Ticker

6/recent/ticker-posts

Kama Yara 'Yan Zanga-Zanga

Dazu na ga an yada wani faifan bidiyo na Dr. Bashir Aliy Umar, yana kokawa a kan sabon kudurin haraji da shugaban kasa ya aike Majalisa don ya zama doka.

Abin da ya fi jan hankalina a cikin bayanansa shi ne nunawa da ya yi cewa: ya wajaba mu dukufa ga addu'a da rokon Allah. Saboda babu yadda za mu yi sai dai mu koma ga Allah. Musamman a yanayin da muke ciki na kuncin rayuwa da wahala, idan mun koma ga Allah, mun roke shi Allah zai amsa mana.

Kuma ai da ma duka mun san cewa; addu'ar wanda aka zalunta ba ta da shamaki zuwa wajen Allah.

Wannan sai ya tuna min fadin Allah:

﴿وَإِذَا مَسَّ ٱلنَّاسَ ضُرࣱّ دَعَوۡا۟ رَبَّهُم مُّنِیبِینَ إِلَیۡهِ ثُمَّ إِذَاۤ أَذَاقَهُم مِّنۡهُ رَحۡمَةً إِذَا فَرِیقࣱ مِّنۡهُم بِرَبِّهِمۡ یُشۡرِكُونَ ۝٣٣﴾ [الروم: ٣٣]

{Idan cutuwa ta shafi mutane sai su kira Allah Ubangijinsu, suna masu komawa gare shi...}.

Kuma ya ce:

﴿أَمَّن یُجِیبُ ٱلۡمُضۡطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَیَكۡشِفُ ٱلسُّوۤءَ وَیَجۡعَلُكُمۡ خُلَفَاۤءَ ٱلۡأَرۡضِۗ أَءِلَـٰهࣱ مَّعَ ٱللَّهِۚ قَلِیلࣰا مَّا تَذَكَّرُونَ ۝٦٢﴾ [النمل: ٦٢]

{Waye yake amsa wanda ya shiga matsi idan ya kira shi, kuma yake yaye mummunan abu...?}.

Saboda haka abin da Allah ya jarabe mu da shi na shiga matsin rayuwa, saboda zaluncin shugabanni, abin da Allah yake so mu aikata shi ne mu koma gare shi, mu kaskantar da kai gare shi, mu roke shi ya yaye mana. Wannan shi ne hikimar wannar jarabawa.

Amma abin takaici, mutane masu yawa ba sa so a ce a koma ga Allah don neman mafita daga wannan matsin rayuwa da zaluncin shugabanni da ake fiskanta. Su a wurinsu mafita ita ce a tunzura yara, su fito zanga - zanga, su yi ta barna da lalata kayayyakin al'umma. Daga karshe a kama su, a je a zubar da su a gidan yari, ba abinci, ba kiyon lafiya.

Lallai abin da ya faru na barnar da yaran suka yi a lokacin zanga - zanga, da kuma kama su da aka yi - da alama an azabtar da su - shi ne abin da Malamai masu ilimi da hangen nesa suka hango suka hana zanga - zanga, amma aka fito ana ta musu rashin kunya, da zagi, da izgilanci da tsageranci.

Su kuma Malaman da suka tunzura yaran, da sauran lauyoyi da 'yan jarida masu tunzurawan ba a gansu a wajen zanga - zangan ba. Sai yanzu suka fito suna ta babatun an zalunci yaran. Alhali su suka tunzura yaran, har aka cutar da su.

Abin nufi a nan shi ne; ba za mu samu canji ba sai mun kama ingantacciyar hanyar gyara, mun koma ga Allah, mun kadaita shi da ibada da roko. Kuma kowa ya gyara halayensa, don kusan mafi yawan mutane azzalumai ne, sai dai idan mutum bai samu daman yin zaluncin ba.

[9:05 pm, 04/11/2024] Umar Aliyu Misau: A kullum in an yi magana a kan Kungiyoyi an ce: 'Yan Kungiyar Salafiyyun, sai wasu su zabura suna cewa: Salafiyya ba KUNGIYA ba ce.

To matsalar ita ce: a gaskiya ba za ka fahimci abin da ake fada ba, matukar ba ka san ma'anonin wadannan kalmomi masu zuwa a Yaren Larabci ba.

الأمة، الملة، الجماعة، الفرقة، الحزب، الطائفة، الفئة، التنظيم

In ka ce: Salafiyya ba Kungiya ba ce, to zan yarda da kai, in Salafiyya a matsayin Manhaji kake nufi, wato Tafarkin Sunna da Sahabbai da Tabi'ai da mabiyansu suke kai a Aqida da bin Sunna da nisantar Bidi'a da yakarta, ba a matsayin mutane mabiya ba.

Amma in Salafiyyun a matsayin mabiya kake nufi to sai in ce maka: idan mutane suka tattaru suka ware daga sauran Ahlus Sunna suka hadu a kan wata manufa, suka kira kansu da 'Yan Salafiyya to kai tsaye sun zama Kungiya. Sawa'un sun yi tsari, sun nada Shugaba da Sakatare da Ma'aji, sun bude office sun tsara aiyuka ko kuma suna zaune ne a barwatse kawai, suna aiyukansu ba tare da wani tartibin tsarin aiki na musamman ba.

Saboda ai da ma mutane ne Kungiyar ba Manhajin da suke kai ba. Saboda da za a rasa ko mutum daya a kan wani Manhaji to da babu kungiya, Amma da zarar an samu mutum 3 zuwa sama a kan wata tafiya, ko Manhaji to sun zama Kungiya kai tsaye (automatically).

Don haka KUNGIYA ba suna ne na Manhaji ba, a'a, suna ne na mutanen da suka tattaru a kan Manhajin. Don haka kamar yadda muke da 'Yan Kungiyar Izala haka muna da 'Yan Kungiyar Salafiyyun, wato mutane ko jama'a da suka tattaru suka fahimci juna, suka ware daga sauran Ahlus Sunna suka ce mu ne: Salafiyyun. Wanda ba ya cikinmu kuwa ya zama Dan Bidi'a, ko Hizbiy, Harkiy, ds.

Wannan ya sa za ka yi mamaki, matasa sun wayi gari suna kutsawa cikin magana a kan KUNGIYOYI da yi musu hukunci amma ko hakikanin ma'anar kalmar ta KUNGIYA ba su sani ba.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments