Amsa Addu'a
Wato idan ka ga halin mutanen da suke jayayya a kan cewa halin matsin rayuwa da ake ciki a dalilin zaluncin shugabanni jarabawa ce daga Allah don mu koma gare shi, sai ka fahimci da alama mutane masu yawa ba su shirya neman mafita daga halin da ake ciki ba.
Alhali duk wanda ya san Allah, ya san sunayensa da
siffofinsa, wato ya san ma'anoninsu, zai san cewa idan muka tashi da gaske muka
kira Allah, muka roke shi to zai amsa mana.
Imam Ibnul Qayyim ya ce:
وهو المجيب يقول من يدعو أجب * -ه أنا المجيب لكل من ناداني
وهو المجيب لدعوة المضطر إذ * يدعوه في سر وفي إعلان
Ma'ana Allah mai amsa kiran dukkan wanda ya kira
shi ne. Yana amsa kiran kowa, hatta kafirai. Yana kuma amsa kiran kibantattun
bayi, kamar wanda ya shiga matsin halin rayuwa, ya shiga tsanani.
Allah ya ce:
﴿أَمَّن یُجِیبُ ٱلۡمُضۡطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَیَكۡشِفُ ٱلسُّوۤءَ﴾
[النمل: ٦٢]
{Waye yake amsa wanda ya shiga matsi idan ya kira
shi, kuma yake yaye mummunan abu...?}.
Kuma kamar yadda yake amsa addu'ar wanda aka
zalunta. Haka yana amsa addu'ar duk wanda ya debe tsammanin samun biyan
bukatarsa daga wajen mutane. Misali; mun gwada zaben shugaba wane mai gaskiya,
amma ba mu ga canji ba. Mun gwada zaben Muslim - Muslim ticket, amma matsin
rayuwan karuwa ya yi, to ya Allah yanzu kam mun yanke tsammani daga kowa sai
kai kadai. Ba mu da wata dabara daga gare mu sai neman agajinka.
Idan da a ce bayi za su san girman Allah, su san
cewa shi mai amsa roko ne, su rataya zukatansu gare shi, su roke shi, su yi
masa naci, su nuna ba su da wata sauran dabara sai gare shi, su kira shi ta
ko'ina, mutanen kasa daga yankuna da jihohi daban - daban, kabilu daban -
daban, da tuni Allah ya amsa addu'arsu, ya karya kashin bayan duk wani
azzalumi.
Amma kash! Mutane da yawa su mafita a wurinsu ita
ce zanga - zanga, da sauran hanyoyin da gurbataccen tunaninsu yake ba su!
A gaskiya idan ba mu dawo cikin hayyacinmu, mun yi
abin da ya kamata ba, za a dade ana shan wahala.
Allah ya sawake.
Ba mu yi Zaton haka a Gomnatin Muslim-Muslim ba
Akwai mamaki yadda hankulan mafi yawan mutane ba
su kai ga kudurin da Hon. Bappa Aliyu Misau ya gabatar a Majalisa ba. Kuduri ne
mai matukar muhimmanci ga wannar Gomnati ta Muslim-Muslim. Amma abin takaici a
bugun farko aka yi watsi da kudurin. Kuma shiru kake ji kamar ba a yi ba.
Kuduri ne wanda ya kunshi sake wa kotunan Shari'ar
Muslunci mara, saboda abu ne da hatta a kundin tsarin mulki yana da hujja.
Kudurin shi ne cire dabaibayi da kaidin da aka yi
wa Shari'ar Muslunci a kotunan Shari'a, inda aka kayyade Shari'ar da kalmar
"Personal", wanda shi dan Majalisar - mai wakiltar Misau/Dambam - ya
nemi a cire kalmar "Personal" din, sai a canza lamarin daga
"Islamic Personal Law", zuwa "Islamic Law", abin da zai ba
da dama a rika yin Shari'a wa Musulmai a kotunan Shari'ar Muslunci da dokokin
Muslunci a sauran harkokinsu na kasuwanci da sauran harkokin yau da kullum.
Wannan abin fa Musulmai kadai ya shafa, kuma dokar
kasa ta bai wa kowa daman a yi masa Sharia da dokokin Addininsa ko al'adarsa.
Tabbatar wannan kuduri da cin nasararsa ba zai
taba fita daga cikin abubuwan da ake kyautata zato wa Gomnatin Muslim-Muslim
ba.
A bara mun kai ziyara ma wani Grand Khadi, Wallahi
wannar matsalar ya koka mana, cewa: an takure Shari'ar kotunansu a kan "الأحوال الشخصية" wato "Personal
Law" kadai. Ya nuna damuwarsa matuka.
Ala ayyi halin, wannan babban kalu-bale ne ga
al'ummar Musulmi, musamman manyan kungiyoyinsu masu iya kira ga Gomnati da 'yan
majalisu. Bai kamata manyan kungiyoyin Musulmai suna mantawa da irin wadannan
muhimman manyan aiyuka ba. Idan kuma suna yin iya kokarinsu a kai, to bai
kamata suna yin shiru ma wadanda suka fito suna sukan kudurin a jaridu ba. Har
dan majalisar ya zama abin zargi, - wai - zai musluntar da Nigeria.
Muna addu'a wa Dan majalisa Hon. Bappa Aliyu Misau
Allah ya saka masa da alheri. Ya taimake shi a kan kyawawan manufofinsa.
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.