Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Liki Kudi A Wurin Biki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, wai menene hukuncin yin liƙi na kuɗi a wurin biki?

HUKUNCIN YIN LIƘI KUƊI A WURIN BIKI:

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

[1] Shi arziƙi niima ce ta Allaah da ya wajaba a tsare ta, a kiyaye ta, kuma a gode wa Allaah a kanta, domin ya cigaba da ƙarowa. Ko kaɗan bai halatta a wulaƙanta ta ba, don kar Allaah ya ɗauke ta, ya hana mana ita.

وَإِذۡ تَأَذَّنَ رَبُّكُمۡ لَىِٕن شَكَرۡتُمۡ لَأَزِیدَنَّكُمۡۖ وَلَىِٕن كَفَرۡتُمۡ إِنَّ عَذَابِی لَشَدِیدࣱ

Ubangijinku ya sanar da cewa: Idan har kuka gode to lallai zai ƙara muku, kuma idan kuka butulce to lallai ne azaba ta mai tsanani ce.

(Surah Ibraahim: 7)

[2] A fili yake kuwa cewa wannan liƙin a wurin biki nauin tozarta dukiya ce, wanda kuma Allaah ya hana. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

وَأَنْهَاكُمْ عَنْ قِيلِ وَقَالِ ، وَكَثْرَةِ السُّؤَالِ ، وَإِضَاعَةِ الْمَالِ

Kuma na hane ku daga yaɗa labarun da ba a tantance gaskiyarsu ba, da yawan tambaya, da kuma tozarta dukiya.

(Al-Albaaniy ya inganta shi a cikin As-Saheehah: 685).

[3] Kuma wannan aikin nau’in almubazzaranci ne, wanda shi ma Allaah Ta’aala ya hana:

...وَلَا تُبَذِّرْ تَبْذِيرًا ۝ إِنَّ الْمُبَذِّرِينَ كَانُوا إِخْوَانَ الشَّيَاطِينِ وَكَانَ الشَّيْطَانُ لِرَبِّهِ كَفُورًا

Kuma kar ku yi ɓarna da dukiya matuƙar ɓarna. Haƙiƙa! Masu yin ɓarna da dukiya ‘yan uwan shaiɗan ne, kuma shaiɗan ya kasance mai kafirce wa Ubangijinsa ne.

(Surah Al-Israa’: 26-27)

[4] Sannan kuma wannan koyi ne da fasiƙai wataƙila ma da kafirai, waɗanda su ake gani suna yin hakan a wuraren bukukuwansu a ƙasar nan. Suna zubar da kuɗaɗe, suna tattaka su da ƙafafuwansu! Tuni dai kuwa Allaah ya hana musulmi yin koyi da su, musamman a cikin ɗabi’u da halayensu da suka keɓanta da su a cikin addininsu da rayuwarsu. To, ina kuma ga abin da ya saɓa kai-tsaye da dokokinsa a kanmu?!

[5] A ƙarshe kuma dukiya tana daga cikin abubuwan da za a tambayi kowannenmu a kan ta a ranar Ƙiyama, sai mu shirya. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

لَا تَزُولُ قَدَمُ ابْنِ آدَمَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ عِنْدِ رَبِّهِ حَتَّى يُسْأَلَ عَنْ خَمْسٍ : عَنْ عُمُرِهِ فِيمَ أَفْنَاهُ ، وَعَنْ شَبَابِهِ فِيمَ أَبْلَاهُ ، وَمَالِهِ مِنْ أَيْنَ اكْتَسَبَهُ وَفِيمَ أَنْفَقَهُ ، ومَاذَا عَمِلَ فِيمَا عَلِمَ

Ƙafar bawa ba za ta motsa a Ranar Ƙiyama a gaban Ubangijinsa ba har sai an tambaye shi a kan abubuwa biyar: A kan rayuwarsa: Ta yaya ya ƙarar da ita? A kan samartakansa: Ta yaya ya tsofar da ita? A kan dukiyarsa: Ta ina ya tattara ta? Kuma a kan me ya kashe ta? Sannan kuma wane irin aiki ya yi a cikin abin da ya sani?

(Al-Albaaniy ya sahhaha shi)

Daga waɗannan nassoshin ya fito fili cewa, wannan liƙin da mutane suke yi a wuraren bukukuwa ga masu kiɗa da waƙa da rawa bai dace da koyarwar Sharia ba. Don haka wajibi ne a nisance shi. Musamman dayake akwai wuraren da suka fi kamata a kashe waɗannan kuɗaɗen a kansu da wuraren da kuma suka fi hakan muhimmanci nesa-ba-kusa ba, kamar: Taimaka wa majinyata da gajiyayyu da talakawa da marayu da zawarawa a asibitoci da gidaje da makarantun Islamiyyah da na boko da cibiyoyin yaɗa da’awar sahihin addini da sauransu.

Allaah ya shiryar da mu.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments