Ticker

6/recent/ticker-posts

Shekarun Balaga

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ko akwai wasu adadin shekaru da sai in Mutum ya kaisune sannan yake zama baligi?

SHEKARUN BALAGA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Mālamai sunyi Saɓāni dangane dacewa Shin nawane adadin Shēkarun da Yāro ko Yārinya zasuyi kāfin sukai ga balaga, akwai Mālaman da sukace Shēkarun balaga yana fārawāne daga Shēkara-10 zuwa Shēkara-16, danhaka kenan abin yā dangantane daga yanayin wani Mutum ɗin zuwa wani, kokuma irin yanayin waje ko Ƙasar da Mutum yatāshi acikinta, to amma aduk irin yanayin da Mutum yake cikinsa to dawuya yakai Shēkara-18 bā tāreda yā balaga ba.

Amma wasu dayawa daga cikin Mālamai Ma’abota Ilimi sun tafine akan cewa balaga tanada wasu Shēkara nata na musamman, wato sune idan Mutum yacika Shēkara-15 aduniya Mace ko Namiji to kawai yā balaga, waɗannan (Mālamai Ma’abota Ilimi) sunkafa Hujjarsu wajen faɗin hakane dawani Hadisi na Abdullāhi-Ɗan-Umar wanda Yace:

عرضت علي النبي(ﷺ) يوم أحد وأنا إبن أربع عشرة سنة فلم يجزني ولم يرني بلغت، فعدت إليه يوم الخندق وأنا إبن خمس عشرة سنة فأجازني, (يعني ورآني قد بلغت)،

MA’ANA:

An bijiro dani a wajen Mαиzoи Aʟʟαн() arānar yāƙin Uhud alokacin inā ɗan Shēkara-14 a duniya, amma bai bāni izinin naje yāƙinba saboda yanā ganin cewa ban balaga ba, sai kuma nasāke dāwowa zuwa gareshi arānar Khandaƙ alokacin inā ɗan Shēkara-15 a duniya sai yabāni dāmar aje yāƙi dani, saboda yanā ganin cewa alokacin nā balaga.

Danhaka sai Mālamai sukace idan Yāro ko Yāriya yakai Shēkara-15 a duniya to kawai yā balaga, hakanan kuma balaga zata’iya riskar Yāro ko Yāriya koda kuwa basu kai Shēkara-15 a duniya ba indai har gāshin gaba yatsiro musu, ko idan Yāro yayi inzālin Maniyyi ta hanyar sha’awa kokuma mafarkin jima’i, ko Yāriya taga Jinin-Haila yāzo mata koda kuwa alokacin Shēkarunsu basuwuce Shēkara-12 aduniya ba to shikean balaga tāzo.

шαʟʟαнυ-тα’αʟα α’αʟαмυ

AMSAWA:

  Mυѕтαρнα Uѕмαи

  08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments