Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mijin Da Ya Yi Tafiya Ya Bar Iyalinsa Tsawon Lokaci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam inna kwana, malam Dan Allah inna da tambaya miji ne ya tafi ya bar mace da yara 4 yanzu shekara yaki yadawo bakuma yaturo musu komai sai karya kullum yace zai dawo Amma shiru Babu Kuma Wanda yasan Inda yake, yaki ya fada. shin yaya mastayin auren su yake?

HUKUNCIN MIJIN DA YA YI TAFIYA YA BAR IYALINSA TSAWON LOKACI

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ciyarwar iyali da shayarwarsu da kulawa da larurorinsu na yau da kullum kamar sutura, muhalli, da ɗaukar nauyin ilmantarwa yana daga cikin tarin nauye-nauyen dake kan Maigida amatsayinsa na Uba ga ‘ya’yansa kuma miji ga matarsa kamar yadda Allah ya fada acikin Alƙur’ani :

"MAZAJE SUNE TSAYAYYU BISA MATAYE SABODA ABINDA ALLAH YA FIFITA SASHENSU AKAN SASHE, DA KUMA ABINDA SUKA CIYAR DAGA DUKIYOYINSU"...

Al Imam Ibnu Katheer Yace : "Namiji shine tsayayye akan lamarin mace domin shine mai kulawa da lamarinta, kuma Shugaba agareta, shine gaba da ita, kuma shine mai yin hukunci akanta kuma mai ladabtar da ita idan ta karkace daga hanyar Allah.

Imam Abu Dawud ya ruwaito daga Wahbu yana cewa wani bararren bawan Sayyiduna Abdullahi bn Amr (radhiyal-Lahu anhu) yazo yayi masa sallama domin wata tafiya da zaiyi, sai Ubangidan nasa wato Abdullahi bn Amr ya tambayeshi : "Shin ka bar wa iyalinka abinda zasu ci acikin watan nan?"

Sai yace "A’a".

Sai Abdullahi (radhiyal-Lahu anhu) yace masa "Tunda hakane koma wajen iyalanka ka bar musu abinda zai ishesu, domin naji Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa : "YA ISHI MUTUM LAIFI MAI GIRMA ACE YA HANA MUTANEN DAKE CI TA KARKASHINSA, ABINDA ZASU CI".

Kuma acikin wani hadisin da Imamu Muslim ya ruwaito Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam bayan ya lissafa wasu hanyoyin da mutum zai iya ciyar da dukiyarsa domin neman lada awajen Allah, kamar ciyarwa domin jihadi, bayar da dukiya domin ‘yantar da bayi, yin sadaƙah ga mabukata, sai yace : "WANDA YAFI LADA ACIKIN WAƊANNAN SHINE SUKUYAR DA KA CIYAR DA IYALINKA".

Don haka wajibi ne ɗaukar nauyin iyali domin yana daga cikin adalcin da Allah ya wajabta shi akan duk namijin da yake da niyyar yin aure.

Idan kuma miji ya gaza sauke wannan nauyin, to ita matar tana da damar kaiwa Ƙararsa gun mahukunta domin su bi mata hakkinta. Alkali yana da damar ya kirawo waliyyan mijin naki, ya tilasta musu suje har inda yake su dawo dashi gida.

Idan kuma hakan ya gagara, to shi alƙalin yana da cikakken ikon raba auren bisa hujjar cewa mijin naki bazai iya ɗaukar nauyin iyali ba. Shi kuwa ikon ɗaukar nauyin iyali yana daga cikin sharudan Ƙulla aure, kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya fada. Yace :

"Yaku taron samari! Wanda duk yake da ikon ɗaukar nauyin iyali daga cikinku, to yayi aure. Domin yin hakan shine zaifi runtsewa ga idanuwa, kuma yafi kiyayewa ga farjojinsu".

Kuma bayan haka ma ga kuma rashin sanin yaushe ne zai dawo, ballantawa samun sauran abubuwan da ake bukata acikin aure kamar biyan bukatar jinsi (ɗauke wa iyali bukatar sha’awa) da sauransu, wanda shima ginshiki ne acikin hakkokin zaman aure.

WALLAHU A’ALAM.

DAGA ZAUREN FIƘHU 07064213990

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments