Ticker

6/recent/ticker-posts

Rukunnan Mika Wuya Ga Allah Da Addininsa

RUKUNNAN MIƘA WUYA GA ALLAH DA ADDININSA

Za ka zama cikakken Musulmi mai imani da Allah da Addininsa da Manzonsa ne idan ka sallama wa Allah da Manzonsa a komai, ka gaskata shi ka yi imani da shi, ka yi imani da Littafinsa da Manzonsa da dukkan abin da ya ce a yi imani da shi.

Akwai wasu rukunnai guda biyar wadanda da su ake mik'a wuya ga Allah da Addininsa a bisa hakika:

1- Ka gaskata Allah da Manzonsa a dukkan labari da ya zo cikin Alkur'ani da Sunnar Manzonsa (saw), ba tare da shakka ba balle kuma karyatawa.

2- Ka yi biyayya ga umurni da hanin Allah da Manzonsa ba tare da jayayya ko jin kunci a rai ba.

3- Ka yi imani da kaddara ta hanyar yin hakuri da yarda da abin da aka kaddara maka, ba tare da kalubalanta ko nuna fushi ba.

4- Ka gabatar da Wahayi (Alkur'ani da Hadisi) a wuraren sabani, kana mai yarda da hukuncinsa.

5- Ka gabatar da Wahayi a kan komai, ba tare da kalubalantarsa da ra'ayi ko mazhaba ko darika ko kungiya ko siyasa ko wani abu daban da ya saba masa ba.

Wanda ya yi imani da Allah da Littafinsa da Manzonsa bisa wadannan rukunai shi ne mai cikakken imani da mik'a wuya ga Allah da Addininsa.

A cikin wannan akwai raddi ga dukkan masu tawili ko inkarin Nassoshi da suka saba son ransu, kamar masu inkari ko tawilin Nassoshin Siffofin Allah, ko masu inkari ko tawilin Hadisan gaibi, ko masu inkari ko tawilin Hadisan hukunce-hukunce da sunan sun saba Mazhaba, ko masu inkari ko tawilin Hadisan da'a ma shugabannin Musulmai da yin hakuri a kan zaluncinsu don sun saba ma tafarkin kungiyarsu ko siyasarsu.

✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments