TAMBAYA (96)❓
Assalam alaykum wa rahmatullah wa barakatuhu mlm da ftn an tachi lafiya tambayar ita ce chin ya halalta sawraren wakar soyayya ko ta fadar bège (musamman ranar Takutaha)
TAKUTAHA:
ZAN IYA SAURARON WAƘAR BEGE KO TA
SOYAYYA
AMSA❗
Waalaikumussalam, warahmatullahi, Wabarakatuh
Alhamdulillah. Yar uwa amsarki tana cikin wasiƙar da na rubutawa mawaƙa
✒WASIƘA ZUWA GA MAWAƘA
@Usmannoor_As-salafy
Salamu alaikum. Warahmatullahi. Wabarakatuhum.
Nasha amsar saƙonnin tambayoyi akan hukuncin sana’ar waƙe-waƙe da kide-kide a addini.
Zanso kowanne mai sauraron kade-kade ya nutsu ya karanta wannan saƙon a matsayin amsar
tambayoyinsu
Akwai wasiƙar da na taba rubutawa wani mawaƙi (wanda bazan kama sunansaba) saidai zan iya bayyana saƙon da ta kunsa maybe
hakan yazamo silar shiriyar dubban mawaƙa masu saka kida a cikin waƙarsu, fatana duk mai jin kade-kade ya tuba ya daina silar karanta wannan saƙon. Ga wasiƙar kamar haka;
Innal hamda lillah, nahmadahu wanastainuhu,
wanastaghfirhu, wanauzu billahi min shururi anfusuna, wamin sayyi ati aamalina,
man yahdiyallahu fala mudillana, waman yahdil fala hadiyala, wa ash hadu anla
ilaha illallah, wahdahu la sharikala, wa ash hadu anna muhammadan abduhu
warasulahu, amma baad
Fainna asdakal hadis kitabullah, wa khairi hadi,
hadi Muhammad SAW, washarril umuri muhdisatiha, wakullu muhdasatin bidia,
wakullu muhdasatin dalala, wakullu dalalatan finnar, aazanallahu minannar. Amma
ba’adu
️Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhum
Na rubuto wannan wasiƙa ne domin tabbatarda cewar alaƙar dake tsakanina dakai
babu karya a ciki domin kuwa duk mai son ka shine zai fada maka abinda zai
fissheka fiddunya wal akhira
Ka kasance mutum mai magoya baya sama da (...) a
instagram page, shawarar da zan bada anan shine, shin mezai hana ka daina saka
kida a waƙoƙinka domin kuwa hakanne
yake sa yan mata da zawarawa da matan aure suke tiƙar rawa a tik-tok kai kuma kana daukar ɓideo dinnasu kana posting, wanda maybe nangaba yayansu ne
zasu ga ɓideos din kuma tabbas sai sun tsinewa mawaƙin da ya zama silar
rawar tasu, anan shaidan yayi nasara kam
Burina shine (...) ya ji sautin waƙar matan Hurul Ayn a
Aljannah (Alfirdous in particular) to ammanfa hakan bazata yiwuba sai an koma
hadisin ma’aiki SAW wanda ya gargadi al’ummarsa akan sharrin sauraren kade-kade
Idan har ka goge ɓideos din wanda Shi Allah SWT mai gafarane, zai iya
gafartawa bawansa idan yaso matuƙar bai mutu yana shirka ba. Zaiyi wuya ka daina saka kida a waƙenka ni shaidane kaima
kasani domin kuwa ka saba amman idan baka mantaba akwai manyan mawaƙan da duniya ta sansu
kuma sun maye gurbin sana’arsu ta industry da neman ilimin addini ka’in da na’in
dakuma yada ilimin ga masu sauraro da ganinsu, kamar irinsu Shaykh Bilal
Philips wanda kafin ya musulunta dacan ya kasance makadin guitar ne a kasar
amurka, ga abin koyi Shaykh Yusuf Estes wanda ya musuluntarda dubunnan
Christians wanda dacan mawaƙine a Catholic Church a kasar amurka, celebrities kamar irinsu: Peggy
Melati Sukma, Teuku , Kartika Putri
Hakama mawaƙiyar Irish Sinead O’Connor wadda ta musulunta a shekarar 2018 ta maida
sunanta Shuhada Sadaƙat, wadda ta rasu a shekararnan da muke ciki, 2023 (Allah ya jikanta tareda
sauran musulmai baki daya)
Kamar irinsu mawaƙi Noor Al-Kautsar, Ucay wanda suka bar sana’ar a
2013 suka koma yada da’awar musulunci. Irinsu Derry Sulaiman tsohon makadin
jita, a yanzun dukkansu suna amfanida sana’arsu wajen janyo hankalin mutane su
san addinin musulunci
Idan kuma ka koya musu ko da Hadisi daya ne to
tabbas zaka samu ladansu idan suka aikata aikin da yake a cikin Hadisin,
daukakarka anan duniya ga kuma lada mai tarin yawa a lahira. Bazaka iya dainawa
a lokaci daya ba saboda nisa a cikin harkar amman a hankali a hankali zaka ga
komai ya sauya idan ka kyautata niyyarka hade da neman addu’ar iyaye, to
ammanfa akwai ƙalubale mai
tarin yawa idan ka guji masu ra’ayi sabanin naka wato yan Kannywood. To amman
ai Allah zaiji dadin haka hakama malamai masu jan hankali akan illolin kide
kiden dakuma rawar tik-tok din
Zanso ace wannan shawarar kayi amfani da ita la’akarida
gaskiyace nake fada ko da kuwan hakan bazai maka dadiba saboda duk mai son ka
don Allah to kamata yayi ya fada maka abinda zai amfaneka fiddunya wal akhira.
Kuma na tabbatar da idan kayi hakan to daukakar da Allah yabaka saidai tayi
sama ba kasa ba, domin kuwa duk wanda ma baya son ka to silar haka saikaga
Allah ya saka masa son ka. Da zaka dau wannan shawarar kuwa da kaine zaka fara
karya record din haka a tarihin mawaƙan hausa baki daya, daukaka bisa daukaka fiddunya wal akhira. Domin kuwa
nidai ban taba jin labarin wani mawaƙi da yabar waƙa domin Allah ba saidai zamani ya shudar da shahararsa. Burin shatan waƙa (Allah yajikan rai)
shine kada yayansa su fada harkan waƙa, haka sukaita takun saƙa da dansa wanda yayi ƙoƙarin shiga harkan, a
karshedai Allah ya ƙaddara ba wanda zai gajeshi a cikin yayansa
A iya dan bicikena na bincika, a gaba dayan
malaman Ahlus Sunnah babu wanda yake goyon bayan sana’ar kide kide, saidai ma
suna hani ne akan hakan la’akarida illolin da hakan ya haifar ga al’umma kuma
zai haifar ga yayan musulmai masu tasowa
Yanzu dai kaduba kaga wancan ƙuote din wanda na gani a kofar studio din daya
daga cikin yaranka, an rubuta "Only in the listening of the music does
heart find peace" ma’ana "Da sauraron kidane zuciya take samun
nutsuwa" wanda hakan yaci karo da ayata 28 cikin Suratu Ra’ad wadda Allah
yace: "Waɗanda suka yi ĩmãni kuma
zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukãta suke
natsuwa," to kaga wannan idan ya rubutane a rashin sani to yakamata ka
nusar dashi illar hakan
(...), kai kanka kasandai da yawan ambaton Allah
zuciya take samun nutsuwa to amman meyasa a cikin studio din yasaka "Da
yawan sauraron kida da waƙa zuciya take samun nutsuwa" ?
To wannan dalilin ne yasa naje dakaina domin bashi
shawarar ya cire wannan "ƙuote" din, lokacin da naje wajen 10 na dare, ban tarardashi ba amman
hancina shine yayimin maraba da warin wiwi da wani yaron yaronnaka yake
nannadawa (Kuma a goman karshen watan ramadana), nace masa ina wane-wane yace
ya tashi saidai wane shima yaje wani waje uzuri yana tafe, na jira a waje inata
tuno wani hadisin da Ma’aiki SAW
Sahihin Hadisin yana cikin Ibn Majah yace: "A
karshen zamani (kafin alƙiyama ta tsaya) al’ummata zasu dinga shan giya su kirata da wani sunan,
zasu dinga saka kayan kide-kide a kunnuwansu, Allah zai sanya kasa ta hadiyesu
sannan ya maidasu birrai da aladu"
A lokacin sai na tuno da cewar ƙwaƙwalwar mutum ta rabu kaso hudu (Temporal lobe,
parietal lobe, occipital lobe dakuma fore lobe) shikuma fore lobe dincan shine
inda ake tattara ayyukan zunubban mutum sabanin occipital lobe wajenda ake
adana danasani wanda hausawa ma kance danasani ƙeyace, shiyasa ma Allah ya gargadi Abu Jahal a
cikin Suratul Alaƙ ayata 15 da ta 16, sakamakon karyar da yake yiwa addinin musulunci:
"A’aha! Lalle ne, idan bai hanu ba (yin ƙarya), lalle ne zã Mu ja
gãshin makwarkwaɗa (ƙwaƙwalwa)"
"Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi"
Nan take kuma na tuno da binciken da masana ƙwaƙwalwa sukai na cewar bangaren lymphatic system a
fore lobe dake ƙwaƙwalwa shine yake adana
son shaye-shaye kamarsu giya, cocaine, wiwi, ananne kuma ake adana zunubban
zinace-zinace dakuma sautin kide-kide dalilin dayasa ake rawa, silar zubewar
mutuncin kamilallen dan Adam
Sai nace a raina "Sadaƙa rasulullah SAW", tabbas ma’aiki SAW yayi
gaskiya. Harkar mata tayi yawa a industry, shaye-shaye abin burgewa ne a harkar
sannan kuma jin kade-kade shine ummul-aba’isin dake janyo faruwar ragowar
laifuffuka
Idan kayi sanarwar cewar ka daina saka kida a waƙenka to tabbas wasu daga
cikin yaranka zasu daina kaga kenan tun anan ka fara samun lada da kuma ƙima a idon duniyar
musulmi. Shin ka tuna abinda (...) daya daga cikin fans dinka ya fada maka wani
lokaci da yazo sabon studio dinka yana sanye da (...) irinnaka da shiga irin
taka yace "Gaskiya (...) da ace yanda muke sauraren waƙoƙinka haka muke sauraron karatu da tuni munyi
sauka". To kaga wannan fan din naka yanzun a shirye yake ya fara koyon
Hadisan Manzon Allah SAW daga wajenka, kuma ko kasan cewar zata iya yiwuwa nine
na canza masa ra’ayi akan son kide-kide harma ya fada maka hakan ?
Allah SWT yace a cikin Suratu Luƙman ayata 6: "Kuma
akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba,
kuma ya riƙe ta abin
izgili! Waɗancan sunã da wata azãba
mai wulãkantãwa."
Waƙar da kake danasanin fitarta itace "(...)", kamar yanda ka fada
lokinda akai interɓiew dakai wadda
har yanzu nasan kana danasanin fitarta duniya kuma kullum za’ayita saurarenta
har komawarka ga Allah, ko kasan maybe idan ka daina saka kida din a waƙoƙinka Allah zai kankare maka zunubbanka ?
Ko kasan shahararriyar jarumar Bollywood, Sana
Khan (wadda sukai film din Jai Ho da Salman Khan, haka kuma sunyi film da
Shahru Khan) ta fito duniya tace daga yau na daina film, an tambayeta dalili
tace mafarki nayi ana ganamin azaba kala-kala a kabarina sakamakon harkar film
da kide-kide da raye-raye da nakeyi. Naga interɓiew dinta a Indian News, tana kuka tana bayani. Harma
Shaikh Dr. Zakir Naik yace yayi matuƙar farin ciki da Sana Khan ta tuba ta gano kuskurenta. Wanda Mufti Menk ma
yayi reacting akan lamarin tareda nuna farin cikinsa. To kaga anan Allah ne
yakesonta da alkhaeri da harma aka nuna mata makomarta idan bata tuba ba, a
yanzu haka ta auri shahararren mai kudinnan Mufti Anas, wanda sukaje aikin
Hajji tare, alhalin da Umrah take zuwa tana dawowa ta cire hijabinta ta ci gaba
da film amman yanzu da ta tuba sai gashi har aikin Hajji tayi. Ka duba
tarihinta idan ka samu lokaci
Abul-sahba yace: na tambayi Ibn Mas’ud ma’anar
waccan ayar ta 6 dake Suratul Luƙman saiyace: Lahwal hadis na nufin waka wato al-ghina (Ibn Jarir 21/62
dakuma Hakim 2/411 da isnadi sahihi)
Ibn Abbas RTA ma ya fassara al-ghina a matsayin
waka da makamantansu
Sa’ad Ibn Yasar ya tambayi Ikhramah ma’anar
lahwal-hadis yace waka ake nufi, Al-hussain, Sa’id Ibn Jubayr, Ƙatadah da Ibrahim
al-Nakh’i duk sun tabbatarda lahwal-hadis na nufin waka
Abdullahi Ibn Umar RTA yaji sautin sarewar
makiyaya, sai ya saka yan yatsunsa a cikin dukkan kunnuwansa, ya karkatar da
abinda yake hawa ya kauce daga kan hanyar. Yace: Ya Nafi’, anajin sautin har
yanzu ? Yace: Na’am. Yacigabada tafiya yana tambaya har saida Nafi’ yace yanzu
ba’ajin sautin, sannan sai Ibn Umar ya sauke hannayensa ya dawo kan hanya.
Sannan yace: Naga Annabi SAW yayi hakan a lokacinda yaji ana busa sarewa (Abu
Dawud 4925 dakuma Bayhaƙi 10/222 da isnadin mai kyau)
An rawaito daga Abdurrahman Ibn Auf RTA cewar:
Manzon Allah SAW yace: "An haneni da sauraron saututtuka biyu, sautin
sarewa a lokacin farin ciki da kuma sautin kuka yayin afkuwar wani iftila’i"
(Tirmidhi 1005 da kuma Tayalisi 1783 da isnadi ingantacce)
Malamai sukace indai har haka magabata suke taka
tsantsan da idan sukaji sautin kida to ya zasuyi kenan idan suka tsinci kansu a
wannan zamanin namu ?
A ƙarshe ina son ka ƙara duba wannan wasiƙa sannan ka tambayi shawarar mutane nagari a cikin makusantanka, sai kayi
amfani da abinda suka ce. Kafinnan kuma zanso ka karanta tafsiran ayoyin da
sukai magana akan "Lahwal hadis" da "Al-lagwu", sannan ka
duba littafin Ibn Al-Ƙayyim mai suna "The Eɓils of Music: Deɓil’s Ɓoice and Instrument" da kuma wani littafi mai suna "Music Made Me
Do It" wallafar Dr. Gohar Mustaƙ da kuma littafin "Talbis iblis" wallafar Ibn al-Ƙayyim
Wannan wasiƙar na rubuta ta ne da kyakkyawar niyyar kawo gyara a rayuwarka kuma ba ina
nufin na fika tsoron Allah bane, maybe ma ka fini kusanci da Allah ta wani
bangaren, wallahu aalam, kawaidai nayi amfanida abinda yake na zahiri ne don
kawarda bidi’a a matsayin dan uwanka musulmi. Musamman la’akari da yanda
yayanka suke tasowa da ilimin addini, kuma gashi (...) tana miming waƙarka ana dorawa a media
platforms, kuma sauraren waƙa baya haduwa da karatun Ƙur’ani kamar yanda Ibn Al-Ƙayyim da magabata suka fada, gwara ayiwa tufkar hanci tunda ice tun yana
danye akan iya tankwarashi. Allah ya yafe maka, nima ka tayani da addu’a Allah
ya yafemin zunubbaina. Zanso ka sauka daga layinnan mara bullewa, ka maida
hankali wajen business dinka. Roƙona Allah yasa da ni dakai da sauran musulmai mu saurari waƙe da kidan Hurul Ayn a
Aljannatil Firdous
Wabi hazal ƙadri kifaya. Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla’ilaha illa
anta, astaghfiruka, wa’atubi ilayk
SHARHI: Kamar yanda na fada da farko ba saina kama
sunan shahararren mawaƙin ba to amman musabbabin da yasa na fitarda bayanan yanada alaƙa da zamanin da muke
ciki wato zamanin social media wanda Allah ne kadai yasan adadin mutanen da
zasu karanta wannan wasiƙa inmadai mawaƙan ko kuma masu sauraren kade-kaden, burina hakan yazama silar kawo sauyi
ga rayuwar wadanda shaidan ya ƙawata musu sauraren kida. Mutum ya karya rodi da haƙoransa shine yafi sauƙi akan son zuciyarsa. Ya Allah ka rabamu da son
zuciya. Amsar tambayarki shine: Tabbas kida yana kawo munafunci a mu’amalance,
kuma yana kawo cututtukan ƙwaƙwalwa a kimiyyance
sannan yana kawo raguwar imani a addinance, maganin hakan shine sauraron
karatun al-Ƙur’ani mai
girma. Allah ya bamu ikon gyarawa
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.