Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ba Ya Tsayar Da Sallar Asubah, Wacce Hanya Ya Kamata Na Bi Don Ya Gyara

TAMBAYA (172)

Aslm. Mlm antashi lfy ya aiki ya dawainiya. Mlm inada tambaya

Mijina baya zuwa sallah asuba koda yatashi da asuba din bai makaraba to bazai fita masallaciba wlh sai dai yayi sallah agida yakoma ya kwanta kuma ni ban isa inmasa maganaba saiyagayamin mummunar magana mlm miye mafita

Ayi hakuri da dogon rubutu. Nagode sainaji daga gareka

MIJINA BA YA TSAYAR DA SALLAR ASUBAH, WACCE HANYA YA KAMATA NA BI DON YA GYARA

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Lahaulwa wala ƙuwwata illa billah

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Banbancin kafiri da musulmi shine Sallah"

(Bukhari da Muslim Haka Kuma Sh. Nasiriddin al-Albany ya kawo hadisin a cikin littafin da muke karantawa na Sifatus Salatin Naby wato littafin gyaran Sallah)

Miji shekara da shekaru ana taredashi amman baya Sallah, akwai damuwa babba kam, ammanfa akwai mafita Kuma dai, in Sha Allah kafin na fadi hanyar da za’a bi a shawo kansa Ina roƙon Allaah yasa shawarata ta zama silar da Allaah zai ganardashi taredamu baki daya

Da farko zanso ki fara sallar Nafilah raka’o’i 2, a sujjadar ƙarshe ki roƙi Allaah yasa wannan miji naki ya dinga Ibadah akan lokacinta. Kiyita Istighfari yayin Sujjadar. Bayan kin sallame saikiyi Salatil Ibrahimiyya ki ƙara roƙon Allaah akan Allaah yasa ya dinga Ibadah, saiki ƙara rufewa da Salatil Ibrahimiyya

A tambayar da kikai min ta farko, naji kince kunada da wanda ya dan tasa, to Ina son ki samu dan naki da shi da ragowar ƙannensa, ki tsara musu gasa ta tsawon kamar sati daya. Gasar itace:

Ki ware lokaci ki kira yayannaki gaba dayansu, ki koya musu alwala Mai kyau sannan ke Kuma a matsayinki na mahaifiyarsu kice musu suje su samu Babansu ya kalli yanda suke Sallah (Raka’o’i 2 wato Asubah tunda na fahimci Asubah din ta fi yi masa Wahalar yi) shi da kansa zai zabi Wanda yafi iyawa a cikin yaran naku. Duk wanda ya zo na 1 a cikinsu yana da kyauta ta musamman (Sai ki yiwa wanda yazo na 1 kyautar kudi ko wani abinci ko sha, special dai)

Ammanfa kada su gano kina hakanne don Babansu ya gyara, saboda idan suka gano manufarki to zasu rainashi, A’a kiyi musu hakan da siyasa don su gyara Ibadarsu Kinga anan kin jefi tsuntsu 2 da hoge 1 kenan

Su fara daga gobe bayan sun dawo daga sallar Juma’ah, lokacin da yake zaune a gida

Zai ƙoƙarin kakkauce musu, amman a hakan zaki ce musu su koma wajennasa ya saka musu lokaci. Su share tsawon sati suna hakan. In Sha Allaahu da kanki Zaki kirani kimin albishir din ya fara canzawa

Idan wannan matakin bai aiki ba, kimin magana akwai mataki na 2 da na 3, in Sha Allaahu har akai ga Nasara amman da izinin Allaah Azzawajallah

Wallahu ta’ala a’alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla’ilaha illa anta astaghfiruka wa’atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments