Ticker

6/recent/ticker-posts

Azzaluman Shugabannin Nigeria - Ku Ji Tsoron Ranar Haduwarku Da Allaah

TAMBAYA (192)

Assalamu alaikum warahamatullahi Allah ya Kara ma malam daraja da daukaka yakara haske yakuma hadamu a aljannah firdausi mlm Bayan nagama sauren voice dinda katuro ta yadda zamuyi koyi da manzom mu annabi Muhammad S a w ta bangaren sallah sai wani abu yatayar mani da hankali wannan abun kuwa shine

Nafarko dai sallan nan da mukeyi munakan rokon Allah nefa yasa karbarbiya ce nadaya kenan

Sannan abu na biyu sai Ina mamaki yadda zakaga wasu bayin Allah sude burinsu sugansu akan karagar mulki Kota halin kaka indai har kudade zasu rinka shigo masu

A gaskiya mlm wata mulkin ko ince shugaban ci musiface wlh meyasa nace Hakan shine

Yanzun kaduba kagani muma damuke zuwa makaranta kuma muna sauraron karantar wankuma dadai sauran su ahaka muna tunanin ta yadda ubangiji zai karbi Ibadunmu

Balantana Kai bawan (Allah) me kwadayin mulki baka tunanin gyara goben ka 😭😭dazarar kasamu mulkin nan indai bawanda (Allah) yaba Shiba to dawuya ibadar sa tatafi basa daidai

Abinda yasa nace Haka shi yau idan kana office Kai ne cike ciken takardu Kaine amsa wayoyin jama, a Kai ne hawan net Kaine baka da lokacin danginka balantana kusada zumunci Kaine tunanin tafiye tafiye Kaine bakada lokacin yin ibada karshen tama kilan kafin katashi office din nan zaka Kai yamma maybe ma sallolin ka gwamatsasu ne wuri sai ankoma gida San nan ayisu subhanallah

to ballema ayi Maganar sauran cikon ibadun to ahaka ne mlm mutun kekokuwar son dorakan a wahala wlh mlm mu mutane muke raina baiwar da Allah yayi muna kobaka da arziki Inhar Allah zabaka damar masa biyayya da koyi da sunnan Manzon s a w to kagode masa Allah ka Kara muna Imani da tsoron (Allah) amin 🤲 nagode

AZZALUMAN SHUGABANNIN NIGERIA - KU JI TSORON RANAR HADUWARKU DA ALLAAH

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Lahaula Wala quwwata illa billah

Lamarin ne yanzu sai addu'a kawai

Amman tabbas wannan rubutun naki qalubale ne  ga ni kaina dakuma sauran alummar musulmai baki daya musamman ma su shigabannin nan da kika magana akansu

Duba Kiga yanda shugabanni suke danne haqqin talakawansu

Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: Dukkan Ku masu kiwone Kuma kowa zaa tambayeshi akan abin da aka bashi kiwo"

(Sahihul Bukhari)

Wallahu shugaban ninmu na Nigeria tausayi suke bani. Saboda kadan daga cikinsu ne suke qoqarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu

Indai har maigida zaa tambayeshi akan yanda ya shugabanci gidansa Mai dauke da shi kadai da matarsa da dansa daya tilo wanda adalcinsa ne kadai zai ceceshi a ranar Lahira to Ina Kuma ga Wanda zai shugabanci mazaba, ko qaramar hukumar, ko shiyya, ko jiha ballantana kuma qasa gaba daya Mai dauke da bayin Allaah dama da miliyan 200

Tabbas Mulki masifa ne indai baa sauke nauyinsa yanda ya kamata ba

Haka zaa zo da masu Mulki a ranar Lahira a daure da sarqa😭adalcin shugaba ne kadai zai sa Mala'iku su kwance wannan sarqar

Ni lamarin shugaban ci yana firgitani matuqa

Ya Allaah ka rabamu da shugabancin da zai zama Dana Sani a duniyarmu da lahirar mu

Amman tabbas yanda qasar Nan ake cikin wannan yanayin alhalin shugabanni suna ci gaba da satar dukiyar talakawansu...to sai ma ka rasa ina zasu kai dukiyar. Kallidai wadanda aka tonawa asiri aka gano sun saci Biliyoyi. Gashi Kuma a ranar Lahira sai an tambayi mutum ya akai ya samu: Sisi, Taro, Sile, Kwabo har zuwa Naira 1. Ballantana Kuma Wanda ya saci Tiriliyan. Wannan zaisha tambaya kam. Ya ya samu kudin sannan ya ya kashe su

Akwai matsala fa !

Allaah dai ya tabbatar damu akan Musulunci Bisa Sunnar Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam Amman tabbas idan talakan Nigeria ya sake ya shiga Wuta to yayi asara 2. Ga asarar yunwa ga Kuma dukan Mala'iku. Shiyasa ake son mutum ya koma ga Allaah

Yayinda azzaluman shugabanni suke shaqatawa a Hilton Hotel ko Kuma suke cin abincin N100k a Sharaton Hotel. Ko Kuma su saci kudin qasa su je Hotel din da yafi kowannen tsada a Duniya Mai suna "Burj al-Arab" dake garin Jumerah a kasar Dubai, su kama daki 1 akan $25,000 (wanda yakai N41,831,750)

Magana ake ta kwana 1 kacal a wannan babban Dakin dake Hotel din sai ka biya Naira Miliyan 41 Kuma akwai Yan Majalisun qasarnan da sanatocinmu da suke zuwa irin wadancan Hotels din alhalin ga talakawansu can suna kwanan yunwa. Bama wannan ba ko kinsan cewar da akwai Yan Siyasar mu da suka Gina manyan Hotels masu tsada a qasashen Larabawa din ?

Dan Nigeria kabi Allaah ka bi Sunnar ManzonSa kawai ka huta. Kada kaje kayi 2 - 0

Amman wata Shari'ar...

Rashin aiki da Aya ta farko da aka saukar a Qur'ani shine babban dalilin da yasa wasunsu basusan ilimin Halak da Haram ba. Shiyasa Allaah Azzawajallah yace:

( اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ )

العلق (1) Al-Alaq

Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.

Domin kuwa ai sai kayi karatu sannan zaka san hukuncin Allaah gameda lamarin shugabancin

Haka Kuma wasunsu Basu san Aya ta qarshe da aka saukar a Qur'ani ba wadda ita kadai ta isa ta sa azzalumin bawa ya ji tsoron haduwa da MahaliccinSa. Allaah Azzawajallah yace:

( وَاتَّقُوا يَوْمًا تُرْجَعُونَ فِيهِ إِلَى اللَّهِ ۖ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفْسٍ مَّا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ )

البقرة (281) Al-Baqara

Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su.

Muna Kuma talakawan da laifinmu domin kuwa Idan bera na da sata itama daddawa tanada wari. Da kowannen mu zai duba laifin da yake aikatawa yayi Taubatun Nasuha da tuni Allaah ya kawo Mana dauki. Amman tabbas indai bazamu gyara halayenmu ba to Allaah bazai daina hadamu da azzaluman shugabanni ba. Ya Allaah ka bamu ikon gyarawa

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments