Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sakin Mace Cikin Jinin Biƙi (Jinin Haihuwa)?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Menene hukuncin sakin mace alhali tana cikin biƙi (jinin haihuwa)? Sannan ya ya lissafin iddarta zai kasance?

HUKUNCIN SAKIN MACE CIKIN JININ BIƘI (JININ HAIHUWA)?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Mai haila ce aka hana miji ya sake ta, saboda maganar Allaah Ta’aala:

يَاأَيُّهَا النَّبِيُّ إِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ

Ya kai Annabi! Idan za ku saki mata, sai ku sake su ga fuskantar iddarsu. (Surah At-Talaaƙ: 1).

Shiyasa lokacin da Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ya saki matarsa a cikin haila, sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya sa shi ya mayar da ita, ya ƙyale ta har sai ta yi tsarki, ta sake yin wata hailar, kuma ta sake yin tsarki, sannan inya ga daman sake sakin sai ya sake ta a lokacin, kafin ya kusance ta. Ya ce:

«فَتِلْكَ العِدَّةُ الَّتِي أَمَرَ اللَّهُ أَنْ تُطَلَّقَ لَهَا النِّسَاءُ»

Wannan ce iddar da Allaah ya yi umurnin a saki mata a halin suna fuskantar ta. (Sahih Al-Bukhaariy: 5251, Sahih Muslim: 1471).

Amma mai ciki ko mai naƙuda ko mai jego ko mara lafiya da sauransu, ba a hana sakin ta ba, matuƙar dai sharuɗɗan sakin sun cika. Kamar na kasantuwar ita ɗin matar aurensa ce a haƙiƙa, kuma shi ɗin mijinta ne baligi mai hankali, kuma mai zaɓin rai, da sauransu.

Haihuwar da matar ta yi dalili ne a kan cewa tana cikin shekarun yin haila kenan. Kuma tsawon iddar irin wannan matar shi ne haila uku, kamar yadda Ubangiji Ta’aala ya faɗa:

وَالْمُطَلَّقَاتُ يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ ثَلَاثَةَ قُرُوءٍ

Kuma matan da aka sake su sai su yi haƙuri da kawunansu har tsawon ƙuru uku. (Surah Al-Baƙara: 228).

Duk da kasantuwar malamai sun sha bamban a kan ma’anar ‘ƙur’u’ a nan, amma dai maganar da ta fi ƙarfi in shaal Laah, ita ce ta waɗanda suka ce: Haila ake nufi. Saboda hadisin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa wa wata mace cewa:

«دعِي الصَّلاةَ أَيَّامَ أَقْرَائِكِ»

Ki daina yin sallah a kwanakin ƙuru’inki. (Al-Arna’uut ya sahhaha shi a cikin takhreejinsa ga Sharhus Sunnah: 9/207).

Kuma abu ne sananne cewa, mata suna barin yin sallah ne kawai a ranakun da suke yin haila.

Wannan fassarar ta ƙur’u kuma ita ce aka riwaito daga Abubakar As-Siddeeƙ, da Umar, da Uthman, da Aliyu, da Abud-Dardaa’i, da Ubaadah Bn As-Saamit, da Anas Bn Maalik, da Ibn Mas’ud, da Mu’aaz, da Ubayy Bn Ka’ab. da Abu-Musa Al-Ash’ariy, da Ibn Abbaas (Radiyaal Laahu Anhum). Sannan kuma daga: Sa’eed Bn Al-Musayyib, da Alƙamah, da Al-Aswad, da Ibrahim, da Mujaahid, da Taawus, da Sa’eed Bn Jubair, da Ikrimah, da Muhammd Bn Seereen, da Al-Hasan, da Ƙataadah, da As-Sha’abiy, da Ar-Rabee’, da Muƙaatil Bn Hayyaan, da As-Suddiy, da Mak-huul, da Ad-Dahhaak, da Ataa’u Al-Khurassaniy (Rahimahumul Laah). (Haka Al-Hafiz Ibn Katheer ya ambato a cikin Tafseerul Ƙur’anil Azeem: 1/608).

Don haka, sai wannan matar ta lissafa zuwan jinin hailarta har sau uku bayan ta gama jinin biƙin. Idan ta yi wanka a bayan ta tsarkaka daga jini na uku, to ta gama iddarta kenan. Sai ta yi aure, in tana buƙata.

Shi kuma mijin da ya sake ta lallai ya san cewa akwai sauran nauye-nauyen aure a kansa matuƙar ba ta gama iddarta ba.

* Haƙƙin ciyarwa, da shayarwa, da magani, da mazauni a gare ta da abin ta haifa duk suna wuyansa, ba su sauka ba.

* Idan kuma ɗayansu ya rasu kafin cikar iddarta, to akwai gado a tsakaninsu.

* A cikin iddar kuma yana iya yin kome (wato ya mayar da ita ga matsayinta na matarsa), ko da ita ko waninta bai yarda ba, matuƙar dai sakin ba na ƙarshe ba ne.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

+2348021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments