Ticker

6/recent/ticker-posts

Bitar Labaran Da Suka Tsallake Zagayen Farko a Gasar Gajerun Labarai Ta ACR. Ahmad Musa Dangiwa (2024)

An tura kimanin labarai sama da ɗari biyu (200) domin shiga Gasar Gajerun Labarai Ta ACR. Ahmad Musa Ɗangiwa (2024). Alƙalan gasar sun tantance labaran a zagayen farko inda suka zaɓi labarai 32 da suka yi nasara. Daga nan an buɗe zauren WhatsApp inda aka saka dukkannin marubutan da labaransu suka samu nasara a zagayen farko. Alƙalan gasar sun tsara musu bita ta musamman domin ba su ƙwarin guiwa da haska musu hanya da kuma yi musu bayani dangane da  jigon gasar. An yi haka ne da manufar ƙara inganta labaran don su samar da sakamako da ake buƙata wadda za ta kai ga cimma manufar gasar.
A ƙasa an kawo yadda bitar labaran ya kasance:
SANARWA
ABIN DA YA KAMATA MARUBUTA SU FAHIMTA DANGANE DA JIGON WANNAN GASA

BURI

Kamar yanda kowa a cikinmu ya sani an saka Jigon wannan gasa na bana ya zama a kan Guri/Buri ko gurukan rayuwa da mabanbantan mutane ke son cimmawa a tsawon lokutan rayuwarsu.

Gurukan da ake magana sun hada da

1. Gurin mutum na kashin kansa, misali wani ya ce ina so na zama malamin makaranta, ko likita ko wanzami ko direba.

2. Gurin iyaye na abinda suke so yayansu su zama.

3. Gurin kawo sauyi, ko gudummuwa da wani ya ke da shi saboda cigaban alumarsa, milasi wanda ya tashi a wurin da ake yaki yayi gurin samar da dawwamammen zaman lafiya, ko Dan manoma yayi gurin kera tarakata, ko wanda babu asibiti a garinsu yayi gurin zama likita domin ya gina asibi a garinsu ya taimaki mutanensu, ko wanda babu makaranta a garinsu yayi gurin nemo ilimi a wani wuri domin ya dawo garinsu ya koyar.

4. Gurin ahali baki daya, misali dangi gaba daya su ginu kan wani guri na samun wani abu da basa da shi, ko wanda suke da shi a baya amma ya kubuce masu, su shirya dabarun sake dawo wa kansu da shi.

5. Haka kuma akwai guri na mutanen gari baki daya, ana iya samun mutanen wani gari da suke da gurin samun wani abu ko wata bukata da suka rasa su hada kai su yi aiki tare domin samun wannan cikar gurin nasu, walau ta hanyar amfani da mutum daya ko fi

Haka kuma wani abu da mafi yawan marubutan da suka shiga wannan gasa basu fahimta ba shi ne, sanin gurin mutum ba shi muke bukata ba. Babban abinda muke bukata shi ne mu ga dabarun cimma guri karara a cikin labarun

Da kuma kalubalen da mai neman cimma guri Ka iya fusknata, koda yake ta wannan fannin anyi kokari, sai dai kuma kusan duka kalubalen da aka rika kawowa gamagarin kalubale ne, kamar mutuwar iyaye, talauci, sabanin ra'ayi tsakanin Yaya da iyayensu Kan abinda su ke son zama da dai sauransu. Duk da cewa su ma wadannan din suna cikin kalubalen, amma dai ba su ne muka fi son gani ba.

Akwai labarun da suka tsallako wanan zangin ba domin su cika sharadi ba, sai dai saboda sun kawo wani abu da mu ke son gani wanda baa samu saura sun kawo shi ba, idan an zo wajen fidar labaru a cikin bitar, kowa zai ji abinda ya kamata ya gyara a cikin labarinsa.

Kwamitin shirya wannan gasa ya so ya ga marubuta sun yi amfani da kwarewa da iya sarrafa alqalami cikin gwaninta da sako Mai Janhankali wajen gina irin wadannan labaru, da zasu kasance cike da karfafa guiwa da ilimimantarwa.

Sai dai kusan dukkan labaru da sama da 200 da aka turo sun fi karkata a kan na farkon, gurin kashin kai, ina so na zam likita, injiniya, malimin makaranta danjarida da dai sauransu. Kadan ne suka dubi sauran batutuwan.

Haka kuma, wani abu mai muhinmanci da marubutan ba su duba ba in banda kadan daga cikin su shi ne, yanda iyaye zasu iya fahimtar inda yaransu suka sa gaba da abindà yafi dacewa da su da hanyoyin da za su iya taimaka wa yaran su yi nasara, da su kansu malaman makarantu, mun sani a tsarkin ilimi na kasar nan akwai (department of Guidance and Counselling) wanda aka tanade shi domin wanan amma dai duk ba mu ga irin wannan a cikin rubutukan ba.  

Labaran da suka yi magana a kan gurin zama likita su ne suka fi yawa, domin sun kai 30, akwai fannonin ilimi masu Jan hankali a wanan zamanin duk bamu gansu ba, muna son ganin sabbin kirkire kirkire na ilimi a cikin labarun nan.

Har a haka muna yaba wa marubutan da suka shiga wannan gasa, wadanda suka samu nasarar zuwa wanan zagaye da ma wadanda basu samu nasara ba.

Zamu yi aiki tare da ku da malaman da muka gayyato domin sake fasalin wasu daga cikin labaran nan ta yanda zasu dace da abinda gasar ke son cimmawa.

Mun gode.

SANARWA
Barkanmu da juma'a da fatan duk muna cikin annashuwa da walwala,  Allah ya kara mana jagorancinsa. 
Bayan kammala bitar dukkan labarai, muna sanar da ku cewa lalai labarin kowa yana da ingancin da zai iya yin zarra a wannan gasa. Musamman in an bibiyi shwarwari da kuma gyare-gyaren da aka bayar. Muna matukar yaba maku da jinjina maku irin yadda kuka bada lokacinku wajen wannan bita duba da irin tarin ayyukan da ke gaban kowa. Muna kuma bada hakuri ga wadanda suke jin mun kausasa masu harshe ita harkar ilimi dama haka take zuma ce ga zaķi ga harbi.
Za a yi la'akari da wadannan abubuwan wajen turo cikakken labari
1. Za a turo cikakken labarin bisa ga wannan email din dangiwaliterary2020@gmail.com 
2. Wajibi ne labarin ya kasance bai gaza kalma 3800 ba kuma kar ya haura 4000
3. Wajibi ne ayi amfani da haruffa masu kugiya a bisa  tsarin Hausa Universal font. (Akwai su a waya da kwamfuta)
4. Za a rufe karbar cikakken labain ranar 27/8/2024 da karfe 12 na dare. Ko yau in Kwai wanda ya kammala kuma zai iya turowa
5. Za a aiko da labarin ne a tsarin Microsoft Office.
Shawara
Labaran da suka zo da suna iri daya marubutan na iya sauya sunan da kansu, haka kuma suna iya bari in labaran sun fada hannun alkalai su sauya masu.
Marubuta su maida hankali wajen nakaltar wadannan abubuwan a cikin labarinsu domin a kansu ne alkalai zasu maida hankali:
* Budewar Labari
* Kalmomi
* Sako
* Taurari
* Ka'idojin Rubutu
* Rike mai karatu
* Yiwuwar buga Labarin
* Salon Marubucin
Duk mai wata tambaya kuma zai iya yi. Mun gode kwarai da gaske.

SANARWA GAME DA RANAKUN BITA

Assalamun alaikum,

Barkanmu da warhaka, fatan duk mun tashi lafiya.

In sha Allah nan ba da dadewa ba za a fitar da jaddawalin fara bita. Za a raba bitar ne rukunin shidda kowane jagoran bita zai yi bita ne kan labarai biyar. Kazalika za a iya sauya fasalin labari a wajen bita musamman labaran da suka karkata kan zama likita, labari ďaya ne za a bukata a wannan fannin.

Bayan fitar da jadawali duk marubucin da yaga lokacin da aka sa masa bita akwai wani babban uziri a tare da shi zai iya magana domin a sauya masa kafin fara bitar, domin da zaran an yi bitar labarin marubuci baya nan to za a iya jingine labarin.

Kazalika ana bukatar marubuci yayi magana kan abin da ya shafi labarin da ya gabatar domin gudun sauya masa akalar labarinsa saboda rashin fahimtar labarin daga masu bita. Tattaunawa ce ta ilimi ake so a yi wadda zata bayar da dama a samu labaran da zasu yi goggaya da sauran labaran duniya, domin a wannan karon akwai tunanin fassara labaran zuwa harsuna uku banda Hausa insha Allah.

Akwai labarai shidda da suka zo da suna iri daya wanda insha Allah shi ma za a duba yiwuwar sauya wa wasu suna, labaran su ne kamar haka:

Tarnaki: Lawan Muhammad PRP

Tarnaki: Fiddausi Muhammad Sodangi

Rai da Buri: Lubabatu Isah

Rai Buri: Fareeda Umar Aliyu

Burin Fatima: Mubarak Idris Abubakar

Burin Fatima: Faridat Hussaini Mshelia.

Wannan bitar za a gabatar da ita ne a Online ko dai ta manhajar Zoom ko kuma Watsapp meeting room. Muna bada shawara ga marubutan da su koyi yadda ake amfani da wadannan manhajoji domin samun sauķin gudanar da bitar cikin nasara.

Za a iya yin tambayoyi daga Darussan da suka gabata da duk wani abu da ake ganin ya shige duhu.

Fatan alheri ga kowa.

RUKUNI NA FARKO RANAR LARABA 17/7/2023 KARFE 11 NA SAFA

1. Hassan Labaran Danlarabawa: Ganin Hadari

2. Fauziyya Sani Jibril: Babu Rashi ga Allah

3. Rabi'atu Sani Katibu: Boyayyar Basira

4. Zainab Abdullahi: Burin Salma

5. Safna Aliyu Jawabi: Mafarki

6. Fiddausi Muhammad Sodangi: Tarnaki

Wadannan sune rukuni na farko da za a yi bitar labaransu insha Allah kamar yadda aka tsara a sama.

RUKUNI NA BIYU RANAR ALHAMIS 18/7/2024

1. Khadija Muhammad Shiru: Hasken Rayuwa

2. Farida Hussain Mshelia: Burin Fatima

3. Badi'at Ibrahim: Kudiri

4. Fiddausi Sani da Hafsat Ibrahim: Nakasa ba Kasawa

5. Aisha Adam Hussain: Duk Girman Giwa

6. Haruna Birniwa: Duniyar Shahara

Wanda zai jagoranci wannan rukunin shi ne Yazid Abdul'aziz Nasudan. @DGW Yazid Abdullahi Nasudan

Za a sanar da manhajar da za a yi amfani zuwa ranar laraba insha Allah.

RUKUNI NA BIYU RANAR ALHAMIS 18/7/2024

1. Khadija Muhammad Shiru: Hasken Rayuwa

2. Farida Hussain Mshelia: Burin Fatima

3. Badi'at Ibrahim: Kudiri

4. Fiddausi Sani da Hafsat Ibrahim: Nakasa ba Kasawa

5. Aisha Adam Hussain: Duk Girman Giwa

6. Haruna Birniwa: Duniyar Shahara

Wanda zai jagoranci wannan rukunin shi ne Yazid Abdul'aziz Nasudan. @DGW Yazid Abdullahi Nasudan

Za a gudanar da bitar ne karfe 11 na ranar insa Allah a manhaje WatsApp meeting

RUKUNI NA UKU RANAR JUMA'A 19/7/2024

1. Rai da Buri: Fareeda Umar Aliyu:

2. Maryamu: Zainab Abdurrahman Aminu

3. Aniya bi Aniya: Binyaminu Zakari Hamisu

4. Cikar Burina: Lantana Jafar

5. Juyin Waina: Dangallima Umar Faruq

Wanda zai jagoranci wannan rukunin shi ne Abubakar Al'mustapha Yar'adua @DGW Abubakar Almustapha Yar'adua

Za a gudar da bitar ne da karfe biyar na Yammacin ranar a manhajar WatsApp meeting

RUKUNI NA HUDU RANAR ASABAR 20/7/2014 DA KARFE 11 NA SAFE

1. Lubabatu Isah: Rai da Buri

2. Nana Aicha Hamissou: Baƙuwar Lamba

3. Abu-Ubaida Sani da Aishatu Muhammad Bazango: Kabarin Burina

4. Lawal Muhammad PRP: Tarnaƙi

5. Faisal Haruna Hunkuyi: Canjin Launi

Wadannan rukunin Nabila Ibrahim Khalil ce za ta jagoranci yi masu bita a ranar Asabar 20/7/2024 a Manhajar Watsapp meeting.

RUKUNI NA BIYAR RANAR LAHADI 21/7/2024

1. Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo: Haka ba haka ba

2. Rabi'atu Sani Katibu: Boyayar Basira

3. Mubarak Idris Abubakar: Burin Fatima

4. Salisu Tukur Gaiwa: Labarina

5. Halima Abdullahi K/Mashi: Dogon Buri

Wanda zai jagoranci wannan rukuni shi ne Mujaheed Abdullahi' Za a yi bitar ne da karfe 11 na ranar Lahadin a manhajar Google Meet insha Allah.

NB: Fiddausi Sodangi ma zata yi a bitar labarinta a ranar.

RUKUNI NA SHIDA RANAR LITININ 22/7/2024

1. Ibrahim Baba: Dacen Rayuwa

2. Hauwa'u Adam Sulaiman: Dahakin da ka Raina

3. Hauwa'u Shehu: Furen Ruhi

4. Abba Abubakar Yakubu: Ƙaddara ta Riga Fata

5. Aisha Abdullahi Yabo: Zanen Ƙaddara

Wannan rukunin za su karbi bitarsa karkashin jagorancin Malama Halima Ahmad Matazu ranar litinin da karfe 11 na safe a manhajar zoom

NB: Akwai Ibrahim Baba da ya bada uzirinsa a ranar za a duba ko zuwa dare sai a yi masa.

Click (an sanya liƙau ɗin Zoom a nan) to start or join a scheduled Zoom meeting.

Gasar Rubutattun Gajerun Labaran Hausa Ta ARC. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation

Post a Comment

0 Comments