RADDI A FASSALE:
A rubutunmu na jiya mun bayyana wa jama'a banbanci tsakanin Akidar Shaikh Muhammad bn Ibrahim da Akidar Sayyid Qutub a Babin "Hakikanin Addini da Imani da Muslunci", inda muka ga cewa; Akidar Shaikh Muhammad bn Ibrahim Akidar Ahlus Sunna ce, shi kuma Sayyid Qutub Akidarsa irin ta Khawarijawa ce. Da wannan za mu san Alkiblar kowanne daga cikinsa idan zai yi magana a kan kowace mas'ala ta Akida.
Sa'annan kuma mun ga cewa; Lafazin
"Hakimiyya" lafazi ne "Mujmali" dunkulalle, wanda ya kunshi
karya da gaskiya. Su kuma Ahlus Sunna ba sa amfani da lafazi
"Mujmali" sai bayan an fayyace ma'anarsa, aka san cewa; bai saba ma Shari'a
ba. Wannan ya sa ba a samu inda Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya yi amfani da
lafazin ba, musamman saboda ba lafazi ne sananne a wajen Malamai ba. A wajen
Maududiy lafazin ya fara bayyana, Sayyid Qutub kuma ya dauke shi ya yi ta yada
shi, bayan ya kirkiri wasu Bidi'o'in khawarijawa, na kafirta al'umma ya kara a
kan na Maududiy.
Don haka "Hakimiyya" a wajen Sayyid
Qutub tana da wani Mafhumi daban, ta yadda ya bayyana mana cewa; ma'anarta ita
ce: Ra'ayin Khawarijawan farko, wadanda ake kiransu da "Muhakkimah",
wadanda suka balle daga Sayyidina Aliyu (ra) bisa kadhiyyar "Tahkimi"
(nada masu hukunci guda biyu), wanda hakan ya sa aka kira su Khawarijawan da
sunan: "Muhakkimah".
Saboda haka Shaikh Muhammad bn Ibrahim ba shi da
alaka da "Hakimiyya", saboda ba shi da alaka da Khawarijanci, kuma
bai taba amfani da lafazin ba, kuma bai taba kafirta al'ummar Musulmi ba, bai
taba siffanta al'umma da Jahiliyya ba, bai taba cewa: a yanzu babu al'ummar
Musulmi ba, alhali mun ga Sayyid Qutub ya fadi wadannan duka a dalilin
"Hakimiyya".
Saboda haka cigaba raddinmu zai kasance ne kashi
biyu kamar haka:
(A) AKIDAR SHAIKH MUHAMMAD BN IBRAHIM A BABIN
"IMAMA" DA SHUGABANCI:
Daga cikin abubuwan da za su kara tabbatar maka
cewa: Shaikh Muhammad bn Ibrahim ba shi da alaka da "Hakimiyya" akwai
mas'alolin Babin " Imama" da Shugabanci. Idan ka duba maganganunsa a
Babin za ka ga ya tabbatar da mas'alolin ne bisa Akida da Manhajin Ahlus Sunna,
sabanin yadda lamarin yake a wajen Sayyid Qutub, wanda shi yake ganin
kwata-kwata babu ma shugaba da ya wajaba a yi masa da'a a bayan kasa. Hasali ma
babu wata hukuma, kai, babu ma al'ummar Musulmi, duka a cikin Jahiliyya ake,
irin Jahiliyyar Larabawa kafin zuwan Muslunci.
Don haka lura da bayanan da Shaikh Muhammad bn
Ibrahim ya yi a kan mas'alolin babin na Imama da shugabanci, wadanda Sayyid
Qutub ya saba ma Ahlus Sunna a cikinsu, zai kara tabbatar mana da barrantarsa
daga "Hakimiyyar" da su Sayyid Qutub din suka kirkira, suka kafirta
al'umma da ita. Ga mas'alolin kamar haka:
1) HANYOYIN NADA SHUGABA:
Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya tabbatar da cewa:
daga cikin hanyoyin nada shugaba a Shari'a akwai GALABA (juyin mulki), da kuma
NADI, (ولاية العهد), kamar yadda tsarin shugabanci yake a Kasar Saudiyya. Ya ce:
((نصب الإمام ضروري يسمع له ويطاع. ثم نعلم أن الولاية تثبت بأمور:
منها: نصب أهل الحل والعقد، وهو الذي نص هنا.
ومنها: أن يأخذها قهرا بسيفه ومن معه، ويكون فيه الأمر الكافي،
ويقهر غيره لا يرجع إلى أحد فإنه يثبت له حكم الولاية.
الثالث: أن يعهد إليه ممن قبله.
والكل والمدار هو إقامة الشرع وحفظ كيان الأمة والقيام بحقوقهم))
فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل
الشيخ (12/ 173)
To ka ga a nan sai ya tabbatar da hanyoyi uku na
kafa shugaba a Shari'a: Zabe ta hanyar shura, juyin mulki, da kuma ta hanyar
shugaba ya nada wanda zai gaje shi.
Hanya ta ukun ita ake bi a Saudiyya, wannan ya sa
'Yan Ikhwan suke tsananin adawa da Saudiyya, saboda a bisa wannan tsari babu
yadda za a yi su cimma mafarkinsu, na kafa Daula da Khilafa karkashin Murshidin
Ikhwan, kamar yadda a yanzu Iran take karkashin Khamenei. Saboda sun san duk
wata Khilafa ko Daula da sunan Muslunci ba za ta yiwu ba matukar Makka da
Madina ba sa karkashin ikonsu. Wannan ya sa suke bakar adawa da kasar ta
Saudiyya, saboda babu hanyar da Ikhwan za ta yi mulki a kasar.
2) DA'A MA SHUGABA:
Manhajin Shaikh Muhammad bn Ibrahim a mas'alar
da'a ma shugabanni irin Manhajin Ahlus Sunna ne, wato wajabcin yi musu da'a.
Sabanin Sayyid Qutub da ya kafirta shugabannin da talakawan da kowa da kowa, ya
ce: duka an koma Jahiliyya, dole a sake sabon samar da Musulmai daga zero, don
babu Musulmai a Duniya. Duka ya fadi wannan ne saboda Akidar
"Hakimiyya".
Ga maganar Shaikh Muhammad bn Ibrahim yana umurtan
wasu mutane da yin da'a ma shugaba, su je wajensa su ba shi goyon baya da hadin
kai:
(3870 - طلبه من بعض (الإخوان) القدوم إلى الإمام لاجتماع الكلمة ومناقشة
المشاكل مع العلماء.)
Sai ya ce:
((فاعلموا وفقكم الله أن عقيدتي التي أنا عليها أنى أدين الله
بالنصح والمحبة لكم ولجميع إخواننا المسلمين إلى أن ألقى الله عز وجل, وأهم شيء أناصحكم
فيه وأعظمه إجابة داعي الشرع وأن لا تلتفتوا عنه يمنه أو يسره, ومن ذلك إجابه داعي
إمام المسلمين ما لم يدع إلى الاجتماع على المعصية , وإنما دعا إلى الاجتماع على طاعة
الله وعدم التفرق والاختلاف , وجميع المشائخ يرون ذلك ويفتون به , وعدم قدومكم على
أمامكم وعلمائكم من الأمور التي لا يرضى بها لكم من في قلبه أدنى محبة لكم أعنى المحبة
الدينية , وهو من أعظم الأمور التي يفرح بها عليكم وعلى جميع المسلمين أعداء الدين
من الكفار والمنافقين , ومن أعظم أسباب شق العصا , وهذا كتاب الله ونفا ير الأئمة له
, وسنة رسول الله صلى الله وعليه وسلام مدونة بشروحها المبينة للمقصود منها , وفى ذلك
كله حل المشكل , وكشف الاشباه , والشفاء لكل داء , والكفالة بالفلاح والهدى , والنجاة
من المهالك والردى...
والمقصود بيان وجوب القدوم على أمام المسلمين وفرضيته عليكم,
وليس لكم عذر في التخلف ولا حجة. فان ذلك من السمع والطاعة التي أوجبها الله ورسوله,
لاسيما وهو يدعوكم إلى الشريعة والرجوع فيما يشكل إلى حملتها))
فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل
الشيخ (12/ 170 - 171)
A nan sai ya bayyana cewa; Akidarsa ita ce son
Musulmai, kuma 'yan'uwansa ne, da yi musu Nasiha a kan amsa kiran shugaban Musulmai
da yi masa da'a.
3) HANI A KAN TAWAYE DA KHURUJI WA SHUGABANNI:
((لأحاديث طافحة بالمنع من الخروج على الأئمة وأن بغوا وظالموا.
هذا ما لم يروا منهم كفرا بواحا كما في الحديث وقوله: (عندكم من الله فيه برهان) على
أنه كفر، وفي حديث أخر (ما صلوا) المعني ما داموا بصفه الإسلام ما فيه إلا كبائر ومعاصي
وجور وظلم هذه لا تمنع ولأيته)).
فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل
الشيخ (12/ 169)
A nan sai ya tabbatar da abin da Hadisai suka zo
da shi, cewa; ba a tawaye wa shugaba matukar dai yana amsa sunan Musulmi. Sai
idan ya kafirta, bisa hujja tabbatacciya kamar rana a tsakiyar sama.
Don haka a fili yake Shaikh Muhammad bn Ibrahim
Akidarsa da Manhajinsa na Ahlus Sunna ne a babin Imama da shugabanci. Ba ya
kafirta al'umma, ya ce: babu al'ummar Musulmi, ko ya ce: an koma Jahiliyya, da
makamancin haka cikin abin da Sayyid Qutub ya yi ta fada, saboda Akidarsa ta
"Hakimiyya".
Saboda haka, idan lamarin haka yake, ta yaya mai
ilimi, kuma mai adalci zai jingina "Hakimiyya" ga Shaikh Muhammad bn
Ibrahim?!
Kuma Akidar Shaikh Muhammad bn Ibrahim a wannan
babi raddi ne ga 'Yan Kungiyar Ikhwan tare da Qutubawansu, ta yadda muka ga
Shaikh Muhammad bn Ibrahim a kan Manhajin Ahlus Sunna yake a wannan babin,
sabanin su da suke kan Manhajin Khawarijawa, amma suke fakewa da maganganunsa,
suke tallata bataccen Manhajinsu. Saboda haka kasancewar sun saba masa a wannan
babi, ba za mu yarda su fake da Shaikh Muhammad bn Ibrahim a mas'alar
"Hukunci da abin da Allah ya saukar" ba, don kawai su tallata Bidi'ar
"Hakimiyya".
(B ) MAZHABAR SHAIKH MUHAMMAD BN IBRAHIM A
MAS'ALAR HUKUNCI DA SABANIN ABIN DA ALLAH YA SAUKAR:
Asali abin da Malamai suka sani shi ne wajabcin
yin hukunci da Shari'ar da Allah ya saukar ma bayi. Duka Malamai sun yi Ijma'i
a kan haka, saboda Allah ya yi hani a kan yin hukunci da sabanin abin da ya
saukar. Shi ya sa suke kiran mas'alar da sunan: "Yin hukunci da abin da ba
Allah ne ya saukar ba" (الحكم بغير ما أنزل الله).
To amma kasancewar Manhaji ne na 'Yan Bidi'a, ba
sa takaituwa da lafuzan Shari'a, sai su yi amfani da wasu lafuza
"Mujmalai", wadanda suke iya daukar karya da gaskiya, don su kunsa
Bidi'o'in da suka kirkira a cikin lafazin. To haka shi ma lafazin
"Hakimiyya", kamar yadda ya gabata ba lafazi ne na Shari'a ba,
Malamai ba su yi amfani da shi ba, Maududiy ne ya fito da shi, shi kuma Sayyid
Qutub ya kunsa Bidi'o'in Khawarijawa a ciki, na kafirta al'umma da kiranta da
Jahiliyya. Wanda har wadanda suka zo daga baya suka tasirantu da shi, suka zo
suka cikata aikin, suka dauki makami a kan al'ummar Musulmi suna kashe su, bisa
hujjar "Hakimiyya".
To idan muka duba rubutun da a cikinsa aka jingina
ma Shaikh Muhammad bn Ibrahim "Hakimiyya" da farko mai rubutun bayan
ya yi shimfida ya dauko maganganun Shaikh Muhammad bn Ibrahim wadanda ya yi su
a kan haramcin sanya Dokokin tsarin mulki da suka saba ma Shari'ar Allah, inda
ya tabbatar da cewa; hakan kafirci ne.
Lallai ko shakka babu wannan gaskiya ne. Canza
hukuncin Allah gaba dayansa, da musanya shi da wani hukuncin daban wanda ya
saba masa kafirci ne. Saboda dalilai masu yawa, wadanda duka Shaikh Muhammad bn
Ibrahim ya ambace su a cikin littatafansa, daga ciki:
a) Allah ya kore imani ga wanda bai yi hukunci da
abin da Allah ya saukar ba, inda ya ce:
{فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ حَتَّى يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ
بَيْنَهُمْ ثُمَّ لَا يَجِدُوا فِي أَنْفُسِهِمْ حَرَجًا مِمَّا قَضَيْتَ وَيُسَلِّمُوا
تَسْلِيمًا} [النساء: 65]
b) Neman hukunci da abin da ba Shari'ar Allah ba
ne neman hukunci ne a wajen Dagutu, Allah ya ce:
{أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا
أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنْزِلَ مِنْ قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَنْ يَتَحَاكَمُوا إِلَى
الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَنْ يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَنْ يُضِلَّهُمْ
ضَلَالًا بَعِيدًا (60) وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا إِلَى مَا أَنْزَلَ اللَّهُ
وَإِلَى الرَّسُولِ رَأَيْتَ الْمُنَافِقِينَ يَصُدُّونَ عَنْكَ صُدُودًا (61)} [النساء:
60، 61]
c) Allah ya siffanta shi da hukuncin Jahiliyya,
inda ya ce:
{أَفَحُكْمَ الْجَاهِلِيَّةِ يَبْغُونَ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللَّهِ
حُكْمًا لِقَوْمٍ يُوقِنُونَ} [المائدة: 50]
d) Allah ya siffanta hakan da kafirci da zalunci
da fasikanci, inda ya ce:
{وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ}
[المائدة: 44]
Ya ce:
{وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ}
[المائدة: 45]
Ya ce:
{وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ}
[المائدة: 47]
Duka wadannan Ayoyi Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya
ambace su, kuma ya tabbatar da abin da suka yi nuni gare shi.
Masu danganta "Hakimiyya" Akidar
Khawarija ga Shaikh Muhammad bn Ibrahim suna kawo maganganunsa da ya yi
"Idlaqin" hukuncin aikin ne kawai. To amma sai dai inda matsalar
take, ba su lura da cewa; shi Shaikh Muhammad bn Ibrahim "Idlaqin"
hukunci yake yi, kamar yadda Allah ya yi, ba tare da Shaikh Ibn Ibrahim ya dora
hukuncin a kan al'umma ba. Amma shi kuma Sayyid Qutub fa, kawai zuwa ya yi ya
kafirta al'umma, ya ce yanzu duka babu Musulmai, babu al'umma Musulma, an koma
Jahiliyya, saboda an bar "Hakimiyya".
Matsala kuma ta biyu; Shi Shaikh Muhammad bn
Ibrahim din ya yi Tafsilin nau'in kafircin da yake tabbatarwa a wannar
mas'alar. Inda ya nuna cewa; kafircin nau'i biyu ne, imma kafirci na aiki
(karamin kafirci) ko kuma kafirci na akida (babban kafirci), ga maganarsa a kan
haka:
(({فإن جاءوك فأحكم بينهم أو أعرض عنهم وإن تعرض عنهم فلن يضروك
شيءئا إن حكمت فحكم بينهم بالقسط إن الله يحب المقسطين}. والقسط هو العدل ولا عدل حقا
إلا حكم الله ورسوله والحكم بخلافه هو الجور والظلم والضلال والكفر والفسوق ولهذا قال
تعالى: {ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكافرون} {ومن لم يحكم بما أنزل الله
فأولئك هم الظالمون} {ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الفاسقون}.
فانظر كيف سجل الله تعالى على الحاكمين بغير ماأنزل الله بالكفر
والظلم والفسوق ومن الممتنع أن يسمى الله سبحانه وتعالى بغير ما أنزل الله (كافرا)
ولا يكون كافرا بل هو كافر مطلقا إما كفر عمل وإما كفر اعتقاد)).
فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل
الشيخ (12/ 287 - 288)
Ka ga a karshe sai ya ce maka: "wanda bai yi
hukunci da abin da Allah ya saukar ba, ta yaya ba zai zama kafiri ba, a'a,
kafiri ne kai tsaye, IMMA KAFIRCI NA AIKI KO NA AKIDA (إما كفر عمل وإما كفر اعتقاد)". KAFIRCI NA AIKI KUWA,
SHI NE KARAMIN KAFIRCI WANDA BA YA FITAR DA MUTUM DAGA MUSLUNCI.
Kuma Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya yi tafsili da
bayani mai tsawo, inda ya nuna cewa; KAFIRCI NA AKIDA (mai fitarwa daga
Muslunci) yana da halaye guda shida. Shi kuma KAFIRCI NA AIKI shi ne wanda
mutum ya yi hukunci a wata kadhiyya, bayan ya yarda da hukuncin Allah a
cikinta, amma sai ya bi son zuciyarsa, kuma yana jin cewa; shi mai sabo ne.
Duba:
فتاوى ورسائل سماحة الشيخ محمد بن إبراهيم بن عبد اللطيف آل
الشيخ (12/ 288 - 291)
To ka ga a fili yake cewa; Shaikh Muhammad bn
Ibrahim bai fita daga Mazhabar Salaf a mas'alar ba, cewa; kafircin da ya zo a
wannan babi nau'i biyu ne; imma ya zama: BABBAN KAFIRCI, ko kuma KARAMIN
KAFIRCI. Kamar yadda aka ruwaito daga Salaf kamar haka:
1) عن ابن عباس قوله:"ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم
الكافرون"، قال: من جحد ما أنزل الله فقد كفر. ومن أقر به ولم يحكم، فهو ظالم
فاسق.
تفسير الطبري = جامع البيان ت شاكر (10/ 357) تفسير ابن أبي
حاتم - محققا (4/ 1142)
2) عن بن طاوس عن أبيه قال: سئل ابن عباس في قوله: ومن لم يحكم
بما أنزل الله فأولئك هم الكافرون قال: هي كبيرة
تفسير ابن أبي حاتم - محققا (4/ 1143)
3) عن عطاء قوله:"ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكافرون"،"ومن
لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الظالمون"،"ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك
هم الفاسقون"، قال: كفر دون كفر، وفسق دون فسق، وظلم دون ظلم.
تفسير الطبري = جامع البيان ت شاكر (10/
355)
4) عن طاوس:"ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكافرون"،
قال: ليس بكفر ينقل عن الملة.
تفسير الطبري = جامع البيان ت شاكر (10/
355)
Shi ya sa Ibnul Qayyim ya ce:
((والصحيح أن الحكم بغير ما أنزل الله يتناول الكفرين، الأصغر
والأكبر بحسب حال الحاكم، فإنه إن اعتقد وجوب الحكم بما أنزل الله في هذه الواقعة،
وعدل عنه عصيانا، مع اعترافه بأنه مستحق للعقوبة، فهذا كفر أصغر، وإن اعتقد أنه غير
واجب، وأنه مخير فيه، مع تيقنه أنه حكم الله، فهذا كفر أكبر، وإن جهله وأخطأه فهذا
مخطئ، له حكم المخطئين))
مدارج السالكين بين منازل إياك نعبد وإياك نستعين (1/
346)
Sai Ibnul Qayyim ya kasa masu hukunci da sabanin
abin da Allah ya saukar zuwa kashi 3:
(1) Wanda yake ganin wajabcin bin Shari'ar Allah,
amma sai ya saba mata, to wannan karamin kafirci ne.
(2) Wanda kuma yake ganin halascin saba Shari'ar
Allah to wannan babban kafirci ne.
(3) Wanda kuma ya saba hukuncin Allah saboda
kuskure ko jahilci to hukuncinsa na mai kuskure ne.
To ka ga a fili yake Shaikh Ibnu Ibrahim ya gina
maganarsa ce a mas'alar bisa Manhajin Salaf, na raba kafircin gida biyu. Sai
dai a tafsilin ne za a iya samun sabani tsakanin Malamai, amma asalin kam guda
daya ne.
To abin tambaya a nan shi ne: Shin haka lamarin
yake a wajen Khawarijawa da Sayyid Qutub?
Yanzu ka dauki maganar Shaikh Muhammad Ibnu
Ibrahim da maganar Ibnul Qayyim, sai ka auna su da wannar magana ta Sayyid
Qutub ka gani:
((والإسلام منهج للحياة كلها. من اتبعه كله فهو مؤمن وفي دين الله.
ومن اتبع غيره ولو في حكم واحد فقد رفض الإيمان واعتدى على ألوهية الله، وخرج من دين
الله. مهما أعلن أنه يحترم العقيدة وأنه مسلم. فاتباعه شريعة غير شريعة الله، يكذب
زعمه ويدمغه بالخروج من دين الله.))
في ظلال القرآن (2/ 972)
A nan shi Sayyid Qutub ko hukunci daya mutum ya
bari, to ya bar imani, ya fita daga Addinin Allah. Ko da kuwa yana girmama
Akida, yana cewa: shi Musulmi ne.
To shin Manhajin Sayyid Qutub iri daya ne da na su
Shaikh Ibnu Ibrahim?
Shin Sayyid Qutub yana kasa kafircin zuwa gida
biyu; BABBAN KAFIRCI mai fitarwa a Muslunci, da kuma KARAMIN KAFIRCI, wanda ba
ya fitar da mutum a Muslunci?
Saboda haka kasa kafirci gida biyu a mas'alar, shi
ne abin da ya raba tsakanin Manhajin Ahlus Sunna, da kuma Manhajin Khawarijawa.
Shi ya sa Sayyid Qutub ya yi ta amfani da lafazin "Hakimiyya" ya yi
ta kafirta al'umma a bisa haka, kamar yadda Khawarijan farko
"Muhakkima" suka yi.
To sai mu tambayi masu jingana
"Hakimiyya" ga Shaikh Muhammad Ibnu Ibrahim mu ce musu:
A ina Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya yi amfani da
lafazin "Hakimiyya" da har za a danganta masa shi?!
Yaushe Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya kafirta
al'umma, ya ce: sun koma Jahiliyya, saboda ba sa hukunci da abin da Allah ya
saukar, kamar yadda Sayyid Qutub ya yi, da har za a danganta masa
"Hakimiyya"?!
Saboda haka babu mai ilimi ko mai adalcin da zai
yi wannan jafa'in ga Shaikh Muhammad Ibnu Ibrahim!
Don haka zuwa yanzu ba mu ga inda Shaikh Muhammad
bn Ibrahim ya tabbatar da "Hakimiyya" ba.
Kuma ba mu ga ya kafirta al'umma ya ce: ta koma
Jahiliyya ba.
Ba mu ga ya kafirta wata "mujtama'a" ta
wata kasa ya ce: ta koma Jahiliyya ba.
Abin da muka gani a wajensa shi ne bayanin
mas'alar "Hukunci da abin da ba Allah ne ya saukar ba" bisa Alkur'ani
da fahimtar Salaf da Manhajin Ahlus Sunna. Kuma ita wannar mas'ala duka Malaman
Muslunci sun yi magana a kanta, tun daga kan Sahabbai har zuwa yau. Kuma Shaikh
Muhammad bn Ibrahim bai fita daga Manhajinsu ba.
Khawarijawa ne suka saba a wannar mas'ala, suka
kafirta Sayyidina Aliyu (ra), suka nuna: ya saba "Hakimiyya", ya yi
"Tahkeem". A kan haka suka yi masa tawaye, suka kafirta shi, suka
kafirta sauran Musulmai, daga karshe suka kashe shi. Kuma wannan tunanin shi
Sayyid Qutub ya dauko ya yada shi cikin al'umma ta hanyar littatafansa, har
wasu matasa jahilai, masu kishin Addini suka tasirantu da shi, suka yi ta kafa
kungiyoyi irin Boko Haram, suna ta'addanci a kan al'ummar Musulmi, saboda ta
saba "Hakimiyya".
Saboda haka Shaikh Muhammad Ibnu Ibrahim ba shi da
alaka da Akidar Khawarijawa ta "Hakimiyya".
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.