Ticker

6/recent/ticker-posts

Takaitaccen Tsokaci Game Da Gajerun Labaran Hausa

An turo waɗannan a matsayin wani ɓangare na bita a zauren WhatsApp na Gasar Gajerun Labarai Ta ACR. Ahmad Musa Dangiwa (2024).

TAƘAITACCEN BAYANI KAN GAJERUN LABARAN HAUSA

Da yake tattaunawa ce tsakanin marubuta da manazarta, ba sai an nanata ma’anar labari ba, sai dai za mu tafi kai-tsaye ga wasu bayanai game da gajerun labarai.

Mun sani cewa su labarai, musamman na adabi, sukan kasance ko dai dogaye ne da za a ɗauki lokaci mai tsawo wajen bayar da su, ko kuma wajen karanta su idan rubutattu ne, ko kuma gajeru ne waɗanda za a iya labarta su a magance ko a karance cikin ƙanƙanin lokaci. Dogayen labarai da gajerun labarai dukkansu nau’o’i ne na ƙagaggun labaran Hausa, sai dai sun sha bamban ta wasu fuskoki ko siffofi da dama. Duk da haka, masana sun nuna cewa babu wani takamaimen bambance-bambance na a-zo-a-gani tsakanin gajerun labarai da dogaye. A ganin wasu masanan, gajarta gajeren labari dabara ce kawai ta fitar da sarƙaƙƙen jigo da kuma tsarin taurarin nau’in adabin. Ke nan, gajeren labari zai iya kasancewa gajere ne ko dai don ya shafi batutuwan da suke a matse ko kuma domin ya matse batutuwan da suke da faɗi, ta bin dabarun bayar da labari kai-tsaye. Saboda haka, hanya mafi sauƙi ta rarrabe tsakanin dogayen labarai da gajerun labarai ita ce ta hanyar adadin kalmominsu da kuma ƙullin da ke damfare da su ta fuskar manufa da tsari. 

TSAKANIN DOGAYEN LABARAI DA GAJERUN LABARAI

Dogayen labarai, labarai ne masu yawan kalmomi da sukan fara tun daga dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700) zuwa sama. Wani lokacin ma sukan wuce dubu arba’in (40,000). Haka kuma, yawa ko tsayin dogayen labarai shi ke haifar da sarƙaƙiya a zubinsu da taurari masu yawa da kuma ƙananan jigogi. Suna da ƙulli da ake warwarewa a hankali tare da gina ƙarin taurari da kuma faɗaɗa zubi mai ƙunshe da ƙananan saƙonni. Ana buƙatar lokaci mai tsawo wajen karanta dogayen labarai.

Ke nan, gajeren labari daidaitaccen aikin zube ne wanda yawanci bai wuce kalmomi dubu goma ba kuma yake ƙunshe da batutuwan ƙirƙira da aka zubo su a tare da wani tauraro da yake fuskantar wani ƙalubale  wanda dole sai ya tunkara.

Shi ya sa wannan nau’i zai iya kasancewa daga gajeren labari mai kalmomi dubu biyar zuwa matsakaicin labari mai kalmomi dubu goma. Ƙagaggen labari ne wanda yake ƙunshe da wani batu ɗaya tal da ya mamaye labarin a kan babban tauraro ɗaya. Kuma yana ƙunshe da zubi wanda yake a matse kuma a tsare domin isar da wani saƙo. Sai dai, a fahimtar mafi rinjaye, adadin kalmomin kowane gajeren labari yana farawa ne daga kalmomi dubu ɗaya (1,000) zuwa dubu bakwai da ɗari biyar (7,500).

Har ila yau, ana iya samun wasu gajerun labarai cikin mafi ƙarancin kalmomi kamar haka:

- Ƙagaggen labarin da bai kai kalmomi ɗari biyar (500) ba, wato Micro-Fiction. Wannan shi ne mafi gajarta.

- Ƙagaggen labarin da bai wuce kalmomi ɗari biyar (500) zuwa dubu ɗaya (1,000) ba, ana kiran sa Walƙiyar Labari, wato Flash Fiction.

- Ɗan gajeren rubutu mai ƙunshe da wani bayani kan wani batu guda ɗaya (cikin falle ɗaya) mai ƙunshe da shafuka huɗu ƙanana, wato Phamplets.

Yawanci akan gina gajerun labarai ne a kan wani batu guda ɗaya, a wani ayyanannen lokaci. Suna da zubi da tsari mai sauƙi, wanda ke ƙunshe da taƙaitattun taurari. Wani lokacin ma tauraro guda ɗaya ne, saboda gajartar labarin. A ire-iren waɗannan labaran, ana warware ƙulli cikin sauri. A wasu lokutan kuma akan ƙare shi a buɗe, a bar mai karatu da yanke hukunci. Ana iya karanta gajeren labari a zama ɗaya kuma ya shiga ran mai karatu ya yi tasiri a zuciyarsa.

Gajerun labarai, kamar sauran nau’o’in adabi, suna tafiya ne ko wanzuwa daidai da sassauyawar rayuwar al’umma. Saboda haka, ana iya yin la’akari da rayuwar gargajiya da kuma samuwar rubutu da karatu wajen rarraba gajerun labarai. Shi ya sa Kalu (2016) ya rarraba gajerun labarai gida biyu: Labarun gargajiya da rubutattun gajerun labarai na zamani. Idan aka ce gargajiya, ana nufin labaran da ake da su tun tale-tale kafin samuwar rubutu da karatu a cikin al’ummar da aka same su. Su ne labaran da ake bayar da su da baka kuma a adana su a ka. Su kuwa rubutattun gajerun labarai, kamar yadda sunansu ya nuna, sun samu ne bayan samuwar rubutu da karatu a cikin al’ummar da aka same su. Gajerun labarun baka ana ƙirƙirar su a ka, a wanzar da su da fatar baki, kuma a adana su a ka. Labarai ne da aka gada daga kaka da kakanni, wato nau’i ne na adabi wanda ke ɗauke da zantuttuka gajeru ko dogaye na hikima waɗanda ke koyar da wasu darrusa.

Ke nan, labarai ne da suke wanzuwa ta hanyar magana. Da baki ake isar da su, kuma a taskace su a ka. Babbar hanyar isar da su ita ce kunne-ya-girmi-kaka (Ɗangambo, 2008).

Yawanci, yara ne a lokacin ƙuruciya ake ba su labarai domin tarbiyyantar da su, a kuma nuna masu al’adun al’umma da abubuwan da ake so a yi da waɗanda ba a so. Akan samu gajerun labaran baka masu kai-komo a tsakanin al’ummomi a dalilin samuwar wasu halittu da suke kewaye da su ko yanayin muhalli ko daidaituwar tunani a tsakaninsu. 

Gajerun labarun baka sun haɗa da labarun gargajiya da tatsuniya da almara da ƙissa da hikaya da tarihi da tarihihi da sauransu. Bugu da ƙari, ana yin su ne a lokacin hira, kamar labarai na jarumai ko `yan fashi ko na almara, irin su labaran hikima ko wasa ƙwaƙwalwa da kuma tatsunniyoyi irin na gizo da ƙoƙi da hikayoyi na iskoki ko kuma aljannu da almara da ƙissa da tarihi da tarihihi.

Su kuwa rubutattun gajerun labarai, kamar yadda sunansu ya nuna, labarai ne waɗanda suka wanzu bayan samuwar karatu da rubutu, wato waɗanda aka wallafa su cikin littafi ko intanet da sauran hanyoyin rubutu da karatu na zamani.

Daga abin da ya gabata, mun fahimci cewa fasahar samar da gajeren labari daɗaɗɗiyar fasaha ce wadda ta wanzu tun tale-tale kuma ta cigaba da wanzuwa. Saboda haka, gajeren labari a matsayin nau’in adabi, ba sabon abu ba ne. Haka kuma, gano ainahin asalin gajeren labari na baka yana da wahala, sai dai an fara ƙirƙiro rubutun da za a iya gani a siffar gajeren labarin Hausa(na adabi) ne bayan samuwar karatu da rubutun boko a ƙasar Hausa.

Mal. Mujahid Abdullahi

Gasar Rubutattun Gajerun Labaran Hausa Ta ARC. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation

Post a Comment

0 Comments