo yana ɗauke da jigon faɗakarwa ne zuwa ga al’ummar Nijeriya su nisanci duk wani da ke da launin baƙi domin babu alheri tare da shi.Don haka mawaƙin ya roƙi Allah da ya kawar da jamiyyar PDP da shugaban ƙasarta daga zukatan yan Nijeriya. Sannan ya roƙi Allah ya bai wa Buhari nasara ya karɓe mulki

Mutane suna farin cikin shiga jam’iyyar da ke da manufofin raya ƙasa da samar wa alumma jin daɗi da walwala. Jam’iyyar PDP, mawaƙin ya kira ta da sunan baƙar malfa saboda ta kasa samar wa jamaa abubuwan more rayuwa kamar yadda ta yi alkawari. Ganin haka ya saka mawaqin ya kira ta da baƙar malfa don ya jawo hankialin talakawa su ƙaurace mata su karɓi jam’iyyar da za ta kawo masu ci gaba. Ya yi wannan habaici ne ga jam’iyyar PDP don ya naƙasa ta a idon mutane, ya kuma tallata jamiyyar APC, wadda Muhammadu Buhari ke takarar kujerar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwarta a 2015.

Mawakin ya yi amfani da salon sifantarwa, inda ya sifanta jam’iyyar PDP da baƙar malfa. Sannan kuma ya sifanta jamiyyar da wata ɗabi’a ta dabbar da ke shan jini.Zaki da kura da kare dabbobi ne masu shan jini, saboda haka mawaƙin ya dabbantar da jamiyyar PDP, don ya jawo hankalin mutane.Wannan salo da mawaƙin ya yi amfani da shi, wata dabara ce ta isar da saƙo ga jamaa su aminta da sabuwar jamiyyar APC da yake kambamawa.

Shi kuwa Ibrahim Yala Hayin Banki ya yi irin wannan habaici zuwa ga wasu jam’iyyu cikinsu har da jam’iyyar PDP, mai mulkin ƙasa. Malamin yana cewa:

Tarkon mutuwa da PDP tai mana,

Halin ha’ula’i da ta jejjefa mana,

Bala’in shawa da tak kokoya mana,

Baba Buhari ne za ya fidda Nijeriya.

 (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

 

Shiga wani hali na damuwa ko na rashin jin daɗin rayuwa, ko talauci yakan jefa mutane cikin tunani da juyayi. Mutane suna zargin jam’iyyar PDP da rashin iya mulki wanda suke ganin shi ne ya jefa ƙasa da alumma cikin halin talauci da yunwa da kuma rashin tsaro. Wannan hasashe da mutane ke yi da ƙorafi ga mulkin jamiyyar PDP ya yawo raayin mawaƙin siyasa Ibrahim Yala ya yi habaici cikin waƙarsa don ya faɗakar da al’umma girma da matsayin jam’iyyar ANPP, ga talakawan Nijeriya. Haka kuma ya jawo hankalinsu su zaɓi jam’iyyar da za ta ceto al’umma daga mawuyacin halin da suke ciki.

Mutane suna farin ciki da murna idan suka sami shugaba mai tausayi da jinqai wajen jajircewa ya samar da ci gaba a ƙasarsa. Duk shugaba da ya yi nasarar kawo sauyi mai aana da fuskoki daban-daban, mutane za su riqa alfari da mulkinsa. Wato za su riƙa cewa a lokacinsa ne tattalin arzikin ƙasa ya bunƙasa, noma kiyon lafiya ya inganta ,mutane suka sami yalwar abinci fatara da talauci suka ƙaura daga alumma.Don haka samun shugaba irin Buhari shi zai fitar da jamaa daga cikin irin halin da jamiyyar PDP ta jefa mutanen ƙasa ciki. Shi ya saka mawaƙin ya ce Baba Buhari ne kaɗai zai ceto Nijeriya idan aka zaɓe shi a jam’iyyar ANPP ya yi shugaban ƙasa a wancan lokaci.Har wa yau, mawaƙin ya ƙara da cewa:

Ke lema baƙad daga kin yi muna yau haka

Ke lema baƙad daga kin muna yau haka

Ba kya maganin ruwa duk mun sha wuya

Ke lema fa mulkinki ba kya gaskiya

ANPP zo ki tallafi Nijeriya.

 (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

 

Lema (Ambraler) wata‘rumfar tafi da gidanka ce da ake anfani da ita domin a kare kai daga zafin rana ko ruwan sama (Ƙamusun Hausa 2016). Wato lema rumfa ce da ake haɗawa da kyalle ko leda a yi mata mariƙa don a riƙa a lokacin da za a yi amfani da ita a kare kai daga tsananin zafin rana ko ruwan sama a lokacin damina k rani. Tsofaffi da mata da sauran ɗaiɗaikun mutane suka fi yin amfani da ita. Wannan lema wata alama ce ta jam’iyyar PDP, wadda ke banbanta ta da sauran jam’iyyu. Mawaƙin ya yi wa wannan jam’iyya habaici, inda ya ambace tada baƙad daga domin ya bayyana sifarta gamutane.Duk da kasancewar lema tana kariya daga zafin rana da ruwan sama, to wannan baƙad daga inji mawaƙin bata yi masu maganin ruwansama ba, balle ta kare su daga zafin rana.Wannan baitin yana faɗakarwa ne zuwa ga al’umma domin su hankalta da illar da jam’iyyar PDP da shugabanninta suka yi wa ‘yan Nijeriya.

Wannan mawaƙin ya yi wa mulkin shugannin PDP habaici keɓantau don ya naƙasa jamiyyar da ma shugabanninta dangane da irin mawuyacin halin da suka jefa ƙasar nan ciki. Don haka yake faɗakar da mutane tare da kambama jam’yyar A.N.P.P ga jama’a domin su zaɓe ta a zaɓen shekarar 2007, wato jam’iyyar da Buhari ke takarar kujerar shugabancin ƙasa a inuwarta.Saboda haka, a wancan lokaci da talakawa ke cikin garari na talauci da rashi abinci da kuma rashin tsaro da ya addabi ‘yan Nijeriya, mawaƙin ya yi amfani da habaici don ya jawo hankalin alumma. Da baro tafiyar jam’iyyar P.D.P, mai mulki. Ya kambama ANPPta hanyar nuna wa talakawa cewa,ita kaɗai ce ta dace ta zo ta mallaki Nijeriya, idan aka zaɓi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa.

Mawaƙin ya yi amfani da salon mutuntarwa, inda ya bai wa jamiyyar ANPP da PDP darajar ɗan adam na yin magana da shugabanci.Misali,ke lema fa mulkinki ba ki da gaskiya, wato, mutum aka sani da yin gaskiya ga al’amurransa cikin hulɗarsa da jama’a. Sai ga shi ya ce Lema ba ta da gaskiya,wato ya mutumta ke nan, ta hanyar ba ta darajar mutum; duk da kasancewar wannan magana habaici ce zuwa ga sugabannin P.D.P mai mulkin ƙasa Haka kuma, ya kira jam’iyyar ANPP da cewa, ta zo ta tallafi Nijeriya. Mutum shi ke ba da tallafi, amma sai mawaƙin ya ce ANPP ta zo ta tallafa.Wato a nan ya bai wa ANPP darajar ɗan Adam na ba da tallafi ga al’ummarsa.Wannan salo da mawaƙin ya yi amfani da shi wata dabara ce ta jawo hankalin mutane su fahimci saƙon da yake isarwa gare su dangane da mahimmancin zaɓen jam’iyyar ANPP ta Muhammadu Buhari.

Shi kuwa Yusuf Fasaha, ya yi wa jam’iyyar PDP habaici inda yake cewa:

Duk talakkan da ke yin PDP

Tuni yai niyya yai asara a duniya.

 (Yusuf Fasaha: Mu bi APC alummar ƙasa).

 

Hasara na nufin rashi ko tavewa daga mallakar wani abin amfani ko dukiya ko jin daɗin rayuwa. Kamar yadda aka sani PDP jam’iyya ce ta siyasa kamar sauran jam’iyyu, wadda ita ce wadda ta kafa gwamnati a farkon jamhuriya ta huɗu a 1999. A wancan lokaci ta zama jam’iyya mai mulki saura kuwa su ne ‘yan adawa. Daga bisani a shekarar 2015 wasu jam’iyyun ANPP da ANC da AC daCPC suka yanke shawarar curewa waje ɗaya suka samar da jam’iyyar APC. A ƙarƙashin inuwar wannan jam’iyya Buhari yake takarar shugaban ƙasa.Yusuf Fasaha ya yi wa al’ummar Nijeriya gargaɗi da su ƙaurace wa sake zaɓen jam’iyyar PDP mai mulki don su kaucewa faɗawa cikin hasara ta duniya, wato hasarar mutunci da dukiya.Mawaƙin ya yi wa jamiyyar PDP habaici cewa, shigar ta asara ce a duniya ga duk talakan da ya shige ta.

A wannan baiti, Yusuf ya yi habaici ga magoya bayan jam’iyya mai mulki don ya tallata ko kambama tasa sabuwar jam’iyya ta APC, wadda Buhari ke neman a zaɓe shi, ya zama shugaban ƙasa a inuwarta. A tunanin mawaƙin duk wanda ya shiga PDP to ta tabata ya yi niyyar yin hasarar rayuwarsa a duniya domin jam’iyyar bata da manufar alheri ga al’ummar ƙasa.Ya kambama Jam’iyyar APC,wadda ya ce, ita ce ta fi dacewa ga talakan Nijeriya.

A wannan baiti, mawaƙin ya yi amfani da salon aron kalma daga harshen Larabci ya yi amfani da ita wajen isar da saƙonsa ga alummar Nijeriya. Bahaushe ya aro kalmar ‘Asara’, daga harshen Larabci.A harshen Larabci, kalmar tana nufin ,rasa wani abu ko rai ko dukiya.Bahaushe ya kira wannan kalma da ‘hasara’ wadda ke da ma’ana iri ɗaya da ta Larabci,wato rasa wani matsayi ko dukiya ko rayuwa. Mawaƙin ya yi amfani da wannan dabara don ya sami damar jawo hankalin mutane su guje wa zaɓen jam’iyyar PDP, wadda ya ce.duk talakan da ke yin ta ya yi asara a duniya.

Shi kuwa Murtala Mamsa Jos ya yi amfani da habaici domin ya naƙasa sauran jam’iyyun Nijeriya domin ya kambama tasa jam’iyyar APC, wadda ya ce sauran jam’iyyu suna bayanta.Yana cewa;

Duka jam’iyyun Nijeriya sun haɗa kai talakawa kun jiya,

Tun da sun haɗa kai talakawa mu bi kar mu yi tambaya,

Kar mu yarda da duk wani wanda za ya zo ya ce muna shi ne ɗan’iya

Sabuwar jam’iya ta zo mu bi ta bai ɗaya ‘yan Nijeriya.

(Murtala Mamsa: Sabuwa ta zo, APC).

Jam’iyyun siyasa wasu ƙungiyoyi ne na wasu mutane masu ra’ayi iri ɗaya.Waɗannan ƙungiyoyi, su ne suke curewa su zama jam’iyyun siyasa waɗanda keda manufar ciyar da ƙasa gaba. Haɗin kaishi ne haɗuwar jama’a wuri ɗaya bisa ga ra’ayi ɗaya.Haɗin kaishi ke kawo ci gaba a kowace irin tafiya ta al’umma, domin a sami nasarar abin daaka yi nufin aiwatarwa. Jam’iyyun siyasa a Nijeriya sun yi ƙoƙarin haɗa kansu wuri guda domin su ceto ƙasar nan daga mawuyacin halin da ta shiga ciki a sanadiyar mulkin ‘yan wata jam’iyyar siyasa. Dangane da haka ne, wasu jam’iyyun suka yarda su haɗa kai don su yaƙi waccan jam’iyya mai mulki. Wannan haɗin kai ya kawo wa ‘yan Nijeriya sauyin gwamnati da aka daɗe ana nema har tsawon shekaru goma- sha shidda. Haɗuwar jam’iyyu daban-daban su ƙirƙiro jam’iyya ɗaya mai ƙarfi ya samu nasara, inda aka sami jam’iyyar APC ta mutanen ƙasa, wadda mawaƙin yace, su bi ta kar su yarda duk wanda zai zo yace masu ya iya.Wato, mawaƙin yana faɗakar da su ne domin su yi hankali da wajen zaɓen jam’iyyar da za ta jefa su cikin garari.

Manufar wannan haɗin kai na jam’iyyu dasuka yarda su cure wuri ɗaya don su kada jam’iyya mai mulki ya sami gagarumar nasara. Dalilin da ya sa sabuwar jam’iyyar ta sami karɓuwa shi ne saboda ta tsayar da ɗan takara da al’ummar ƙasa ke muradi, mai gaskiya da riƙon amana. Mawaƙin ya yi wa jam’iyya mai mulki habaici na rashin iya tafiyar da mulki cikin adalci. Ya jawo hankalin ‘yan Nijeriya su zo su bi sabuwar jam’iyyar APC, don aka kawo sauyi mai ma’ana a Nijeriya.

Mawaƙin ya yi amfani da dabarar jawo hankalin talakawa ta hanyar amfani da kalmomin lamirin suna domin ya ɓoye sunan waɗanda yake yi wa habaici.’Ɗan iya’, yana nufin mutum mai nuna cewa, ya san komi, koko shi ya iya komi.Wato, komi-da-ruwanka (master of known all).Wannan wani salo ne na isar da saƙo ba tare da wata matsala ba. Mawaƙin ya yi amfani da wannan salo na ɓoye sunan wanda yake yi wa habaici domin ya jawo hankalin masu sauraro su yi dogon tunane kafin su gane wanda ake yi wa habaicin, sannan su fahimci inda saƙon ya nufa.

4.2.4. Habaici ta fuskar Ɗantakara

Gaskiya tana nufin kyawawan halaye da ɗabi’u nagari da riƙon amana da tsoron Allah wajen gudanar da mu’amula tsakanin mutum da mutum ko tsakanin mutum da dabba (Abdullahi 1987:11-13). Wato gaskiya da riƙon amana na nufin adana wani abu na dukiya ko sirri sai buƙatar sa ta taso a bayar da shi kamar yadda yake, wannan ita ke tabbatar da nagartar kowane mutum a zamantakewarsa da sauran mutane.Idan kuma sirri ne ba za a sanar da kowa ba,daga kai sai wanda ya sanar da kai. Amana tana daga cikin nagartattun ɗabi’u da ake buƙatar kowane ɗan takara ko shugaba ya kasance ya mallake ta, hakan zai tabbatar wa da mutane cewa, mutum ko shugaba mai gaskiya ne da riƙon amana ga muamularsa da alumma. Wato abu ce da ke bayyana nagartar ɗan Adam a idon duniya. Sallau [2013:719], ya ce,”shugaba mutum ne wanda ke da mabiya ko wanda yake yi wa mutane jagora ko taimako. Saboda haka ya kamata ya kasance mutum mai amana da gaskiya wajen tafiyar da harkokin shugabancinsa. Wajibi ne ga kowane shugaba a same shi da sassauci da tausayi ga dabba da tsirrai, balle ma ga ɗan Adam domin ya tabbatar da gaskiyarsa da tsoron Allah a dukkan lamurransa.

Masana sun bayyana cewa, kafin mutum ya cancanci zama shugaba da za a yi alfahari da shi, sai in ya mallaki abubuwa da suka haɗa da;‘gaskiya da riƙon amana,kirki, da natsuwa, da tsoron Allah’, waɗanda ɗabi’u ne da ke bayyana sahihancinsa da nagartarsa wajen zamowarsa shugaba (Aminu:1979:2-4).Kafin zuwan wannan zamani, an san Hausawa da bin gaskiya da riƙon amana ga dukkan al’amurransu na rayuwa.Dalilin haka ne ya sa a wancan zamani kafin zuwan addinin Musulunci a ƙasar Hausa,al’ummar Hauswa (Maguzawa), basu faɗar ƙarya komi tsanani ko daɗi. Wannan dalili ne ya sa har Hausawa ke faɗin wata karin magana cewa,’faɗin gaskiya kamar arne’.Wato, Hausawa mutane ne masu gaskiya da riƙon amana,duk halin tsanani da matsi da suka shiga a wancan zamani.

Idan ka kawo masu wani abu wanda ya shafi dukiya ko wasu kaya ko kuɗi, ka bai wa Bahaushe ajiya; ko ka ba shi saƙo ya kai wa wani,duk irin halin da ya sami kansa na matsuwa ba zai taɓa amfani da wannan ajiyar ba. Zai ci gaba da ajiya har sai lokacin da mai abu ya buƙata; sannan ya ɗauko ya miƙi masa abinsa.Haka kuma, idan saƙo ne, aka ba shi ya kai wa wani, to, zai kai masa kamar yadda aka bashi, ba tare daya rage wani abu ba.Idan kuma ka sanar dashi wani sirrinka, ba zai faɗa wa wani ba daga hai saishi.Wannan abu ya taimaka wajen samar da nagartattun shugabanni masu gaskiya da riƙon amana a wancan lokaci.A sanadiyar haka aka sami cikakken zaman lafiya tsaknin al’ummar Hausawa da sauran al’ummomi da suke hulɗa dasu.Saboda tsare gaskiyar Hausawa ya sa ake wata karin magana cewa ‘gaskiya kamar Bamaguje’.Wannan karin magana ta nuna muhimmancin gaskiya da riƙon amana a tsakanin al’ummar Hausawa.Misali,‘in za ka faɗi, faɗi gaskiya’,ko ‘gaskiya dokin ƙarfe’,ko ‘ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi’.Duk waɗannan karin maganganu za a iya fahimtar cewa, irin rawar da gaskiya da riƙon amana ketakawa wajen samar da shugabanni masu nagarta a cikin tafiyar da jagorancin jama’a ba ƙarama ba ce .

Bayan zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa,an sami ayoyin Alƙur’ani masu magana akan gaskiya da riƙon amana.Haka kuma akwai Hadisan manzon Allah [S.W.A] waɗanda suka yi bayani a kan muhimmancin gaskiya da riƙon amana a tsakanin al’umma..Yin imani da su, da kuma biyayya gare su zai sa mutuum ya zama nagartacce a cikin al’ummarsa. Sannan ya zauna lafiya tare da amincin Allah a wannan duniya da makoma mai kyau a gobe kiyama. Idan mutum bai yi biyayya gare suba, kuma zai sa mutum ya rasa zama lafiya a wannan duniya.Sannan ya sami mummunar makoma a lahira[wutar jahannama].Misali,a cikin Alƙur’ani mai girma, sura ta {3: 60),Allah {S.W.A.] yana cewa;

“Gaskiya daga Ubangijinka take,saboda haka kada

ka kasance daga masu shakka.[Gummi,1979;84]

Hadisin Sunanu ibn Majah, juzi’i na biyu, an ruwaito cewa, Annabi (S A W), na cewa,’’Na rantse da wanda raina ke hannunsa, babu yadda za a yi ka shiga aljanna sai in har kun ba da gaskiya da kulliyar abin da na zo da shi. Wannan ba zai samu ba sai in kuna son juna.Ga abin da za ku yi ku so juna, ‘’ku riƙa yaɗa zaman lafiya tsakaninku’’.

Mawaƙan siyasa na jamhuriya ta huɗu sun taka rawar gani wajen faɗakar da al’umma dangane da nauyin da Allah ya ɗora masu na zaɓen nagartattun mutanen masu kirki, da gaskiya da riƙon amana, su wakilce su a muƙaman gwamnati daban-daban.Misali, Dauda Kahutu Rarara yana cewa:

An yi gaskiya an gyara ƙasa

Su algaza sai ciwon baki.

(Rarara: Maraba da tsoho oyoyo).

Wannan ɗan waƙa yana ɗauke da jigon nagarta wajen zaɓen shugabanni. Aiki da gaskiya shi ne tushen gyara ƙasa. Saboda haka ayyukan da Buhari ya yi na gyara ƙasa da aka zaɓe shi, shi ne ya yi wa ‘yan adawa zafi, da har suke murnar ya mutu su huta da baƙin ciki. Wannan habaici maras ƙaidi yana suka ne ga mutanen da suka yi farin ciki da rashin lafiyar da Buhari ya yi,wadda ta sa har aka kai shi Ingila wajen neman magani.Bayan ya sami sauƙi ya dawo Nijeriya, sai Rarara ya yi wa ‘yan adawa habaici cewa, su algaza sai ciwon baki, wato ba su yi farin ciki da dawowar Buhari ba.Ya kira ‘yan adawa da suna, ‘su algaza’ domin ya musguna wa masu baƙin cikin dawowar Buhari lafiya. Sannan, ya ƙarfafa wa gwaninsa guiwa wajen tafiyar da mulkin Nijeriya har sai wa’adin mulkinsa ya cika.

Rarara yana faɗakar da ‘yan adawa da ke son Buhari ya kau cewa, su sani, ciwo ko rashin lafiya ba mutuwa ba ce, saboda haka masu baƙin ciki Buhariya dawo saisu san inda dare ya yi masu. Duk manufarsu ta son Buhari ya kau daga mulki, su ko su sami dama su haye kujerar shugabancin ƙasa ba ta sami gurbi ba. Don haka, sai ciwon baki suke,wato faɗi banza, faɗi wofi na rashin madafa.Mulki na Allah ne, shi ke bai wa wanda ya so, ya kuma karɓe ga wanda ya so. Saboda haka sai su yi haƙuri har wa’adin mulkinsa ya cika.Rashin gaskiya da rashin adalci ɗabi’u ne da ke haifar da rashin zaman lafiya a cikin ƙasa. Saboda haka ‘yan siyasa su kasance masu kyawawan ɗabi’u kafin a zaɓe su su shugabanci al’umma, wanda yin haka zai sa a sami shugabanni nagari a Najeriya.

Mawaƙin ya yi amfani da dabarar isar da saƙo ta hanyar saƙa kalmar Larabci domin ya nuna ƙwarewarsa ga sarrafa harsuna biyu. Kalmar algazaru, kalma ce ta Larabci da ke nufin maɓannaci da dukiya. Mawaƙin ya aro wannan kalma,sai ya gunce ta,wato ya yanke gaɓar ƙarshe ta ru, ta koma algaza, (Bergery 1993:20),wato mai ɓarnar dukiya (almubazzari) don ya samu damar fitar da karin waƙarsa daidai. Wannan wani salon sarrafa harshe ne da mawaƙan Hausa ke amfani da shi domin su burge masu saurarensu, su kuma isar da saƙonsu cikin raha.

4.2.5. Habaici ta Fuskar Tabbatar da Adalci.

Adalci shi ne, kamanta gaskiya tsakanin abokan hulɗa ta shugabanci ko ta harkokin yau da kullum. Bargery [1934:4] ya bayyana cewa,adalci na nufin gaskiya,ko tsoron Allah ga aiwatar da al’amuran jama’a.Wannan ma’ana ta yi daidai da tunanin,Al-Mallah [2011:180] inda yake cewa,Adalci shi ne, bai wa kowane ɗan ƙasa dama daidai da kowa babu bambancin ƙabilanci ko addini ko ɓangaranci,fifikon matsayi,sutura ko daraja a cikin al’umma.Abubuwan da ke tabbatar da adalci sun haɗa da:

i.Adalci tsakanin ‘yan ƙasa a idon shari’a da dokokin da majalisar dokoki ta tanada.

ii.Adalci a al’amuran shari’a da kotuna.

iii.Adalci tsakanin dukkan ‘yan ƙasa ga abin da ya shafi biyan haraji,yadda kowane ɗan ƙasa zai biya daidai da kowa.

iv..Adalci a rabon ayyukan gwamnati da sauran muƙaman alfarma ga ‘yan ƙasa.

Kamar yadda masana suka bayyana adalci da cewa, ‘’gaskiya da riƙon amana da tsoron Allah wajen gudanar da al’amuran jama’a ta hanyar bai wa kowa haƙƙinsa, shi ne adalci’’ (Bargery, 1934, Pp .4). Shugaba adili shi ne wanda ke da gaskiya da riƙon amana da tsoron Allah wajen tafiyar da al’amarin mulkinsa.Wato mutumen da aka bai wa amanar dukiyar al’umma,sannan yake bai wa dukkan ‘yan ƙasa haƙƙinsu ba tare da nuna wariyar ya\nki, ko ƙabilanci ba. Haka kuma bai nuna banbancin addini da sauransu ba [Ɗangulbi, 2003, Pp.108]. Irin wannan shugaba shi ake kira adili.Rashin aiwatar da abubuwan da aka ambata a sama shi ne rashin adalci.

Tsarin mulkin addinin Musulunci shi ne ya fara fito da tsarin mulkin adalci,kamar yadda bayanai suka gabata.Bayan zuwan Annabi Muhammadu,tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi,salon shugabanci na jahiliya ya fara gushewa; aka samu sabon salon mulki wanda adalci ya yi tasiri a cikinsa.A shari’ance,kowane musulmi ana ba shi dama ya nemi haƙƙinsa idan aka zo yi masa hukunci tsakaninsa da musulmi xan’uwansa a kotu. Dukkansu sun yi imani tare da miqa wuya ga waxannan dokokin da addinin musulunci ya zo da su,da kuma karɓar hukuncin da aka zartar masu da adalci, ba tare da nuna banbanci tsakanin masu wadata da marasa wadata,da kuma tsakanin masu mulki da talakawa ba,Al-Mallah [2011].

Babban ginshiƙin tafiyar da kowane irin mulki shi ne adalci, manufa ita ce, shugaba ya zama mai adalci wajen tafiyar da mulkinsa ba tare da nuna bambanci ba.Ya kuma ba kowa haƙƙinsa ba tare da la’akari da nasabarsa, ko muƙaminsa ba. Dukkan ƙasar da take da shugabanni masu yin adalci ga talakawansu, babu shakka wannan ƙasa za ta zama mai cikakken zaman lafiya da ƙaruwar tattalin arziki.A ƙasar Hausa kafin zuwan addinin musulunci da wannan zamani za a ga cewa, ana gudanar da mulki bisa adalci; domin akwai zaman lafiya tsakanin al’ummomin wannan ƙasa. A wancan zamani za a sami a gida ko unguwa ko gari, manya suna da ikon hukunta duk wanda suka ga yana cuta wa na ƙasa gare shi, ko da kuwa ba su da wata alaƙa ta jini. A tunaninsu, ɗa na kowa ne, muddin dai ka ga yana aikata wani abu da ba daidai ba. Matuƙar ba ka tsawata masa ba,to a al’ adar zamantakewar Hausawa ba ka yi daidai ba.Wancan zamani, babban mutum kan iya hukunta duk wani rashin daidai da ya tarar ana yi, ko da kuwa zai kai ya doki wanda ya tarar yana yin rashin daidai; ko ya san shi ko bai san shi ba.

Addinin Musulunci ya shimfiɗa yadda ya kamata a gudanar da mulkin adalci ga kowace al’umma ta yadda za a samu zamanlafiya a cikin al’umma.Haka kuma wannan al’umma ta sami dauwamammen cigaban tattalin arzikinta.Saboda haka addini Musulunci ya tsara gudanar da mulkin adalci kamar yadda Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rubuta maƙala mai taken Usul al-Siyasa, ya ba Malam Umaru Dallaji, wanda aka ba tutar jihadi a ƙasar Katsina. Bayanan da ya yi a cikin maƙalarsa, ya jawo hankalin masana su ƙarfafa bincike a kan yadda mulkin adalci yake. Ga kaɗan daga abin da maƙalar take magana kamar haka:

‘’Ka sani kai ɗan’uwa, babbar ƙaddara da za ta faɗa a kan bawan Allah,

ita ce,a ba shi shugabancin jama’a,domin kuwa ka sani, za a tambayi

kowane mutum abin da bakinsa ya faɗa, ayyukan da ya yi, da abubuwan

da suka biyo bayansu. Idan ya kasance shi shugaba ne, za a ƙara da tambayar sa yadda ya gudanar da mulkinsa tsakaninsa da talakawansa. Idan ya kasance ba ya iya sauke nauyin kansa,to,ta yaya zai iya sauke nauyin jama’ar da take ƙarƙashinsa. Saboda haka ne, ya sa wasu suke cewa; dukkan wanda Allah bai ɗora masa wani nauyi na Shugabanci ba, ya ƙara yi masa godiya,don ya sauke masa nauyin da za a tambaye shi yadda ya gudanar da shi. Saboda haka, Allah ya cece shi daga fitinun duniya, don kuwa ba kome cikinta sai tashin hankali da azabtarwa a gobe lahira’’.

 

Saboda haka idan mutum ya bi yaudarar shaiɗan ya hana shi yin adalci ko aiki da gaskiya a mulkinsa,to,zai kasance cikin baƙin ciki da da-na-sani,wanda Hausawa ke cewa;”Ƙeya ce”.Mulkin adalci shi ne gimshiƙin samar da zaman lafiya,kuma shi ke ɗorewa; amma mulki da zalunci ba ya ɗorewa komi kyawonsa. Ibn Taimiyya a cikin Littafinsa mai suna “Al’istiƙamatu juzu’i na biyu shafi na 247, malam yana cewa: ‘’Allah yana tsayar da daula mai yin adalci ko da ta kafirci ce; Allah ba ya tsayar da daula ta zalunci ko da ta Musulunci ce. Duniya tana tsayuwa ko da jagororinta kafirai ne, idan akwai adalci. Gwamnatin zalunci ba ta tsayuwa ko da jagororinta Musulmi ne’’.

Mawaƙa daban-daban da suka yi wa Muhammadu Buhari waƙa, sun taka rawar gani wajen amfani da habaici cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin masu sauraro su fahimci muhimmancintsayar da adalci ga shugaba a kan talakawansa. Lokacin da Buhari ya shugabanci hukumar kula da kuɗin rarar man fetur da Shugaban ƙasa Janar Sani Abacha ya ɗora masa nauyin tafiyar da hukumar, Muhammadu Buhari ya kamanta adalci ga ‘yan Nijeriya wajen raba ayyukan ci gaban ƙasa daidai a kowane lungu da saƙo na Nijeriya. Wannan dalili ne ya jawo hankalin mawaƙan siyasa suka yi amfani da wannan dama suka tallata shi, sannan a lokaci guda suka musguna ma sauran yan siyasa domin su wayar wa mutane kawunansu.Misali Dauda Rarara yana cewa:

“Kibiya ta mai ƙin adalci harba”.

Kibiya (arrow) wani makami ne mai kama da mashi, sai dai bai kai mashi girma ko tsawo ba.Ana amfani da ita wajen farauta ko wajen yaƙi domin a kare kai daga abokan gaba, ko farautar dabba. Wannan ɗan waƙa yana faɗakarwa tare da ilmantar da mutane cewa, adalci shi ne babban jigon gudanar da mulki. Shugaba mai ƙin adalci tamkar dabba yake, sabodahaka baabin daya kamata a yaƙe shi dashi, sai kibiya.Mulkin adalci shi ne tafarkin samar da zama lafiya a kowace ƙasa.Wannan mawaƙi ya gargaɗi mutanen Nijeriya su dawo daga rakiyar azzaluman shugabanni waɗanda suka jefa Nijeriya cikin halin rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa a dalilin handame dukiyar al’umma da suka yi.Ya ƙara da cewa,zaɓen Buhari ga ‘yan Nijeriya shi kaɗai ne zai cetoƙasar nan daga halin da take ciki saboda mutum ne mai kamanta gaskiya da adalci, waɗanda su ne, ginshiƙan samar da mulkin adalci a ƙasa.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kamantawa,inda ya kamanta shugaba da kibiya domin ya tsorata ‘yan adawa da shugabanni marasa gaskiya.Wannan salon kamace da mawaƙin ya yi wa Buhari na siffanta aƙidarsada kibiya mai karya zalunci wata dabara ce ta jawo hankalin al’umma su fahimci kyakkyawar manufar wanda yake waƙewa domin su ƙara son sa a zukatansu.Wannan maganagaskiya ce, inji Aminu Ladan A bubakar Alan waƙa.Yana cewa:

Muƙami in da adalci

Yana yiwuwa da yardarka.

Akan ce ko da kafirci

Kana yarda ya ɗaukakka.

Akan ce ko da Musulunci

Kana hana yay yi albarka

 (Alan waƙa: Guguwar sauyi).

Muƙami wani matsayi ne na jagorancin jama’a, wanda akan ɗora wa mutumin da ya cancanta.Yin adalci ga shugabanci wani abu ne da Allah ke yi wa shugaba baiwa da shi.Mawaƙin yana son ya faɗakar da al’umma game da alfanun da mulkin adalci yake haifarwa a cikin al’umma,musamman ta fusakr samar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma.Mawaƙan siyasa suna yi wa shugabanni habaicidon su gyara kurakuransu. Don haka adalci shi ke tabbatar da mulki cikin nasara ko da kuwa na kafirci ne, kamar a Amerika da sauan ƙasashen da ba na musulunci ba. Amma idan babu adalci ko da musulunci Allah ba zai bari mulkin ya yi albarka ba.Dalilin haka ya sa mawaƙin ya yi wa mulkin mai malfa habaici don ya jawo hankalin talakawan Nijeriya su yarda da jam’iyyar APC, su zaɓi Muhammadu Buhari domin a sami sauyi a mulkin Nijeriya.

A waɗannan baitoci da Alan waƙa ya kawo a sama, ya yi habaici ne zuwa ga shugannin jam’iyyar PDP, don ya nuna masu illar da rashin adalci yake kawowa a ƙasa ta fuskar rashin zaman lafiya da taɓarɓarewar tattalin arziki da yawaitar ayyukan ta’addanci da cin hanci da rashawa.Mawaƙin ya jawo hankalin jama’a su gane irin illar da rashin adalci namulkin ‘ya’yan jam’iyyar PDP ya kawo a Nijeriya Mulkin da ya yi sanadiyar taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa,da kuma samuwar rashin tsaro a wasu sassan yankunan Arewacin Nijeriya da ‘yan boko-haram da ‘yan ta’adda masu satar mutane suna yin garkuwa da su don neman kuɗin fansa. Saboda haka, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su sauya gwamnati ta hanyar zaɓen Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC. Domin a kawo ƙarshen waɗannan masifun rashin adalci masu mulkin P.D.P suka haddasar.Mawaƙin ya roƙi, Allah ya kawo guguwar sauyiJanar Buhari ya karɓi gwamnati, wato, ya karɓi mulkin Nijeriya.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kamance inda ya nuna fifikon matsayin da addinin musulunci yake da shi ga musulmi bisa ga kafirci.An sani cewa, musulunci shi ne gaba da kowane irin addini a duniya.Amma saboda adalcin musulunci ga daƙushe ayyukan zalunci da shugabanni ke yi, sai ya nuna cewa,Allah (S.W.A.) yana ɗaukaka darajar shugaba da ya yi adalci a mulkinsa ko da kafiri ne. Amma yana ƙasƙantar da shugaba da ya yi zalunci ko da musulmi ne.Wannan hukunci da mawaƙin ya tsakuro daga addinin musulunci, ya kuma kawo cikin waƙarsa, wani salon isar da saƙo ne ya yi amfani da shi don ya gargaɗi shugabanni su guje wa aikata zalunci a mulkinsu domin su sami ɗaukaka kamar yadda ya ce, Muhammadu Buhari ya yi a lokacin da ya riƙa muƙamai daban-daban a Nijeriya.

Shi ma, da yake faɗar albarkacin bakinsa, Yusuf Fasaha Kano ya yi wa shugabannin jam’iyyar P.D.P, mai mulki habaici, inda yake cewa:

I, shekaru sha shidda kan mulki

Sun hana mu komai na rayuwa.

 (Yusuf Fasaha: mu bi APC al’ummar ƙasa).

 

Tauye wa al’umma haƙƙinsu shi a hana masu komai na rayuwa kamar yadda mawaƙin ya yi amfani da kalmar a cikin waƙarsa. Wato shugabanni su tauyewa jama’a haƙƙoƙinsu na arzikin ƙasa, yana nufin a hana masu koai na rayuwa, musamman ‘yancin walwala da zaman lafiya a ƙasa.Mawaƙin yana gargaɗin ‘ya’yan jam’iyya mai mulki da su tattara nasu-ya nasu su bar wa Muhammadu Buhari mulkin ƙasa.Domin sun saɓa wa alƙawurran da suka ɗauka a lokacin da suke yaƙin neman zaɓe. Wannan tauyewar da suka yi wa ‘yan Nijeriya,shi ne, ya jefa talakawa cikin halin rashin wadatar abinci da rashin tsaro a ƙasar nan.Wannan baitiyayi wa ‘yan Nijeriya hannunka- mai –sanda ne domin su fahimci irin halin da suke ciki, wanda masu mulki suka saka su.Saboda haka yanzu canji ake nema don a ceto talakawa daga uƙubar da suke ciki a sanadiyar mulkin fir’aunaci na jam’iyyar PDP. Jin daɗi da walwala, shi ne ke saka talaka ya san ‘yancinsa.Matuƙar ya kasa samun haka, to dole ya nema wa kansa mafita. Saboda haka Yusuf Fasaha ya yi wannan habaici ne don ya jawo ra’ayin talakawan Nijeriya su zaɓi Buhari domin ya ceto al’umma daga mawuyacin halin da suka samu kansu. Muhammadu Buhari mutum ne mai gaskiya wanda ake hasashen idan ya riƙa gwamnati zai yi wa talakawa adalci.

