𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaamu Alaikum. Ko akwai wata addu’a, ko wani
abu da za a iya yi wa yaro mai zuciya?
Addu’a Ga Mai Zuciya
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa
Barakaatuh.
A hausa idan aka ce: ‘Wane mai zuciya ne’ yana ɗaukar ma’ana kyakkyawa da kuma wata ma’ana mummuna. Mai
zuciya na iya zama mai himma da ƙoƙari wurin neman
na-kansa, watau neman kuɗin da zai rufa
wa kansa asiri, ba tare da dogaro ko zama nauyi a kan wani, ko wasu ba. Haka
kuma mai zuciya na iya zama mai saurin fushi, ko mai tsananin fushi, irin wanda
wani lokaci in ya fusata yakan iya yi wa kansa ko waninsa illa.
Wannan fassarar ta biyu ce ake nufi a nan, tun da
dai, kamar yadda ya zo a cikin tambayar, maganin abin ake nema.
A cikin hadisi Annabi Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya bayyana mana cewa: Shi fushi daga shaiɗan ne, don haka maganinsa sai a ɗauki matakan da za su kore shaiɗanin daga mai fushin kawai, kamar ta yin isti’azah.
Al-Bukhaariy: 6048 da Muslim: 2610 sun riwaito
hadisi da isnadinsu ingantacce daga Sahabi Sulaiman Bn Surad (Radiyal Laahu
Anhu) ya ce: Watarana ina zaune a wurin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ga kuma wasu mutane biyu suna faɗa, suna zagin junansu. Ɗayansu idanunsa sun yi ja-zur! Kuma jijiyoyin
wuyarsa sun kumbura! Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya ce: Na san wata kalmar da in da zai faɗe ta da kuwa
abin da yake ji ya rabu da shi:
In da zai
ce: A’uuzu bil Laah minas-Shaitaanir Rajeem (Ina roƙon Allaah ya tsare ni daga shaiɗan jefaffe), da kuwa abin da yake ji ya rabu da shi.
Sannan kuma, har yara kanana ma ana yi musu addu’o’in
neman Allaah ya tsare su daga shaiɗan, kamar yadda
Al-Bukhaariy: 3371 ya riwaito daga Abdullaah Bn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa)
cewa: Manzon Allaah ( Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana roƙa wa Alhasan da Alhusain
(Radiyal Laahu Anhumaa) kariyar Allaah yana cewa:
أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ
اللهِ التَّامَّةِ ، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ ، وَمِنْ كُلِّ عِيْنٍ لَامَّةٍ
Ina tsare
ku da Kalmomin Allaah Cikakku, daga duk wani shaiɗani da dabba mai dafi, kuma da duk wani kambin-ido mai
cutarwa.
Allaah ya shiryar da mu, ya shiryar da ‘ya’yanmu,
ya sa su zama sanyin ido, kuma masu amfani gare mu a duniya da lahira.
Wal Laahu A’lam.
sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.