Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Limamin Da Ya Ja Mutane Sallah Alhali Bashi Da Tsarki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam mune mukayi sallah muna karewa liman yace yamanta baida tsarki yayi fitsari baiyi tsarki ba. zamu maida wata sallah ne kota liman ce kawai babu tunda mu da tsarkinmu ko har tashi tayi daidai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa’alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

To ɗan’uwa sallar liman ta ɓaci, kuma dole ya sake, amma ku sallarku ta inganta, a zance mafi inganci, saboda dalilai kamar haka:

1. An rawaito daga Umar- Allah ya yarda da shi cewa: ya taɓa yiwa mutane limancin sallar asuba, bayan an gama sallah, sai ya ga maniyyin mafarki a jikin tufansa, sai ya sake sallah, amma mamun ba su sake ba.

2. Sayyidina Aliyu yana cewa: "Idan mai janaba ya yiwa mutane limanci, zan umarce shi ya yi wanka, ya sake sallah, amma ba zan ce da mamun su sake ba.

3. Abdullahi dan Umar - Allah ya yarda da shi- ya taɓa yiwa mutane sallar asuba, sai ya tuna ba shi da alwala, sai ya sake amma mamu basu sake ba.

Abinda ya gabata aikin sahabbai ne, aikin sahabi hujja ne, in ba’a samu wani sahabin ya saɓa masa ba.

Don neman Karin bayani duba: Almugni 1\419.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments