Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayanin Zakkar Abin Da Yake Fitowa Daga Cikin Kasa

TAMBAYA

Assalamu Alaiku malam.

Allah ya qara ilimi mai amfani da amfanarwa.

Don Allah mu na neman cikakken bayani ne akan zakkar manoma, Wanda ake fitar wa bayan an cire amfanin gona.

Jazakumullah bi khair 🙏🏽

BAYANIN ZAKKAR ABIN DA YAKE FITOWA DAGA CIKIN KASA (WATO ZAKKAR AMFANIN GONA)

AMSAH

Shi ne duk abin da yake fitowa daga qasa, kuma ana iya amfani da shi

*Na Farko : ‘Ya ‘Yan Itace Da Qwayoyi

Bayanin Qwayoyi Da 'Ya'yan itace.Qwayoyi

Shi ne dukkan qwayar da ake ajiyewa, ta sha'ir ko alkama da sauransu

'Ya'yan Itace Su ne duk wani Ɗan ice da ake ajiye wa, kamar dabino da zabibi da kwayar auduga

Hukincin Zakkar Qwaya Da ‘Ya’Yan Itace Ba da zakkar qwaya ko ‘ya ‘yan itace wajibi ne, saboda faɗin Allah mai girma da buwaya “Ku bayar da haqqinsa ranar girbinsa”(Al-an’am : 141)

Da faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Cikin abin da sama ta shayar, ko wanda yake da jijiya [Wanda yake da jijiya : Ita ce shukar da take shan ruwa da kanta, ko dai ta hanyar jijiyoyinta, ko kuma daga ruwan sama da qoramu] (yake shan ruwa da kansa) za a ba da kaso ɗaya bisa goma.

Amma abin da aka shayar [Wanda aka shayar da ban ruwa, shi ne wanda aka sha wahala wajen fito da ruwan] da shi za a ba da rabin kashi ɗaya bisa goma” [Bukhari ne ya rawaito shi]

Sharuɗɗan Wajabcin Zakkar Qwayoyi Da ‘Ya’yan Itace

1 – Ya zama za a iya ajiye shi : Idan ya zama ba a ajiye shi ake ba, abinci ne na yau-da-gobe, to babu zakka a cikinsa, saboda abin da ba ajiye shi ake ba to ba dukiya ba ce cikakkiya, don ba za a iya amfanuwa da shi ba a gaba.

2 –Ya zama abin da ake aunawa ne :Ma’ana ta zama ana aunata da ma’auni, don a qiyastawa, saboda faɗin Manzon Allah( صلى الله عليه وسلم ) “Babu Zakka a cikin qwaya ko dabino har sai ya kai wusiki biyar [Wuski shi ne : Sa’i Sittin] ” [Muslim ne ya rawaito shi].

Saboda haka idan ba a auna abun kamar ganye (Salak da danginsa) ko kayan lambu, to babu zakka a cikinsu.

3–Ya zama mutum ne ya shuka shi a gonarsa. Idan abin ya fito da kansa ne to babu zakka a cikinsa.

4–Ya kai nisabi :

Shi ne wusiki biyar, saboda faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ). *“Babu Zakka a cikin qwaya ko dabino har sai ya kai wusiki biyar” [Muslim ne ya rawaito shi].

Don haka nisabin sai ya zama sa’i ɗari uku, wanda ya yi daidai da (612kg) na kykkyawar alkama.

Ana iya haɗa kala-kala idan dai iri ɗaya ne, don a samar da nisabi, kamar a hada dabino wanda ake cewa “Sukkari” da wanda ake kira “Burji” misali, saboda duk dangi xaya ne.

Amma ba a haɗa wani dangi daban da wani dangi don a samar da nisabi, kamar a haxa shinkafa da dabino.

- Ba a Sharɗanta ba : a cikin ZAKKAR kayan gona.

Ba a Sharɗanta cewa sai shekara ta kewayo a kan zakkar kayan gonaa da ‘ya’yan itace ba, saboda faɗin Allah mai girma da buwaya : “Ku ba da haqqinsa ranar girbinsa”. (Al an’am : 141)

Lokacin Da Yake Wajaba A Ba da Zakkar Qwayoyi Da ‘Ya’yan itace.

Zakkar qwaya na kayan gona tana wajaba daga lokacin da qwayar ta yi qwari. ‘Ya’yan itace kuma idan sun fara nuna, ta yadda za su iya zama yadda za a iya ci.

Wanda duk ya sayar da qwayar kayan gona bayan zakka ta wajaba a a kansu, to wannan zakkar tana kan mai sayarwa, saboda shi ne ya mallaki abin lokacin da zakkar da wajaba a cikinsu.

Gwargwadon Zakkar Da Ta Wajaba A Cikin Qwayar Kayan Gona Da ‘Ya’yan Itace.

1 – Kashi ɗaya bisa goma (10%) yana wajaba a cikin abin aka shayar da shi ba da wata wahala ba, kamar wanda aka shayar da ruwan sama ko qoramu.

2 – Rabin kashi ɗaya bisa goma (5%) yana wajaba cikin abin da aka shayar da wahala, kamar wanda aka shayar da ruwan rijiya.

3 – Kashi uku cikin kashi xaya bisa goma (7.5%) yana wajaba a cikin abin da aka shayar das hi da duka biyun, kamar wanda aka shayar da ruwan sama a wani lokaci, wani lokaci kuma da ruwan rijiya.

Dalili faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Cikin abin da sama da qoramu suka shayar za a ba da kashi ɗaya bisa goma, a cikin abin da aka shayar da raqumi kuma za a ba da rabin kashi ɗaya bisa goma” [Muslim ne ya rawaito shi].

Lalacewar Qwaya Ko 'Ya'yan Itace :

Idan qwayar kayan noma ko ‘ya’yan itace suka lalace ba tare da sakacin mai kayan ba, to babu zakka a kansa. Idan kuma shi ne ya lalata su da kansa bayan zakka ta wajab.

Wallahu taala aalam

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments