Sunan shi Arc. Ahmed Musa Dangiwa Ministan Gidaje da Tsara
Birane na Najeriya. Shugaba kuma jagora sannan mu'asasi na Gidauniyar Adabi ta
Dangiwa.
Haifaffen garin Kankiya ne, a Jihar Katsina. Ya yi karatun
firamare a garin Katsina da Kankiya da Bindawa da Malumfashi. Ya yi makarantar
sakandire a Makarantar tunawa da Sardauna (Sardauna Memorial Callege) Ya
halarci makarantar share fagen shiga jami’a (CAS Zaria) daga bisani ya shiga
Jami’ar Ahmadu Bello Zaria inda ya samu digirinsa na farko a fannin kimiyyar
zane da tsara gidaje (Bsc Architectural Science).
Daga baya ya sake komawa Jami'ar ABU ya samu shaidai kammala
karatun digiri na biyu (Msc).
Yayi bautar kasa a Jihar Cross Rivers dake kudancin
Nijeriya. Ya yi aikin gwamnati na dan takaitaccen wa’adi a shekarar 1988 inda
yayi koyarwa a kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina(HUK Poly), da
kuma ma’aikatar lafiya ta Jihar Katsina.
Ya bar aikin gwamnati ya tsunduma aiki da kamfanoni masu
zaman kansu.
Daga bisani ya kafa nasa kamfani mai suna AM Consult Wanda a
karkashinsa ya gudanar da ayyuka masu dunbin yawa a fadin Nijeriya.
Ya shigo siyasa a shekarar 2003 a karkashin jamiyyyar ANPP.
Yayi takara a matakai daban-daban
Yana daya daga cikin mambobin kwamitin rukon kwaryar
jamiyyyar CPC na jihar Katsina da uwar jam’iyyyar ta kasa ta turo karkashin
kantoman ruko Faruk Adamu Aliyu. Shi ne shugaban Jam’iyyyar APC na farko na
jihar Katsina. Ya rike mukamin Manajin Darkta na Bankin Bayar da Lamunin Gina
Gidaje na kasa karkashin gwamnatin Shugaba Buhari daga 2017 -2022.
Shi ne tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina daga ranar
31 ga watan Mayu 2023 har zuwa 27 ga watan Yuni da aka aika sunanshi a matsayin
wanda za a tantance mukamin Minista daga jihar Katsina.
Mu na tare da shi a wannan zaure da za a gabatar da bitar
gasar gajerun Labarai ta 2024.
Sunan shi Mal. Yazid Abdul'azi (Nasudan) shi ne shugaban kwamitin
shirya wannan gasa.
Yana da digiri kan harshen Turanci, sannan yayi digiri na
biyu kan Sadarwa da Isar da saķo. Marubuci ne kuma manazarci. Kazalika mai
fashin baƙi
ne kan matsalolin da ke damun al'umma da samar da makoma nagartacciya, ɗaya ne daga cikin uwayen Ƙungiyar
Marubuta ta jihar Katsina.
Ya yi alkalanci a mabambata gasar adabi da ake shiryawa.
Fasihi ne kuma jajirtacce wajen bunkasa adabi da son cigaban sa.
Sunanta Malama Halima Ahmad Matazu
Ta yi digiri na ɗaya
da na biyu a ɓangaren
harshen Hausa. Marubuciya ce ta gwadawa
a allon majigi, ita ta rubuta littafin Amon 'Yanci wanda ya yi shuhura kuma
yake cikin yi a fagen nazari a manyan makarantun ƙasar nan.
Ta jagoranci alƙalanci da yawa a manya gasar rubutun
adabi da aka yi a baya, kamar gasar Gusau Institute da gasar Dangiwa ta 2020 da
sauransu.
Tana bisa hanyarta na samun digiri na uku a ɗaya daga cikin jami'o'in ƙasashen
Yammacin duniya.
Sunan shi Mal. Abubakar A'mustapha Yar'adua
Ya yi digiri na ɗaya
da ba biyu a ɓangaren
addinin Musulunci, sannan yana bisa hanyar kammala digiri na uku a ɓangaren.
Marubuci ne shadidan kuma manazarci ne da yake kallon
zamantakewar al'umma a cikin adabinsu da addininsu.
Shi ne shugaban ƙungiyar Marubuta ta jihar Katsina baki ɗaya.
Magatakarda ne a Kwalejin Karatu mai zurfi ta Pleasant
Library da ke Katsina.
Sunan shi Mal. Mujahid Abdullahi
Yana da digiri na ɗaya
da na biyu a ɓangaren
harshen Hausa. Yana kuma bisa hanyar kammala digiri na uku a fagen.
Manazarci ne na zuwa gaban sarki. Shi ne sahabi na farko da
ya fara daddage gajerun labaran Hausa a Afrika ta Yamma baki ɗaya. Sannan marubuci ne da
ya samar da litattafan wasan kwaikwayo guda biyu.
Malami ne a sashen Nazarin Harsuna Nijeriya Harsuna a
Jami'ar Jihar Kaduna (KASU). Ya yi aiki sosai kan tacewa da samar da litattafai
da dama na gasa, kamar littafin Dambarwar Siyasa da Furen Ƙarya
da Ɗaukar
Jinka da Muhalli, Sutura da sauransu da dama.
Malama Nabilah Ibrahim Khalil marubuciya kuma 'yarjarida, malama
mai fàɗakarwa a kan
matsalolin zamantakewa da ilimi da lafiya da mu'amala. Ta samu digirinta na
farko a kan fannin Kimiyyar Kula da Ɗakunan Karatu ( Library Science) daga
jamiar Bayero, Kano.
Nabila yar asalin jihar Katsina ce, kuma tana rubutu a cikin
harsunan Ingilishi da Hausa, ta rubuta litattafai da dama da suka hada Masoyi
Zaki da Sha'awa Romon ma'aurata da Tangles in the Heart da Burin Masoya Aure da
Labarin Rayuwa da dai sauransu da dama, wasu sun fito wasu na kan hanya.
Nabila ta yi aiki da mujallar Film a baya, da Leadership,
haka kuma ta kwashe shekaru sama da 10 tana rubutu tare da amsa tambayoyin masu
karatu a kan zamantakewa a shafin Duniyar Ma'aurata na Jaridar Aminiya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.