Mawaƙin ya yi amfani da salonisar da saƙo ta hanyar amfani da kalmomin lamirin suna don ya ɓoye sunayen shugabannin da yake yi wa habaici.Kalmar sun, ita ce lamirin sunan jam’i, wanda yake tabbatar da nuna habaici ne ga shugabanni.Wannan dabara ta sakaya suna wani salo ne da mawaƙin ya yi amfani da shi don ya jawo hankalin masu nsaurare su yi dogon tunani wajen fahimtar abin da saƙon yake son a sani.Wani lokaci mawaƙa sukan so su ɓoye suna domin gudun tashin hankali da ka iya faruwa idan mai sunan ko wani nasa ya ji cewa, shi ne ake ɓaci.

Haka shi ma IbrahinYala Hayin banki yana cewa:

Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya

Baba Buhari kai muke so Nijeriya.

Mutum mai adalci shi ne, abin so ga jama’a. ‘Yan Nijeriya sun yarda da imanin Muhammadu Buhari saboda irin ayyukan da ya yi daban- daban a lokacin da ya yi shugabancin ƙasa a lokacin mulkin soja ba tare da ya saci dukiyar al’umma ba.. Haka kuma da irin muƙaman da ya riƙa bai yi zalunci ba, a lokacin da ya yi minstan man fetur da kuma shugabancin hukumar amintattu na asusun na rarar kuɗin man fetur na ƙasa a lokacin mulkin Janar Sani Abacha. Adalcin da ya yi na rabon arzikin rarar man fetur a kowane bangare na Nijeriya.Waɗannan ayyuka daban daban da ya yi su ne suka ƙara fito da adalcinsa a fili, har ‘yan Nijeriya suke ɗokin ya yi shugabancin ƙasa a ƙarƙashin tsarin mulkin siyasa don a sami cigaba da bunƙasa tattalin arziki da zaman lafiya a Nijeriya..

Matsayin da Buhaari yake da shi a Nijeriya ba ƙarami ba ne a idon ‘yan Nijeriya.Ba komi ya kaishi ga wannan matsayi ba, face gaskiyarsa da adalcinsa a mu’amalarsa da al’umma.Haka kuma da kyakkyawar kulawa da kange dukiyar ƙasa daga taɓarɓarewa a hannun azzaluman shugabanni.Mutanen Nijeriya suna buƙatar Muhammadu Buhari ya shugabance su,domin a zatonsu,shi ne mutumin da ya fi cancanta da shugabancin Nijeriya. Mawaƙan Hausa na zamani sun yi namijin ƙoƙari wajen jawo hankalin ‘yan Nijeriya su zabi Muhammadu Buhari a zaven 2015, wanda ya ɗora shi a kujerar mulki a inuwar jam’iyyar APC, har zuwa wannan lokaci da ake gudanar da wannan bincike.

4.2.6 Habaici ta Fuskar Hana Zalunci

Rashin bai wa mai haƙƙi haƙƙinsa da raba arzikin ƙasa daidai ga kowane yanki, da kuma taushe dukiyar ƙasa a maida ita mallakar wasu ‘yan tsirarrun mutane, shi ne zalunci. Bergery [1934], ya nuna cewa,zalunci wani abu ne da ke gudana a tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulkata hanyar danne haƙƙinsu, ko dukiyar ƙasa, da kuma danne haƙƙin maras ƙarfi, shi ma zalunci ne. Bayani ya gabata cewa, matuƙar masu mulki suka kasa bai wa talakawa haƙƙinsu da ya rataya a kansu,to sun zalunce su ke nan. Rashin riƙe amana da gaskiya a lokacin da shugaba yake kan mulki,shi ma yin haka ya zama zalunci. Wato idan shugaba ya kasa riƙe amanar dukiyar ƙasa da aka ɗora masa riƙo,sai ya riƙa facaka da ita, yana bai wa wanda yake so, kuma yana hana ma wanda ba ya so; to wannan shugaba ya zama azzalumi. Tauye haƙƙi ko yin sama-da-faɗi da ƙadarorin jama’a da yin ha’inci ga wani ko wasu don a cuce shi/su, shi ake nufi da zalunci [Ƙamusun Hausa 2006:488]. Mawaƙan siyasa sukan yi amfani da habaici a cikin waƙoƙinsu domin su yi wa shugabanni hannunka-mai- sanda dangane da bayyana koken talakawa a kan yadda aka danne masu haƙƙi da ‘yancin walwala. Mawaƙan siyasa suna yin haka ne; domin su jawo hankalin ‘yan siyasa da shugabanni su fahimci halin da talakawansu suke ciki don su gyara kurakuransu wajen tafiyar da mulkinsu domin samun sauƙirayuwa.

A cikin waƙarsa ta jam’iyyar A.P.C., Alfazazi ya bayyana zalunci a matsayin tauye haƙƙin talakawa. Zaluncin da shugabannin siyasa suke yi, ya jefa iyaye da sauran al’umma cikin wani hali da ya haddasa rashin zuwa makaranta ga yaransu saboda rashin zaman lafiya a wasu sassan Nijeriya. Tallace-tallacen yara mata da maza a kan tituna ya yi yawa a cikin ƙasa. Shugabanni sun danne arzikin ƙasa, sun mayar da shi mallakar kansu.Sun saka mutane cikin ƙuncin rayuwa da rashin walwala. Rikicin siyasa, da ta’addanci, da garkuwa da mutane, da ‘yan yaƙin sunƙuru da sunan boko haramun da faɗace-faƙacen addini, duk sun mamaye ƙasa, musamman a yankinarewacin Nijeriya.Mutanen ƙasar nan ba su san wani abu gudun hijira ba, sai da zaluncin shugabanni ya mamaye ƙasa. Daga ƙarshe mawaƙin yayi kira ga ‘yan Nijeriya su fito su nemi haƙƙinsu ta hanyar jefa ƙuria domin a kawo gyara da sauyi a cikin wannan ƙasa.Misali yana cewa:

“Ga misali zan maka ɗan uwa talakawa na a cikin wuya,

Bi gefen titi za ka ga ‘yan tallarmu suna ta ɗawainiya,

Mabarata birni da karkara ko’ina a ƙasar Nijeriya,

Ba karatu babu sana’a to ya ƙasar nan za tai lafiya.

Jam’iyyar da take mulkin ƙasar ta zame mana tarkon dattsiya,

 [Waƙar A.P.C. ta Alfazazi,]

 

Tara dukiyar haramun wani nau’i ne na zalunci. Mawaƙin yana zargin cewa waɗanda suke mulkin Nijeriya haramun suke ci domin ta hanyar zalunci suka tara dukiyar al’umma suna yin yadda suke so da ita. Masu mulkin Nijeriya sun kasance azzalumai kamar yadda mawaƙin jam’iyyar ta A.P.C ya bayyana.Ya ƙara da cewa, tara dukiyar zalunci ita ke saka shugabanni su manta da nauyin da aka ɗora masu na al’umma. Ba su tsaya wajen yin zalunci da tara haramun kaɗai ba, a’a har ma ayukkan fitsara, da kashe-kashen gilla suke yi wa ‘ya’yan talakawa don yin asiri (tsafi) da wasu sassan jikinsu.

Saƙonnin da baitocin suke ɗauke da su, su ne mawaƙin yana ƙoƙarin bayyana wa jama’a cewa, ‘yan Nijeriya suna cikin wani hali da ba su iya fitar da kansu, wanda jam’iyya mai mulki ta jefa su a ciki. Ya yi habaici da kalmomin da, da zaran an ji su lalle za a san sun dace da bagiren da aka yi amfani da su. Misali kalmomin wuya, ɗawainiya, mabarata, dattsiya, maƙure da gudun hijira.Waɗannan kalmomi ne da ke bayyana irin halin da jam’iyya mai mulki ta jefa al’ummar ƙasa ciki. Domin rashin adalci na shugabannin da ke mulki na wannan jam’iyya su ne ummul haba’isin jefa talakawan Nijeriya cikin halin shan wuya da ɗawainiyar neman abin da za su saka wa bakin salati. A dalilin haka tallace-tallace da yara maza da mata ke yi a bisa titinan ƙasar nan suka yi yawa. Haka kuma saboda rashin tsaro da kashe-kashen mutane a lungu da saqo na ƙasar nan ya haifar da mutane suna gudu daga garuruwansu na asali. Suna yin hijira daga mahaifarsu zuwa wasu garuruwa na cikin gida da kuma ƙasashen ƙetare, kamar Nijar da Kamaru da Chadi.

Mawaƙin ya faɗakar da ‘yan Nijeriya ne dangane da irin salon mulkin zalunci da shugabannin jam’iyyar da ke mulki suke yi. Wannan ya haifar da rashin zama lafiya, da rashin aikin yi, da ta’addanci da ya haddasa wasu ‘yan Nijeriya suna barin garuruwansu na haifuwa suna hijira zuwa wasu wurare, domin ceton rayuwarsu da dukiyoyinsu. Ya yi amfani da salon kwatance ne, inda ya kwatanta mulkin da da na yanzu da shugabannin da ba abin duniya ne a gabansu ba. Yanzu kuwa, mutane suna neman mulki ne don abin da za su samu na haramun.Wannan dabarar isar da saƙo da mawaƙin ya yi amfani da ita ta yi matuƙar tasiri ga tallata sabuwar jam’iyya da ta zo, wadda za ta taimaka wa al’umma su sami zaman lafiya da walwala, da wadatar abinci, ba sai sun yi bara ko roƙo ba. Don haka su fito ƙwansu da kwarkwatarsu su zaɓi jam’iyyar A.P.C. a lokacin zaɓe don ta kawo sauyi/canji mai ma’ana da adalci zai maye gurbin zalunci. Don haka talakawan Nijeriya su kula da ‘yan siyasa masu ra’ayin tara wa kansu kuɗi ba su yi wa talakawa aiki ba, sai don su wasashe dukiyar ƙasa wanda yake babban zalunci ne

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa Ibrahim Yala hayin banki ya yi wa jama’ar Najeriya gargaxi a cikin waqarsa ta jam’iyyar A.P.P/A.N.P.P, mai suna sungumin bugun lema, inda yake yi wa masu mulkin jam’iyyar habaici a kan zalunci yana cewa:

Ka zo ka fitar da mu a ƙuncin da muke ciki

Yau mun sha wuya a kullum sai farmaki

Ana satar kuɗinmu a yau ba shamaki

Ka ji halin da mu muke ciki Nijeriya.

(Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya)

Ƙunci, da wuya, da farmaki, da satar kuɗi duk xabi’u ne da masu son zalunci suke jefa al’umma ciki a lokacin da suke mulki. Don haka a wannan baiti mawaƙin ya yi wa azzaluman shugabannin da suke mulki a jam’iyyar PDP habaici dangane da zalunci da satar kuɗin gwamnati, wanda ya saka jama’ar Nijeriya cikin ƙuncin rayuwa da zaman ɗar-ɗar saboda farmaki da ake yawan kai masu ba ƙaƙƙautawa. Haka ya jefa Nijeriya cikin halin ni ‘yasu.Shugabannin PDP sun kasance azzalumai masu satar dukiyar Nijeriya suna tara wa kawunansu. Wannan ya sa jama’a suna fama da talauci day a haddasa rashin abinci da rashin tsaro. Yanzu kuwa ga sauyi ya zo, idan ‘Yan Nijeriya za su daure su zaɓi Buhari na jam’iyyar APC ya yi mulkin ƙasa a sami adalci ya ɗore a ƙasa. Jamiyyar da ta tsayar da Buhari ya yi takarar kujerar shugabancin ƙasa,tana da kyawawan manufofi na kawo sauyi ga talakawa. Mawaƙin ya jawo hankalin talakawa ta hanyar yi wa PDP habaici domin ya naƙasa shugabanninta da ya ce, suna satar kuɗin al’umma don tsabagen zalunci, su bar jama’a cikin halin ha’ula’i.Saboda haka mai son a yi masa adalci , to ya zavi jam’iyyar APC mai alamar tsintsiya, wadda Buhari ke takara a ƙarƙashin inuwarta a 2015. Sabda irin rawar da mawaƙan siyasa suka taka wajen yayata kyawawan manufofin Buhari, ya sa talakawa suka jajirce suka zaɓe shi.

4.2.7. Habaici ta Fuskar Hana Ha’inci

Yaudara cikin ma’amala tsakanin mutane ko tsakanin mutane da dabbobi shi ne “Ha’inci”.Wato mutum ya gudanar da ma’amalarsa tsakaninsa da wasu,amma yana nuna nuƙu-nuƙu ga hulɗarsa ta hanyar yaudara da danne haƙƙoƙan al’umma da aka ba shi amana. A hira da na yi da Alhaji Lawali Saraki (Director zonal Education, Gusau) a ranar Alhamis 03/09/2020 da ƙarfe 11:30 na safe, ya bayyana cewa: “Ha’inci na nufin tauye wani haƙƙi ko wata dama da ya dace a bai wa wani mutum, amma sai a hana mashi abin da aka yi masa alkawari duka”. Ya ƙara da cewa, ana iya saka cin hanci da rashawa cikin ha’inci, wanda a halin yanzu ya dabaibaye dukkan al’amuran rayuwar ‘Yan Nijeriya.Wannan bayani ya yi kama da ma’anar da,[ Ƙamusun Hausa :1934] ya ce, “Ha’inci shi ne yaudara da ta shafi kowane fanni na zamantakewar ɗan Adam a rayuwar yau da kullum”.

Idan aka duba za a ga cewa matsalar ha’inci ta bazu cikin kowane fanni na rayuwar ‘yan Nijeriya tun daga ma’amalar yau da kullum tsakanin al’umma har zuwa ga wuraren kasuwanci da na wuraren ayyukan hukuma ko gwamnati. Akwai ha’inci a makarantu da tashoshin mota da ofisoshin ma’aikata da asibitoci; da duk wurin da mutane ke cuɗanya ta harkokin rayuwa.Wannan ya nuna mana cewa, shi ha’inci yana faruwa ko gudana a cikin ma’amular yau da kullum.Ba wai cin hanci da rashawa, ko yaura kaɗai ne ha’inci ba,a’a hatta ka ga wani sharri ko wani bala’i zai sami wani mutum da kake tare da shi ka ƙyale ka ƙi faɗa masa, sai abin ya same shi; sannan ka ce, masa ‘na so in gaya maka’,shi ma nau’i ne na ha’inci.Ko kuma a ba ka wani abu ka bai wa wani, sai ka rage wani abu daga cikin abin da aka ba ka ka ba shi, duk ha’inci ne. Haka kuma ‘yan kasuwa suna yin ha’inci ga abin da suke sayarwa ta hanyar cakuɗa abu mai kyau da maras kyau don ya ƙara yawa, ko ya yi abki. Bugu da ƙari, ya ce, tauye ma’auni wajen awon kaya, ko wani abin da ake aunawa a sikeli,shi kansa ha’inci ne.

A tsarin shugabanci na siyasa, akan sami shugaba ya mayar da dukiyar al’umma abir jin daɗinsa shi kaɗai, to,babu shakka ya ha’incimutanen da suka ba shi amanar jagorancinsu, domin bai yi koyi da shugabannin musulunci ba irin su halifofin da suka gabata.Ya zo cikin Hadisi cewa Sayyidina Umar [yardar Allah ta tabbata a gare shi], kullum ba ya cin abincin dare sai an yi shela a Madina ko akwai wanda bai ci abinci ba. An tambaye shi dalilin yin haka,sai ya ce ; don kada Allah ya tambaye shi a Ranar Hisabi cewa,yaya an ba shi kiwon mutane amma ya bar ɗaya da yunwa,shi ko ya kwana a ƙoshe,(Riyadhussalihin ). Haka kuma yakan ce,

”Wallahi in raƙumi ya mutu da ƙishirwa ko ya faɗa rame,

ya yi rauni a ƙasar Islama ni ne da alhaki”.

An samu cewa, Halifa Umar Ibn Abdul Aziz ya zauna da suturarsa ba wanki har matarsa ta yi masa magana.Ya ce,”Wallahi ba ni da sabulu, kuma ba ni da kuxi”.Ta ce, ba ka karvowa daga baitulmali”? Y a ce “A ranar Hisabi zan iya ba da dalilin da ban yi wanki ba. Amma ba zan iya ba da dalilin ɗsibar kayan amana ba”.[Buhari da Musulum:].

Daga bayanan da muka gani na Sahabban Manzon Allah [S.A.W.] mun fahimci cewa, yin amfani da dukiyar ƙasa da shugabanni ke yi don azurta kansu, da azurta wanda suke so, babban ha’inci ne ga dukiyar al’umma, [Aminu;2003:2].’Yan siyasa su ne suka fi kowa ha’intar al’ummar da suke shugabanta wajen yi wa dukiyar ƙasa rib- da –ciki da danne haƙƙoƙan al’umma da da suka rataya a wuyansu.Mawaƙan siyasa sukan dubi irin nauyin da aka ɗora wa shugabannin al’umma, musamman a lokacin mulkin siyasa (dimokuraɗiyya) su yi nazarin yadda shugabannin ke tafiyar da dukiyar ta hanyar yi wa talakawa ha’inci.Wato suna facaka da dukiyar bisa son ransu; su bar talakawa cikin halin Lahaula. Dukkan ikon sarrafa ko gudanar da dukiyar ƙasa yana hannunsu, amma su kasa bai wa talakawa haƙƙoƙannsu,alhali kuwa sun san cewa Allah zai tambaye su yadda suka gudanar da mulkin al’ummarsu da dukiyarsu da aka basu amana.Kowane mataki na hukuma ana samun masu ha’intar jama’a ga amanar da aka ba su ta dukiya.Misali za a samu cewa,waɗanda aka zaɓe su, su wakilci mutane a majalisu daban-daban suna taka rawa wajen tauye haƙƙoƙan jama’a.Idan sun karɓo wani abu daga Gwamnatin Tarayya ko Gwamnatocin jihohi, sai su ware wani kaso su adana ma kansu. Haka su ma’yan majalisar jihohi da na ƙananan hukumomi suma yin ha’inci ga dukiyar ƙasa.Ha’inci bai tsaya ga shugabanni kaɗai ba,a’a har ma da fagen kasuwanci inda ‘yan kasuwa kan ha’inci abokan hulɗarsu ta hanyar tauye ma’auni ko cakuɗa abu mai kyau da maras kyau domin ya ƙara yawa ko abki.

A siyasance mutane sukan yi ƙoƙarin neman haƙƙoƙansu da aka tauye, sai dai abin ban takaici shi ne,shugabanni ba sukan kula da kukan talakawa ba. Kamar yadda aka ambata a sama, cewa har a makarantu ana samun ha’inci ta ɓangaren malamai idan suka ƙi shiga cikin aji su karantar ko karɓar kuɗi ga ɗalibai da uwayen yara don su gyara masu jarabawarsu. Bugu da ƙari, su ma ɗalibai da ke satar jarabawa ko maguɗin jarabawa duk ɗabi’u ne na ha’inci. Idan ‘yan siyasa ko ‘yan takara suka yi amfani da kuɗi a lokacin yaƙin neman zaɓe ko lokacin jefa ƙuri’a don a zaɓe su, ko ba su cancanta ba;yin haka ya zama ha’inci. Da wannan dalili ne ya sa marubuta waƙoƙin siyasa da na baka sukan duƙufa wajen yi wa shugabanni gargaɗi tare da jawo hankalinsu da su daina yin amfani da kuɗi don mutane su zaɓe su. Domin yin haka shi zai sa a sami shugabanni da ba su da adalci masu ƙarfafa hainci a cikin alumma. Misali Yala hayin banki ya yi wa Ibrahim Badamasi Babangida da gwamnatinsa habaici domin mutane su fahimta da irin illar da ha’inci yake haifarwa ga lalacewar tarbiyar al’umma.Mawaƙin ya kawo misali da lokacin mulkin janar Ibrahim Babangida wanda ya rushe zaɓen “jun tuweb” a jamhuriya ta uku da ba ta yi nasara ba.Wannan mataki na rushe zaɓen jun Tuwel da ake zargin an yi ha’inci ya haddasa tashe-tashen hankula, da yin hijirar dole daga arewanin Nijeriya zuwa kudancin Nijeriya,wanda mutanen kudu suka yi. A sanadiyar haka an rasa ɗimbin dukiyoyi da rayuka saboda haɗarukkan motoci da aka yi ta samu a hanyoyinmu na Nijeriya. Mawaƙin yi wa gwamnatin Babangida habaici inda yake cewa:

Duk wahalar da muke ciki yau to ɗan Minna ya saka mu fama,

Wai burinsa ya wanke laifi na jun tuweb a wurin na yamma,

Yau son kanka ya samu halin da za adaɗe babu warwarewa.

Dubi halin da ya sa arewa ya mance takara zai yowa,

Wai Baba me ka bari haƙiƙa da za mu bari har kayo wucewa,

Koma ka ƙare yaƙin gidanka gwamnanka zai kai ka kushewa.

 (Ibrahim Yala Hayin Banki: C P C Canji).

 

A irin yunƙurin da gwamnatin mulkin soja ta wancan lokaci ta yi na neman zarcewa ga mulki ta hanyar kafa jam’iyyun siyasa, da ita kanta ta ƙirƙiro su.An gudanar da zaɓe a ranar, 12/6/1993, domin maida mulki ga hannun farar hulla, amma saboda ana tuhumar an tafka maguɗin zaɓe, wato an yi ha’inci ga zaɓen ta hanyar arigizon ƙuriu ya sa aka soke zaɓen na jun tuweb. Soke zaɓen ya jefa ƙasar nan cikin ruɗami. Mawaƙin ya yi amfani da habaici cikin waƙarsa don ya gargaɗi ‘yan Nijeriya da su sa ido game da abin da ya faru a baya. Saboda haka ya nuna wa jama’a cewa, idan suka sake suka bari irin wannan abu ya sake faruwa, to za su kuka da kansu.Mawaƙin yayi amfani da kalmaomin ,ɗan Minna,da baba, domin ya jawo hankalin mutane su fahimci saƙon da yake son isarwa ba tare da ya ambaci sunan shugaban ba.Da waɗannan kalmomi ne ya bayyana wa mutane halin da shi wannan shugaba da ya soke zaɓen jun tuweb ya jefa ‘yan Nijeriya cikin halin wahalar da suka sami kansu ciki. Domin cimma wata manufa ta ƙashhin kansa.Ɗan Minna, da baba, yana nufin Ibrahim Babangida wanda ya ƙirƙiro jamiyyar S.D.P. da N.R.C. domin ya cire kakin soja ya saka kayan farar hula.

Mawaƙin ya yi wa wancan shugaba habaici ne da cewa,duk mulkin da ya yi da kuma ha’incin da ya yi wa ‘yan Nijeriya na soke zaɓen jun tuweb,1993,bai ishe shi ba.Saboda haka yake tunatar da shi cewa, me ya manta a gidan gwamnati wanda yake son ya koma domin ya ɗauko ?.Ko laifin da ya yi wa mutanen yamma yake son ya wanke? Don haka mutane su sani cewa ha’inci ba komi yake haifarwa ba, face hassasa fitina da rashin zama lafiya da talauci a ƙasa. Saboda haka mutane su daure ranar zaɓe su zaɓi Buhari mutum nagari, wanda ba zai ha’ince su ba wajen rabon dukiyar ƙasa. Haka kuma ba za ya yi sama- da –faɗi da kuɗaɗen gwamnati don ƙashin kansa ba; kamar shugabannin jam’iyyar PDP da ake mulki a lokacin da yake ƙoƙarin tallata Muhammadu Buhari ga yan Nijeriya. Ha’inci babbar illa ce ga shugabanni; domin yakan dushe kwarjininsu a idon talakawa.Yankin arewa ,yanki ne da ke fama da rashin masu kishin cigaba,wanda ya jawo wa yankin faɗawa cikin babban ƙalubale na “kuɗi ya fi mutunci’’..Wannan ya sa aka wayi gari yankin ba ya da wani tasiri na a zo a gani dangane da cigaba tun lokacin da aka dawo mulkin siyasa har zuwa wannan zamani da muke ciki a yau.

Mawaƙin ya yi amfani da salon jawo hankali inda ya yi amfani da aron kalmar Turanci June twelve. Sannan kuma ya yi amfani da kalmar lamiri don ya sakaya sunan wanda yake yi wa habaici. Da wannan salon sakaya suna da kuma fadar june twelve, ya jawo hankalin masu saurare su tsunduma cikin kogin tunanin gano wanda ake nufi da habaicin.Amma don ya fayyace wa masu saurare, sai ya ambace shi da ɗan Minna da kuma baba na yamma. Wannan wata dabara ce ta jawo hankalin masu saurare su tuna tarihin abin da ya faru a shekarar 1993.Wato, soke zaɓen da aka yi wa Abiola na jam’iyyar SDP, wanda ya haddasa tashe-tashen hankula tsakanin ‘yan Nijeriya, har wasu ƙabilu suna hijira suna komawa yankunansu na asali. Wannan dabara ta isar da saƙo da mawaƙin ya yi amfani da ita ta yi matuƙar tasiri wajen wayar wa mutane kawunansu cikin ƙanƙanen lokaci har aka samu sauyin gwamnati mai maan a Nijeriya.

Har wa yau, Ibrahim Yala, a cikin waƙarsa ta APP/ANPP, ya yi wa P.D.P. habaici, inda ya nuna cewa shugabannin PDP su ne ɓarayi waɗanda suka kwashe kuɗin ƙasa saboda tsabagen ha’inci har dukiyar marayu ma ba su bari ba. Misali, yana cewa:

 Ku da kuke ta sukan Buhari uban ƙasa,

Ku ne kun ka kwashe Fetur da kuɗin ƙasa,

Don tsabar rashin mutuncinku cikin ƙasa,

Har ma dukiyar marayu kun murɗiya.

 (Ibrahim Yala Hayin banki: waƙar APP)

 

Mawaƙin ya na faɗakar da ‘yan Nijeriya game da satar dukiyar al’umma da wasu shugabanni suka yi a lokacin da suke bisa karagar mulki. Ya bayyana cewa,kwashe man fetur da kuɗi su mallake don amfanin kansu, shi ne ha’inci ,don yin haka ya saɓa wa ƙa’idar hukuma da amanar da aka ɗora a kansu. Ma’ana, kyakkyawar manufa ta kowace jam’iyya ita za ta sa a zaɓi ‘yantakararta, masu manufa mai kyau, don haka Buhari shi ne ya fi cancanta ya mulki ƙasar nan.

Mawaƙin yana son ya gargaɗi ‘yan siyasa da su guji yin ha’inci ga zaɓuɓɓuka ta hanyar ba da kuɗi ga talakawa don su sayi ƙuri’ursu. Idan har suka yi amfani da kuɗi suka ci zaɓe, babu shakka ba za su yi wa talakawa aikin komi ba sai sun maida kuɗaɗen da suka kashe suka ci zaɓe.

Ha’inci yana nufin maguɗi ko aikata wani abu da ya saɓa wa ƙa’idar wata al’umma ko shari’a a lokacin gudanar da ma’amula tsakanin mutane ta shugabanci ko jagorancin wannan al’ummar. Ibrahim Yala ya haskaka fitilarsa ga ‘yan Nijeriya domin su gane kyakkyawar hanyar da za su bi su sami nasarar zaɓen mutanen da suka dace. Masu kishin ƙasa, waɗanda ba su ha’inci ga amanar da aka ɗora masu da kuma tauye haƙƙoƙin talakawa. Ga abin da yake cewa:

Zan yi kiran ku Ribas, Fatakol da ‘yan Imo

Gar ku bari a cuce ku da tarin rantsuwa

Dan na tabbata ada ba ku da damuwa,

Yanzu kuma ga Buhari shi ne bai danniya.

 (Ibrahim Yala Hayin Banki: APP/ANPP).

Dukiyar da shugabanni suke dannewa ta talakawa, su maishe ta tasu ba ta kanyi albarka ba komi yawanta.Saboda haka masu gurin su shiga siyasa don su ci dukiyar jam’a,wannan babban kuskure ne.Su sani duk abin da suka tara za a wayi gari ya ƙare, ko a mutu a bar shi. Hausawa suna wata Karin Magana cewa; ”Kashin Kare bai Taki”.Wato duk abin da mutum ya mallaka ta hanyar ha’inci ba zai ɗore ba. Babu ko shakka duk abin da aka same shi ta hanyar ha’inci, komi kyawonsa ko yawansa ba zai tafi ko’ina ba.Manufa, ba zai yi albarka ba. Wato, a nan mawaƙin yana gargaɗin masu sauraron waƙa su fahimci yadda ha’inci yake yin illa ga masu yinsa da waɗanda ake yi wa, wato talakawan ƙasa dasu kansu masu mulki. Wannan baiti da mawaƙin ya kawo yana faɗakar da mutane da ‘yan siyasa musamman na jahohin da mawaƙin ya ambata cewa,ita dukiyar da aka tara ta hanyar zamba ko ha’inci, musamman wadda shugabanni da aka zaɓa don su wakilci al’umma suka sata a gwamnatin tarayya, ko a jihohi ko ƙananan hukumomi, ba ta ɗorewa ko cigaba. Saboda kuɗin haramun ne ko kuma dukiyar zalunci.Don haka mutane su sani cewa akwai hisabi a gobe kiyama ga duk wanda ya ha’inci al’umma ko ya zambace su, ya kwashe dukiyar ƙasa don ya ji daɗi da shi da matansa da ‘ya’yansa; ya bar talakawan da suka zaɓe shi cikin ƙuncin rayuwa.Yala ya yi kira ga talakawa da ‘yan siyasa da su guji ha’inci ko zambatar talakawa wajen sace dukiyar ƙasa suna gina kansu da ita.Su sani cewa, dukiyar cin amana ko ha’inci da aka tara ta hanyar yin amfani da ƙarfin mulki, ba ta ƙarko, kuma ba ta albarka, komi yawanta kuma komi kyanta. Dalilin haka ya sa Hausawa ke wannan karin Magana, cewa “kashin kare bai taki”.

A nan mawaƙin ya yi amfani da dabarar isar da saƙo ta hanyar faɗaɗa kiransa ga dukkan al’ummar Nijeriya, ba wai Hausawa ko Fulani da suke yankin Arewacin Nijeriya ba. Ya kira sauran ƙabilu da ke Ribas, da Fatakol da ke kudu-maso kudu don su ma su san ana yi da su.Wannan wata dabara ce ta kawar da siyasar ƙabilanci da mawaƙin ya yi amfani da ita domin ya jawo hankalin yan Nijeriya cewa har yanzu Nijeriya muna nan uwa ɗaya, uba ɗaya. Wani misalin ha’inci shi ne inda Yala yake cewa:

Su suka sanya rashawa yau tay yo yawa

Su suka tsaida arzikin’yan Nijeriya

Su ke kulle kamfani don har sun saya

Sun raba talaka da aiki ‘ya’yan tsiya.

 (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

 

Karbar rashawa wani nau’I ne na ha’inci wanda shugabanni da masu riƙe da muƙamin gwamnati ke yi,idan wani ya je neman wata buƙata wurinsu.Mawaƙin ya faɗakar da al’umma cewa, ha’inci yana saka arzikin ƙasa ya rushe domin Allah ya la’anci mai ba da rashawa da mai karva. (Hadisi na ) Sayar da kamfuna na gwamnati da shugabannin da suka gabata suka yi ya saɓa wa manufar dimokuraxiyya. Haka kuma duk inda rashawa ta yawaita, to rashin aikin yi zai yi tsamari; domin ba duka kowa ke iya ba da kuɗi kafin ya sami aiki ba. Wannan hali na ha’inci, wato cin hanci da rashawa da satar dukiyar al’umma wani abu ne da yake ci wa ‘yan Nijeriya tuwo a ƙwarya. Wannnan ya yi matuƙar tasiri ga taɓarɓarewar arzikin ƙasa da rashin aikin yi ga dubban ‘yan Nijeriya.

Kamar yadda tsarin mulki ya tanada, kariyar dukiyoyi da mutuncin al’umma yana daga cikin manufofin ko qa’idojin da kowace jam’iyya za ta cika kafin a yi mata rijista, (Draft Constitutions: 1998). Saboda haka duk jam’iyyar da ta kasa cika ƙa’idojin ko ta saɓa wa manufofinta na kare mutunci da dukiyar al’umma, babu shakka za ta kasance ta ha’inci mutanen ƙasa. Don haka mawaƙin ya yi wa jam’iyya mai mulki gargaɗi da kada ta saɓa wa waɗannan ƙa’idoji na kare mutuncin al’umma da dukiyar ƙasa. Kamar yadda mawaƙin ya ce, masu riƙe da gwamnatin waccan jam’iyya, su ne suka assasa cin hanci da rashawa, wanda ya jefa ‘yan Nijeriya cikin halin ha’ula’i da rashin aikin yi ga mutane da matasa da dama. Wannan ya faru ne a sanadiyar sayar da kamfanonin gwamnati ga mwasu ‘yan tsiraru.Hakan ya kawo wa‘yan Nijeriya da dama rasa ayyukansu inda suke samun abin da suka ci da kansu da iyalansu. Saboda haka mawaƙin ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su yarda su zaɓi Muhammadu Buhari donya ceto ƙasa daga mawuyacin halin da ta faɗa ciki.

Mawaƙin ya yi amfani da salon habaici inda ya ɓoye sunan waɗanda yake suka, sai ya yi amfani da kalmomin lamirin suna na ‘su’ don ya jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da yake isarwa gare su.Wannan sakaya suna da mawaƙin ya yi wata dabara ce ta ɓoye sunan waɗanda ake yi wa habaici don kariyar mutuncinsu a idon duniya.Ga al’adar Bahaushe ba ya kan so ya riƙa faɗar sunan wanda yake yi habaici ba don gudun ka da ya ci fuskar mutumin dayake yi wa habaicin; domin yin haka yana kawo fitina atsakanin al’uma da wanda ake yi wa habaici.Saboda haka sai mawaka su riƙa amfani da kalmomin lamiri ko siffofin wanda ake jifa da habaici.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a cikin waƙarsa, Dauda Rarara,yana cewa:

Uwar cuku-cuku an kawar da shi,

Babu cuku-cuku yanzu ko na rabin awa.

 (Rarara: Waƙar Baba Tsoho ya sauka APC).

Cuku-cuku wata ɗabi’a ce ta wasu mutane don yin ha’inci wurin hulɗa tsakaninsu da abokan hulɗa. Wasu shuganni suna amfani da damarsu ta mulki su riƙa karɓar cin hanci a lokacin da suke kan karagar mulki. Da irin wannan ɗabi’a ce Rarara yake faɗakar da masu irin wannan ɗabi’a cewa yanzu fa ƙarya ta ƙarewa uwar cuku-cuku ba zi sake yi ba;saboda tun da mai gaskiya ya yi nasara lashe zaɓe duk wani ha’inci zai kau.Wato, nasarar zaɓen Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa,uwar cuku-cuku da ‘yan korensu ƙaryarsu ta ƙare. Ha’incin da suke yi na cuku-cuku, wato karɓar na goro ga masu neman buƙata yakau.Haka ma murɗiya da handame dukiyar al’umma za sugushe, saboda basu da bagiren yin haka ko na rabin awa domin basu ga fili ba. Wannan habaici da Rarara ya yi wa wasu ‘yan siyasa na jam’iyyar PDP, wani gargaɗi ne ga mutane domin su gyara halayensu na ha’incin dukiyar ƙasa da kuma kuma cin hanci da rashawa.

Wannan baiti yana gargaɗin mutane cewa, duk matsayin da kake a kansa mutane ba su son ka, har dai a ce kai shugaba ne mai ha’inci ko da kuwa su ‘ya’yan jam’iyyar da ke mulki ne. Don haka mawaƙin ya yi wannan habaici ne don ya jawo hankalin ‘yan Nijeriya su kula su zaɓi Buhari duk da kasancewar suna cikin jam’iyya mai mulki ko ‘ya’yan jam’iyya ɗaya ne.Yin haka shi ne zai sa a kaucewa uwar cuku-cuku.

Mawaƙin ya yi amfani da salon sarrafa harshe ta hanyar amfani da malmomin cuku-cuku da suka bayyana suna siffatau a tsarin nahawun Hausa. Cuku-cuku ta nufin murɗiya ko kai- komo da mutum ke yi don ya sami wani abu da yake buƙata ga mutane ko da bai cancanci samun abun ba.Wato, mutum ya bi hanyar da ba ta dace ba wajen neman biyan buƙata.Mawakin ya yi amfani da wannan kalma ta cuku-cuku domin ya yi wa wani ɗan siyasa habaici.Ya yi amfani da wannan dabara don ya jawo hankalin mutane su kula da mutumen ya kira shi da suna ‘uwar cuku-cuku domin ka da ya jefa su cikin ɗabi’unsa na cin hanci da rashawa.

Kamilu ɗan almajirin mawaƙa ya yi irin wannan habaici a cikin waƙarsa mai suna,” Karen bana maganin zomo”. Mawaƙin yana cewa:

Gurin APC ta yi aiki,

Gurin jaki ya dau kaya.

 (Kamilu: waƙar APC)

Jaki wata dabba ce mai ƙafa huɗu kamar sauran dabbobi. Ana amfani dashi wajen ɗaukar kaya don sufari ko kuma a wasu ayyukan gida nayau da kullum. Kamilu kwatanta manufar jam’iyyar APC ta yi wa talakawa aiki idan ta kafa gwamnati da sauran jam’iyyun siyasa da muke da su.Ya ce, jam’iyyarsa za sa samar da abubuwan more rayuwa da jindaɗi da walwala; da kuma ayyukan raya birane da karkara da ƙasa baki ɗaya,suna daga cikin manufofin kowace jam’iyya.Saboda haka jam’iyyar APC manufarta ita ce, ta yi wa talakawa aiki da za su amfana dashi. Shi kuwa jaki don ɗaukar kaya aka yi shi, ya ɗauka ya kai wani gari ko inda ake so.Wannan baiti yana fadakar da mutane cewa, manufar jam’iyyar APC ta banbanta da ta jaki ta fuskar haɓɓaka tattalin arziki da wadata ƙasa da abubuwan more rayuwar talakwa.Shi kuwa jaki a nan ,mawaƙin yana habaici ne ga wani ɗankara na wata jam’iyya da take neman ta kafa gwamnati.Mawaƙin ya kwatanta wannan ɗankara da jaki,inda ya bayyana cewa manufarsa kawai ya ɗau kaya, ba ya samar da kayan ba.Wato, idan aka zaɓe shi,zai wawushe dukiyar al’umma. Ita kuma jam’iyyar APC za ta gina ƙasa, ta samar da wadatar abinci da ayyukan yi ga mutane. Saboda haka mawaƙin yake gargaɗin mutane da su zaɓi jam’iyyar APC domin ta cika gurinta.

Mawaƙin ya kwatanta wani mai neman shugabancin ƙasa da jaki, saboda manufarsa ya ha’inci al’umma ga amanar da za a ɗora masa. Ɗaukar kaya a nan yana nufin satar dukiyar al’umma kamaryadda mawaƙin ya siffanta jaki,haka nan shi wannan ɗansiyasa yake da nufin ɗaukar kuɗin gwamnati idan ya sami muƙami. Wannan ya nuna mana cewa masu ha’intar dukiyar jama’a idan suka riƙa wata kujera ta gwamnati kamar jaki suke afagen ɗaukar kaya. Saboda haka a zaɓi Buhari shi ne mafita ga hana wancan jaki ɗaukar dukiyar al’umma ya mallaka wa kansa.

A wannan baiti da ya gabata mawaƙin ya yi amfani da salon kamce, a inda ya kwatanta wani ɗan siyasa da jaki. Jaki yana da ɗabi’u daban daban da suka haɗa da rashin basira,wato daƙiƙanci wanda bai da wata dabara sai wadda aka ɗora shi a kai.Haka kuma ba a cin namansa sai dai idan ya mutum a yar da shi bola.Sanna kuma ya fi ƙwazo a wurin ɗaukar kaya.Wannan salon kwatance ko kamance da mawaƙin ya yi amfani da shi wata dabarar isar da saƙo ce ga jamaa ta hanyar dabbantar da ɗan takara domin a jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da ake son isarwa gare su.

A taƙaice ha’inci yana nufin zamba ko tauye wa masu haƙƙi haƙƙinsu; ko ha’intar al’umma ta hanyar tauye masu haƙƙin da ya dace a ba su. Ko kuma a yi musu aikin da ya dace bisa ga dokar tsarin mulkin ƙasa.Wato,cin amanar ƙasa ta hanyar yin sama da faɗi da dukiyar ƙasa da wasu shugabanni da masu muƙaman gwamnati ke yi shi ne ha’inci. Don haka marubuta da sauran mawaƙan siyasa da dama suna amfani da habaici cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin jama’a wajen sa ido ga yadda shugabanni suke tafiyar da mulki da kuma nuna wa ‘yan siyasa muhimmancin zaɓen mutanen da suka dace masu gaskiya da riƙon amana.Kamar yadda muka gani a sama cewa shugabanni na wannan zamani sun fi mai da hankali ga abin da za su samu ga mulki bisa ga yi wa talakawa aiki. Don haka ne ma suke fafatakar ganin sun zarce ga mulkinsu ko ta wane hali, saboda su sami damar yi wa jama’a ha’inci ga dukiyar da aka ba su amana.Wato su ha’ince su, su wasashe dukiyar ƙasa,ko ƙin yi masu ayyukan ci gaban ƙasa dasuka ɗauki alƙawura a lokacin da suka je yaƙin neman zaɓe.

4.2.8. Habaici ta Fuskar Rashin Cika Alƙawari

Shi kuwa Ibrahim Yala Hayin Banki a nasa tunani, yana ganin cewa, habaici ga shugabanni dangane da alƙawuran da suka ɗauka a lokacin da suke yaƙin neman zaɓe wata hanya ce ta faɗakar da shugabanni da sauran al’umma su gyara halayensu ta hanyar cika alƙawalin da suka ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe. Ya yi amfani da kalmomin habaici don ya tozartar da shugabannin wata jam’iya, sannan ya yaba ma manufofin jam’iyyarsa ta APC zuwa ga al’ummar Nijeriya. Sannan kuma ya gargaɗi jama’a su ƙaurace wa zaɓen ‘yan takara marasa mutunci da rashin cika alkawali.Yana cewa:

Wasu sun yi mulki a baya Nijeriya,

Sun kashe wanda ba su so sun cirri dukiya

Sun raba kanmu sun yi mulki ba waiwaya

Ka ji su baba ɗan gajere maras gaskiya.

 (Yala:Yau Nijeriya riƙo sai mai gasiya).

 

Shugaganni da suka yi mulki a shekaru da suka wuce sun yi abubuwa da damana kashe al’umma ta hanyar jefa su cikin matsin tattalin arzik da talauci da yunwa da rashin aikin yi.Da wannan hali ne mawaƙin yake jifar waɗancan shugabanni da habaici domin ya faɗakar da ‘yan Nijeriya game irin halin da shugabannin suka jefa su.Wannan baiti da mawaƙin ya kawo a sama saƙon gargaɗi ne zuwa ga ‘yan Nijeriya da ka da su kuskura su sake maimaita wani kuskure na sake zaɓen waɗancan mutane da suka kashe mutane a lokacin mulkinsu, suka kuma sace dukiyar al’ummar ƙasa.Abubuwan da suka jawo jefa jamaa cikin halin da suka samu kansu, akwai rashin cika alkawali da shugabanni suka kasa cikawa,wanda ya saka suka kasa yin abin da talakawa za su amfana da shi. Maimakon su yi abubuwan da suka ɗauki alkawali a lokacin yaƙin neman zaɓe, sai suka maida hakali ga satar dukiya da kashe duk wanda basu so, da kuma raba kawunan ‘yan Nijeriya ta fuskar addini da ƙabilanci ko ɓangaranci. Su wane ne suka yi haka, su ne waɗanda suka yi mulki a farkon jamhuriya ta huɗu ,wato,’yan jam’iyyar PDP.

Rashin cika alkawali ga shugabanni ba ƙaramar illa bace, domin yakan haifar da koma baya ga kowane fanni na rayuwar al’umma.Dubi yadda shugabanni suka fita batun aiwatar da ayyukan da suka yi wa talakawa alƙawali, sai suka mai da hankali ga satar dukiyar al’ummar ƙasa suna Tarawa ɗiyansu don gudun ka dasu yi talauci. Wannan ya sa suka manta da abubuwan dasuka yi talakawa alƙawari na samar masu ingantaccen ilimi da wutar lantarki,ruwan sha a birane da ƙauyuka, da dai sauran abubuwan more rayuwa. Wannan dalili ne ya sa mawaƙin yake gargaɗin talakawa da su zaɓi Muhammadu Buhari domin ya kawo masu ci gaba ta fannoni daban daban.

Mawaƙin ya yi amfani da salon jawo hankali, inda ya siffanta masu mulkin da wata halitta da cewa su suka raba kan yan Nijeriya domin su tafiyar da mulkinsu ba tare da an tsamgwame su ba. Kalmar ɗan gajere, siffa ce ta halitta, wadda mawaƙin ya laɓe a kanta ya soki masu mulkin.Wannan dabara ce ta isar da saƙo ba tare da an faɗi ko an ambaci sunan mutum ba. Haka ya sa jama’a su farga da saƙon da ake son isarwa gare su cikin gaggawa, suka zaɓi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa.

Har wa yau Ibrahim Yala ya ci gaba da cewa:

Su suka rusa ilimi yau Nijeriya

Su suka ɓata tattalin yau Nijeriya

Lantarki ƙasarmu yau yaz zama na jiya

Allah ya isa macutan Nijeriya.

 (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

 

‘Yan siyasa sukan ɗau alƙawalin cewa idan aka zave su suka kafa gwamnati, za su maida hankali wajen ilimi da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kum samar da wutar lantarki a ƙasa. Da zaran aka zaɓe su, saisu manta da alƙawurran da suka ɗauka. Wannan ne ya sa mawaƙan siyasa suke amfani da habaici domin su faɗakar da al’umma cewa waɗannan mutane da suka saɓa suka kasa cika alƙawali; bai kamata a sake zaɓen suba. Sannan kuma su gargaɗi ko tunatar da shugabanni game da rashin cika alƙawalin da suka yina samar da abubuwan more rayuwa ga talakawa.

Mawaƙin ya yi wannan habaici ne don ya tunatar da shugabanni da suka wuce, cewa, alƙawurran da suka ɗauka basu cika suba. Saboda haka, ko sun fito neman wani muƙami ba za a kula dasu ba, domin sun kasa cika alƙawurran da suka ɗauka a lokacin da suka yi mulki.Azamanin mulkinsu, komai ya lalace, babu ruwan sha,harkar ilim ta lalace.Babu wadatacciyar wutar lantarki, tattalin arzikin ƙasa ya ruguje.Saboda haka, yanzu lokaci ya yi datalakawa za su kaucewa zaɓen waɗannan mutane, su zo su zaɓi Buhari domin talaka ya wala ya sami wadata, ya ɗanɗani roman dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Mawaƙin ya yi amfani da dabarunjawo hankalin mutane ta tunatar da su abubuwan da yan siyasa da ke mulki suka kasa aiwatarwa bayan da suka ɗare kujerar mulkin ƙasa. Abubuwan sun haɗa da ilimi da lantarki da kuma ruguje tattalin arziki. Waɗannan muhimman abubuwa ne ga al’ummar Nijeriya, domin su ne gimshiƙin ci gaban kowace alumma ta duniya,ba wai Nijeriya kaɗai ba. Duk ƙasar da ta kasa samar da su to, za ta zama koma baya ga sauran ƙasashe.Domin ya isar da saƙonsa ga jamaa sai ya ƙara da cewaAllah ya isa saboda ya jawo hanklin mutane su ɗauki saƙon da muhimmanci.

Dauda kahutu Rarara ya yi wa wasu shugabanni habaici dangane da rashin cika alkawalin da suka yi wa talakawa a lokacin yaƙin neman zaɓe. Yana cewa:

Al’ummar birni da ƙauyuka,akwai wani ɗan saƙo,

Baba yace a gaya wa ɗan gari ko kuma baƙo

Mui ta noma kiyo abinci ba zai yanke ba.

 (Dauda Rarara: Baba Tsoho ya sauka).

 

Wasu mawaƙan siyasa sukan so su faɗakar da al’umma game da yanayin da ake ciki na manufar ‘yan takara ko waɗanda suka riga suka kafa gwamnati.Haka ya sa Rarara ya taka tasa rawa wajen faɗakar da al’umma dangane da ƙudurin Muhammadu Buhari na bunƙasa aikin gona da kiwo waɗanda su ne gimshiƙi daga cikin manyan hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Shugabanci kowane iri ne, dole a tsara shi ta yadda zai amfani waɗanda za a mulka,wato, talakawa. Tsarin mulkin siyasa ya tanadi a faɗakar da al’umma irin shirin da kowace jam’iyya ta yi domin taimaka ma talakawan da suka zaɓe ta. Saboda haka jam’iyyar APC ta Muhammadu Buhari ta ƙuduri haɓɓaka aikin gona da kiwo domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuma dogaro da kai. Dalilin haka ya sa Rarara ya yi wa wasu jamiyyu habaici don ya soki irin tsarin da suka yi. Ya jawo hankalin mutanen birni da ƙauyuka su zaɓi APC don ta taimaka masu ga aikin gona ta hanyar samar masu da wadataccen takin zamani.Idan mutane suka mai da hankalinsu ga noma, to, babu shakka abinci zai wadata.Idan aka sami wadatar abinci a ƙasa, to, za a sami bunƙasar tattalin arziki.Saboda haka Muhammadu Buhari wanda ke da aniyar kawo ci gaba ta fukoki da dama a Nijeriya ya cika alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe na samar da wadataccen takin zamani da kuma harkar kiwon dabbobi.

Mawakin ya yi amfani da salon siffantawa a cikin wannan baiti. Ya siffanta Buhari da damina, wadda Hausawa ke cewa, ‘uwar albarka’. Saboda irin alherin da ke cikin damina na samun wadataccen abinci ya sa Rarara ya siffanta mulkin Buhari da damina domin ya samar da abubuwan da suka taimaka ma manoma wajen bunƙasa harkokin noma. Wannan salo da mawaƙin ya yi amfani da shi, wata dabara ce ta jawo hankalin mutane su fahimci saƙon da ake isarwa gare su.

Shi ma da yake habaici zuwa ga masu mulki da suka gabata na jam’iyyar PDP, Ibrahim Yala yana cewa:

Kun cuce mu da, da yanzu mun ankare,

Kar ku sake ku zo wurinmu ba ma tare,

Don na san da kai na yamma mai halin kare,

Mun riƙe mu Buhari shi ne mai gaskiya.

 (Ibrahim Yala: Waƙar APP).

Mawaƙin yana faɗakar da shugabannin PDP cewa, su tuna irin cutar da suka yi wa al’ummar Nijeriya, suka hana kowa ya ji daɗi. Saboda haka duk wani yunƙurin tazarce da suke so ba zai yi tasiri ba; domin yan Nijeriya an sha su sun warke.DON haka, sun riƙe Buhari shi mai gaskiyar da zai iya cika alƙawurran da ya ɗauka na samar da wadatar abinci, da lafiya da sauran abubuwan more rayuwa.

Saƙon da wannan baiti yake ɗauke da shi shi ne, yanzu talakawan Nijeriya canjin gwamnati suke nema mai adalci da za ta taimakawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a ƙasa.Samun haka kuwa ba zai yiwu ba, sai an zaɓi Buhari mai gaskiya wanda shi kaɗai zai iya kawo wa Nijeriya da al’ummarta sauƙin rayuwa saboda gaskiyarsa.Cika alƙawari sai dattijo, wanda ba ruwansa da tara abin duniya irin Muhammadu Buhari.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kamance, inda ya kamanta shugaban Nijeriya na jamiyyar PDP da kare. Kare wata dabba ce daga cikin dabbobin gida da ake amfani da shi wajen gadin gida da farauta da sauran ayyukan tsaro.Sai dai kare yana da wata ɗabi’a ta rashin dangana, musamman a harakar mata. Irin wannan ɗabi’a ce mawaƙin ya kamanta wannan shugaba da ita, har ya ce,kar su sake su zo wurinsu wajen neman a sake zaɓen su zarce domin a yanzu ba su tare.,Wato ‘ya’yan jam’iyyar PDP, da shugabansu da ke mulki,su nesanta kansu da mutane domin ba a tare. Mutane Buhari suke so, kuma shi za su zaɓa.Wannan dabarar isar da saƙo da mawaƙin ya yi amfani da ita ta taimaka wa yan Nijeriya wajen zaɓen mutumin da ya dace ya shugabanci al’ummar Nijeriya.

4.2.9.Habaici ta Fuskar Adawa

Bahaushe yana kallon adawa a matsayin rashin gamsuwa ko kushewa ga yadda wasu suke gudanar da wani abu da ya shafi rayuwar yau da kullum, ko mulki da shugabanni ke aikwatarwa.Wato kushewa ga wani mutum da Allah ya ba shugabanci ko dukiya ko wata ɗaukaka ta ilimi da dai sauransu.Wannan irin jiyewa da mutane ke nuna wa ga wanda Allah ya yi wa wata baiwa, ko ɗaukaka tana shiga cikin zukatan masu yin ta, har su riƙa jifar masu wannan baiw da kalaman ɓatanci don su ruguza kwarjininsu a idon jama’a.Idan shugabanni ne, sai a riƙa jifar su da ƙazuffa iri-iri; don su tayar masu da hankali.

Asalin adawa ya fito tun daga farkon hallitar ɗan Adam a doron ƙasa.Allah [S.W.A.] ya faɗa a cikin Alƙur’ani mai tsarki cewa, ya halicci ɗan Adam,sannan ya umarci Mala’iku su yi masa sujada, kamar haka:

“Sai suka yi sujada, face Ibilisu ya ƙi, kuma ya yi girman kai,kuma ya

Kasance daga kafirai”, [Qur’ani 2:34].

Farkon nuna adawa a duniya ita ce, wadda Ibilis ya nuna wa Annabi Adam lokacin da Allah ya umurci Mala’iku su yi masa sujada. Da wannan adawa ce da Iblis ya nuna wa Adamu, za a iya cewa, adawa ba ƙaramar ƙiyayya ce ba tsakanin ɗan Adam da Ibilis.

Kamar yadda aka gani a ayoyin da suka gabata,Allah [S.W.A.] Yana faɗakar da ‘ya’yan Adamu su nisanci maƙiyin Ubansu,wanda ya sabbaba musu wahalar zuwa duniya da haɗuwa da takalifi a cikinta. Kuma bin wannan takalifi ya zame musu sauƙi idan sun bi shi yadda Allah ya ce, amma idan sun bi hanyar shaiɗan ,maƙiyinsu, to, babu abin da zai samu a gare su face ƙarin wahala daga duniya har lahira. Don haka adawa ko ƙiyayya da ɗan Adam ke yi wa wani ko wasu mutane da Allah ya yi wa wata baiwa, ta samo asali ne daga adawar da Shaiɗan ya nuna wa Annabi Adamu [A.S.] da matarsa Hauwa’u.

Duba da irin bayanai da suka gabata daga Alƙur’ani mai girma, za a fahimci cewa, adawa ta samo asali tun farkon halittar ɗan Adam. Kuma kalma ce ta Larabci, wato “Adawawadda ke nufin ƙiyayya ko nuna rashin gamsuwa ga wani abu ko shugabanci da wani ko wasu mutane ke aiwatarwa.Bahaushe ya aro wannan kalma sannan ya bar ta kamar yadda take daga harshen Larabci, ‘Adawa, domin ta dace da ginin Kalmar Hausa da isar da saƙon da yake son isarwa ga jama’a. Amma ma’anarta ta harshen Larabci ba ta canja ba. Kalmar adawa tana nufin nuna ƙiyayya ko kushewa ga wani mutum a kan wata ɗabi’a ko matsayi da wani ko wasu mutane ke aikatawa a bayyane ko a ɓoye. Sai dai, shi Bahaushe yana kallon adawa a matsayin jiyewa ko kushewa da sa ido ga abubuwan da masu mulki suke aiwatarw. Idan aka tattara waɗannan ma’anoni damasana da Hausawa suka ba adawa, za a iya cewa, adawa tana da alaƙa makusanciya da hassada sai dai ɗan bambancinsu kaɗan ne.Idan aka koma a ɓangaren zamantakewar ɗan Adam, da hulɗarsa tsakaninsa da sauran jinsin mutane ta yau da kullum, adawa tana taka rawar gani wajen haskaw wa masu mulki ko shugabannin siyasa fitila su gyara kurakuran da suke aikatawa a mulkinsu.Wato, adawa ‘gyara kayanka ce, wadda ta fi sauke mu raba’ a sha’anin mulki da sauran mu’amulolin yau da kullum..

Adawa ta yi tasirin gaske wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, musamman ta fuskar sana,o’inmu na gargajiya da masana’antu daban-dabanidan aka lura da yadda adawa ta taka rawa wajen jawo hankalin masu sana’o’in gargajiya su ƙara ƙwazo ga haɓaka sana’o’insuna gargajiya kamar su wazanci da ƙira da sauransu.Akwai adawa mai ƙarfi tsakanin wanzamai da ‘yan uwansu da kuma tsakanin maƙera da ‘yan uwansu, wadda ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin waɗannan sana’o’i a ƙasar Hausa [Bunza 2006].Wani lokaci akan sami adawa tsakanin masu sana’o’i irin sata da fashi da makami da sauransu.Misali a cikin littafin Magana jari ce na ɗaya,wasu maɗinka abokan juna suka riƙa satar likkafani. Idan mutum ya mutu aka kai shi maƙabarta, sai su bi sawu cikin dare su sace likkafaninsa. Suna ɗinkawa suna sayarwa. Ashe mutane sun sa masu ido, da dubunsu ta cika, sai Wazirin garin ya mutu. Da aka rufe shi, sai ɓarayin suka bi dare suka tona ƙabarinsa. Lokacin da suka tona ƙabarin waziri don su sace zoɓensa na zinari da sauran kayan ado da aka rufe shi dasu, sai adawar wanda ya shiga ƙabarin ta shiga zuciyarsu; suka yanke shawarar su rufe shi ciki. Saboda ha’inci da ya yi masu na ɓoye zoben da ya sata. Da Allah ya so shi da kuɓuta, sai can cikin dare wasu ɓarayin suka ƙaraso wurin kabarin waziri don su sace kayan da aka rufe shi da su. Ƙadara ta sa ɗayansu ya jefa ƙafarsa cikin ƙabarin, sai wanda ke cikin ƙabarin ya riƙe masa ƙafa. Da ya yi kururuwa, sai‘yan uwansa suka gudu suka bar shi. Da ya samu ya kuɓuta, sai shi ma, wanda ‘yan uwansa suka rufe shi a ciki saboda adawa ya kuɓuta [Imam,1939, P].Haka kuma ko a cikin sana’o’in zamani akan samu abokan sana’a su riƙa adawar wanda ya fi su ɗaukaka a cikin sana’arsu. Za ka ji ‘yan adawarsa suna ƙorafi tare da zarginsa cewa yana bin wasu hanyoyi maras kyau domin ya tara dukiya.

Da irin wannan salon adawa ne, ya sa, su ma ‘yan siyasa ba a bar su a baya ba wajen nuna adawa ga shugabanni,sai dai bambancin da ke akwai; shi ne ita adawar da ake nuna wa shugabanni ta ‘gyara–kayanka’ce, wadda Bahaushe ke cewa, ta fi sauke mu raba’.Wato tana taimakawa wanda aka yi wa adawar ya kula da kurakuransa ya gyara.Idan shugabannisuka kasa cika alkawuran da suka yi wa talakawa na taimaka masu da tallafin kuɗin sana’a ko samar wa mutane aikin yi da sauransu,to mutane da mawaƙan siyasa kan zage damtse wajen rubuce-rubucen waƙoƙi domin su faɗakar da al’umma dasu kansu masu mulki game da kurakuransu na rashin cika alkawari.Haka kuma adawar da ake nuna wa shugabanni tana taimakawa wajen tunzura masu mulki su yunƙura su aiwatar da ayyukan raya ƙasa ta hanyar basu jari su bunƙasa masana’antu manya da ƙanana dom bunƙasa tattalin arzikinsu.Idan gwamnati ta tallafa wa jama’a ta kafa masana’antu da kamfunna za a rage zaman banza da yawon maula da ayyukan ta’addanci da barace-barace a titunan ƙasar nan.