Ticker

6/recent/ticker-posts

Masu Yanke Zumunci

TAMBAYA (175)

Slm malan Dan Allah ataimaka min da wa azi akan matan da suke Raba Miji da Yan uwasa

Matsalarda take damuna kenan mahaifinmu ya rasu Kuma babban yayanmu ce

Matarsa batason mukusanceshi ko zuwa mukayi gidan ranta abace zata amsa sallamanmu tahade rai dole mufita mubargidan

Munyi shawara akan zamusanar da mijinta mahaifiyarmu tahana tace kar mugayamasa komai karmuhadashi da matarsa

MASU YANKE ZUMUNCI

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Duk Wanda ya yanke zumunci, bazai shiga Aljannah ba"

(Sahihul Bukhari: 5984)

Rashin sanin darajar zumunci shine yakesa wasu matan suke aikata irin haka

Babban waazin da zaayi Mata shine a sanar da ita cewar taji tsoron al-Jabbaru, Allaah wanda ya halicci zumunci Kuma yace a sadashi

Akwai hadisil Ƙudsi Wanda a cikin hadisin Zumunci ya kasance yana roƙon Allaah cewar ya Allaah ka Sadar da duk Wanda ya Sadar dani ka yanke Rahamar ka ga duk Wanda ya yanke Ni

Muna roƙon Allaah ya ganarda su mukuma yabamu ikon Sadar da zumunci

Wallahu taala aalam

 Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla’ilaha illa anta astaghfiruka wa’atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments