Ticker

6/recent/ticker-posts

Usmannoor Online Academy

MANUFAR BUDE USMANNOOR ONLINE ACADEMY

Usmannoor_Assalafy

Assalamu alaikum, Warahmatullahi, Wabarakatuhu

Dalilin da yasa na yi tunanin bude USMANNOOR ONLINE ACADEMY shi ne: don na zama silar gyaruwar Ibadar al'ummar musulmi baki daya, a maimakon yanda muke maida hankali a Media Platforms muna asarar Data dinmu a al'amuran Dunya sai naga ai a ɓangaren Gyaran addini ya kamata mu dinga amfani da data dinmu, riba biyu: ga lada ga Kuma wayewar addini

Ni ba malami baneba, kamar yanda wasu suke tunani, ni dan qaramin dalibin ilimi ne don haka manufata shi ne na dora mutane akan hanyar da za ta sadasu zuwa ga malaman Ahlus Sunnah ta yanda zasu koyi cikakkiyar Ibadah musamman Sallah, kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar. Don Haka idan na yi kuskure ya kamata ku karbi uzuri na a matsayina na Dan Adam Wanda ba Ma'asumi ba.

Daga 12 August, 2024 zuwa yanzu haka (da kake karanta wannan saqon) mun samu sababbin dalibai Mata da maza (Hausawa) sama da 2,800 da sukai Online Registration daga qasashe sama da 10: (Saudi Arabia, Makkah, Nigeria, Niger, Ghana, Cote de voir, Cameroon, Libya, Togo, Mali, Burkina Faso, Algeria, and still counting. Alhamdulillah). Manufata itace: a dinga dabbaqa Sunnar Manzon Allaah Sallallahu alaihi wasallam a dukkan al'amuran da muke gudanarwa na yau da gobe domin kuwa rashin koyi da fiyayyen halitta ne yasa muka tsinci kanmu a halin da muke ciki a yanzu. Wanne irin sauyi kake tunanin zaka samu idan kana dabbaqa abinda muka karanta a cikin karatun SUNNONI 1,000 din can

Muna karatun littafin (THE 1,000 SUNAN by Shaikh Khalid Husaynaan) SUNNONIN MA'AIKI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM guda 1,000 wanda za'a dinga gabatar da guda 3 ko sama da haka a duk daren Alhamis sannan Kuma a amfana da karatun littafin: SIFATU SALATIN NABY (THE DESCRIPTION OF THE PROPHET'S PRAYER by Shaikh Nasiriddin al-Albany) wato SIFFAR YANDA ANNABI YAKE SALLAH, a daren Juma'a da Kuma littafin KIMIYYA DA AL'AJABAN QUR'ANI a daren Asabar. In Sha Allaah (Wannan Kuma bincike nane saidai ban Kai ga wallafa littafin ba)

Registration: N2,000 (Ko Kuma Sefa jaka 5 ga maqotanmu musamman NIGER)

Opay/Moneypoint Account;
Usman Danliti
7035387476

Ko

Zenith Bank
Usman Danliti
2118853750

NITA: 0023407035387476

Sannan Kuma duk karshen wata zaka turo monthly contribution (N500 ko sama da hakan ga masu niyya) don gudanar da karatuttukan da akeyi laakarida siyan DATA da sauran gudanarwa. Sannan Kuma ko da gudunmawa ko babu, zamu ci gaba da karatuttukan in Sha Allaahu. Fatanmu shi ne Allaah yasa mu gudu tare mu tsira tare, Ya sa Kuma mu dinga aikin da ikhlasi yakuma rabamu da riya

Muna roqon Allaah ya bamu ikon amfana da ilimin muyi aiki dashi har ma wasu su amfana musamman Sallah. Allaah Azzawajallah yace:

( الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ )

البقرة (3) Al-Baqara

Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.

( وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَارْكَعُوا مَعَ الرَّاكِعِينَ )

البقرة (43) Al-Baqara

Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi rukũ'i tãre da yin rukũ'i.

Annabi {Sallallahu alaihi wasallam} yace: "Idan Allaah Yana son bawa da alkhairi sai ya fahimtar dashi addini"

Bukhari da Muslim

Zaku iya sharing saqon (batareda kun canza harafi ko guda 1 ba) domin kuwa duk Wanda ka zama silar gyaruwar addininsa to zaka samu share na ladan da zai samu. Bonanza akan Bonus kenan

✍️ADMIN: ZAUREN TAMBAYA DA AMSA:
Founder/Proprietor: USMANNOOR ONLINE ACADEMY
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
©️Copyright

Contact School Management through WhatsApp number: 07035387476

Usmannoor Online Academy

Post a Comment

0 Comments