Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Halatta Na Yi Aiki A Event Center

TAMBAYA (181)

Allah ya gafartawa Malam, dan Allah shin ya halasta nayi aiki a Event Center ba'a lokacin biki ba kamar da rana ana musu share-share da wanke-wanke, shin zan iya yin wannan aikin dan na samu kudi.

YA HALATTA NA YI AIKI A EVENT CENTER

AMSA

Wannan kam ya halatta

Amman kada ka sake ko anan gaba kayi tunanin zuwa matakin masu kula da sabgar bikin saidai idan zasuyi walima ne irin wadda shari'a ta halatta

Amman irinsu bawa Dj gudunmawa, wannan idan kayi participating to Kaima kanada kamasho a cikin zunubin domin kuwa duk Albarkar aure mostly a wajen Dj take zubewa

Wannan sai ya tunamin wani rubutu da nayi kwanakin baya Kuma Alhamdulillah fadakarwan tayi trending sosai a media platform:

Sauraren kida a boye haramun ne, laifi na 2 shine: saurarensa a cikin mutane, laifi na 3 shine: ka cewa mutane su dinga saurara, laifi na 4 shine: ka halattawa mutane saurarensa, laifi na 5 shine: tirsasawa mutane su saurara, na 6 shine: ka dinga fada da mutanen da suke cewa haramun ne, na 7: ka kira Dj a cashe a bikinka, na 8: ka liqa Naira a goshin mawaqin, na 9: ka tattake kudin, na 10: ka ce Allaah ka bamu zaman lafiya a bikinnan. Ya Allaah ka bamu ikon gyarawa @Usmannoor_Assalafy

Wadannan abubuwan Bidi'ah da ake a lokutan bukukuwa suna daga cikin dalilan da suka sa muka bude sabuwar makaranta, Online mai suna: MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI. Mai ra'ayin Registration zai iya min magana direct ta Private Chat

(WhatsApp: 07035387476)

Wallahu taala aalam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments