Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Wace Hanya Ake Gane Miji Nagari?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam barka dai Tayaya zan gane mijin aure nagari Kuma mai amana nagode Allah ya kara ilimi mai amfani

TA WACE HANYA AKE GANE MIJI NAGARI?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullah wabarakatuhu

Mafarkin kowace mace wacce ta isa aure da kuma kowanne iyaye masu tunani arayuwa baya wuce miji nagari. Domin shine mafi dacen da ‘ya mace zatayi arayuwa. Kasancewar shi miji bawai abokin zama ne kaɗai ba. Sau da dama yakan zama kamar malami mai tarbiyya ne ga mace.

Akwai abubuwa da dama daya kamata mu duba a tare da mutum don kokarin gano shin zai iya kasancewa miji nagari, kodai miji gama-gari. Waɗannan suffofi zamu iya dubansu ta mahanga da dama. Kamar mahangar addini da al’ada da sauransu. Haka nan kuma zamu kalli yanayi ko suffar mazan da ake saran zasu iya zama maza nagarin, kafin da kuma bayan aurensu.

Miji Nagari Kafin Aure dayake addini shine mafi girman mizani da zamu iya auna komai na rayuwa dashi, Hakika mafi dacewa abu daya kamata a duba ga namiji don tantance ko nagari ne shine, rikon addini da kuma kyan dabi’arsa. Bisa la’akari da faɗin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam): “Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi’arsa yazo muku (neman aure) toku aurar masa"

Yanada kyau matuka mata da iyaye su lura da maganar dabi’ar nan sosai. Domin sau da dama akan sami mutumin da ya suffantu da addini amma bashi da dabi’u masu kyau. Wannan kuma yana daya daga cikin mafiya wahalar da matan yanzu ke karkashinsu.

Mutum mai kyakkyawar dabi’a duk inda yake zaka sameshi karɓebe ne awurin al’umar dayake ciki, Kuma dabi’arsa karbabbiya ce. Ba lallai ne ya kasance mai abokai da yawa ba. Amma zaka taras tun abokansa na yarinta har yanzu suna tare. Ba kuma wai don basa cutar dashi ko ɓata masa rai ba. Kawai saboda kasancewarsa mai yawan yiwa mutane uzuri. Kuma zaka sameshi mai kallon kyakkyawan ayyuka da daraja, mai kauda kai ga kurakurai da ayyukan tir ɗin mutanen daya tsinci kansa aciki. Wannan dabi’a tana taimaka masa kwarai wurin tattalin zamantakewarsa.

Zaka tarar dashi ba mai rama mugunta da mugunta bane. Yanada kyau mu sani cewa rama mugunta da mugunta yana daga cikin manyan abubuwan da suke haddasa mutuwar soyayya tsakanin ma’aurata. Domin yayinda mace tayi zargin cewa mijinta ya daina yimata wani abu daya sabayi mata na kyautatawa, itama ta janye abinda takeyi masa na kyautatawa, to wannan soyayyar a saurari ranar mutuwarta. Amma idan kuwa akayi dace da miji nagari, sai akasin hakan ya faru, domin shi baya rama mummuna da mummuna. Yayinda kikayi wa mutum wani abu mai muni kuma yakau dakai kuma yarama miki da mai kyau, to lokaci guda zaki tsinci kanki cikin wani yanayi najin kunya da nadama. Don haka duk wani yunkuri na maimaita wannan kuskuren saiya rasa gurbi aranki.

A Al’adance kuma tun asali Bahaushe yanada sigogi da yawa na auna hankali da tunani ko mu’amular wanda ko wadda zai aura daga ciki akwai ɗaya daga manyan matakan da akebi wurin auna miji nagari shine, duba yadda yake mu’amulantar mahaifansa. Wato idan aka tarar mutum yanada kyakkyawar mu’amula da mahaifansa, Yakan zauna suyi hira ya taya su wasu ayyuka da sauran abubuwa dake kyautata dangantaka, sai ace, lallai wannan zai kyautatawa matarsa yayin kuruciyarta. Kuma inta tsufa zai tausaya mata. Amma wanda akaga baya kyautata mu’amula ta mahaifiyarsa, ba yayin wani abu na nuna mata tausayawa. Baya sauraro da girmama maganarta to wannan sai ace, ba zai tausayawa matarsa yayin data tsufa ba. Kawai dai zai iya sonta da zumudin tane alokutan datake kan ganiyar kuruciyarta. Domin shi so da sha’awar mace dole ne, kamar yadda son mazan ya zame wa matan dabi’a. Saboda dabi’a ce da Ubangiji ya gina kowa akai, Don haka kowama zai iya son mace amma girmamata da ganin kima da tausaya mata kuma dabi’ace daba kowane keda ita ba. Allaj yadatar damu.

WALLAHU A’ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments