Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Yawan Ganin Budurwata Da Wani Saurayi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu'alaikum malam dan Allah inada tambaya akan wani Abu da ya shige min duhu malam wallahi ina tare da wacce nake so kuma maganar ma takai harga Iyaye ma amma kuma malam ina saminta da wasu abubuwa da bana so. Na farko malam ina saminta da wani saurayi tana fira amma da na mata magana sai ta cemin wai ba saurayinta bane kuma malam na nuna mata cewa bana son hakan amma kuma yau ma na sameta suna waya da shi amma idan nayi magana sai tace ba haka ba ne. Wallahi ni kuma gaskiya malam ina da zuciya sosai da wani lokacin ma nakanji kamar zan iya samin matsala shiyasa nake so malam dan Allah taimaka min da shawarar yadda Zanyi dan samin masalahar haka.

INA YAWAN GANIN BUDURWATA DA WANI SAURAYI

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

A tawa Shawarar!!! ka sami iyayenka da ka Aika Gidan Su Wannan Yarinyar. Su Gayawa Iyayenta ga abinda yake Faruwa. Sabida yankan Hanzari. Kar Iyayenka suce ba ka gaya Musu ba ka je Chan ka Yanke Shawara a Karan kanka. Sannan Itama Iyayenta suna ganin kamar ba ka kyautata Musu ba. Nasan idan anbi wannan Channel ɗin Za'a sami gyara in sha Allah.

Idan kuma ba ta Kiyayewa ba. Ma'ana idan har ba'a sami gyara ba. Kawai ka Rabu da ita. Domin Wannan Kenan Ya Nuna Maka Cewar Wannan yarinya ta fi Karfin Iyayenta. Sabida na sani Cewar irin wannan yana Faruwa. Kai kana ganin matar da zaka aura ce. Ka Kiyaye Mutuncin ka da nata. Amma kuma sai wani ya zo yana tattaba mata jiki ko yana Iskanci da ita. Wanda kuma tana jin daɗin wannan Abinda yake yimata Ne ma yasa ba zata Iya Rabuwa da shi ba na har Abada. Sabida yana Yimata Abinda Kai ba ka Yi mata. Wanda kuma ko da bayan ka Aureta, wallahi ba zasu taɓa Rabuwa ba. A haka zasu ke cin Amanar ka shi da ita. Domin wallahi na tabbatar Maka da Cewar ko da bayan Kunyi Aure da ita. Wata Rana sai ka same shi har a Cikin Falon Gidanka. Ko kuma idan ta Fita Unguwa ace maka an gansu tare da shi. Kuma Maganar da ta saba Gayama na Cewar ba Saurayin ta bane. ita dai zata sake Maimaita maka. Cewar Ba saurayinta bane. Ko Tace maka Saurayin kawarta Ne suka sami matsala. Shine ya kawo kashenta, Akan zata sasanta su.

Wallahi ka sani ba Waɗanda suka fi Renawa Maza Hankali kuma irin Waɗanda suka zo nemansu da Aure, da gaske irin 'yan matan wannan zamanin. Sabida haka Karya take Yimaka. Ta yaya ba saurayinta ba kullum Suna tare? Alhalin kuma kai anyi Maganar Aure da iyayenka da Nata Iyayen?

Karshe Dai Maganar gaskiya. Idan Iyayenta ba zasu iya Raba su ba. Ka bar musu yarsu. Amma kar ka yanke Hukunci har sai ka ga Iya Gudun Ruwansu akan wannan Lamarin. Idan Kuma har sun kasa Raba su. Sai ka bar musu 'yarsu. Ka je ka Nemi Wata ta gari. Domin duk wadda ta fi Karfin Iyayenta. Kai kuma me zakayi da ita? Idan wani Abu ya Taso Anan Gaba, Wa zaka Tinkara?

Allah shine Masani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments